Idan matan suka riƙa shan ruwa sosai, to hakan yana ɗauke musu zarnin fitsarin. Haka kuma idan ba su ɗaukar abu mai nauyi to za su samu waraka cikin yardar Allah. Sai kuma muhimmin abu shi ne kula da kansu wajen tsabta.
Dokta Abdallah ya ce idan mace ta warke daga yoyon fitsari za ta iya ci gaba da haihuwarta ba tare da matsala ba. Sai dai kuma bisa shawarwari da suka zanta da abokan aikinsa ya ce,
“Akwai buƙatar gwamnati da hukumomi su yi abin da ya dace wajen kyautata harkar haihuwa ga mata.
Akwai buƙatar mai juna biyu ta samu kulawar da take buƙata tun daga lokacin da ta dauki ciki har zuwa haihuwarta. A samu asibiti a kusa a wadata asibitin da duk kayan aikin da ake buƙata.
Haka idan buƙatar zuwa wani asibiti ta taso ya zama akwai mota da ke jira ta ɗauki marasa lafiya. Shi ma asibitin da za a je a tabbatar komai akwai a kasa tun daga kan likitoci har zuwa kayan aiki da sauransu.Idan ba a samar da kyakkyawan yanayin haihuwa ga mai juna biyu ba, to za a ci gaba da samun karuwar wannan cuta a tsakanin matanmu, tunda dai ba a daina haihuwa ba.
Shirin ne ya katse, wanda ya yi daidai da katsewar duk wata laka ta Maryam. Zuciyarta ta dinga wani irin dokawa, ke nan matsalar da take damunta ke nan amma ba ta fuskanta ba? Haka ta yini sukuku da ita.
Lokacin da Nuhu ya dawo dare ya tsala sosai, domin sai da ya tsaya wurin masu karta ya buga a bar sa. Kasancewa ta yi masa daɗi da damin kuɗin da ya lallo a caca sai ya shigo yana walwala da komai. Wannan walwalar da ta gani kan fuskarsa ya sanya ta tunkareshi da batun matsalarta.
Ranar ta gwamace kiɗa da karatu, domin a cikin wannan daren sai da ya yi mata tijarar da ta tashi kaf mutanen gidan tare da barbaɗar da abin da yake damunta. Nan da nan kuwa aka shiga tsegumi masu tausayi na yi masu dariya na yi.
Washegri haka ta tashi ranta sam babu daɗi, Saubhn da ta lura ya fita daga gidan tun asub hakan ya taɓa zuciyarta ta dinga zuba idanu ta ga ta inda zai shigo amma kuma ko ƙyalins ba ta gani ba.
Haka ta yini zungur lokaci zuwa lokaci tana share hawaye. Zuciyarta na yi mata zafi sosai. A haka ta kasance har zuwa ƙarfe huɗu da Saubahn y shigo hannunsa riƙe d leda mai sanda guda biyu. Kowace cike take taf, matan gidan suna zaune ana hira jefi-jefi kuma kan maganarta ne. Tana daga ƙofar ɗakinta tana jin su. Gaba ɗaya suka raka Saubahn ɗin da idanu, ledojin hannunsa kawai suke kallo.
Dankalin hausa ne manya shaƙe a ledar farko, sai ta biyun mai ne da ƙuli da barkono da kuma maggi sai masara mai zafi gassashiya. Ɗakin ya shiga suka rakashi da namujiya suna gulma. A zaune ya sameta ta tanƙwashe ƙafafu da alama shi take jira domin yana shigowa ta shige cikin ɗakin.
Zama ya yi tare da tanƙwashe ƙafafu ya kwance kayan. Wata baƙar leda ya ɗauko ya kwance mata ƙulin nama da bai taka kara ya karya ba. Naman ta zubawa ido wani abu na tasowa a ƙirjinta. Rabonta da ta sa nama a bakinta har ta manta. Wani miyau ta haɗiya muƙut,
“Bana ci! Daga ina kake?”
Karyar da wuya ya yi,
“Duk ind zan shiga duk inda zan je ki tabbatar albarki na tare da ni. Duk kuma halin da zan shiga ba zan kaucewa tarbiyarki da umarnin ubangiji ba sai dai ƙarfin ƙaddara. Don haka ki ci kin mai tabbatarwa da kanki cewar ɗan ki halali ya nema kuma shi ya kawo miki. Kamar yadda ku ka ci da ni da kuma tufatar da ni da halal.”
Gaba ɗaya ya gama kashe mata jiki, don haka ba musu ta ɗauki nama ɗaya ta tauna, zaƙinsa ya gauraya kowace kafa ta bakinta. Lalai ta gamsu ta yi kewar tauna nama. Tana ci yana kallonta yana murmushi har ta kammala ya kawo mata ruwa ta sha. Hannu ya sanya a aljihu ya fito da kuɗi ‘yan ɗari biyar ne guda goma. Miƙa mata ya yi, idanu ta zaro,
“Ina kuma ka samo wannan?”
“Aikin kwasar tifar yashi muka yi guda biyu, shi ya sa ki ka ga na fita tun asuba. Na so ace su Madu na saka makaranta tun da nawa karatun ya soma nisa. Amma hakan ba zai samu ba”
Ƙwala ya share,
“Don Allah Mammah ki je asibiti don Allah!”
Ya faɗa yana roƙonta,
“Akwai aikin da za mu yi nan kusa sai a saka su makarantar amma lafiyarki ta fi mana komai”
Wani kuka ne ya taho mata kawai sai ta rungume Saubahn tana shassheƙa.
“Ba sai ka roƙe ni ba zan je Saubahn.”
Adakarta ta ɗaga ta saka kuɗin tare da ƙudurce ranar Littinin za ta hau mota ta shiga cikin garin Katsina, daga nan ta wuce babban asibitinsu. Ras! Gabanta ya faɗi zuciyarta ta yi wani irin dokawa yayin da wata zuciyar ta tuna mta da fuskar Dr Asiya. Nan take zuciyarta ta shiga kai komo ta kasa tantance me ya kamata ta yi.
*****
Haka ta ci gaba da haƙuri da jurar duk wata baƙar magana daga Nuhu. Shawarwarin da ta ji a rediyo kuma ta cigab da amfani da su har zuwa ranar littinin ɗin da za je asibiti.
Ranar kuwa kuɗi suka ce ɗaukarmu in da ki ka ganmu, ƙasa da sama ta gama dubanta ba ta gansu ba, kawai sai ta sanya kuka domin tasan Nuhu ne zai ɗauke su.
Tashin hankalinta shi ne yadda Saubahn ya damu da zuwa asibitin har wata rama ya yi. Ga shi kuma matsalarta ƙara gaba take domin tana tsaye sai dai ta ga fitsari na bin ƙafafunta. Ta yi kukan da bata taɓa yin irinsa ba. Sai kuma ranar ta ƙara tsanar Nuhu tsana mafi muni da takaici.
Ranar kuka ta yini tana yi, duk wurin da take tunanin samun rance ta je amma abu ya faskara. Haka ta haƙura sai dai gaba ɗaya ranar ba ta da walwala. Saubahn da ya dawo ba ta ɓoye masa ba. Bai ce komai ba amma dai ta san ya shaƙa. Domin ta ga hakan a ƙwayar idanunsa.
Haka ta haƙura suka rungume hannu suna zaman jiran tsamanin warrabuka. Bayan sati biyu da ƙyar da siɗin goshi Saubahn ya sake bata wasu kuɗin sai dai su ɗin ma tun a daren aka ɗaukesu. Lamarin da ya ɓata ranta matuƙa.
Take kuma jin bai kamata ya sani ba. Sau biyu yana ba ta kuɗin zuwa asibitin wanda yake tarawa da guminsa da tsantasar wahala ana ɗaukewa. Don haka kai tsaye ta yanke za ta takawa lamarin burki. Don haka ranar har ɗaya na dare bata kwanta ba tana jiransa. Tana nan zaune ya dawo, ba ta damu da yanayin fuskarsa ba. Kai tsaye ta tunkareshi,
“Nuhu ina kuɗina da ka ɗauka?”
Da farko ta ba shi mamaki domin bai zaton za ta iya tanka masa ba, don haka ya sha mur tare da furta,
“Me ne?”
“Kuɗina da Saubahn ya ba ni har sau biyu da ka ɗauka, kuma ina sane da kai ba su ne farau ba duk lokacin dana ajiye kuɗi sai na ga saɓanin hakan.”
“Kuma aka ce miki ni ne ɓarawon tunda ni kaɗai ne a ɗakin ko? Su waɗancan balagaggun ‘ya’yan naki sahabai ne da ba za su ɗauka ba?”
“Da su ne su ke ɗauka ma ba za ka ji labari ba, su da suka bayar kuma idon sun dawo sun ɗauka me za su yi da su?”
“A taƙaice dai kina so ki ce da ni ɓarawo ko.”
“Babu laifi idan na kiraka hakan, saboda ɗauka ka yi ba sadaka ba…”
Ɗauketa ya yi da mari sannan ya shiga dukanta kamar ya samu jaka. Tun tana ƙoƙarin karewa har ya zama ta kasa kataɓus sai da ya yi mata lis. Kuma hakan bai hanshi neman buƙatarsa ba ya tsallake ya barta tana gwamma numfashi.
Hawaye ne wani kan wani yake silalo mata. Ba yau ya saba tozartata ba sai dai ba ta yi tsamanin zai mata irin wannan dukan ba. Da ƙyar ta rarrafa ta koma kusa da Afnan da ta farke take kuka ta ɗauketa.
“Allah na yafe masa, ubangiji kadda ka jarrabaci wannan yaran nasa da maza masu irin ɗabi’arsa. Kadda ka hukunta su da laifin son zuciyar mahaifin su.”
Ta furta tana rungume da su a ƙirjinta. Washegari haka ta tashi jiki ya yi tsami. Idanu duk a kumbure. Saubahn da ya yi mata batun tafiya asibiti ta ce ya barta sai wani satin. Zuwa lokacin ta samu ta haɗa ko da rabin kuɗin ne da ɗan surfen da take yi. Ƙwafa kawai ya yi domin ya fahimci akwai abin da ta ɓoye masa. Don haka ya ƙyaleta.
Duk yadda ta so haɗa kuɗin nan sun gagara har sati ya zagayo ya sake zagayowa. Ga ciwo na ƙara gaba ta rasa yadda za ta yi. Ga shi gari ya ɗauka har ba a jin kunyar sakar mata baƙar magana a gabanta. Wasu lokutan sai dai ta shiga ɗaki ta yi kuka.
Saubhan haka ya dage ya sake haɗa wasu kuɗin ba tare da ya yi shawara da ita b. Daga ƙarshe da ya gaji da rayuwar da suke yi ne kawai sai ji ta yi ya ce,
“Mammah ki shirya gobe za mu bi Bala driver a motarsa za ki Katsina ganin likita!”
Ba ta yi mamaki ba, saboda tana hango tsanar yanayin da take ciki da yake yi, domin hata da kayan da take siyarwa sai da aka daina siya. Saboda gida-gida Mama Sumaye ta bi tana yaɗa ciwon da yake tattare da ita.
Da ma ƙosai da fanke da kuma awara take yi da safe. Da rana ɗanwake da dare kuma ta yi tuwo da wainar gero banɗasho da ƙuli. Sosai take ciniki amma lokaci ɗaya wannan cinikin ya tsaya. Hakan ba ƙaramin naƙasu ya kawo musu ba, wanda tilas tana ji tana gani Saubanhn ya kama dakon da ba ta ƙauna a cikin tasha.
Don haka ba ta yi musu ba. Saboda tafi shi jin takaicin rayuwar da suke fuskanta. Washegari suka ɗauki hanyar zuwa asibiti cike da tunanin abin da za su riska.
Kasancewar sun yi safko, ba su sha wata wahala ba suka isa da wuri. Bayan bin dogon layin amsar kati suka zauna jiran likita. Mata ne burjik ire-irenta masu lalurar wasu an basu gado wasu kuma an ɗora su kan magani ne sun dawo.
Sai a lokacin Maryam ta sake godewa ubangiji, ta kuma tabbatar a cikin ni’imarsa take. Domin ita a sanadin haihuwa ne ta kamu da lalurar, amma saura da ta gani da yawansu ƙananun yara ne da suke ɗauke da lalurar a sanadin fyaɗe da aka yi musu. Wasun su ma har da haɗuwa da ciwon HIV ta tausayawa iyayansu sosai.
Gab da za su bar asibitin ne ta ga wata kamar Dr Asiya ta shiga mota ta tayar ta fita, ta yi yunƙurin bin motar amma kuma ta yi mata nisa. Da idanu ta rakata tana kisima wani abu a ranta,
“Mammah kin santa ne.”
“A’a Saubahn kama kawai ta yi mini da wata.”
Haka suka je suka dawo bayan an ba ta magunguna tare da shawarwari da kuma robar fitsari da aka saka mata, wadda aka gwada mata yadda za ta dinga sauyata lokaci zuwa lokaci da kuma awoyin da ake so ta ɗauka.
Ta ji daɗi sosai a zuciyarta kuma ta ƙara godiya ga ubangijin da ya ba ta Saubahn matsayin ɗa mai jin ƙai. Tun dawowarta ta mayar da hankali wurin kula da kanta. Ga Nuhu kuwa wulaƙancin yau daban na gobe daban amma haka take shanyewa ta nuna masa kamar ba da ita yake ba.
A haka ta cigaba da karɓar magani, tana shanye duk wata hantara da kyara da su Mama Sumaye suke yi mata har Allah ubangiji ya bata lafiya. Ita bata daga cikin waɗanda aka yi wa aiki, domin na ta bai kai tsamarin hakan ba.
Daga lokacin ta ƙara ƙaimi wurin tallafawa ‘ya’yanta akan komai na rayuwarsu. Ta miƙe haiƙan wurin yin sana’a kala kala domin hana Saubahn zuwa ta sha. Wuta ta buɗe masa sosai ya koma makaranta kamar ƙannansa. Haka ya tatara ya koma makaranta gadan-gadan domin zuwa lokacin sun samu wadatar makarantu a ƙauyan ƙauran na Moɗa nasu har ma da makarantun kuɗi.
Nuhu kuwa ta shata masa layi mai girma tsakaninta da shi da kuma yaranta. Taƙi bashi duk wata ƙofa da zai ga lagwanta har ya cimma muradinsa. Abu ɗaya ne ya yi matuƙar girgizata shi ne lokacin da ta riske shi a zaure da yayarsa suna ƙula yadda za su kawar da yaronta Saubahn kawai domin su mallaki wannan gona.
Ta kaɗu iya kaɗuwa domin har sai da ta kwanta ciwo. Hakan kuma ya yi masa daɗi, sai ya yi amfani da damar ya shiga yin abin da zai taɓa ‘ya’yan matuƙar tana wuri. Ba ƙaramin kasara zuciyarta ya yi ba, sai dai ganin yana neman cimmata ya sanya ta ɗaura ɗamara.
Daga lokacin da ta fuskanci ya gane ‘ya’yanta ne makasar rauninta daga lokacin ya samu ƙofar yin duk abin ɗa yake so a kanta. Ala dole ta tislata musu danganta shi da mahaifi amma kuma ya himmatu wurin tabbatar da ƙasƙantuwar ƙimarsu zuwa ga matsayin agola. Allah kaɗai ya san iya abin da ta haɗiya a wannan tsakanin.
Yaranta kaɗai take duba ta ji sanyi a ranta, ta zamo kamar baiwar da ta gaza samun mai sayenta. Hasalima, surfe da wankau da shi ne ta ɗauki ragamar rayuwar ci da sha da kuma suturarsu har zuwa lokacin da Nuhu ya kwashe su suka koma cikin garin Katsina da zama da sunan ya samu aikin gadi.
Gidan haya suka samu madaidaici na ƙasa, amma saboda mugunta da kuma ƙeta ita ce take biyan kuɗin hayar da kuɗin da take ɗan tarawa. A cewarsa yaranta sun fi nasa yawa. A lokacin Saubahn ya gama fahimtar manufar mijin mahaifiyasa a kan su, sai ya himmatu wurin tabbatar da duk wani abu da zai sake taimakawa mahaifiyasa domin kula da su. Kusufa-kusufa ya san hanyoyin neman kuɗi.
Tana jin sa har cikin zuciyarta tana ƙaunar himmarsa ya sha tsurata da tambaya,
“Mamma wai me ya sa ki ka zaɓi sarayar da ƙima da kuma tabbatuwr gobenmu zuwa ga jiɓantuwa ga wannan majanunin?”
Ranar farko da ya yi furucin a gaban Nuhu ranar ya ga ɓacin ranta mafi muni, hukunci na farko a rayuwarsa da ta taɓa yi masa shi ne tagomashin mari tare da ɗaukewar mu’amar magana ta kwana uku. Abin da ya takura shi ya kuma ƙara tsananta gaba tsakanin su mai ƙarfi. Daga lokacin kuma ya ƙara ƙaimi wurin ƙuntatawa Nuhun ba tare da sanin Mammar ba. Daga ranar kuma bai gajiya ba wurin nanata mata kalar tambayar har zuwa ranar da ta bashi amsa gamsashiya.