Skip to content
Part 5 of 30 in the Series Fasaha Haimaniyya by Haiman Raees

KUKAN KURCIYA

Da sunan sarkina zan fara

Wannan da shi ne ya yiwo fara

Ya yi kare kana ya yo kura

Ya yi ruwa kuma kana ya yo ƙura

Hikimar Allah sam ba ta da iyaka.

*****

Tsira da aminci gun baban Zahra

Wannan da cikin annabawa ya yo zarra

Wanda duk wata daraja tuni ya tara

Sahabbai da alihi duka na tara

Salati gare shi na ke furtawa babu iyaka.

*****

Wai mu yaushe ne za ko mu hankalta

Mu zam nutsuwa da neman mafita

A wayi gari junanmu za mu fifita

Ai ya fi ace kawunanmu muka fifita

Ko ba komai hakan ai zai fishe ka.

*****

Mu kawunanmu kawai muke hange

Ba makwancin duban wanda yake a jikin shinge

Na ƙoluwa kawai muke hange

Taddo shi kawai muka daddage

Kai mai dogon buri kam kaiconka.

*****

Ƙaddara dai kowa da akwai ta sa

Riga ce da babu mai cire ta sa

Da zamu gane mu daina sa-in-sa

Akan abin da zai zo komai nisa

In ko mun ƙi mun yi ta’asa

kamar wanda ya sha molanka.

*****

Allah ka tsare mu da na shina

Ka sa mu zamo masu yin murna

Da duk abin da ka tsara mana

Alfarmar annabinka mijin Nana

Ka sa kar mu zamo cikin masu yin shirka.

*****

Jamilu ne ke waƙar daga nan gefen

Domin isar da saƙo ga ‘yan can gefen

Fatana kowa ko ya amfana

Da ɗan abinda na samu a karatuna

Wannan ita ce riba da ba ta da iyaka.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.8 / 5. Rating: 8

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Fasaha Haimaniyya 4Fasaha Haimaniyya 6 >>

2 thoughts on “Fasaha Haimaniyya 5”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×