Skip to content
Part 1 of 6 in the Series Kushewar Badi by Kabiru Yusuf Fagge

Tsakure

Tsawon shekaru Almustapha da matarsa Lajja suna tare, suna matukar so da kaunar junansu, so irin na don Allah. Abubuwa biyu ne kadai ke damunsu a rayuwa; rashin haihuwa, da kuma wani al’amari mai firgitarwa da ke tare da Lajjar. Kwatsam! Wata rana tsaka a cikin ire-iren ranekun babi-babi na rayuwarsu, wani mutum mai suna Alhaji Hammad ya bayyana tare da shaidun cewar Lajja fa matarsa ce. Hujjojin da ya kawo sun tabbatar da abin da ya fada haka yake. Don haka alkali ta karbe Lajjar daga hannun Almustapha aka ba Alhaji Hammad. Shekara daya da faruwar wannan abu Allah ya yi wa Lajja haihuwa. To a wannan lokaci ne kuma wasu hujjojin suka kuma bayyana, kuma suka tabbatar wa duniya Lajja ba matar Alhaji Hammad ba ce! To matar wane ne?

Gargadi

Kirkirarren labari ne daga marubucin. Yin amfani da wani sashe na labarin ba tare da izinin marubucin ba na iya zama karya ka’ida, musamman ta fuskar shari’a don haka sai a kiyaye!

Tunawa

Da iyayenmu da suka riga mu gidan gaskiya, da sauran ‘yan’uwa Musulmi bakidaya, Allah ya ji kansu, ya gafarta musu, amin summa amin.

Domin

‘Yan’uwa da abokan arziki

Manazarta

Bashir Reader Fagge

Ibrahim Muhd. Indabawa (Mu’azzam)

Jamilu Haruna (Jibeka)

Ibrahim Birniwa

Yabawa

Abdullahi Yusuf, Ahmed Y. Amo, Sama’ila Yusuf, Hassan Hussaini, Muhd. Y. Rayyan, Hayat Bagobiri, Baba Ali.

A Karkashin

Inuwar Marubuta Littattafan Hausa (Hausa Authors Forum)

Da sunan Allah Mai rahama Mai jin kai.

FARKON LABARIN

Shekara Ta 2022

Titin Mandawari                                

Hatsarin da motar ta haddasa, ta hanyar dukan motar dake gabanta da motar bangaren damanta a lokaci guda ita ta haifar da faruwar wasu abubuwan da dama wadanda suka hadar da rudewar wasu mutane, barnatar da dukiya, da raunatarwa.

Mintuna biyu da faruwar hatsarin wurin ya cika da jama’a, ‘yan kallo da masu agaji. Da yake akwai ofishin ‘yansanda a kusa, tuni ‘yansanda suka halarci wurin don tabbatar da abin da ya faru, da kuma aiwatar da aikinsu.

Almustapha da Lajja da suke tafe a motarsu, suna daga daya bangaren, su kansu hatsarin ya ja hankalinsu.

Mota daya ce ta yi sanadiyyar faruwar hatsarin, amma sai da motoci akalla bakwai suka farfashe, babura hudu suka fadi, mutane da dama wadanda suka hadar da na cikin motocin, na kan babura, masu tafiya a kasa da ma wadanda ke zaune a gefen wurin suka raunata.

Mutumin da ya haddasa hatsarin fari ne, amma ba kal ba, yana da dan jiki da tsayi. Sanye yake da yadi fari wanda ake kira da 500 ‘Euro’ ko ka ce ‘kafi-boyel’. Kansa yana dauke da hula zanna-bukar dinkin inji. Babu abin da ya same shi, kuma a fuskarsa kwata-kwata babu alamun damuwa da abin da ya haddasa, asali ma dai fuskar tasa na dauke da wani abu daban. Hankalinsa da ganinsa duk sun tafi ga kallon motar Almustapha dake titin daya bangaren. Wanda tun tuni ta gifta inda yake – kallon motar ya faro ne tun kafin afkuwar hatsarin.

A gaggauce ya fito daga cikin motarsa, bai yi wata-wata ba, kuma bai damu da hatsarin da ya haddasa ba kamar yadda tun farko fuskarsa ta nuna, ya tsallaka zuwa daya titin, ya tari babur mai taya uku, yana cewa.

“Yi sauri mu bi motar can.” Cikin gaggawa ya umarci mai babur din, a lokacin da ya nuna masa motar Almustapha kirar Sienna.  Tuni ya gama shigewa cikin babur din mai rumfa.

Mamaki da al’ajabi suka kama sauran jama’ar da ke wurin ganin Alhajin zai gudu ya bar tamfatsetsiyar motarsa mai tsada, wadda a kiyasi ta haura miliyan ashirin zuwa talatin. A kiyasce idan za a siyar da ita, za ta biya duk wata barna da aka yi a wurin, idan ma har biyan ya rataya a wuyansa kenan.

Wasu mutane da ke wurin sun yi tunanin don kada a yi masa wauta ne ya sa, ya gudu. Wasu masu babura da ‘yansanda har da masu motoci suka bi shi.

Saboda tsananin kaguwa duk da irin gudun da mai babur din yake yi don cika umarninsa ko ya sami karin kudi, shi Alhajin gani yake kamar ba gudu yake ba. Ji ya yi tamkar ya kwace babur din shi ya tuka ya kamo su.

Almustapha ya kalli Lajja a daidai lokacin da yake kokarin karya kwana domin shiga titin da ke jikin gidan sarautar Kano, titin da ya nufi unguwannin Gwangwazo da Indabawa da kuma kofar Nassarawa.

“Amma mutanen zamanin nan sun baci da yawa. Ni na ma rasa gane shin me ya ke kallo? Kawai mutum da girmansa da komai ya rika kallon matan mutane. Allah dai ya kara, ai ga shi nan abin da kallon ya jawo masa, ko banza ya lalata motarsa, ya lalata wa mutane tasu, kuma ya haddasa hatsari.”

Lajja ba ta dubi mijinta Almustapha ba, kallon gabanta kawai take yi, tamkar ita ke tuka motar. Sai dai kuma gabanta sai bugawa yake yi, kuma ta rasa tsayayyen dalilin hakan. Tun da ta hada ido da mutumin, wanda Almustapha yake magana a kansa ta ji gabanta ya fadi, kuma har suka bar wurin suka ci gaba da tafiya ba ta iya cewa uffan ba sai ‘uhm’ da ‘e’. Ta matsu su karasa gida.

Abin ya yi matukar ba ta haushi, kuma ya bata mamaki yadda mutumin ya kura mata ido, har sai da suka yi ido hudu. Wasu abubuwa da ta gani shimfide a cikin kallon nasa ne suka haddasa mata faduwar gaba.

Ba ta farga ba a karo na biyu ta ji tamkar zuciyarta za ta faso kirjinta ta yo waje. Ba komai ba ne ya haddasa mata hakan ba face tsinkayar mutumin da ta yi a daf da ita, a cikin babur mai taya uku, yana kokarin tsayar da su. Idanuwansa kar a kanta, ba ya ko kiftawa. A kidime, firgice da mamaki karara yake.

Tashin hankali! Hakika da ita ce ke tuka motar to da babu abin da zai hana ta haddasa mummunan hatsari a karo na biyu a wannan rana. Domin ko tantama babu ba za ta iya tsayawa ba, kuma ba ta san irin tukin da za ta yi ba. Gabadaya yanayinta ya koma na matukar firgita da tsoro ga wannan Alhaji.

A hankali, fuskarsa dauke da tarin alamomin tambaya Almustapha ya yi gefe, ya tsaya da motar. Kasa bude baki Lajja ta yi, amma da tabbas sai ta hana shi tsayawa, musamman da yake ita ba ta ga dalilin tsayawar ba.

A cikinsu babu wanda ya yi yunkurin da ya nuna za su fito daga motar. Zukatansu cike da abubuwa da dama. A gaggauce Alhajin ya diro daga kan babur din, ya nufi wurin motar bangaren da Lajja take, yana fadin. “Lajjanatu!” Da karfi, kuma tattare da matukar kaduwa da mamaki ya kira sunan.

Tsoro ya kama Lajja, ta kurma ihu, tare da gaggawar bige hannunsa.

Mamakin da ya sauyu kuma ya halittu radau a fuskar Alhajin bai hana shi ci gaba da abin da ya wanzu a kai ba.

A daidai wannan lokacin ne ‘yansanda, da masu babura da sauran masu motocin da suka biyo bayansa suka karaso wurin. Ganin faruwar wannan abu ne ya sa wasu daga cikinsu suka kara yarda da zarginsu na cewar Alhajin yana da tabin hankali, wasu kuwa daga cikinsu tunanin wani waje ya karkata.

Tabbatarwa tare da kyautata zaton tabuwar hankalin Alhajin ne ya sanya tausayi a zukatan mafiya yawan mutanen da suka biyo bayan shi, har ma da ‘yansandan, don haka suka ga ya dace su taimaka masa, su sada shi da iyalin shi, ko wurin da ya dace kamar asibiti, don kar abin ya yi muni.

“Wasu ire-iren cutar haukan da yake damun su kenan.” Cewar wani dattijo, daya daga cikin masu motocin da suka biyo Alhajin.

Kartai biyar ne suka rike shi kam-kam. Duk da haka, kasancewar yana da karfi, sai da ya rinka jijjiga su, yana kokarin kwacewa. Amma da yake ya riku, kuma shi da kansa ya tabbatar da hakan sai ya rinka kokarin yi musu bayani ta yadda za su fahimce shi.

“Ku sake ni don Allah! Wallahi matata ce! Da hankalina.”

A tsammanin mutanen da ke rike da Alhajin haukan ne ya sanya shi yin haka.  Dada rike shi kam-kam suka yi.

A hankali, Lajja ta dago kanta suka hada ido da Almustapha, wanda ya kafa mata ido, kamar bai taba ganinta ba. Zuciyarta ta yi zafi, hankalinta ya dada tashi. Hawaye ya biyo ta cikin idonta ya malalo kan fatar kumatunta, dumi da takaicin da hawayen ke dauke da su, suka kona mata zuciya.

“Ku sake ni don Allah! Wallahi matata ce!”

A can cikin zuciyarsa, Almustapha ya ji maganar Alhajin tana maimaita kanta. Amo da sautin muryar Alhajin tana dauke da tabbacin abin da ya fada, kuma muryar na dauke da tausayi gami da makalallen rauni. Kalaman suna sanya kuna da takaici a zuciyar wanda ya fade su da kuma wanda aka fadawa, har ma da wanda ya ji alhalin abin bai shafe shi ba.

Cikin dacin da ya yi rub da ciki a zuciyarsa, ya rintse idanuwan shi.

Ya fara tunani a ransa cewa to shi wannan a mahaukatan wane ne shi?

*****

Alhaji Hammad ya kalli abokinsa, Alhaji Zuhairu.

“Kar ka yi shakku ko inkari ga abin da na gaya maka. Wallahi, in kara rantse maka, matata Lajjanatu na gani a mota tare da wani…”

Tun daga ranar da ya ga Lajjar baya iya karasa duk wata magana da ya fara fada, yau kwanaki biyu kenan. A kodayaushe ka kalli fuskarsa za ka ganta dauke da matukar mamaki, al’ajabi da takaici.

“Abin da ya dan kwantar min da hankali kamar yadda ka sani shi ne da Malam Bashir direba ya tabbatar mini da sanin inda take, amma ba don haka ba, da ba ni da wani abin yi da ya wuce kai wa gareta a kowane hali, kuma…”

A ranar da al’amarin ya faru, lokacin da kartan nan da ‘yansanda suka raba shi da jikin motar su Almustapha, sai suka nufi gidansa da shi kasancewarsa fitaccen attajiri. Sai dai kuma tun kafin su karasa gidan suka gane cewar da hankalinsa, duk abin da ya ke aikatawa da aiwatarwa a tattare da shi akwai tabbacin gaskiya. Sai kuma suka rinka ba shi hakuri.

Ba don Malam Bashir ba, daya daga cikin direbobinsa, ya ba shi tabbacin sanin ainihin gidan da Lajjar take to da ba shakka sai ya dauki tsattsauran mataki a kan mutanen da ‘yansandan da suka rike shi baki daya.

Hatsarin da ya haddasa kuwa ya tura wakilansa don daukar nauyin duk wasu abubuwan hawansu da biyan kudin magunguna da kulawar wadanda suka yi rauni.

Alhaji Zuhairu ya kura wa Alhaji Hammad ido. “Kuma tun da muke da kai ba ka taba ba ni labarin da ya shafi wannan abu ba.”

Alhaji Hammad ya gyada kai tare da cije lebe. “Bari kai dai Alhaji! Akwai wani sirri da wani boyayyen al’amari a tsakanina da ita, wadanda suka hana ni gaya wa kowa cewar na zo wannan kasar ne don neman matata, kuma ba na tunanin zan gaya wa wani har sai zuwa ranar da na ganta. Amma da yake muna tare da kai, idan har ka lura da ni ai ka san a iya tsawon zaman da muka yi da kai ina tattare da wani hali da yanayi matsananci.”

Alhaji Zuhairu ya dan yi shiru, sannan ya gyada kai, alamar tabbatar da zancen abokin nasa.

“To wannan na zahiri ne, kuma mai sauki, amma a badini wanda ke zuciyata ya zarce komai rashin dadi. Na san za ka iya lura da hakan kuma za ka yarda da ni bisa hujjojin kasancewata marar mata iya tsawon zaman da na yi da kai, alhalin lafiyata kalau, ina da kudi. Amma kuma babu tsantsar kwanciyar hankali a tare da ni. Sannan….”

Har yanzu kallon sa kawai Alhaji Zuhairu yake yi.

Idan bai manta ba tun a shekara ta dubu biyu da hudu (2004) suka hadu da Alhaji Hammad a lokacin da ya zo kasar Najeriya daga Saudiyya. Kamar yadda ya gaya masa, shi asalin mutumin kasa Masar ne, ya je Saudiyya ne yin Umra daga can ya zarto nan kasar don bude ido da yin kasuwanci, musamman na abin da ya shafi gwala-gwalai. Sannu a hankali suna tare har Allah ya habaka Alhaji Hammad din, kasancewar ya zo da kudinsa masu yawa, ya zama shahararren attajiri, ya mallaki gidaje da kamfanunnuka da shaguna da motoci da kuma tarin kadarori a bainar hamshakai na kasar Najeriya.

A iya zamansu da rayuwarsu, Alhaji Zuhairu ya san wasu abubuwa da sirrikan Alhaji Hammad din, haka nan halaye da dabi’unsa. Mutum ne mai mutumci, mai kyawawan halaye da dabi’u, mai ibada da taimakon al’ummar Musulmi, mai sanin ya kamata da adalci.

Abubuwa biyu ne kacal suka kudundune tunanin Alhaji Zuhairu dangane da rayuwa da kuma al’amuran abokin nasa. Wato rashin yin aure, sai kuma wani hali da Alhajin ke shiga jefi-jefi wanda ya shafi matsananciyar damuwa. Wadannan abubuwa su Alhaji Zuhairu ya nakalta a tattare da abokin nasa wadanda sam bai fahimce su ba, sai yanzu da yake shirin bambance masa zare da abawa.

“Ina da aure, kuma ina tattare da wani sirri.”

Wannan ita ce wata amsa guda daya da Alhaji Hammad ya taba gaya wa Alhaji Zuhairu, ta wata tambaya da ya taba yi masa a can wani lokaci na baya. Duk da cewa Alhaji Zuhairu ko kadan bai fahimci wannan amsa ta abokin nasa ba, sai ya kyale shi, domin ya fuskanci bai ji dadin tambayar ba. Shi kuma ko kadan ba ya son abin da zai bata wa abokin nasa rai.

Alhaji Hammad ya dubi Alhaji Zuhairu.

“Na auri matar tawa ne a can kasarmu Masar. Auren soyayya, rayuwar aurenmu ta zamo kyakkyawa, muna kaunar junanmu, hankulanmu a kwance. Farantawa junanmu shi ne aikinmu, kowannenmu yana dokin dan’uwansa. Mun rabu irin bakar rabuwar nan mai dauke da tsantsar takaici, bakin ciki, mai dauke da tsananin muni. Hakan ya samo asali ya faru a wata rana, wani sabani ya shiga tsakaninmu. Tsautsayi ya sanya Lajjanatu ta goranta min tare da bankada asalin kabilarmu ta hanyar munanasu da danganta su da wata kabila.

“A al’ada da dabi’ar kabilun kasarmu idan irin wannan ta faru to al’amura sun dagule kenan, sun munana, babu sauran kwanciyar hankali, don haka ba wai aure ba, komai ma ya kan iya rabuwa. A wani lokaci har yaki da tashe-tashen hankula hakan ke haifarwa. Wannan ya tilasta mana rabuwa. Rabuwar da ba za mu dawo mu sake zaman auren junanmu ba, sai dai ko idan ba a kasarmu ba, ko kuma wani babban dalili da yake da girma, musamman dalilin tsananin soyayya da kulawa. Sai……” Ya tsahirta, ba tare da ya yi motsin da zai haddasawa idonsa kallon wani wuri ba, ko hannunsa ya taba wani abu ba, ko kuma kafarsa ta motsa.

“Al’ada, matsalarta da illolinta sun fi kyawunta da nasarorinta yawa. Na fuskanci hakan, kuma na san hakan, ga al’ummarmu…” Ya maimaita yin shiru. Kana ya numfasa.

“Mu dai ‘yan kabilar Ramusawa ne, wadanda tarihi ke nuna mu a matsayin tsatson Fir’auna Ramsisi dan Seti ne. Sai dai mun samu kanmu a Musulmai bisa dalili mai girma. To da wannan sabani ya shiga tsakaninmu sai ta danganta danginmu da tsatson Fir’auna Amenhotef (Amenhotep) wadanda kabilunsu ake kiransu da Amenho. Ni kuma da na ji haushi sai na dangantata da kabilun Fir’auna Tutankamun (Tutankhamun) dan’uwan Akanato (Akhenaton) wadanda ake kiran kabilunsu da Tutankamawa. Hakan ya zamo babban kuskure, ya haddasa daidaita mu, ya raba ni da matata, abar kaunarta.

“Lajjanatu ta yi bulagaro zuwa Saudiyya a lokacin da ni kuma sai na nausa tsibirin Dishu dake birnin Tibesti a can kasar Chadi. Ina ji ina gani zama da nutsuwa suka gagare ni, a dole na tattara yanawa-yanawa na nufi Saudiya, don neman matata. Na fuskanci idan ba na tare da ita, to hakika rayuwata ba za ta ci gaba da wanzuwa a doron duniya ba. A Saudiyyar ne kuma na sami labarin an ga tahowar ta nan Najeriya, wai ita da wata Bahaushiya. Don haka ban zauna ba, na taho nan. Kusan shekaru bakwai kenan amma sai a wannan lokaci Allah ya nuna min ita na….”

Yamutse kuma a hautsine fuskarsa take, karshe kuma hawaye ne a fuskar tasa.

Alhaji Zuhairu ya tausaya masa, kuma ya kudiri niyyar taimaka masa.

******

Maganar ta zamewa Lajja da Almustapha wata iri. Suna cikin mamaki da takaici. Wannan ya zamo sama da duk wasu al’amura da suka faru a kansu a baya. Idan ma dai na bayan suna da yawa, to wannan karon ya ninka, kuma ya ruba.

Lajja ta dubi Almustapha, ta kawar da kanta, akwai kwalla a gurbin idanunta, ta fara da cewa.

“Ranar Lahadi bakwai ga watan Janairu, shekara ta dubu daya da dari tara da tamanin da shida (7/1/1986) aka haife ni, a unguwar masaukar alhazai (Hajj-Camp). Na halarci makarantar firamare wadda ke kan titin Katsina (Katsina Road) Daga shekara ta dubu daya da dari tara da biyu (1992), zuwa shekara ta dubu daya da dari tara da takwas (1998), daga nan na zarce zuwa sakandiren ‘yanmata ta Maryam Abacha daga wannan shekara (1998) zuwa shekara ta (2001) inda kuma na zarce babbar sakandire anan daga wannan shekara zuwa shekara ta 2004. Bayan kammala jarrabawarmu ta (WAEC) muka yi ‘Jamb’ na sami tsallaka wa jami’ar Bayero na karanci Medicine daga shekara ta (2005).

“Na aure ka tun kafin in kammala karatuna. Na fara aiki bayan kammala karatuna. Mahaifina ya rasu tun ina da shekaru uku a duniya, mahaifiyata tana nan a raye kamar yadda ka sani. Hakazalika muna da daidaikun dangi. Shin ko akwai wani abu? Ko kuma kana so ka tabbatar kuma ka nuna min kai ma ka yarda da abin da Alhaji Hammad ya fada, sauran mutanen gari suka yarda?’

Tun da Lajja take ba ta taba gaya wa mijinta magana ranta a bace ba sai a wannan rana, a wannan lokacin, ga shi kuma har da karaji. Tsananin bacin rai ne ya sanya ta kara karanto masa tarihin rayuwarta, alhalin ta san ya sani.

Ma’auratan suna cikin wani hali ne mai abin mamaki, domin ko da yaushe yana yi mata wani irin kallo da tambayoyi.

Abin kamar wasa, faruwar al’amarin tare da maganar da Alhaji Hammad din ya fada kuma ya ba da tabbaci sun yi matukar tasiri, mutane abin ya zame musu abin tattauawa. Maganar ta zamo maganar da aka yi jiya, ake yi yau kuma ake jiran yin ta a gobe da jibi. Ciki da batsewar jihar Kano ta wadata da labarin.

Da yawa mutane suna zargin cewa Lajja ko dai aljana ce, ko kuma wata hatsabibiya ce. Sannan kuma wasu na ganin mayaudariya ce, ta auri Alhaji Hammad ba tare da rabuwa ba ta koma ga Almustapha ta aure shi shi ma. Wato mace daya ta auri maza biyu.

Al’amarin da wasu suka dauka a matsayin wasa kuma almara yana neman zama gaske.

Almustapha dai ya zamanto a cikin halin rudu da firgicewa. Ya yi tunani a kan kansa, ya hanga, a karshe ya gaza cimma burinsa na gane; shin wai wace ce Lajja? Hakan shi ya tilasta masa yi mata tambayar da bai taba tunanin yi mata kwatankwacinta ba, musamman a cikin babin rayuwarsu. Ya kuma matsa a kan haka, a tunaninsa wai ko zai fuskanci wani abu daga gareta.

“Mene ne gaskiyar lamari game da rayuwarki da kuma al’amuranki? Wace ce ke?”

Wadannan sune tambayoyi biyu da ya yi mata.

Idan akwai abu biyu da Lajja ta tsana a rayuwarta to ba shakka na farkon ba zai wuce zargi ba, ta tsani zargi, a kan zargi tana iya shiga kowanne irin hali. Abin takaici sai ta ga mijinta, gudan jinin da take ji dashi a ranta yana zarginta da wani abu wanda ba ta san shi ba. Don haka cikin tsananin bacin rai da takaici mai girma ta zayyano masa tarihin rayuwarta.

Ko kadan hankalin Almustapha bai kwanta da wannan abu ba.

To ko ma dai mene ne kuma ko me ake ciki, sannan ko mene ne zai faru, shi dai Alhaji Hammad ya ji, ya gani kuma ya sha alwashin ganin matarsa Lajja ta dawo gare shi. Zuciyar shi da tunanin shi gaba daya sun tattara sun koma gareta, soyayyarta da kaunarta sun dawo masa sabbi, musamman da ya kyalla idanu ya ganta, a ganinsa ba zai iya ci gaba da sauran rayuwa ba sai da ita. Ya tanadi duk wasu hujjoji da bayanai na zahiri da zasu tabbatarwa da kowa da kuma duniya cewa Lajja matar shi ce, ta auren sunna, mallakarsa ce halak malak, mai hana shi karbarta a wannan lokacin sai dai ko Ubangijin da ya halicce shi.

Mataki na farko da Alhaji Hammad ya fara dauka shi ne shigar da kara da ya yi a kotu, musamman don ganin an mallaka masa matarsa ta hanyar da yake ganin ita ce mataki ta farko kuma sassauka.

A nasu bangaren, hujjoji gami da tabbataccen tabbacin da ke wurin Lajja da Almustapha masu karfi ne. Sun zauna da taimakon babban abokinsa Albashir, sun zube rayuwar Lajjar kacokam a kan faifai, sun tankade tare da rairayewa sun kuma tabbatar da cewa maganar Alhaji Hammad tatsuniya ce, kuma hauka yake yi. Ba mamaki ma akwai wata manufa da ya zo musu da ita ta cutarwa garesu.

Ranar hudu ga watan Oktoba, ita ce ranar da za a gabatar da shari’ar da shi Alhaji Hammad din ya shigar – Almustapha ya sami sammaci daga kotun.

*****

A nutse, amma kuma cikin fushi ya yi jifa da jaridar Daily Trust dake rike a hannunsa kan kujerar da ke bangaren damansa. Gwanine a bangaren karance-karancen jaridu da mujallu. Babu wata rana daya da za ta fito ta koma ba tare da ya karanta jarida ko mujalla a kalla daya ko biyu ba, to amma tun da wannan abu ya faru, idanunsa suka hango masa matarsa, wacce ya dade yana son gani, sai wannan abu ya sauya a gare shi. Asalima dai komai nasa sauyawa ya yi, muwalatinsa ya karanta, alamun damuwa da firgicewa har da nuna alamar rama sun dade da samun mafaka a tattare da shi. Bai ma cika cin abinci sosai ba.

Ya mike a hankali, ya fara takawa kadan-kadan kamar ba zai iya ba, ya doshi wurin dirowarsa. Idanuwansa cike da kwalla saboda tsananin tausayin kansa da shi kansa ya ke ji, tunaninsa a tsawaice kuma a yawaice. Ya tsugunna, ya bude dirowar, ya dauke wasu tarin takardu dake cikin dirowar daga sama. A kasan takardun ya ci karo da ‘yar karamar jakar, ya daukota, kana ya mayar da takardun da ya dauke gurinsu, ya rufe dirowar. Dukkanin abubuwan da yake yi, yana yinsu ne a hankali kamar marar lafiya, ya koma ya zauna.

Jakar tana dauke ne da hotuna guda uku tare da wata takarda falle daya, mai dauke da rubutu gaba da baya.

Alhaji Hammad ya zube hotunan a kan dan teburin dake gabansa, ya zuba musu ido. Hotunansa ne dana matarsa Lajjanatu, sun yi matukar kyau hotunan. An dauke su ne a lokacin daurin aurensu a can kasar Masar.

Zuciyar shi da hankalin shi suka hadu wuri guda, suka shiga tunanin ainihin tsantsar rayuwar soyayyarsa da Lajja. Yadda suka kaunaci junansu da aurensu da dalilin rabuwarsu da kuma barinta kasarsu Masar.

Ya tuna yadda ya bar iyayensa da ‘yan uwansa da abokansa da kasarsa ta haihuwa, ya bazama neman Lajjanatu. Ya tuno ire-iren wahalhalun da ya sha wajen nemanta, da ire-iren wulakanci da tashi-fadin da ya sha. Duk da haka wadannan ba su fiye kona masa rai ba face yadda Lajjar ta nuna ba ta ma san shi ba, babu ruwanta da shi.

Zuciyarsa ta yi kuna, wutar soyayya ta ci gaba da ruruwa a ruhinsa. “Me ya sa Lajjanatu ta yi min haka?” Ya tambayi kansa.

Da alama ya yi nadamar zamowarsa halitta a wannan lokacin, kuma ya yi bakin cikin kasancewarsa dan adam. Ya zargi kansa da ya zamo mai amincewa soyayya, ya ji haushin kansa da ya yarda kuma ya sakankance da bukatar zuciyarsa. A karshe kuma ya sha alwashin kasancewa da matarsa ko da kuwa zai rasa ransa.

Kushewar Badi 2 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×