Skip to content
Part 7 of 8 in the Series Kudi Ko Rai by Mustapha Abbas

“Duk da haka muna cikin barazana matuƙar Hajiya Sabuwa tana raye, shakku babu na san ya faɗa mata komai, wace hanya zamu bi don kawar da wannan matsalar, ina nufin kawar da zargin hukuma kan binciken silar mutuwar Suraj daga kanmu? Kamar fa mun yi kuskure a wannan aikin.”

Habib ya gyara zaman wayar sosai a kunnensa, a dai-dai lokacin agogon ɗakinsa ya buga ƙarfe goma na dare, kuma tun ƙarfe tara CIKA AIKI ya bugo masa waya ya tabbatar masa ya cika aikinsa kamar yadda suka sa shi, ya rage saura haɗuwar su gobe da safe inda ba shi ragowar kuɗaɗen aikinsa kamar yadda ya ɗauki alƙawari.

Ko kaɗan ba mu yi kuskuren aikawa da Suraj barzahu ba, kuskuren mu ɗaya da muka yi jinkiri, har mu ka bari ya sanar da ita, ya zama dole daga yau zuwa gobe ita ma ta bi bayansa muddin ba ma so asirin mu ya tonu, da zarar ta ji labarin ɓacewarsa babu wanda za ta yi zargi sai mu.”

Zinatu ta sauke ajiyar zuciya zuciya, “Meye mafita kenan, ta ina kake ganin za a ɓullo mata?”

“Ki bar komai a hannuna Sister, zuwa gobe za mu hadu da Cika aiki.” Jin wannan kalami ne ya sa hankalin ta ya ɗan kwanta ta kashe wayar ta wurgar da ita gefe, ta yunƙura za ta kwanta kenan ta ji sallama a falon ƙasa, Zinatu ta tsaya cak, muryar kamar ta Hajiya Sabuwa, zargin ta ya tabbata gaskiya lokacin da ta sake tsinkayen muryar a karo na biyu, da sauri ta yi tsalle ta duro daga kan gadon ta fito ta yiwa falon tsinke.

Hajiya Sabuwa na tsaye, cikin hasken ƙwayayen lantarkin da suka haska wadataccen falon, ta hangi jajayen idanunta da suka ci kuka suka gaji, gabanta ya faɗi, cikin ladabi da mamakin da ya kasa boyuwa kan fuskarta ta ƙaraso inda Hajiya Sabuwa take, ta ɗan russuna za ta gaishe ta

“Dakata Zinatu.” Hajiya Sabuwa ta furta gami da ɗaga mata hannu, “Na san kin san abinda ya kawo ni gidan nan yanzu haka? Ina so ki faɗa min inda ɗana yake a daren nan ina son ganawa da shi.”

Zinatu ta dube ta ƙirjinta yana dukan uku-uku, amma sai ta dake ta ce, “Hajiya ban gane me ki ke nufi ba?”

“Da hausa nake miki magana Zinatu, ina so in san halin da Suraj yake ciki, shin kun kashe shi? Idan kun kashe shi ki faɗa min inda gawarsa ta ke.” Ta idashe furucin da share hawayen da suka zubo kan kuncinta.

Cikin kuka muryar Hajiya Sabuwa ta ci gaba da amsa kuwwa a cikin falon, “Shi kaɗai nake da shi, shi ke nan yanzu na rasa shi, Zinatu kin cuce ni ke da ɗan uwanki, kun sabauta min rayuwa, ina zan sa kaina da wannan baƙin cikin? Wallahi ba zan yarda ba, ba zan ɗauki ƙaddara ba.”

Zinatu ta daure fuska sosai, “Saurara min Hajiya Sabuwa, ni fa sam ban gane inda wannan sambatun naki ya sa gaba ba, wani ne ya je ya ce maki na kashe miki ɗa? Lallai bakin ki ya ci gaba da furta irin waɗannan kalaman a kaina zan ɗauki tsatstsauran mataki a kanki, hukuma ce za ta raba ni da ke, tunda ke ba kya iya tauna magana kafin ki furta ta, babu makawa bakin ki zai kai ki ya baro.”

Hajiya Sabuwa ta sa gefen mayafinta tana ci gaba da share hawayen da ke saraftu a kan kumatunta ta ce, “Ni fa ba sa’insa na zo mu yi da ke ba, na riga na san komai, mai afkuwa ta riga ta afku, kawai ki faɗa min in da kuka kai gawar don na san halin makircinki, ina son ƙara tabbatarwa ne kawa, ko babu komai ina son yiwa Suraj ganin ƙarshe, sannan a yi masa sutura ta mutunci.” Ta sake rushewa da kuka.
Zinatu dai ta rasa yadda za ta yi da ita kawai sai ta juya da sauri ta haye sama ɗakinta ta bar Hajiya Sabuwa tsaye a falon, tana shiga ta rufo ƙofar. Wayar ta ta ɗauka ta kira Habib ta fada masa halin da ake ciki.

Habib ya kaɗu matuka da jin zancen, ya ya a ka yi ta sani har ta yi tattaki ta zo a daren nan? Lallai akwai wani daban da ya faɗa mata, to waye? Ya tambayi kansa, babu amsa, Babbar magana, za ayi baya ba zani ke nan, akwai matsala babba.

Habib kai nake saurare ya zan yi da matar nan ne, ta fara hau min kai?” Zinatu ta dakatar da tunaninsa, ta ci gaba da cewa, “Yanzu haka tana falo tana ta kururuwa, daga yanzu zuwa ko wane lokaci komai zai iya faruwa, asirin mu fa zai tonu Habib.”

Ya sauke ajiyar Zuciya, “Kin san meye Sister?”
“Ina sauraronka” Ta faɗa cike da zaƙuwa.

“Ki ɗauke ta a mota kawai kuje can gidan.” Ta firfito ido waje tare da dafe ƙirji tamkar yana gabant, “What? In ɗauke ta mu je ina Habib? Ka yi tunani mana, hakan fa yana nufin in amsa mata cewa mu muka kashe mata ɗa? no ba zai yiyu ba Habib, a sake wata dabarar.”

Daga can ɓangaren Habib ya yi wani murmushi mai wuyar fassarawa, sannan kai tsaye ya ce, “Hakan fa za a yi Sister, ki yi kamar yadda na ce, ni na san abinda na shirya.” Sai da Zinatu ta ɗan yi jim sannan ta ce, “Meye wannan ka shirya da har kake faɗa min cike da ƙwarin gwiwa, alamun cewa ka yi babban target a gurin?”

“Haka ne Sister.” Ya faɗa yana jijjiga ƙafa daga kwancen da yake. “Wane target ne? sanar da ni da sauri.”

“Lokaci ya yi da Hajiya Sabuwa za ta bi bayan ɗanta zuwa in da ya tafi a daren nan, kawai abin da nake so da ke ki aiwatar da komai kamar yadda na umarce ki.”

“To shikenan zan yi yadda ka ce.”

“a kashe wayar da sauri, ta fito zuwa falon har yanzu zuciyarta na raba ɗayan biyu kan bin umarninsa. Hajiya Sabuwa na nan a tsaye kamar yadda ta bar ta, tana ganin fitowar ta ta yi saurin matsawa ta tare ta ta ci kwalar ta, “Wallahi Zinatu ba zan yarda ba duk yadda za a yi sai kun fito min da ɗana a daren nan.” Zinatu ta ce da ita, “Hajiya ya kamata dai ki sake ni matuƙar kina son abinda kike nema sai muje in kai ki inda yake.”

Jin wannan ya sake ta, har yanzu idanunta suna zubar da hawaye kamar an ɓalle famfo, ta ɗaga ƙafa ta fara tafiya a kan kilishin falon, ta nufi bakin ƙofar shigowa, Hajiya Sabuwa ta rufa mata baya suka fito wajen motoci.

Sai da Zinatu ta tashi motar sannan ta umarce ta da ta shigo su tafi. Lokacin da ta shiga motar ta zauna ne Zinatu ta gamsu da shawarar ɗan uwanta lallai abin da ya kamaci Hajiya Sabuwa kenan. Da sauri Maigadi ya taso ya buɗe musu ƙofa suka fice daga gidan.

Bayan Habib sun gama magana da Zinatu, bai ɓata lokaci ba ya sake kiran Cika Aiki.
“Ya a ka yi ne ran ka ya daɗe? Daga can ɓangaren Cika Aiki ya faɗa.

Habib ya gyara zaman wayar sosai a kunnensa, “Kana ji na? Wani aikin ne ya samu, kuma za ka yi shi a daren nan kafin wayewar gari.”

“Me yake faruwa ne Yallaɓai?” Cika ya buƙata.
“Mahaifiyar gayen nan ce ta kawo kanta tun daga Zaria, wai tana so lallai a nuna mata gawar ɗanta, yanzu haka na sa Hajiya ta tafi da ita can gidan da ka rutsa shi gayen, ina so a yanzu ka fita ka bi bayan su, kar ka yi komai sai ka tabbatar sun shiga gidan.”

“An gama yallaɓai, dama nima na fi son aiki da dare ya fi daɗi hankalin mutum kwance.”

Lokacin da suka iso ƙofar gidan a rufe suka tarar da ƙyauren get ɗin, sai dai ba a sa kwaɗo ba, Zinatu ce ta tako ta fito daga motar ta tura ƙofar a hankali ta buɗe, sannan ta koma ta shiga motar ta ƙarasa da su zuwa cikin farfajiyar gidan, ta sake fitowa ta kullo babbar ƙofar get ɗin sannan ta buɗe ‘yar ƙaramar kofar ta karo ta, kai tsaye suka yi wa falon tsinke, ba tare da ɗayan su ya yi magana ba tun fitowar su daga gidan Alhaji, sai sautin shesshekar kukan Hajiya Sabuwa dake tashi, duk ta bi ta fita a haiyacinta, kana kuma tana matse ta ga halin da Suraj yake ciki.

Daga can daura da ƙofar gidan duk a kan idon Cika Aiki komai yake faruwa, bayan shigar su da minti ɗaya ne to ya rufa musu baya.

Har lokacin Hajiya Sabuwa ba ta daina kukan da take ba tamkar ƙaramar yarinya, shigowar su falon ya sa ta kara tsananta kukan nata bisa tabbaci da take da shi kan ko Suraj ba ya ciki to ya kasance a falon na wani lokaci kafin zuwan su, domin matuƙar ba hancinta ke son yaudararta ba ƙamshin turaren da yake amfani da shi da ta shaƙa.

Zinatu ji take tamkar ta shaƙe ta don haushin yadda ta cika mata kunne da ihu tare da sambatu, ko can ta san Hajiya Sabuwa da kafirar mita da kukan tsiya, ta ɗan murmusa a lokacin da ta tuna cewa sa’anni kaɗan ya rage ita ma ta leƙa garin da ba a dawo wa.

Hajiya Sabuwa ta ci gaba da ƙarewa falon kallo, tamkar idanunta za su hasko mata Suraj, kai tsaye Zinatu ta zarce ɗakin da ya shiga a ɗazu, hakan ya sa ita ma Hajiya Sabuwar ta bi ta a baya gabanta yana tsananta bugawa, katsam! ta yi tuntuɓe da wayar salularshi a tsakanin kujera da kujera da suka bada hanya don shigewa ɗakin wanda tuni Zinatu ta kama ƙofar ta murɗa.

Hajiya Sabuwa ta durƙusa ta kai hannu ta cafki wayar sai ta ƙara rushewa da wani sabon kukan, dalilin da ya janyo hankalin Zinatu kan ta lokacin da take ɗaure wayar a haɓar zaninta cikin kuka ta ce, “Shikenan yanzu na tabbatar na rasa ka Suraj, wayyo Allah! ni Sabuwa ina zan sa kai na?”

Idan banda gidan babban gida ne babu abinda zai hana jama’ar da ke waje su jiyo hargowar Hajiya Sabuwa, ta ɗaga kai ta dubi Zinatu da idanunta da suka canza launi zuwa ja saboda tsananin kuka sannan ta ci gaba da cewa, “Zinatu me yasa ku ka kashe min ɗa? Me ya yi muku? Saboda abin duniya, dukiyar da kuma ba ku da gadonta, ko kuwa ta ubanki ce? To Ki sani cewa asirin ku ya tonu shegiya tsintacciyar mage wadda ba ta taɓa zama mage, wallahi kin ji na rantse miki ba zan yarda ba, ko ni ko ku, ba…”

Sauran furucin ya maƙale a fatar bakinta sakamakon wani abu da ta ji mai kama da guduma ya sauka a tsakiyar kanta, wanda ya tilasta mata zubewa ƙasa a gurin, ta ɗora hannu a ka cikin ruɗu tana baza idanu don ganin abinda ya faɗo mata a ka, bibbiyu idanun ta suke ganin Cika Aiki dake tsaye yana muzurai, Hajiya Sabuwa ta tabbatar shi ne ya buga mata wani abu a kanta, sai dai ta kasa ganin abin da ya buga mata din…A taƙaice dai fashin kwakwa ya yi mata da gabjejen hannun sa a tsakiyar ka.

<< Kudi Ko Rai 6Kudi Ko Rai 8 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.