Skip to content
Part 12 of 23 in the Series Kuskuren Wasu by Sanah Matazu

Komawarta gida bai haifar da komai ba, domin abinci ma sai ya soma gagararta. Rayuwar tala da ta tsana tun ƙuruciyarta ita ce rayuwar da yaranta suka durfafa ka’in da na’in. Wata rana sai sun je talla sun dawo sannan su samu abin da za su kai bakin salati. Tana ji tana gani ta haƙura da karatun su, saboda kafin su siyar su dawo an ci rabin karatu ko kuma an ma tashi.

Su za su fita da rogo da ƙuli idan sun saido da su take amfani wurin hidimar mahaifinta na abin da ya danganci omo da sauran kayan buƙatu. Duk yaunƙurinta na akai shi asibiti sun gagara fahimtarta. Mama Sumaye da yaranta kuwa duniya sabuwa karan su suke ci ba tare da babbaka ba.

A haka lokaci ya ja. Mahaifinta ya kawashi shekara ɗaya da rabi a kwance. Wanda ya yi daidai da shakarun shuɗewar numfashin mijinta. Ya kuma yi daidai da shuɗewar duk wasu buruka na cikar muradan rayuwarta. Cikin zuciya da ruhinta tana jin yadda kowane buri yake ɗaiɗaicewa a saiɓance ba tare da ta yi wani ƙwaƙwaran motsin da zai tabbatar da cikarsa ba.

Tun tana kuka har ya kasance zuciyarta ta ƙeƙashe, da hannu suke hira da mahaifinta wasu lokutan, domin hannunsa na dama yana motsawa da taimakon addu’ar da take tofa masa. Haka kuma ta kan jingina shi a bango idan ya ga ji da kwanciyar. Murmushi shi ne abin da ya ka iya sadaukar mata da shi a duk lokacin da ta yi mas wata hidima.
Wani babban tashin hankalin da ya baibayeta kuma shi ne, yadda aka soma bibiyar shigo mata ɗaki cikin dare domin wata mummunar manufa da ta fahimta. Hankalinta ba ƙaramin tashi ya yi ba, ranar farko da hakan ya auku kusan kwana da yini ta yi tana kuka. Babu yadda Saubahn bai yi ba ta sanar da shi abin da yake faruwa amma taƙi tilas ya haƙura.

Wannan barazanar ce ta sanyata rama farat ɗaya ta fita hayyacinta. Bacci ya ƙauracewa idanunta hakan ya sanya ta soma fama da ciwon kai mai tsanani da kuma yawan tunanin. Idan kuwa tana zaune ita kaɗai sai ta yi ta surutu, cikin ƙanƙanin lokaci damuwa ta soma yi mata yawa. Idan kanta yana ciwo har ba ta gani saboda har ƙeyarta yake zagayawa. Tsoro ya soma kamata, tana ganin wautar zuciyarta da ta gaabeta da abin da take da tabbacin sai iya yin sanadin numfashinta.

Yaranta kan su sun kasa tantance ainihin abin da yake damunta, ana hakan wata rana da daddare kimanin ƙarfe ɗaya da rabi. Bayan ta gyara mahaifinta ta Abdallah da Ahmad ne ke kusa da shi ita kuma tana gefe a kwance.

Saubahn kuwa da ma sarkin jin zafi ne a ƙofar ɗakin yake kwanciya. Gyangyaɗi take yi, barci take ji sosai amma kuma tunani ya hanata kwanciyar sannu a hanakali har barci ɓarawo ya saceta.
Cikin barcinta ta soma cin ana taɓata, gabanta ya yanke ya faɗi, ta juya sai ta ji an rufe mata baki kamar an ɗaure shi da wani abu tsuma ko kuma ɗanƙwali. Wasu hawaye ne masu zafi hannu ta kai domin ba wa kanta kariya, sai dai ji ta yi an ɓallaƙa hannunta baya har sai da ya yi ƙara. Lamarin da ya sakata sakin ƙarar wahala ke nan. Ƙafarta ta daki wata silver da take damawa mahaifinta fura. Hakan ya sanya silver ɗin ta yi ƙarar da ta farkar da Abdallah.

Saubahn ya yi tsaye, hannuwansa a harɗe a ƙirjinsa. Zuciyarsa babu abin da take yi ban da tafasa. Zuwa yanzu ya gama fahimtar ƙuncin mahaifiyarsa na kwanakin da suka shuɗe. Tabbas sai ya nunawa kowa ye kuransa. Don haka sam bai kula da farkarwa Abdallah ba kasancewar akwai duhu. Jiyawa ya yi ya ɗauko gorar da yake ta ajiye da ita tsawon lokaci ba tare da sanin me zai yi da ita ba ashe amfaninta na zuwa.

Yana sawo kai ɗakin ana kawo wutar nepa. Hakan ya sanya ya ga Abdallah a tsaye wanda shi kuma idanunsa suka sauka kan Mamma hannun wani ƙato yana kiciyar ɗaure mata hannu. Shi ƙoƙarinsa ya gani, ban da ƙarfin hali mace a ɗaki cikin ‘ya’yanta kana neman tozartata. Wani kukan kura ya yi ya nufi kansa, sai dai kafin ya ƙarasa Saubahn ya isa kansa ya sauke masa gora a ƙoƙon gwiwarsa. Ya yi haka ne domin hanashi tsira daga hannunsu babu damar guduwa.

Daidai lokacin Ahmad ya farka, ganin su cirko-cirko ga Mamma na kuka ya bashi tabbacin ba ƙalau ba. Hannu Abdallah ya sanya yana ƙoƙarin cire abin da ya rufe fuskarsa da shi amma yana ƙoƙarin hana afukuwar hakan.

“Ku ƙyale shi Abdallah ni dai ya yi niyyar zortawa kuma ubangiji bai ba shi nasara ba bana buƙatar ganin ko waye?”

“Haba Mamma mana, ki bari mu kili ɗan akuya.”

Madu ya furta da sai yanzu ya fuskanci komai. Hannu ya dunƙuƙe ya naushi mutumin a fuska hakan ya ba da damar cirewar abin da ya rufe fuska da shi. Take fuskar Nuhu ta bayyana cikin ƙwan lantarki. Gaba ɗaya suka zuba masa idanu cike da mamaki, ban da Saubahn da shi da ma shi ne mutumin da zuciyarsa ta ba shi zai aikata hakan.

Hamɓare shi Abdallah ya yi da ƙafa kamar ya samu tamola. Ya yi mursisi kamar ya ba shi ba. Sai raba idanu yake yi.

“Zo ka fita kafin na yi ajalinka”

Saubahn ya furta cikin tafasar zuciya,

“Ya je ina Yah Saubahn kana ganin fa abin da ya aikata.”

“Na gani na kuma ce ya zo ya fita, ai dai mun fuskanci waye mai harin nan gaba duk abin da muka gani kwatankwacin hakan sai mu yi wa mutum sabuwar kaciya.”

Cikin jan jiki Nuhu ya fice babu kunya. Mahaifinta da tun ƙarar farko ya farka ya lumshe idanu hawaye na zubar masa. A zuciyarsa yana jin kamar shi ne silar jarrabawarta. Ita ma hawayen ta share tana raka Nuhu da idanu yana jan ƙafa da ƙyar har ya fita sai dai ta jinjinawa Saubahn da har ya iya karantar abin da yake cikin zuciyarta.

“Yah Saubahn baka kyauta mana ba.”

Madu ya furta yana hura hanci.

“Ba za ku fahimta ba, ku ƙyale shi Madu hakan ne mafita. Da niyya aka yi, niyya kuma ta tozarci matuƙar zancen nan ya fita ba mu da mafita ya samu hanyar tozarta mahaifiyarmu. Ku fahimci hujja ta.”

Kai suka gyaɗa masa, sai dai tun daga lokacin gaba mai tsanani ta ƙulu tsakanin Madu da Nuhu har ta so kere takun saƙar su da Saubahn.

Washegari haka suka tashi duk wanda ya ga Nuhu ya tambaye shi sai ya ce haɗari ya yi mai mashin ya bige shi. Kafin la’asar ƙafa ta kumbure ba ya iya zuwa ko’ina. Mama Sumaye ce ta je ta kira mai gyara har gida aka samu matasa suka danne shi. Ciki kuwa har da Madu ya fi kowa maƙure masa wuya, faɗi yake,

“Ƙuda wurin kwaɗayi yake mutuwa, bi sannu dai mai gyara murɗata da kyau ta koma dai-dai.”

Nuhu da ya san manufarsa ji yake kamar ya shaƙe shi ya mutu, sai dai ba damar ya nuna wani abu ko kaɗan da zai tona asirinsa.

*****
Haka aka cigaba da takun saƙa tsakanin su da shi, sai dai har gobe mummunar manufarsa na kanta. Wasu lokutan sai tana shanya sai faki idon mutane ya daketa a mazaunai. Ko ya leƙata a banɗaki. Baƙin cikin ya yi mata yawa. Zuwa lokacin ji take ba domin mahaifinta ba za ta iya haƙura da komai su bar Malumfashi.

Duk da tana ƙoƙarin ɓoye wasu lamuran tana snae akwai abin da Saubahn yake ankare da su kawai magana ne ba ya yi. Wata ranar Asabar da safe, bayan su Madu sun ɗauki fanke sun fita, Saubahn na gefenta yana ta ya ta wankin mahaifinta. Yayin da Madu da Abdallah suke a gefe suna aikin ɓare rogon da za ta dafa musu su fita da shi. Kamar an jeho shi ya faɗo gidan babu ko sallama.

Ba kowa ba ne face Nuhu. Ta lura da kusan hakan ya mayar da shi al’adarsa sai ya daidaici tana aiki sai ya soma sukuruftu a tsakar gida kamar mazurun da ya ga budurwar kyanwa. Gabanta ya faɗi wani lokacin har mamaki take yadda take riskar kanta a komar tsoronsa cikin kwanaki wani irin kwarjini yake yi mata.

Da sauri ta gyara rigarta kasancewar mai babban wuya ce kuma a sunkuye take, gaida shi ta yi ya amsa yana lasar leɓe kamar wani maye. Saubahn na ankare da shi kuma ya zo wuya. Tun ba yau ba ya ƙula masa saboda duk lokacin da zai haɗu da su sai ya goranta musu rashin asali.

“Ke kuma haka za ki ƙare ba za ki samu wani ya rufa miki asiri ba da ƙuruciyarki da komai.”

“Ka ganta nan dai, yo waya san abin da ke aukuwa cikin sunƙuru tunda ta saka ya kore matan ɗaya bayan ɗaya.”

Mama Sumaye ta furta tana dariya ƙasa-ƙasa. Kamar gunki haka ta ƙame domin kalaman sun shigeta, sai dai bata san su fahimci rauninta. Ba ta yi aune ba ta hango Saubahn ya sungumi wani ƙaton faskare ya tunkari Nuhu ana rirriƙe shi.

“Da ma idan ba ka yi haka ba, ai ba zaka nunawa duniya cewa kai ɗin ɗan mara asali ba ne.”

“Duk rashin asalinmu ai ba ma tare ‘ya’yan mutane a lungu muna taɓa su.”

Saubahn ya furta da ƙarfi yana ƙwacewa daga riƙon da Lanto ta yi masa. Ai kuwa Nuhu ya shaƙa domin kwana uku ke nan da fitowasa an kamashi yana shirin haikewa wata ƙaramar yarinya. Kuma su Saubahn ɗin ne suka tona shi domin sun ga lokacin da ya ja hannunta. Nan fa ya hau zage-zage yana aibata Maryam da mahaifiyarta.

Allaha Ya ba Saubahn sa’a ya ƙwace daga hannun matan ya ɗauki dutse ji ka ke ƙwal ya samu goshinsa. Take jini ya wanke masa fuska mata suka hau sallalami.

“La’ananiya kina gani ɗanki yana yi min illa ko?”

Tamkar dutse haka ta mayar da shi domin ba ta tanka masa ba, ganin ya hau mata ɗa duka ta taso babu kunya ta ingije shi da duk wani ƙarfinta ta ɗauke ɗanta.

“Ba dai saboda mahaifiyarka ka yi mini haka ba. A gaban idanunka sai na mayar da ita baiwa mafi ƙasƙanci sai kun girbi shukar da ku ka yi mu zuba ni da ku.”

“Ka yi ka gama.”

Saubahn ya ba shi amsa a ƙufule.

“Ɗan Bazawara karuwar gida” Ya faɗa cike da haushi.

“Ita kuma ake nema kamar a mutu amma kuma ta gagara samuwa.”

Saubahn ya ba shi amsa kamar ba shi ya yi furucin ba. Daga Nuhu har Maryam ya ba su mamaki. A ɓangarenta kuwa sam abin da Nuhun ya furta bai wani dameta ba.

Kalmar ta zame mata jiki. Sam bata ɓata mata rai saboda ba yau ne karon farko da ta soma jin hakan ba. Tun bayan wata ɗaya da rasuwar Tasi aka soma yi mata tururuwa sai dai yaranta da mahaifinta su ne kaɗai a gabanta.

Ganin taƙi bayar da fuska ne da yawa suka sarara mata. Kallon Saubahn ta yi kallom gargaɗi. Tana jin sanda Nuhu ya yi ƙwafa ya wuce. Ta raka shi da idanu zuciyarta na bugawa. Tsoro take ji matuƙa, ta ga lokacin da ya kaɗa kai kamar marayan ɗa ta ya wuce ciki. Ta raka shi da ido, ta dawo da idanunta kan Saubahn,

“Ka yi da kowa amma ban yarda sa’insa ta haɗaka da duk wani ahali na Mama Sumayye ba, zan iya komai domin zama katanga wa rayuwarku amma ba zan juri rasa ku ba ka riƙe wannan Saubahn.”

Kai ya jinjina, ranar haka ta yini sukuku da ita. Wani tsoro ne yake zagayata tana jin kamar wani abu na ƙoƙarin yi ma ta shamaki da farin cikin da ya yi mata kantaga. Haka ya fita yana bambami. Ita kuma ta ja Saubahn ɗaki tana yi masa faɗa,
“Saubahn da me ka ke so na ji? Haka ka ke so na yi ta kuka ko?”
“Ki yi haƙuri Mamma amma babu wanda zai zage ki ina kallo wallahi sai inda ƙarfina ya ƙare”
Tun daga wannan lokacin gaba mai tsanani ta ƙulu tsakanin yaranta da Nuhu. Saubahn kuwa haɗuwa goma sai ya zage shi da mahaifiyarsa shi kuma sai ya yi masa ruwan duwatsu tamkar wasu sa’ani.
***
“Sumaye amma dai kin sani sarai ni bana jira, kina ganin wancan ƙaramin ƙwaron ma da zai kawo mana tasgaro yadda na kawar da shi bare kuma wannan da ya rage mana aiki. Wai me kike jira, me kuma ki ke tsoro ne?”

“Nuhu ba fa tsoro bane, ni na iya allona ne, shi ya sa sai na biya ma haddace na wanke ba tare da kowa ya fahimci yaushe aka saka babbaƙun ba, kai dai ka bi abin da na ce. Ita kanta uwar gayyar ƙiris…..”

Da sauri Maryam ta yi baya, sai dai ta makara ta ganta. Allah Ya sani wani abu daban ya kawo ta wurin ba wai laɓe ba, sai dai zantukan ne take ji kamar sun shafeta, tana son ɗaga duga-duganta ta bar wurin amma kuma zuciyarta ta ƙi ba ta wannan damar har mai afkuwa ta afku. Sai dai ga mamakinta babu wanda ya tankata a cikin su haka ta ja ƙafafunta da suka yi mata nauyi ta bar wurin, zantukan su take haɗawa amma kuma ta kasa yi musu fashin baƙin da za ta fahimta tilas ta haƙura.

*****
Kamar ƙiftawar idanu ta ga wulgawar mutum da matsanancin gudu, ya fita a ɗakin. Idanu ta muttsuttsuka, saboda duhun dare sai dai kuma zuciyarta ta shiga faɗa mata gizo ne kawai. Ɗakin mahaifin nata ta nufa bayan ta jiye butar hannunta. Gabanta na tsananta faɗuwa, sai dai tun daga bakin ƙofa jikinta ya soma sanyi sakammakon ganin komai a hargitse. Tana ƙarasawa ta hango kansa can ya yi gefe ɗaya. Da sassarfa ta ƙarasa. Daidai lokacin Saubahn ya shigo ɗakin,

“Saubahn ka ga Baba?”

Da rashin fahimta yake kallonta, domin bai fahimci abin da take magana akai ba.

“Kamar fa ba ya numfashi…”

Da hanzari ya ƙarasa, zuciyarsa na dokawa, burkitoshi ya yi sai ga wuyansa a karye sai ɗan jini da ya fita ta gefen hancinsa. Hannunsa kuma dafe da zuciyarsa, ido ya zaro yana kallonta,

“Mammah, waye ya shigo ina ki ka je?”

Tambayoyin sun ɗaure kanta,

“Saubanhn ban sani ba, na shiga kewaye ne zan yi alwala ina fitowa na ga kamar mutum ya fita…”

Gabansa ya doka, da ya tuna wanda ya yi karo da shi da zai shigo ya fita yana haki da alamun rashin gaskiya, a hankali laɓɓansa suka motsa,

“Nuhu Mammah…”

Zuciyarta ce ta yi tsale kamar za ta faso daga ƙirjinta, wanda ya yi daidai da haskowar fitila cikin ɗakin mai tsanin haske,

“Yauwa kun ga ni ba, ga shi nan uwa da ɗa sun haɗu sun kashe shi ni dama wannan jinyar ta munafunci na san ba banza ba. Mace yarinya da ita ga manema burjik amma ace ta tabe a jinya. Lallai a rina an saci zanin mahauciya.”

Idanu a furgice take kallon su, yayunta ne maza su takwas zagaye da ɗakin sai kuma Nuhu da Mama Sumayye. Lallai wannan ita ce baƙar ƙaddara mafi muni da za ta ƙarar a rayuwarta…

‘Sharin kisa, kisan ma kuma na mahaifinta’

<< Kuskuren Wasu 11Kuskuren Wasu 13 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×