Skip to content

To, fitar Anty Sakina ke nan ta isa titi ta tari Adaidaita Sahu, ta yo wa gidansu tsinke, zuciyarta a tunzure kamar ta fashe. Tun a cikin Adaidaitar take jin wani sabon kukan na neman balle mata, amma ta daure. Suna tafe kafin a iso da ita gida ta fara binciken wayar Humairar, domin abin da ya daure mata kai shi ne, yadda alaka ta kullu tsakanin Usman da Humaira har ya samu lambar wayarta. Kuma har suka yi sabon da mu’amala irin wannan take wanzuwa a tsakaninsu?

Lambobin wayar ta rika bi tana bincika daya bayan daya, har ta ga lambar Usman din an yi saving da suna Yaya Usman. Bayan nan sai ta shiga binciken wayar lungu da sako, ciki da waje. A cikin sakonnin karta-kwana wato (SMS) ta ga abubuwan da kanta ya sake kullewa hade da sara mata, irin zantukan batsar da Usman yake tura wa Humaira.

Tunani ta shiga nan da nan, shin yaushe Humaira ta zama haka? Anya ma  Usman din kawai take kulawa, ba a makaranta ba ne kuwa ta hadu da mutanen banza suka sauya mata rayuwa? Sai dai bayan ta gama bincikar sakonnin sai ta takaita zarginta akan Usman, domin ba ta samu wani koda sau daya ba ya taba turo mata irin makamancin sakon da shi Usman din yake turo mata. Ko Najib da zai aure ta ba ya mata sakon karta-kwana, sai dai ya kira ta kawai. Kuma akalla ya yi kusan sati uku bai kira ta ba saboda ba cika sauraren sa take ba. Tun uzurin karya da ta gindaya masa na cewa ba za ta iya hada karatu da soyayya ba, ya sa shi numfasawa da kiran nata ko ma zuwa zance.

“To kodai yarinyar nan tana kallon fina-finan batsa ne? Har hakan ya kai ta jefa rayuwarta cikin wannan hali?”

Tunanin da Anty Sakina ta yi ke nan wanda kuma ya haska mata cewa ta sake kutsawa cikin wayar dai da bincike, domin waya waje ne da akan samu bayanan sirri game da mai ita. Hakan kuwa ta yi, cikin memoryn ta shiga da nufin ko za ta gani irin wadancan bidiyoyi da take zargin Humairar na kalla. Tana budewa, folder farko Audio ne, ta shiga ta duba, duk wakokin Hausa ne na ‘yan nanaye. Folda ta biyu kuma an rubuta *Call Recorder*, wato wayar tana da tsarin nan na idan mutum ya yi waya, za ta nadar masa muryoyin zantukan da suka tattauna ta ajiye a cikin memorin. Budewa ta yi, ga jerin muryoyi nan da yawa, recording na farko da ta cikaro da shi shi ne, na maganar da Humairar ta yi da Usman dazu da safe lokacin da ta fito daga gida take sanar masa cewa tana kan hanya. Jin wannan murya ya sa Anty Sakina ta girgiza kai hade da jinjina lamarin. Haka nan ta rika bude muryoyin daya bayan daya tana sauraren abubuwa marasa dadin ji, har aka kawo ta kofar gida ba ta iya gama sauraren su gabadaya ba. Wani recording din ka ji suna tattauna wajen da za su hadu, a hotel kaza, da dai sauran wuraren da yake daukar ta ko kuma ya kira ta zo su sheke ayarsu.

“Wannan ma sun isa hujja.”

Ta fada a ranta daidai lokacin da Mai Adaidaita Sahun ya tsaya cak a kofar gidansu, ta zaro kudi ta biya shi kudinsa ta sauka ta shige gidan. Mummy na kitchen tana dafa abincin rana, ita kadai ce a gidan su Haidar na makaranta. Anty Sakina ta yi sallama hade da zubewa a tsakar gida ,hawaye suka fara zarya a kan kuncinta.

Daga cikin kitchen din Mummy ta amsa sallama, “Wa alaikumus salamu, muryar wa nake ji kamar Sakina?” Ta fada tare da fitowa, “SubhanAllah! Ya ya dai Sakina, lafiya?”

To, lokacin da Humaira ta isa gidansu Binta, iske ta ta yi a tsakar gida tana wankin kayanta da na Baba Abu, a hannu guda kuma ta dora girkin abincin rana. Babu sallama Humaira ta danna kai, gabadaya a kideme take tamkar wacce dimuwa ta kama, kallo daya za ka yi mata ka fahimci cewa lallai ba a cikin hayyacinta da nutsuwarta take ba, “Ikon Allah! Ko sallama babu kawai sai dai a gan ki tsudum.”

Binta ta fada bayan ta ji sautin taku ta dago kanta, Humaira ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya tare da waiga bayanta sannan ta ja kujera ta zauna tana sauke numfashi wani na korar wani. Mamaki ne ya dabaibaye Binta ganin Humaira cikin yanayin firgici mai tsanani, tsame hannunta ta yi daga cikin kayan wankin ta yo wajenta tana cewa, “Ya ya dai mene ne ke faruwa na gan ki duk a razane har kina waige-waigen baya? Wani ne ya biyo ki?”

Numfashi kawai Humaira take saukewa, zuwa can ta nisa tare da bude baki ta ce, “Ina Baba take?”

“Ina tambayar ki lafiya kike, kin ki ba ni amsa kuma kina tambaya ta! To Baba tana daki tana barci.”

“Na shiga uku na lalace.”

Humaira ta fada hade da sakin wasu hawaye masu dumi, ta dora hannayenta bisa cinyar Binta ta ci gaba fadin, “Ya ya zan yi? Wayyo Allahna ina zan sa kaina!”

Cikin rarraunar murya Binta ta ce, “Idan ba kukan kike so ni ma ki sa ni ba, ya kamata ki fada mini abin da yake damunki. Ko mutuwa a ka yi muku? Kin ga tashi mu shiga cikin daki.”

Ta kama hannun Humaira suka mike suka shiga dakin, suna shiga Binta ta sake dora mata tambayar, “Me ya faru? Ki daina kuka ki fada mini, idan kuma kin ki zan kyale ki na koma kan wankina na ci gaba.”

Humaira ta buga kanta a bango, kumm! Ta saki wani sautin kuka me tayar da hankali, “Wai kina hauka ne Humaira? Ciwo za ki ji wa kanki? To indai haka za ki yi kin ga tashi ki bar gidan nan gaskiya! Ya ya za ki zo kina neman illata kanki, an tambaye ki kin yi sai kuka.”

“Binta na shiga uku! Wallahi da zan mutu yanzu sai na fi farinciki akan na ci gaba da rayuwa a wannan duniyar. Yanzu ba na ganin hasken komai a fadin duniya, komai ya zama mai duhu a idona.”

“Ban gane me kike nufi ba, kina ba ni maganar ne a baibai. Ya kamata ki tsaya ki nutsu ki fadi abin da yake damunki, ina jin dai watakila kin zo wajena ne domin ki fada mini damuwarki, sannan na ba ki shawara ko a samu mafita ko? To idan haka ne ba kuka za ki yi ba, sai ki yi mini bayani dalla-dalla yadda zan fahimci matsalar sannan na iya ba ki shawarar da ta dace.”

Sautin kukan ta daina fitarwa kawai amma hawayen sai ci gaba da ambaliya suke, ta kuta tare da cewa, “Binta na cuci kaina! Na biye wa son zuciya da kururuwar shaidan, na hallaka rayuwata da kaina! Na yi abin da iyayena ba za su taba yafe mini, babu tabbas din Abbana zai ci gaba da bari na ina zama a gidansa.” Ta yi sakamakon kukan da ya ci karfinta.

“Hmm! Har yanzu ban gane abin da kike nufi ba, shin wane laifi ne kika yi da har iyayen naki ba za su yafe miki ba?”

Humaira ta kifa kanta a kan cinyar Binta ta cewa, “Na ketare iyaka! Na saba wa Ubangijina! Na aikata laifi mafi muni a rayuwar ‘ya mace budurwa.”

Binta ta zaro idanu tare da, “SubhanAllah! Inna liLlahi Wa Inna Ilaihir raji’un! Kawata garin ya ya haka ta faru? Kuma ke da waye kika aikata wannan danyen aiki haka?” Ta fada tana me jinjina al’amarin a ranta, sam ba ta yin tsammanin abin da Humairar ta yi ba ke nan! A tunaninta sata ta yi shi ne take ta zuke-zuke ta gaza fada. “Lallai maganar Hausawa sun yi gaskiya da suka ce kai dai ka ga mutum! Kuma ba a yabon dan kuturu sai ya tsufa da yatsunsa.” Binta a zuciyarta ta yi wannan zance ,yayin da Humaira ta balle da kuka sosai ta ci gaba da cewa, “Ya cuce ni, wallahi yaya Usman ka cuce ni! Allah Ya isa tsakanina da kai.”

Cikin sigar mamaki Binta ta ce, Ban gane ba? Na ji kin ambaci wani suna yaya Usman, waye shi din? Shi ne wanda ya yi abin.”

“Shi ne mana! Shi ne wannan mutumin da ya taba zuwa ya dauke ni a makaranta. Mijin Antyna ne.”

Wata irin faduwar gaba ce mafi tsanani ta riski Binta, kunnuwanta suka yi mata dumm na wani dan lokaci sannan kirjinta ya ci gaba da bugawa da sauri. Kanta ta ji yana juya mata alamun jiri, a zaune take amma sai ta ji kamar za ta fadi, ta yi talau wani duhu-duhu ke kokarin rufe mata ido, salati ta fara yi, “INNA LILLAHI WA INNA ILAIHIR RAJI’UN! ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI, ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI!”

Kafin ta gama addu’ar tuni gumi ya karyo mata, bayan addu’ar ba ta sake cewa komai ba, bakinta ya rufe ruf! Ta rasa kalmar furtawa, shiru ta yi, sai sautin kukan Humaira ke tashi kasa-kasa. Kimanin mintuna uku zuwa biyar suna a wannan yanayi, zuwa can Binta ta share gumin da ya jike mata fuska zuwa dokin wuyanta ,ta sauke wata ajiyar zuciya sannan ta ce, “Amma garin ya ya haka ta faru? Gaskiya akwai sakacinki, mijin yayarki fa? Har ki amince da shi akan wannan bakar bukata tasa? Gaskiya Humaira da yardarki.”

“Wallahi shi ne ya rika damu na, yana takura mini tun ba na so har ya batar mini da tunanina. Lokaci zuwa lokaci sai ya kira ni a waya na je hostel na same shi ko kuma gida, to shi ne yau ma da safe ya kira ni ya ce na je gida na same shi. Ashe wata makwabciyar Antyna din ta gan ni ina shiga gidan har sau biyu lokacin Antyn tawa ba ta nan,  shi ne ta kira ta ta zo ta gan ni tare da shi.”

“SubhanAllah! Kai kai kai! Gaskiya kin tafka babban kuskure. Gara ma a ce wani daban ne ba shi ba, ko kuma a ce ba a gidan kuke yi ba. Gaskiya wannan lamarin yana da tsanani, dole ne su Mummy da Abba ransu ya baci. Wannan tabo ne da ba kanki kawai kika yi wa ba, ya shafi dukkan wani mutum a danginku.”

“Na shiga uku! Binta ba zan iya komawa gida ba, hawan jinin Mummy zai iya tashi, kuma idan ya tashi tamkar ba za ta rayu ba. Ganina, na iya sawa zuciyarta ta buga ta mutu ma gabadaya.”

“Ki daina cewa kin shiga ukun nan, tuba da addu’a ya kama ce ki a halin yanzu. Sannan ki sani rashin komawarki gida shi zai fi muni a rayuwarki, kuma shi ne zai kashe Mummy din. Gara ki koma ko mene ne zai faru da ke ya faru kina gidan, ko me za a yi miki gara a yi miki shi a gidanku. Ki koma ki nemi gafarar iyayenki, ki nemi gafarar Antynki su yafe miki.”

“Allah ba zan iya zuwa ba.”

“Ki daina rantsuwa fa, haka nan za ki koma tilas kuma ke kadai. Domin yanzu watakila ita Antyn ta je gidan, ba lallai ba ne maganar ta fita. To amma rashin komawarki ke kadai shi zai fitar da maganar a gari, kin ga kin fallasa kanki.”

“Yaya Usman ba zan taba yafe maka ba, Allah Ya saka mini! Yanzu shi kenan ka raba ni da Najib, na san ba zai taba yarda da ni ba.”

Binta ta ce, “Waye kuma Najib?”

“Shi ne dan aminin Abbana wanda suke kasuwa daya tare, shi ne wanda alkawarin aurena yake kansa idan na gama karatun nan zai aure ni. To na san yanzu cewa zai yi ba zai auri karuwa ba, da ma ba sauraren sa nake ba sosai. Wayyo Allahna! Wayyo kaina! “

Shiru suka yi Binta na nazarin yadda za su bullo wa lamarin  zuwa can ta sauke wani numfashi hadi da fesar da iska me tsananin dumi sannan ta ce, “Gabadaya ma kaina ya kulle na rasa yadda ma za a yi. Lamirin ne ba abin bayyanawa ba ne, dole sai an yi taka-tsantsan saboda jama’a. Yanzu kamar jira ake wani iftila’in ya fada wa mutum sai a dauki maganar a yi ta yadawa, mutane ba su da gadonka amma suna da gadon maganarka. Abin da za a yi yanzu ki zauna tukunna zuwa anjima sai mu je na raka ki gidan, amma ba zan shiga ba, zan raka ki ne domin na tabbatar kin shiga gidan, idan kin shiga duk abin da za a yi miki kada ki daga kai, ki nuna matukar nadamarki ta hanyar yin kuka fiye da wanda kika yi a nan. Koda Abba ko Mummy wani daga cikinsu ya ce ki fita ki bar gidan kada ki kuskura ki yi koda motsi, ki zubar da hawaye matukar zubarwa, In Sha Allah za zukatansu za su dan lafa musu da radadin. Daga baya sai ki fara ba su hakuri kina mai bayyana nadama ,ki nemi yafiyar Antynki sosai.”

“To shi kenan na gode, na ji kuma zan yi duk yadda kika ce.”

“Yawwa! Bari na duba girki.”

Binta ta fada tare da mikewa ta nufi kitchen ta zubo musu abinci, daidai lokacin Baba Abu ta tashi daga barci, Binta ta ce, “Kin ga Baba ta tashi daga barci ma, ki yi sauri ki goge fuskarki, idan ta gan ki cikin wannan yanayin za ta matsa da tambaya kuma daga karshe ta hana ni fitar.”

To abincin ma dai Humaira ba ta iya ci ba, sam ta manta wani abu wai shi abinci bare kuma yunwa. Tashin hankalin da ke gabanta ya wuce na ta ji yunwa, fatanta dai yanzu bai wuce na iyayen nata su yi hakuri su yafe mata ba. Binta ta yi fama da ita akan ta ci abinci ln koda kadan ne amma ta ki, ita kadai ta ci abinta, sai dai ita din ma ba ta ci yadda ya kamata ba, ita ma abin ya taba sosai.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×