Murmushin takaici Suraj ya yi, “Zinatu kenan, wani abu da ki ka kasa ganewa a rayuwarki shine, duk makircinki baki isa ki yi min abinda abinda Allah bai min ba, ke mayaudariya ce, maci amana, wacce imani ya gaza samun gurbi a zuciyarta, ki sani dole na kare ɗan uwana daga sharrinki.
Tun farko ma rashin sani ne ya sa kaza ta kwana kan dami, na baki fuskar da ki ka samu damar tunkara ta da mummunar aniyarki ban fallasa ki ba, amma yanzu na san kaina, na gane hanyar da ya kamata in bi ta ɓulle da ni, na gane gaskiya, kuma lokaci ya yi da mijinki zai san ko wa ce ce ke a rayuwarsa, zan fasa baragurɓin ƙwan nan Zinatu, zan kwance duk wani ƙulli da ki ka tona rami ki ka binne.”
Zinatu ta ƙyalƙyale da dariya har da guntun hawaye, sai da ta yi mai isar ta kana ta dakata tana masa kallon sauna.
“Ka yi babban kuskure Suraj, me ya sa idanunka suka rufe ka manta baya? Ka manta lokacin da muka shuka abubuwa iri iri a kan ɗan uwanka kuma tare da kai, ka manta kai ka nuna mana hanyoyi daban-daban da zamu bi mu cuce shi, mu saci dukiyarsa mu damfare shi.
Ba ka da tunani ko kaɗan, kware mana baya da ka ke kokarin yi dai-dai ya ke da ka ɗauki kakkaifar wuka ka yi kururuwa sannan ka daɓawa cikinka, na ma fi tunanin kai ne za ka kwana ciki, ko kaɗan ba na nufin hana ka aiwatar da abinda ka yi niyya, babu laifi mu zuba mu gani.”
Ta rufe kalaminta da dariyar da ta fi komai ƙular da shi, sannan ta duƙa ta kwashe kuɗaɗenta ta yi gaba.
Suraj ya yi shiru, shirun da ke cike da ɗumbin nadamar kuskuren da ya aikata, me yasa idonsa ya rufe ne? Babu abu mafi dagula masa lissafi kamar idan ya tuna mawuyacin halin da suka jefa Mashkur bai ji ba bai gani ba.
Da na sani yake marar amfani, ba wani ba ne, shine da kansa ya biye musu suka aikata wannan ɗanyen aiki a matsayinsa na wanda ya fi kowa kusanci da Alhaji da Mashkur ɗin. Duk ranar da gaskiyar nan ta fito sai ya fi su shiga matsala kasancewar duk inda za a je a dawo Alhaji da Mashkur nasa ne, ina zai kai wannan abin kunyar? da wane ido zai dube su da sauran mutane musamman ragowar ‘yan uwansu waɗanda kamar dama jira suke su ji wani abu ya ɓullo.
Tun sa’ar da ya ƙauro ya dawo gidan suke ta tsegume-tsegume, kowa da abinda yake faɗa, har da masu cewa kwaɗayi ne irin na su shi da mahaifiyarsa, ya sa shi raɓar su, abin da su suke jin sam ba za su iya ba, don tuntuni suka tattara suka watsar da lamarin Alhaji Ahmad, a sakamakon girman kai da hassadar da suka ɗorawa kan su, sai shine yake bibbiyar su duk inda suke, alheri kuwa bai fasa yi musu ba sai dai rashin godiyar Allah da kiyayyar da suke masa ba zai bari su ga farinsa ba.
Babban abinda ke sa shi al ajabi har da ‘yan uwan da suka fito ciki ɗaya. Da fari sun ɗauki karan tsana sun dora kan marigayiyar matarsa da suke ganin ita ce ta mallake shi ta raba shi da su, bayan ranta kuma suka mayar da tsanar kan ɗan da ta haifa Mashkur wanda a dole ba don yana so ba Mashkur ya janye jiki daga shiga hulɗar dangin mahaifinsa idan ba abinda ya zama dole ba.
*****
Wannan karon su biyu ne zaune a gaban boka Ƙuzurgu, bayan sun gabatar masa da abinda ke tafe da su. Ya dube su a tsanake, “Wannan ba zai ji kira ba ya riga ya yi nisa, ƙoƙari ya ke ya farke muku laya, don a yanzu haka yana nan yana neman hanyar da zai bi ya rusa duk shirin da ku ka yi ba tare da an zargi cewa tare ku ke da shi ba, kuma matuƙar ya samu wannan hanya komai zai iya faruwa.”
Zinatu ta gyara zama sosai tana fuskantar boka Ƙazurgu bayan da ya sa aya a maganganunsa, ta ce, “Boka me zai hana a ɓatar da shi? Ina ganin ta haka ne kawai za mu samu kwanciyar hankali, tunda ba zai gane ba, ina nufin a shafe babinsa daga doron ƙasa, kafin ‘yan uwansa su biyo bayansa, shi sai ya riga su wuce wa tunda haka ya zaɓa wa kansa, ko ya ka gani Habib?”
Habib ya ce “Gaskiya kam ina ganin babu hanyar da ta fi wannan din, tunda dama komai daren daɗewa sai mun kauda shi, mun yi amfani da shi ne domin sanin wasu abubuwa da suka shafi Alhaji da Mashkur wanda ba mu sani ba, shi muka sa ya zuba wa Mashkur magani a kujerar mota ya zauna, abin tambayar shine ta wace hanya shi za mu ɓullo masa, sanin kanki ne hatta abincin gidan nan yanzu Suraj ya daina ci, ya bi duk wasu hanyoyi da zai ga ya kuɓuta gami da kare kai daga abinda ya san ko wane lokaci zai iya faruwa da shi, wannan kuwa ya biyo bayan sanin makama da sirrikanmu.”
Boka ya ce “Wannan mai sauƙi ne matuƙar za ku iya abinda zan sa ku.” Ya buɗe tafukan hannayensa sai ga wata farar kwalba mai ɗauke da wani farin ruwa kamar turare a ciki ta bayyana kana ya ɗaga kai ya dube su, “Duk yadda za ayi ku zuba masa wannan a cikin ruwa ko lemo ya sha.”
Zinatu ta sauke ajiyar zuciya, “Allah gafarta malam ana nan dai, shin ta yaya zamu samu damar ba shi ruwa ko lemo ya sha? Kana ji fa abinda Habib ya gama faɗa yanzu?”
Boka Ƙazurgu ya yi murmushi duk da cewa murmushin ba kyau yake masa ba, saboda tsananin munin fuskarsa ya ce, “Hajiya ina mamakin yadda har yanzu baki san dabaru da makamar aiki ba, Ba lallai ne abin da za ku ba shi ya biyo ta hannunku ba, ina fatan kin gane?”
Zinatu bata gamsu ba, haka dai ta amshi maganin bisa ƙwarin gwiwa ɗaya da take da shi wato Habib da ya tabbatar mata akwai hanyar da zai bi.
*****
Baki buɗe Hajiya Sabuwa take duban Suraj da ke tsugunne a gefenta, shi ma ita yake kallo ba tare da fargabar hukuncin da zata zartar masa ba, don yana da yaƙinin ba za ta yi masa komai ba, kaɗuwar da ya gani a tare da ita kawai ta tsabar mamaki gami da al’ajabin yadda a ka yi tsawon lokaci bai taɓa faɗa mata halin da ake ciki a gidan ba sai yanzu da ta fara kwaɓewa. A gefe guda irin tsananin kulawar da Zinatu ke wa mijinta a she duk wani abu ne daga aikin makircinta.
“Ai ko wannan mata ta cika makira, ka duba ka ga irin ladabin da take mana mu kan mu, har ana yabonta, ana ganin ta fi marigayiya kirki, ashe mage ce mai kwanciyar ɗaukan rai, shegiyar duniya ta fi mu sanin hanyoyin da zata mallake komai na Alhaji ita ɗaya.”
Suraj dai ya yi shiru yana saurarenta.
Ta gyara zama, “Ka san meye mafitarka kamar yadda ka nema yamzu?
Ya girgiza kai, “Sai kin faɗa Umma.”
“Ka koma ka yi abinda take so, ina nufin ku ci gaba da shirin da ku ka fara.”
Ya ɗago kai da sauri ya dube ta da mamaki a fuskarsa. Duk da cewa ya jima da sanin munanan halayenta, a wannan karon sai da ya kaɗu da jin furucin bakinta.
“Me ki ke son faɗa ne Umma?”
Hajiya Sabuwa ta dube shi sosai, “Na san ka san abinda nake nufi sai dai ka nemi ƙarin bayani kurum, wannan ita ce dama guda daɗa tak da muke da ita ta yin arziki farat ɗaya, mu huce haushin talaucin da ya daɗe yana bibiyar rayuwarmu kamar inuwa, mu rabu da ƙasƙancin da muke gani tsawon lokaci, ko dai mu yi KUƊI ko mu MUTU Suraj.
Da zarar ka yi sake wannan damar ta ta kuɓuce sai dai mu haɗiye burin mu, mu mutu da shi, kada ka manta na ɗauki tsawon lokaci ina ina neman hanyar da zan bi na sama mana rayuwar farin ciki, ka duba irin halin da muke ciki a gidan nan, tun da Allah Ya sa mahaifinku ya faɗi ya rasu, aka yi wannan rabon gadon na zalunci, ka tuna irin dukiyar da ya bari, wai amma duk ciki bamu tsira da komai ba sai wannan gidan da wasu ‘yan tsirarin kuɗi da basu taka kara sun karya ba, ba su je ko ina ba suka ƙare, muka koma abin tausayi.
Suraj kadara a gidan nan babu irin wadda ban siyar ba, don kawai in ga mun samu mun rufawa kanmu asiri, in banda wani lokacin Alhaji Ahmad ɗin na zagayowa ya ajiye mana ɗan buhun abinci da sai dai muna ji muna gani yunwa ta kashe mu, ina ranar talauci? Ban gan ta ba wallahi, bana so mu ci gaba da tozarta a idon maƙiyanmu Suraj, don haka dole mu yi amfani da wannan damar mu ma mu cika daɗaɗɗen burin mu, za mu yiwa Hajiya Zinatu abin nan da ake kira YANKAN BAYA.
Sai ta gama nata aikin mu kuma sai mu ɗora namu, SAI TA GINA RAMIN MU KUMA SAI MU SHIGE. Da zarar ka tona musu asiri yanzu, babu mu ba cikar namu burin, tunda bamu da makaman yaƙin da zamu ɗora daga inda ta tsaya, kuma tonuwar asirinsu a yanzu dai dai yake da tonuwar namu asirin.”