Skip to content
Part 9 of 30 in the Series Ƙuda Ba Ka Haram by Sadik Abubakar

To wadannan mutane guda biyu wato Anty Zara’u da Malam Sadik, abokan aikin Anty Sakina su kadai ne take dan fadawa matsalarta su taushi kirjinta ta samu sauki a ranta. Sun zama aminanta, ta su ta zo daya, su ukun nan tamkar ‘yan uwan jini suke. Haka suke mu’amalarsu duk abin da ya samu daya to tamkar su ukun ya samu, sawa’un abin farin ciki ne ko kuma akasin hakan ne. Sukan hadu su yi duk me yiyuwa idan wata damuwa ta samu daya su samar da mafita ko kuma aƙalla su rage wa wanda abin ya samu damuwa. Sukan tallafa wa junansu da kuɗi idan sabga ta samu, walau sha’anin bikin suna ko na aure. Wannan ke nan.

*****

Shi kuwa Usman na gama cin abincinsa shimfiɗewa ya yi, ya shari barcinsa mai isar shi sai misalin ƙarfe 12:00pm na rana ya tashi a gaggauce domin ya kusa makara, ya shirya ya fice wajen aiki. Ficewarsa ke da wuya Anty Sakina ta dawo daga wajen aiki, babu laifi ta ɗan samu sauƙin ɓacin ran da ta fita da shi sakamakon dannar ƙirjin da aminan nata suka mata, ba kamar lokacin da fita ba.

Sai dai kuma zaman doya da manja ne mai matuƙar tsanani ya sake dawowa tsakaninta da Usman, kusan babu mai tanka wa wani, kowa sha’aninsa gabansa yake. Duk lokacin da ya ga dama ya fita haka nan duk lokacin da ya yi niyya ya dawo. Kazalika halin nan nasa na yin waya da matan nasa na nan. Duk dai wani nau’in halin rashin kirki da iskanci babu wanda Usman ya fasa ko kuma ya rage.

BAYAN MAKO GUDA

To kawo yanzu dai an kafe wa su Humaira admission kuma sunanta ya fito cikin jerin ɗaliban da suka yi nasarar samun gurbin karatu a makarantar Kimiyya da Fasaha ta Kano, za ta karanta fannin Harkokin Kasuwanci (Business Administration) a Turance. Bayan ta duba sunanta, Usman ne mutumin farko da ta fara kira ta faɗa masa, ya ce, “Kai Masha Allah, amma na ji daɗi fa sosai. Congratulations, kin ga yanzu mun samu dama sosai, babu wani abu da zai zama cikas a tsakaninmu. A kowane lokaci za mu iya haɗuwa, ko ya ya kika ce?”

Murmushi mai sauti ta yi sannan ta ce, “E haka ne.”

“To yanzu ya ya za a yi, yaushe za a fara registration ɗin?”

“Sun babmu sati biyu daga yau ɗin nan.”

“Okay to yanzu yaushe za mu sake haɗuwa ke nan?”

“Duk lokacin da kake so amma fa gaskiya ina jin tsoron sake zuwa gidan nan, kada watarana Anty ta dawo ta riske mu fa, ka ga abin da take zargi sai ya tabbata, ka ga matsala ce za’l a samu babba.”

“Haba don Allah daina wannan tunanin kin ji, babu wani dawowar da za ta yi, indai ta tafi aiki ba ta dawowa sai lokacin tashi ya yi. Kuma kin san indai ni na tsara abu ba a samun wata tangarɗa, kawai ma kin ga gobe Talata ki zo gidan, ki zo kamar lokacin da kika zo waccan ranar.”

“Hmm! To shike nan babu damuwa zan zo ɗin.”

“Okay idan kin taho ki yi mini waya kin ji.”

“To shike nan na gode.”

Bayan ta gama waya da Usman Abbanta ta kira take masa albishir ɗin samun admission, bayan ya ɗaga wayar ta ce, “Abba albishirinka? Sunana ya fito a jerin sunayen mutanen da suka samu admission, yanzu ma ina cikin makarantar.”

“Alhamdulillah, Masha Allah wane course kika samu?”

“Abba wallahi abin da na cike shi na samu, Business Administration.”

“Ya yi kyau, Allah ya ba da nasara, sai na dawo ke nan?”

“E Abba dabma ina son na faɗa maka zan sayi wasu kayayyaki kuma takalmana duka sun tsufa.”

“Na ji duk ki bari sai na dawo gida sai a san yadda za a yi ko?”

“To Abba sai ka dawo, ka taho mana da yoghurt ɗin nan da kilishi.”

“Hmm! Humaira kebnan, ke ba ki san yanzu yanayin kasuwar ba yadda yake a da ba ne, hakuri ake yi, zama ya fi yawa babu ciniki sannan yanzu ga hidimar kashe kuɗi ta taso.”

“Abba don Allah ko yoghurt ɗin ne kawai ka taho mana da shi.”

“To shike nan za a taho da shi, sai na dawo ɗin.”

A cikin makarantar take wannan wayar, jama’a ne maza da mata matasa birjik! Kowa na ta ƙoƙarin duba sunansa. Wata ‘yar madaidaiciyar matashiya ce wacce  shekarunta ba za su wuce na Humairan ba, sai dai ita ba mai jiki ba ce kamar Humaira. Zuba wa Humaira ido ta yi yayin da take wayar, bayan ta gama ta matso kusa da ita ta ce, “Baiwar Allah sannu.”

Humaira ta amsa mata da cewa, “Yawwa sannu dai ya kike?”

“Lafiya lau ashe kin ga sunanki, na ji kina faɗa wa Abbanki.”

“E wallahi kuwa, ke fa kin ga naki sunan?”

“Hmm! E na gani amma ni ganin ma ba shi da wani amfani a wajena.”

“Kamar ya ya? Ban gane ba, shin ba ke kika nema ba ne, kuma ga shi har kin zo ki duba ko kin dace, amma ki fadi haka?”

“Hmm! Ni ce na na nema ban san haka tsarin yake ba, gaskiya abu ne mai matuƙar wahala na iya samun damar yin karatun nan.”

“Baiwar Allah a baibai ki ba ni maganar ki yi mini bayani sosai yadda zan gane. Na lura da ke tun ɗazu kin yi tagumi kin yi jugun alhali duk wanda ya ga sunansa murna da farinciki yake, ke kuma akasin hakan ne. Shin ko zan iya sanin dalili?”

“Hmm! Yar’uwa labarina mai tsayi ne, idan mun sake haɗuwa zan faɗa miki koda ba duka. Yanzu dai a taƙaice ban san ana biyan kuɗin registration da yawa ba haka, sai yanzu da na zo na ji wasu suna faɗin kudin sun kai dubu goma sha-biyar. Ni kuwa ban san a wace duniya zan samo waɗannan maƙudan kuɗaɗe haka ba. Iyayena ba masu ƙarfi ba ne kuma sun mutu, a wajen kakata nake. Mu biyu ne a ɗakinmu ni ce babba kanena namiji.”

Cike da tausayawa Humaira ta ce, “Allah sarki sannu kin ji, na tausaya miki sosai wallahi, Allah ya jiƙan su Allah ya yi musu rahama, Allah ya sa sun huta.”

“Amin ya Allah, na gode.”

“A wace unguwa kuke ne?”

“A Jakara muke.”

“Allah sarki, sannu. Sunana Humaira Adam Maigoro, ni kuma a Zaitawa muke.”

“Ni kuma sunana Binta Bashir.”

“Ya yi kyau. To na ce kin je kin karɓi screening form da teller ta biyan kuɗin?”

“Hmm! ‘Yar’uwa ke nan, wallahi ban karɓa ba, ai tunanin karɓar nake domin na ga lokacin da aka bayar kowa ya kammala registration ɗin ma ba shi da yawa balle na yi ‘yan bige-bigen da zan samu ko kuma na kai takardar gidan radiyo, filin *‘Na-Annabi’*. Gaskiya na fitar da rai da karatun nan, na haƙura.”

Humaira ta faɗa kafaɗarta cikin yanayin tausayawa sannan ta ce, “Ki daina faɗar haka kin ji, insha Allah za ki yi wannan karatu tunda dai har Allah ya sa sunanki ya fito ba za a bari gurbin ya tafi a banza ba. Ni ma ɗin ba wani hali ba ne da iyayena sosai, amma Alhamdulillah. Kada ki damu ki kwantar da hankalinki, yanzu zo mu je mu karɓi teller da screening form ɗin.”

Ofis ɗin da ake karɓar takardun suka nufa, layi ne ake bi, idan aka zo kan mutum sai ya faɗi sunansa da admission number, sannan kuma ya ba da naira dubu ɗaya da ɗari biyar (₦1,500) a ba shi takardun. Layin su ma su Humairan suka hau, Binta ce a gaba Humaira na bayanta. Layin na ja sosai. Koda Binta ta hango ana ba da kuɗi kafin a ba mutum form ɗin, sai ta zame ta fita daga layin.

Hunairan ta ce, “Ya ya lafiya dai, ina za ki kuma ga layi ya kusa zuwa kanmu?”

“Gidan zan koma na faɗa miki ba…”

Humaira ta yi saurin katse ta da cewa, “Ya isa haka koma kan layinki sai mun gama komai za ki tafi, kada ki damu kin ji.”

Layin na zuwa kansu suka shiga tare Humaira ta biya musu kuɗin su biyu naira dubu uku  cif! Aka ba su takardun. Bayan sun fito daga ofis ɗin Humaira ta dubi Binta ta ce “Ba ni lambar wayarki gobe ko jibi zan kira ki mu haɗu mu je banki mu biya kuɗin.”

“Ni fa ba ni da kuɗin da zan yi registration kuma babu inda zan same su. Da kin sani da ba ki kashe kuɗinki ba kin karɓar mini form ɗin nan.”

“Kin ga ki bar wannan maganar na ji duk abin da kika faɗa kuma na fahimce ki, kawai ki ba ni lambarki zan kira ki mu je mu biya tare.”

“Wallahi ba ni da waya, amma ke ɗin ya ya za ki yi? Na ji fa Abbanki kika faɗawa zai biya miki.”

“Ki bar wannan maganar na ce, ke dai mene burinki, ba ki yi karatu ba. Yanzu idan kin gama abin da kike za mu iya tafiya tare na ga gidanku tunda babu waya a hannunki idan ya so goben sai na biyo miki mu je bankin, ko ya ya kika gani?”

“To shike nan na gode sosai Allah ya saka da alkairi, za mu iya tafiya ɗin na gode ƙwarai wallahi.”

“Hmm! Babu komai wallahi kada ki damu ai duk yi wa kai ne, mu tafi.”

Fitowa suka yi daga makarantar suka tari Adaidaita Sahu ya kai su unguwar Jakara, unguwar su Binta ke nan. Wani ɗan ƙanƙanen gida ne mai ɗakuna uku, kakar Binta ce zaune a tsakar gidan tana kaɗa auduga, sana’ar yin lagwani take.

Sallama suka yi ta amsa musu, Humaira ta gai da ita cikin ladabi da girmamawa. Binta ta ce, “Baba Mero wannan ƙawata ce a Zaitawa suke ita ma ta samu nasara sunanta na cikin ɗaliban da aka ɗiba.”

Baba Mero ta ce, “Kai madalla Allah ya taimaka, Allah ya sa ku fara karatun a sa’a, Allah kuma ya yi muku albarka.”

“Amin ya Allah.” Humaira ta fada tare da mikewa sannan ta kara da cewa, “To ni zan wuce, sai goben ki shirya da wuri kin ga dai layi ake yi.”

“To shike nan babu komai na gode sosai insha Allah zan kintsa da wuri. Mu je na raka ki, ki yi hakuri ga shi ko ruwa ma ban kawo miki ba.”

“Kada ki damu haba, idan ina bukata ai zan ce ki kawo mini.”

Rako ta Bintar ta yi har wajen da za ta samu mai Adaidaita Sahun da zai ƙarasa da ita gida. Da murnarta ta shiga gidan tana cewa, “Mummy, mummy wallahi na samu admission kuma course ɗin da na nema na samu.”

Ita ma mummyn murnar ta fara yi tare da cewa, “Ke don Allah, kai Masha Allah! Alhamdulillah, Allah mun gode maka, Allah ya sanya albarka, ya kuma ba da sa’a. Sai a mayar da hankali ban da wasa, kin ga dai babbar makaranta ba kamar secondary ba ce, idan mutum ya yi wasa to korar sa ake yi kwatakwata. Sannan ki sani babu ruwanki da ƙawayen banza.”

“To mummy, na ma faɗa wa Abba ya ce sai ya dawo. Mummy don Allah ki saka baki ya ba ni kuɗi sosai zan sayi wasu abubuwan kafin mu fara karatu.”

“Hmm! Humaira ke nan, ke dai ba kya rabuwa da hidimoni, me kuma za ki saya? Kin san fa yadda Abban naku yake cewa babu ciniki sosai, amma babu komai ni dai fatana kada ki yi wasa, ki tsaya ki maida hankali kin ji ko?”

“To mummy insha Allah ba zan yi wasa ba, na gode. Yunwa nake ji mummy.” Cikin sigar shagwaba Humaira ta kare maganar, yayin da mummyn ta ce mata, “To ai an gama abinci ga shi can a kicin sai a zuba a yi ta ci.”

<< Kuda Ba Ka Haram 8Kuda Ba Ka Haram 10 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×