“Kausar don ubanki me ki ke sha…”
Hajiya Kulu ta yi furucin tana ɗaga kwalbar dake gefen ɗiyarta, wasu ƙwalla na suɓuce mata tana tuna kalaman bokanta.
“Daga ranar da wani sashi ya soma karo da wani sashi na danginku da kuma jinjin Tukur daga ranar za ki soma fuskantar barazana da masifa kala-kala har sai ya tabbata wannan ƙulaliyar alaƙar ta wanzu.”
Sai yanzu take nadama da kuma danasanin shiga hurumin ubangiji kan lamarin ƙanwarta da mijinta da kuma abin da suka haifa. Yau gashi komai akanta yake ƙarewa.
Wayarta ce ta yi ƙara,
“Mama kayan da muka ɗorawa ɗan dako za a kai miki tashar ibadan yaron ya ce an ƙwace. Amma dai gamu tare da yaron a hannun ‘yan sanda.”
Ƙara ta saki tare da ƙunduma ashar, kayan kusan dubu ɗari biyar ne da abokan kasuwancinta na yanar gizo suka ba ta ta siya musu ta ɗora ‘yar ribarta. Su ake ce mata babu an sace, ina za ta yarda da wannan lamarin. Hannunta na rawa ta dana kiran wayar a karo na biyu kamar zautaciya,
“Kuna wane station?”
“Bakin kasuwa”
“Su tumurmusashi kafin na iso”
Tana katsewa ta kira layin bokanta, ko zagi da kirakin data saba yi masa bata yi masa ba,
“Me zan gani bo…”
“Ba ki ga komai ba Kulu, domin komai na gab da ƙarewa. Da ma na faɗa miki ƙaddarar da ta kawo ɗiyar Khadija zama a bigirenku mai girma ce. Kuma ita ce ƙaddarar da za ta tarwatsa komai. A yanzu haka wasu ruhikan sun gamu. Wasu kuma suna hanyar gamuwa…”
Sai ya ƙyalƙyale da dariya kamar mahaukaci. Da hanzari ta sauke wayar jin zai fasa mata dodon kunnenta. Kamar mahaukaciya ta fita daga gidan ko ta kan Kausar ba ta sake bi ba.
*****
Lokacin da Madu da Mamma suka garzayo domin ganin abin da yake faruwa ba ƙaramar kaɗuwa suka yi ba, Abdallah ne riƙe a hannun ‘yansanda hannuwansa sanye da ankwa.
Gabanta ya faɗi ras!
“Ina mahaifiyarsa?”
Bakinta na rawa ta furta,
“Ga ni yallaɓai.”
“To ki biyo mu station na bakin kasuwa domin amsa wasu tambayoyi.”
Ƙafafunta ne suka soma rawa, Madu dake gefenta ya tareta, Nuhu kuwa wata muguwar dariya ya saki kamar wani tsohon bamaguje.
“Ba sai ta zo ba yallaɓai ko ma me ya yi ni zan zo.”
Daga haka ya ja hannuwanta suka nufi komawa gida, idanunta akan Abdallah da ya ƙi yarda su haɗa idanu da ita. Takaici da nadama ne suka baibayeta. Duk ita ta ja hakan kawai saboda farantawa mutumin da babu abin da yake buƙata sama da ganin bayanta.
‘To Saubahn fa?’
Wata zuciyar ta tambayeta, kamar Nuhu yasan me take ayanawa,
“Ƙila shi kuma wancan babban kwabon yana gidan gala”
Ya furta yana aje kallonsa a saitinta. So yake ta tabbata cikin rauni, kuma ya yi nasara. Hakan ya yi matuƙar kasara karsashinta ta kwacewa riƙon Madu tare da zubewa ƙasa. Afnan da Afra suka yi kanta suna kuka wiwi.
Taune gefan baki Madu ya yi tare da auna masa wata muguwar harara sai ga shi ya nufi hanyar waje yana surutai. Da ƙyar suka samu numfashinta ya daidaita, lokacin da Madu ya yi nufin bin Abdallah dagewa ta yi sai sun bi shi. Haka suka kule gidan suka ɗunguma gaba ɗaya.
*****
Lokacin da suka isa station wannan kurtun suka hango. Gefansa wata mata ce sai huci take kamar baƙar macijiya.
“Wallahi sai an biya ni kayana, daga dako? Mutane maƙiya Allah kana tausayinsu suna iskanc…”
Maganar ta ta ta maƙale sa’ilin da idanunta suka sarƙe cikin na Maryam,
‘Inna Kulu’
Mamma ta yi furucin ƙasan zuciya. Ina za ta manta da wannan fuskar. Fuskar da ba ta da maraba da ta mahifiyarta. Fuskar da ta yi mata shamaki tsakinta da taka bigiren da mahifiyarta take rayuwa.
“Kadda ki sake taka ƙofar gidan nan, ba gidan ubanki ba ne. Ke ɗin annoba ce a duniyar ƙanwata idan na sake ganinki sai na sa an ɓatar dake a doron ƙasa. Ko da ya ke ki zo ma, ni ce fa Kulu wallahi da kuɗi aka ce miki ki zo sai kin koma domin ko hanyar gidan sai ta ɓace a wannan ƙwaƙwalwar taki ta mutanen ƙauye”
Furucin da ta yi mata na ƙarshe ke nan, wanda daga ranar kamar cirewar allura ta ji an cire mata kwaɗayi da son kasantuwa da mahaifiyarta sai dai ba t daina jin ƙunar hakan a ranta ba. Ɗauke ta yi kamar ba ta son Yaya Kulu ba, ita kuwa ta daskare da mamaki da kuma kaɗuwa domin tsaf ta ganeta.
“Ke ce mahaifiyar yaron?”
Wani tsamurmurin ɗan sanda ya furta,
“Ni ce yallaɓai”
“to ai ta kwana gidan sauƙi ga me kayan sai ku daidaita”
“Ba sai mun daidaita ba, ta faɗi kayan na nawane sai mu shaci adadin lokacin da muke ganin za mu iya biyanta”
Mamma ta faɗa kanta tsaye, idanunta kan Abdallah da ya yi zuru-zuru farat ɗaya ya fita hayyacinsa. Tana da tabbacin ba shi ya ɗauki kayan ba domin ba ta gina yaranta da haram ba tana da tabbacin ba za ta ba su sha’awa ba. Ta san ba ta da ko asin biyan kuɗin, amma so take ta nunawa Yaya Kulu iyakarta, so take ta nuna mata ita ɗin mutum ce kamar kowa.
Ta kuma yi nasara. Domin ta yi furucin ne tare da ɗauke kanta yayinda Yaya Kulu da Abdallah da kuma Madu suka zuba mata idanu cike da mamaki da kuma tunanin mene ne togonta. Ita kuwa Yaya Kulu wani tsoro ne mai girma ya ɗar su a ranta. Domin daidai lokacin babban yayansu ya iso gurin. Baban yayansu da ya fi kowa ƙaunar Khadija da kuma takaicin yanayin da aka jefa rayuwarta.
Ta kuma tabbatar da tsatson da ya fito daga ahalin Audu Baduko, babu wanda zai dubi Maryam ya ce ba ta da jiɓi da ahalinsu domin babu abin da ya bambanta ta da mahaifiyarta Khadija.
*****
Ci gaba mahaifin Fatima ya yi da riƙe Saubahn wanda hakan ya sa mahaifiyar Fatima ƙarasowa. Idanu ta ƙureshi da su, hawaye na zuba daga cikinsu murya cike da rauni.
“Abban Fatima wannan duk inda yake jinin yaya Tasi’u ne wallahi. Kaico! Kaico abin da ba ka da ƙarfin sauya shi ko kuma ikon dakatar da faruwarsa.”
Ta furta cikin shassheƙar kuka, riƙeta Fatima ta yi, sai dai zuciyarta cike da mamaki domin kaf zuri’arsu babba da yaro babu wnada bai da labarin kawu Tasi’u da kuma barinsa gida. Har gobe akwai masu burin saka ashi a idanunsu. Wanda suka san shi da wanda aka haifa bayan baya nan.
“Ka ba ni labarin ɗan’uwana ya kai Saubahn.”
Saubahn kuwa, mamaki, farin ciki da kuma ɗimuwa ne suka kama shi lokaci ɗaya. Wai magana ake akan mahaifinsa. Abin da suka shafe tsayin lokaci suka nema ruwa a jallo wani da zai ɗaga yatsa ya ce shi ne wane, wane daga ahalin mahaifinsa.
“Bai kamata ya yi magana daga mu har shi ba, kamata ya yi mu je gida,
“Tabbas na shiga farin ciki ne Saudatu”
Ya faɗa yana kama hannun Saubahn ɗin, a hankali ya turje tare da ɗaga idanunsa sai lokacin mikin rashin mahaifi yake sake cin ransa,
“Mamma na je?”
Ya faɗa yana kallon Hajiya Khadija, shi dai jin matar yake kamar wani sashi na rayuwarsa. In fact ji yake kamar da Mamma yake magana,
“Ka je Saubahn, ban san rayuwarka ba, ban san waye kai ba amma bisa dukan alamu wani haske ne yake neman ratso rayuwarka!”
“Ba zan je ba sai tare da ke Mamma!”
“A’a Saubahn abu ne da ya shafi ahali”
“Ke ma ahalina ce!”
Kalmar ta amsa dum a kanta! Ta ɗago da wani irin yanayi za ta sake magana ya haɗe hannayensa,
“Don Allah Mamma mana!”
Wani rauni ne ya mamayeta har wasu hawaye suka gindaya tsakanin idanunta,
“Ki yi haƙuri ki bi mu”
Mahaifin Fatima ya furta,
“Mu je! Amma yana da kyau aje tare da Malaminsu, domin kadda ayi masa rashin kyautawa”
Ta furta cike da dauriya. Haka suka ɗunguma suka shiga mota suka bar gidan kowa da abin da yake sakawa a ransa. Kai tsaye suka nufi gidan Mal bayan dogon bayani ya shirya ya bi su, domin Saubahn kamar ɗa yake a wurinsa.
Haka suka bar Samir tsaye kamar wani sakarai yana saƙar zuci. Ya sani mugun ganganci ne yanzu ya tari mahaifinsa da batun komawar Fatima. Jiki a sanyaye ya ɗauki waya ya zai kira Jabir sai kuma y suuketa domin Jabir ya daɗe da barin layin rayuwar da suke mara alfanu.
*****
Lokacin da su Saubahn suka ƙara main family na su Fatima ba ƙaramin mamaki Haj Khadija ta yi ba, domin ta haƙiƙance Fatima ta fito daga gidan gata da za a iya ƙwatar mata ‘yanci kawai fushin mahaifa ne ya ja mata rayuwar ƙasƙanci. Ba ta sake tsinkewa da lamarin ba sai da suka shiga ciki. Wuri ne iy wuri na alfarma. Nan da nan aka shiga tarbar su domin kafin zuwansu Ashir ya kai rahoto ta waya.
Wani babban fallo suka shiga, wata tsohuwa suka hango tukuf da ita, sai dai hakan bai hana nuna asalin haskenta ba. Jajir take, har hasken nata ya zama tsani na nuna tambarin dake ƙasan haɓarta wanda ba shi da bambanci dana Saubahn. Tunda suka shigo ta kafe Saubahn da ido ko ƙiftawa ba ta yi har kowa ya zauna, gefanta kuma maza ne magidanta kimanin mutum shida sun kewayeta kamar masu zaman fada.
Hannu ta miƙa a saitin Saubahn da yake shirin zama a ƙasa kus da kujerar da aka ce Haj Khadij ta zauna, fahimtar manufarta ya sanya mahaifin Fatima kama hannun Saubahn ya kai shi har kusa da ita. Hannunsa ta danƙe sosai. Saubahn ya zubawa hannuwanta idanu yayin da yake kallon zoban azurfar dake hannunta sak irin na mahaifinsa wanda yanzu yake a hannunsa na dama.
Ƙam ta riƙe shi,
“Tabbas kai jini na ne!”
Wasu hawaye ne suka kwaranyo masa, a yanzu kam ba shi da hujja ta ƙaryata wannan ahali babban burinsa shi ne yanzu ya gan shi gaban Mamma. Ya gan shi yana mai shaida mata wannan rayuwa. Bai musa mata ba sai ma zobansa da ya yi mata nuni da shi wanda take jikinta ya som tsuma. Murya can ƙasa ta furta,
“Sunanka fa yaro?”
“Saubahn Tasi’u Umar!”
“Ina mahaifinka?”
“Shuɗaɗɗan abu ne!”
Ya ba ta amsa yana mayar da ƙwallarsa, wani abu na naushin ƙirjinsa. Ai sai ta sake shi ta fashe da kuka, babu wanda ya dakatar da ita, a hankali mutane suka ci gaba da shigowa fallon, wanda bisa alamu yanzu labarin ya riske su. Sai da tsayin fallon ya kusa cika da manyan mutane maza da mata, kimanin mutum ashirin da huɗu maza da mata. Maza (14) sai mata (10).
Duk wanda ka kalla cikinsu daula da wadata ta jiƙa shi da kuma rufin asiri. Saubahn ne kaɗai ƙarami cikinsu don Fatima ma tun shigowarta ta wuce sashin mahaifiyarta. Duk wanda ya shigo ya kali Saubahn sai ya zubar da hawaye. Lamarin ya ba shi mamaki matuƙa. Ana haka aka shigo da wani farin dattijo mai cikar suma da hasken fata. Wasu matasa ne a bayansa riƙe da wata akwati, hannunsa riƙe da sanda yana dogarawa har ya zauna kusa da wannan tsohuwar da suka samu.
Murya can ƙasa ya soma magana,
“Na sanar da ku wannan ranar za ta zo ko bayan raina sai dai ashe ina da rabon ganinta”
“Ka yi haƙuri Appah”
Su ka haɗa baki wurin furtawa, muryarsa wadda girma ya gama bayyana cikinta ya sake buɗewa.
“Ubangiji da kuma ahalinsa, su za ku roƙa ya yafe muku amma ni ba ni da hurumi da rayuwarku”
“Saurayi ya ya sunanka, mene ne labarinka?”
Sunkuyar da kai Saubahn ya yi a hankali cikin muryar da shi kansa bai san ya aka yi ta zo masa ba ya shiga ba su labarin tahirin rayuwar su iya abin da ya sani. Tun daga lokacin da ya soma mallakar hankalinsa har zuwa girmansa. Sai wani ɓangare na sashin rayuwar mahaifiyarsa da ita ta basu labarin ƙuruciyarta da muradinta akan karatu har zuwa labarin mahaifiyarta.
Gaba ɗaya ɗakin ya yi tsit, Haj Khadija ce ta shiga wani yanayi mai wuyar fassaruwa. Appah kuwa kuka yake kamar wani ƙaramin yaro.
“Ni na san Tasi’u na raye aka yi mini musu, sai dai duk wanda ya yi da kyau zai ga da kyau. Allah Ya jiƙan Tasi’u tabbas kun ga rayuwa kun yi gwagwarmaya amma in sha Allahu kukan ku ya ƙare”
Ya furta murya a sarƙe,
“Saubahn ka ce sunan mahaifiyarka Maryam Tukur Malumfashi?”
“Tabbas Mamma!”
Ya ba Hajiya Khadija amsa yana jin ubangiji ya tabbatar da fatansa,
“Wane gari a Malumfashi?”
“Ƙauran namoda”
“Saubahn kai jikana ne, ni ce mahaifiyarta Khadija.”
Take ɗakin ya ɗauki kabbara, Saubahn bai wata-wata ba ya rungume Hajiya Khadija yana kuka mai tsuma rai. A zuciya da zahiri yana fatan ya buɗe ido ya gan shi a gaban Mamma. Mal kuwa babu abin da yake sai godiya ga ubangiji tun zuwan Saubahn gidan sa yake fatan Allah Ya bayyana wani cikin ahalin yaron. Yana da yaƙinin da hankalinsa kawai ɓacin rai ne ya yi masa yawa, sai ga shi Allah Ya amsa fatansa.
“Na daɗe da jin hakan a jikina Mamma sai dai na ga za furtawa saboda ba ni da madogara. Kamaninki da mahaifiyata sun tsananta matuƙa! Amma Mamma daga ke har dangin Abbiey ina da tambaya a kan ku ina ƙalubalantarku kan me ya sa kuka wofintar da mahaifana har muka fuskanci tsananin rayuwa.”
“Saubahn ba zan iya cewa ga dalilina na wofintar da mahaifiyarka ba, a duk lokacin da na yi yunƙurin tunata wani abu mai nauyi ne yake tokare ƙirjina har na nemi fita hayyacina. Game da dangina kuwa idan har mahaifiyarka ba ɓoye maka ta yi ba kasan komai game da ƙiyayyar da suke mata don haka ina neman afuwarku!”
Kai ya jinjina mata, bai taɓa jin hakan zai iya zama shammaki tsakaninsa da ita ba, Allah Ya sanya masa ƙaunar matar tun kafin ya san wace ce ita gareshi. Idanunsa ya mayar kan Appah,
“Appah…”
“Ka yi haƙuri Saubahn ba zan iya cewa komai ba har sai mun je ga mahaifiya da kuma sauran ‘yan uwanka.”
Kai ya jinjina yan jin ƙunar tsohon har cikin ransa. Ana haka wata mata baƙa ta shigo kamar an jehota sai surutai take yi,
“An ce jinin Tasi’u ya bayyana ko? Ƙarya ne Appah, ni fa na kashe uwar Tasi’u na kashe ubansa na kuma tura baƙaƙen buzaye tun daga damagaran aka je har garin da yake aka kashe shi, ta ina wani jininsa zai bayyana?”
Sai ta kwashe da dariya, wani cikin mazan dake zauna ne ya miƙe yana riƙe da ita,
“Hajja ki bari”
Tureshi ta yi ya faɗi,
“Na bar me? Duk ba saboda ku na yi ba.”
Sai ta ƙwace ta fita tana dariya kamar zautaciya. Appah ne ya saki ajiyar zuciya, Gaba ɗaya tausayin yaran ya kamashi, babu abin da ya fi tashin ga rayuwar ɗa ace mahaifiyarsa na da wani tabo da duniya za ta kalla ta yi masa wani tambarin muni da shi. Sai dai abu ne da ba za su iya da shi ba.
Kuskuren da ya yi sanadin rayuka da yawa.
Kuskuren da ya yi sanadin zumunci da yawa.
Kuskuren da ya ɓata komai.