“Asiya bana son wasa kina son sanar da ni cewa wai wannan mutumin da ya fita a wacen ranar kina da alaƙa da shi ne?”
“Haka nake tunanin Dr sai dai shegen karambaninka ya ɓata komai. Wannan dogon bayanin na gargaɗeka da yi wa duk wani mai yunƙurin yin planing shi musamman mutanen karkara da basa bambance fari da baƙi.”
“Look Asiyah mene ne aibun abin da na yi, wannan shi ne ƙa’idar aiki fa yanzu idan wata matsalar ta taso da wa za su yi kuka. Idan kuma min riga da mun yi musu bayani ba shi ke nan an wuce wurin ba sai dai ka ɗora mutum kan shawara ko magani.”
“Hmmm! Allah ko? To wallahi ka ki ya ti ranar da director zai san abin da ka ke yi.”
Ta faɗa tana tarkata files ɗin gabanta. Zuciyrta na yi mata ƙunar ta ga samu ta ga rashi. Duk da ta san suɓucewar nasararta har da kiran da director ya yi mata amma ta yi takaici matuƙa. Tabbas duk inda wannan bawan Allah ya fito tsatsonsu ne, sai yanzu ma take takaicin me ya sa ba ta shamace shi ta yi masa hoto ba?
“Ko bayan raina ku saka a ranku ina da ɗan’uwa wanda wata ƙaddara ta shata mana layi tsakaninmu da shi…..”
Abin da mahaifin su ya sanar da su ke nan a wani meeting da suka gabatar na ƙashen shekara. Wayarta ce ta yi ƙara ta saka hannu na ɗaga,
“Aunty wallahi na gari. Samir dukana yake yi kamar jaka.”
“Sai dai haƙuri Fatima ai duk wanda ya sayi rariya ya san ɗole sai ta zubar da ruwa kuma wanda bai ji bari ba zai ji wowo. Ko da Samir ya fito gidan nagarta ai kinsan ɗabi’unsa kin san waye shi. Babu yadda ba ayi ki bar shi ba ki ka shafawa idanunki kwalin Audu. Yawo kuwa babu inda baku zaga ba na shan ice cream a garin nan ke kina ganin wayewa ce yanzu wa gari ya waya?
Ta furta tana mai jin tsananin ƙunar zuciya tare da jin zafin ‘yar uwarta ta wadda a baya ta mayar da ita abokiyar gabarta kawai saboda tana faɗa mata gaskiya.
“Aunty yanz…”
“Kin ga akwai abin da zan yi mai muhimmanci sai anjima kawai.”
Ta faɗa tare da katse kiran. Wani kuka mai cin rai Fatiman ta saki yayin da wata irin nadama ta baibayeta.
****
Maryam ta ajiye komai a gefe ta rungumi yaranta yadda ya kamata. Lokuta da dama idan Tasi ya dawo aiki musamman ranar Juma’a ya kan sanar da ita,
“Maryama Baba na gaishe dake. Sau tari idan ya sanar da ita hakan murmushi kawai take yi, ko kuma ta furta,
“Hmmm Abu Saubah ban da zolaya.”
Abin na ba ta mamaki tasan Babansu baya sakewa da mutane, bare kuma ace suruki wanda ya kasance ta ɓangarenta. Sai dai takan amsa tare da ajiyewa ranta cewar don kawai ya faranta mata ne yake aikata hakan. Sam ba ta san cewa wannan duhun na gidan su ya soma yayewa ba ta hanyar haziƙin miji irin nata.
Kwanci tashi babu wuya wurin ubangiji. Maryam tana zamanta lafiya. Tasi ya tsaya musu daidai gwargwado yana kamantawa. Mutum ne mai zuciya da neman na kansa.
Sai dai maganar dangi ne baya buƙata daga gareta abu ɗaya ta ta sani shi ɗin ya jiɓanci buzayen ƙasar nijar. Saboda yanayin hausarsa, haka kuma shigarsa da mu’amalarsa da shayi kodayaushe.
Sai sunan garinsu da ta riƙe shi ma hana rantsuwa a rubuce ta gani cikin littafin da yake yi wa ɓoyon amarya. Kuma tun daga ranar ya yi mata iyaka da ɗaukar littafin da ta gani a ciki. Tare da kakkausar murya ya yi mata kashedin matuƙar ta ƙara ɗaukar masa littafi a bakin auranta.
Lamarin ya yi matuƙar girgizata. Mutumin da ko faɗa ba ya yi mata, shi ne har da saka sharaɗi. Don haka tun daga ranar ta ɗorawa littafin karon tsana. Ko ga ta ga shi ya ajiye ba ta ko dubansa.
Domin ta lura da mugun ɓoyon da ya yi wa littafin wanda baya ɗauko shi sai ya je garin su ya dawo shi ma sai cikin dare sahu ya ɗauke. Don haka ta tattara ta watsar da lamarinsa ta rungumi rayuwar ƴaƴanta.
Duk yaran ya saka su a makaranta, Saubahn me shekaru bakwai sai su Madu masu shekara biyar da watanni. Akwai soyyaya da shaƙuwa tsakanin yaran. Ga su da wayau da shiga rai an ginasu kan ƙaunar junan su sosai. Ɗaya baya iya mallakar abu ba tare da ya mallakawa ɗan uwansa ba.
*****
Kwanci tashi asarar mai rai sai ga su Maryam sun zana jarrabawa kuma ta fito da sakamako mafi kyau fiye dana kowa. Don haka makaranta ta shirya taro na musamman tare da yi musu kyautuka ita da ire-irenta.
Taron da ya haɗa manyan mutane, a wurin ne maigarin ya miƙe bayan dogon jawabi ya nemi alfarmar Maryam da abokan karatunta kan su dage wurin ganin sun tafiyar da abin da suka smu ta hanyar da ya dace. Wato su zamo ɗaya daga cikin su na bayar da gudunmawa ga ƙananun makarantun primary na karkarar.
Ranar Maryam ta yi kukan farin ciki da na baƙin ciki, zuciyarta na kwaɗaita mata ina ma mahaifiyarta za ta zo ta ga yadda ta zamo. Walima sosai Tasi ya shirya mata ta gayyato ƙawayenta aka sha shagali.
Su Inna Sumaye ma sun zo, sai dai kamar su cinyeta don baƙin ciki. Hasalima ba su tsaya sun karɓi kayan da aka raba ba. Musamman yadda suka ga Maryam cikin shigar alfarma da ke ce raini. Haka kuma Tasi na ta nan, nan da ita duk inda ta saka ƙafa yana biye da ita gwanin ban sha’awa.
Da yamma suka shirya zuwa gidan mahaifinta, tana jin ba za ta taɓa raba farin cikin nan da iya na kewaye da ita ba hadda shi. Domin shi ɗin wani jigo ne na rayuwarta kuma ko babu komai zuciyarta na faɗa mata ya fi mahaifiyarta, tunda ya rayu tare da ita ko da kuwa babu kulawa. Wani sashi na zuciyarta kuma na tunatar da ita baƙin cikin da za ta kwaso amma tana dannewa.
Ba ta manta yadda Mama Sumayye ta haɗa mata gungun mata a gidan sunan ɗiyar Barira ba. Suna aibata ta suna faɗin karuwanci suke zuwa, kasancewar zawarawa sun fi yawa a makarantar ta su. Ranar ta yi kukan baƙin ciki sosai duk da ta zage ta mayar musu da martani. Kuma daga ranar ta yi wa kanta shamaki da duk wata sabga da ta san za su haɗu da matan gidan su.
Dai dai lokacin da ya sauketa kan mashin ɗinsa ta ɗaga kai tana kallon ƙofar gidan da take tantamar gidan da ta yi rayuwa ne. Sai dai tun kafin ta samu zarafin magana ta hango babban yayan su na shiga gidan. Dan haka ta amince nan ne, jiki a saɓule ta bi shi a baya suka shiga. Nan ta sake cika da mamaki.
An gyara gidan an shafe shi da suminti sosai an yi masa fenti. Daga ciki kuwa an gyara duk wani ɓagure-ɓaguren daya zama naƙasu a gidan. Bata ƙara cika da mamaki ba sai da ta ga yaran gidan tsaf da kayan makaranta. Wani lumshe idanu ta yi hawaye na kwaranyo mata, wannan sauyin take buri.
Wannan canjin take muradin gani cikin ahalinta. Ashe za ta gani kafin mutuwarta? Amma mene ne jigonsa? Ya aka yi hakan ta kasance? Maimakon rige-rigen ɗaukar talla yau yaran gidan su rige-rigen tafiya makaranta suke yi.
Ta rasa da wa za ta raba wannan farin cikin? Hannunta ta damƙe cikin na Tasi tana son gwada masa yanayin da take ciki. Karaf suka haɗa idanu da Mama Sumayye, ta ɗora hannu aka tare da kwatsa sallamami.
“Na shiga tara ni Sumayyatu me zan gani karuwanci da safiyar Allah?”
Kafin ka ce kwabo sauran matan gidan sun yi wa wajen tsinke. Duk sai ta muzanta. Ga hannunta cikin nasa ta kasa cirewa. Jikinta har wani rawa yake yi tsabar takaici da ɓacin rai. Ganin yanayin da take ciki ya sanya Tasi ƙara riƙeta sosai.
Ta cikin idanunsa take hangen ƙarfin guiwa da jajircewa dan haka tuni ta koma daidai bayan aro juriya ta yafa. Sum-sum matan suka bar wajen tana raka su da ido har suka shiga sashin da take da tabbacin sashin mahaifinta ne na da.
A haka suka ƙarasa, ta riski mahaifinta zaune kan tabarma, ga matansa zagaye da shi kowace tsaf da ita. Cike da sassarfa ta ƙarasa tare da zubewa ƙasa tana gaida shi. Ya amsa fuska a sake. Haka ma matan duk suka amsa mata idan ka ɗauke Mama Sumayye da ta amsa fuska a ɗaure. Motsi bakinta ya ke yi tana son magana amma kuma ta rasa me za ta ce, fahimtar yanayin da take ciki ya sa mahaifinta sakin murmushi.
Tun lokacin da ta shigo ya sauke idanunsa a kanta, sosai ta koma masa Khadija sak, wani takaicin hallayarsa ta baya ya dawo masa fil a ransa. Yadda ya maida mata rigar sawa ba dan haka ba da tuni yana tare da Khadijansa.
“Maryama ya aka yi ne bakinki akwai magana ko?”
Ta sake samun kanta cikin ruɗu, ashe akwai ranar da mahaifin su zai fahimci karatun kan fuskar su ba tare da bakunan su sun furta ba?
“Ba. Ban. Mu”
Ta yi furucin a rarrabe tamkar mai koyon magana ta ci gaba,
“Babanmu ka sauya gaba ɗaya ba ma kai ba duka gidan”
“Maryama ai sauyin ba daga ni bane, daga gareki yake”
Ya faɗa yana ajiye kallonsa a saitin Tasi da ya sunkuyar da kai. Ya cigaba,
“Allah Ya yi miki albarka ya kuma albarkaci rayuwarki Maryam. Allah Ya kawo haske cikin rayuwata amma ke ce sila domin mijinki shi ya yi wannan jihadin.”
Ya sauke idanunsa a kan matansa da suka bi shi da kallo baki buɗe. Tun wata guda da sauyin da aka samu a gidan suke bibbinin san sanin mene ne ya kawo sauyin amma kuma ba su sami amsar hakan ba. Sai a yau da ya furta a gaban su. Zuciyoyin su cike da mamaki wasu kuma cike da kƴashin abin da yake furtawa aka ɗiyar ta shi.
“Silarki aka samu sauyi Maryam. Kullum maigidanki cikin yi min nasiha yake duk da ina hantararsa, ban taɓa tunanin abin da nake yi wa iyalina ya yi tsamari ba sai da na sami ƴaƴana na cikina na shawarar yadda za su kashe ni su ci dukiyata. Na yi nadama na yi kuka ba tare da sanin kowa ba, tun daga lokacin na soma tunanin kawo sauyi cikin ahalina.
Mijinki shi ya tallafi min da komai, yanzu haka duk wasu hidindinmuna na gonakina shi ya ke kula da su kuma masha Allahu. Domin dai kwaliya ta biya kuɗin sabulu ni kaina yanzu nafi jin daɗin kaina da kuma rayuwata. Ƴaƴana na mutuntani haka ma matana. Insha Allahu bana ma da ni za aje aikin hajji ban ga amfanin tara dukiyar da ba a cinta ba.”
Mama Sumaye ta ƙara cika da takaici, domin tana ganin yaranta su ne suka cancanci karɓar ragamar gidan amma arasa abin ɗorawa sai wanda ba asan asalinsa ba. Kuma mijin Maryam lallai dole ta ɗauki mataki.
Fuu! Ta tashi tana ƙunƙuni ta bar wajen duk suka bita da idanu. Anan Maryam ta gabatarwa da mahaifinta ƙudurin mijinta na maida ita makaranta. Albarka ya sanya musu sosai tare da fatan alkhairi. Ya kuma ba ta tabbacin labarin abin da ya faru a wurin taro ya zo masa tare da sake ƙarfafa mata guiwa.
Da za su tafi ya sa aka rako su da ƙwaryar ƙwan zabbi dana kaji, haka ta koma gida cike da nishaɗi. Babu mai iya fasalta farin cikin da ta sami kanta a lokacin. Sauyi dai ya tabbata sosai a gidan su sai dai kuma kash sauyin shi ne ya zamo sillar ƙalubalan rayuwarta. Sauyin da ya dasa mata tabon da ya gaza goguwa a duniyarta. Har gobe kuma shi ne sauyin da yake tayar mata da mikin tabbunan da ya yi mata cikin tsokar dake tsakanin a wazunta.
*****
Kwanci tashi babu wuya wurin ubangiji. Tun daga lokacin ya kasance duk sati sai an kawo mata ƙwaryar ƙwan zabbi da na kaji. Sai kuma yankakiyar kaza da zabuwa da agwagwa ɗaya. Saƙo ne daga mahaifinta zuwa gareta. Ba ma ita kaɗai ba, duk wata ɗiya da ya aurar haka ake kai mata wannan ƙwarya. Sai dai ta Maryam ta fi girma.
Gonarsa da ake noman kayan lambu kuwa duk ƙarshen wata ana kawo mata kayan gwari kwando-kwando. Sosai Maryam take jin daɗin abin da ya ke faruwa. Ta rasa da wane baki za ta godewa Tasi. Shi ya sa dare da rana ba ta da abin yi sai yi masa addu’ar ubangiji ya yaye duhun da ya gewaye rayuwarsa.
Cikin ikon Allah takardunta suka fito da kyau. Tasi ya fi kowa murna da kansa ya taka ya kai wa mahifinta ya sanya musu albarka. A lokacin saura sati biyu tafiyarsa. Sosai ya yi musu nasiha tare da ƙarfafa musu guiwa kan zumunci. Ya nuna wa Maryam duk abin da ake yi mata ya sani. A nan ya sako zancen mahaifiyarta wanda take a wajen ta sauya fuska. Murmushi ya yi irin na manya a fili ya furta,
“Maryama ni na san abin da baki sani ba, duk runtsi ki nemi mahaifiyarki ba shawara ba ce umarni ne.”
Daga nan ya ɗauko kundinsa na duk wata dukiya ya miƙawa Tasi. Muryarsa a raunane ya soma magana,
“Ba mu da masaniya kan yadda rayuwa za ta kasance, amma duk runtsi naɓsan cewar za ka yi dubi a yayinda ƙasa ta rufe idanuna. Ina ji ajikina kamar na kai wani mataki amma ba mu da tabbaci. Wannan kundin duk wata dukiya ta ce, ka zamo katanga ga ahalina don Allah! Ku tashi ku je Allah ya yi muku albarka. Maryam duk lokacin da kika haɗu da Khadija ki nemamun afuwarta.”
Kuka ne ya ci ƙarfin Maryam amma ya hanata magana, ta juya a raunane tana hango wani rauni a idanun mahafinta da ba ta taɓa gani ba amma be ba ta damar magana ba. Suna fitowa suka yi kiciɓus da Baba Sumayye ta yi ƙwafa tare da wurga musu kallon zamu haɗu da ku ne.
Haka suka nufi gida jiki a saɓule. Cikin satin gaba ɗaya Maryam ta sare tun Tasi na lallashi har ya soma faɗa. A haka mahaifinta ya tafi ƙasa mai tsarki. Tafiyar da ta zamo sillar rugujewar gobanta.
Tun bayan tafiyarsa sau ɗaya tak ta je gida. Shi ma zuwan na da nasaba da duba halin da su Saudatu suke, musamman yanzu da ta yi uwa ta yi makarɓiya ta dage suka shiga makaranta. Don haka take zaga su akai akai domin tabbatar da suna zuwa ɗin.
Sai dai zuwan be yi mata daɗi ba. Mama Sumaye ta sa yara suka yi mata ruwan duwatsu, ranar ta ga ɓacin ran Tasi rigima har gaban mai gari domin ya rantse sai ya ƙwatar mata ‘yanci. Lamarin da ya zamo abin tsegumi cikin gari na cewar har yaushe aka yi mata auren da za ta dinga yin fito na fito da matar mahaifinta. Matar da ta raine ta.
Assalamu alaikum