Skip to content
Part 21 of 23 in the Series Kuskuren Wasu by Sanah Matazu

“Dukanku kuna da labarin abin da ta aikata, sai dai babu yadda za mu yi domin ita ɗin jininmu ce kuma mahaifiyarku ce duk lalacewar uwa uwa ce, don haka ban lamunci ku ƙuntata mata ba. Ku barta ta girbi abin da ta shuka shi ubangiji alhakimu ne.”

Kai suka jinjina gaba ɗayansu, sai lokacin Saubahn ya lura ɗazu rashin fahimta da kuma tambarin fuskarsu ya sa yake zaton duk kamar su ɗaya sai yanzu ya lura mata huɗu da maza biyar na wurin sun fi kama da matar da zai iya kira da mahaukaciya.
Cikin ƙanƙanin lokaci aka tsayar da magana cewar washegari za a ɗauki wasu cikin manyan gidan domin zuwa ga Mamma, tafiyar da za a yi ta hadda Haj Khadija da kuma Mal da take ji kamar ta yi tsuntsuwa ta tafi. Ala’ala take a tashi taron ta tafi da Saubahn ta sake yin hirar Maryama da shi. Sai dai kuma kash ƙememe suka hanata tafiya da shi. Haka ta tafi jiki a sanyaye tana fatan gari ya waye.
*****
Saubahn kallon kansa yake kamar wani baƙauye, sai yau ya sake tabbatar da maganar Mamma,
“Saubahn wata rana fa dole ne za ku yi farin ciki ko bana raye.”

Ɗakin da yake ciki yake ƙarewa kallo, ko a mafarki bai tsamaci hakan ba. Tun bayan da ya yi wanka. Matasa ne sa’o’insa suke ta shigowa daga wanda zasu rungume shi wai wanda za su yi selfy da shi. A haka ka kira shi su je wurin cin abinci. Sai. Lokacin ya sake ganin Fatima wadda ta sake cikin ‘yan uwanta sai walwala take. Sai ya ji tausayinta domin bai taɓa ganinta tana farin ciki haka ba.
*****
Lokacin da Haj Khadija ta koma gida ba ƙaramin mamaki ta yi ba ganin masu gidan sun dawo. Ƙarima ce ta taho da gudu ta rungumeta,
“Mama ina ki ka je ina ta jiranki tun biyu muka dawo?”
“Ayya ɗiyar Mama, na je gano Fatima ne tana asibiti daga nan kuma wani babban lamari ya taso dole muka nufi gidansu. Amma yanzu alhamdulillahi komai lafiya ƙala…”
“Kadda ki sake ki ƙarasa shigo mini gida ki koma inda ki ka fito..”
Muryar Alhaji Salisu ta ratso kunnuwanta. Kallonsa ta yi tana jin wani shauƙi da ba ta san ko mene ne ba a zuciyarta. Tamkar wadda aka saukewa wani ƙaton dutse a kanta.
“Na gode ƙwarai da wannan tukuicin Yaya Salisu, da ka san a yanayin da nake ciki da ka tabbatar Hajji da Umara ka yi mini a yau amma babu komai, ina neman alfarmar shiga na ɗauki duk wani abu da zan iya ɗauka kafin saura su biyu baya. Saboda tafiyata na nufin na tafi har abada”
“Umma ta gaida asha, in dai ni ne na sauwaƙe miki igiya biyu, kaya kuma ki je ki kwasa”
Hamdala ta yi tare da juyawa ƙwalla ta share, tsayin shekaru nauyin da take ji a ƙirjinta sai yanzu ya sauka har wani abu ta ji ya yi ƙut ya wuce ta zuciyarta. Haj Hauwa jikinta ba ƙaramin sanyi ya yi ba.
Sai yanzu ta hango wautarta na barinsa ya saketa. Domin bokanta ya ba ta tabbacin matuƙar babu Khadija a gidan wadda ita ce yake wa son gaskiya dole zuciyarsa za ta yi ta kwaɗaita masa matan waje kuma dole zai dinga aure-aure.
Shi ya sa a baya ta dinga turawa Kulu maƙudan kuɗi na fitar hankali har ta yi murɗa murɗar da ta haɗa auren wanda bayan shigowar Khadijan kuma ta yi aikin da aka sakawa zuƙatansu shamaki mai ƙarfi. Don haka hankali tashe ta kira Yaya Kulu ta rattamata abin da yake faruwa.
Tuni Haj Khadija ta haɗa kayanta, zuciyarta ta amince kan ta je gidan Mal ta kwana tunda da safe za su nufi Katsina. Karima na kuka ita na kuka haka suka rabu, lokacin da ta isa gidan Mal bata ɓoye masa komai ba. Bai ji daɗi ba amma ya yi mata fatan Allah Ya sa hakan shi ya fi alheri.
*****
Ajiyar zuciya Yaya Kulu ta saki sakammakon ganin yayansu ya ja tunga ya yafiyota da hannu, har sai da Maryam ta saci kallonta ganin abin da ta yi. Da sassarfa ta nufi wurinsa dan ma kadda ya ƙaraso. Tana ba da baya Madu ya dubeta,
“Mamma me ya sa ki ka ce haka? A bari ayi sulhu mana. Kin fa san ba mu da kuɗin nan!”
“Madu ubangiji yana sane da bayinsa ba zai taba bari mu wulaƙanta ba”
“Amma Mamma!”
“Madu mana pls”
*****
“Kulu ki bar wannan shirmen kawai ki zo mu je gida akwai matsala gagaruma, Baba tun safe muka tashi ba ta jin daɗi yanzu babu abin da take kira sai a kira mata Khadija ta nemo mata takwararta”
Cikinta ne ya murɗa,
‘Takwararta Maryam ke nan. Wannan fa ɗake gabanta’
Wata zufa ce ta keto mata,
“Ina zuwa yaya”
Ta furta tana juyawa, ji take kamar ta saki kashi a wando,
“Yallaɓai a sallame su ni dai na yafe”
Furucinta ya sandarar da Mamma da Madu, domin ba su yi tsamanin hakan ba.
“Ungulu ba kya jewar banza!”
Mamma ta furta tana sakin wani marayan murmushi, Yaya Kulu ba ta bi takanta ba ta juya suka bar wurin. Nan aka ba su Abdallah suka tafi da shi. Tun a hanya Abdallah ya soma shan ranƙwashi wurin Madu.
Tun Mamma na saka masa idanu har ta soma rama masa. Domin ta san da shaƙiyanci yake yi da ma kuma gwani ne wurin hakan. Aikuwa ya shiga yi mata dariya yana kwatanta yadda ta dinga ɗaurewa Yaya Kulu fuska.
“Gidanku zan ci Madu!”
“Mamma gaskiya na faɗa fa, wallahi boss ki ka koma da ma haka kikewa wannan mijin naki…”
Bakinsa ta kaiwa duka ya kauce yana duban Abdallah,
“Ba haka bane Ya akkei?”
“Haka ne wallahi bro tsoronsa take”
“Zare mata idanu yake fa”
Humaiyrah ta faɗa tana toshe dariyar da ta suɓuce mata. Mamma murmushi kawai ta saki tana zagaya idanunta akan yaran nata, rabon da ta ji farin ciki irin wannan har ta manta. Hannu ta sany ta share guntun hawayen da ya zubo mata.
“Mamma matar can fa…”
“Me kuma ta yi Madun Mamma!”
“Mamma na rasa dalilin dagiyar da kika yi mata, kamar…
“Yayar mahaifiyata ce Madu, hakan kuma baya nufin ku nomo su ban lamunta ba Madu!”
Wani shork yaran suka ji gaba ɗayan su, suka kalleta da maɗaukakin mamaki. Madu kuwa har wata fosta ya yi. Baki a buɗe kamar an ba shi kyautar budurwa. Daidai lokacin da mai napep ya tsaya a ƙofar gidan su. Bai san an biya mai napep ɗin ba sai da Mamma ta kama hannunsa. Hannunsa take ja kamar yaro ɗan shekara biyar. A haka har suka ƙarasa cikin gidan.
“Mamma yayar…”
“Madu ban aminta ba, kadda wanda ya sake yi mini maganarta a gidan nan matuƙar kuna son farincikina”
Kai ya jinjina mata, daga haka ta shiga ɗaki ta bar su ɗauke da mamaki a fuskarsu. Tana shiga ɗakin ta saki ajiyar zuciya. A ranta tana mamakin dalilin da ya sa ta furta musu dangantar dake tsakanin su. Sai dai wani baƙon lamari ta ji yana baƙuntar ruhi da ƙafafuwanta, wani yanayi da ta kwashe shekaru rabonta da shi. Wani yanayi da ke tabbatar mata ta warke daga cutar manta ahalinta. Kewa take ji, kewar mahaifiyarta take ji tana ratsa kowace gaɓa da ruhinta.
*****
Tun sanyin safiya motoci suka yi jerin gwano a gidansu Fatima, motar farko ɗauke take da maza ta biyun kuma mata, sai ta uku wadda matasa ne irin Saubahn da shi kansa Saubahn ɗin. Haj Khadija na cikin motar matan yayin da Mal ke cikin ta mazan. Tafiya ce suka yi ta cike da ci da zuci masu raunin cikin su kuwa har lokacin suna share hawaye.

Lokacin da suka shiga garin Katsina an yi sallah, Haj Khadija ta roƙi alfarmar su ƙarasa gidan su su yi sallah kafin su kai ga ƙarasawa can ɗin. Sun so yi mata musu, sai ta ji zafin hakan ganinta ta fi su ɗokantuwa da son ganin Maryam amma sai ta share. Appah ne ya girmama muradinta tare da nuna musu ayi yadda take so ɗin. Domin ya lura kamar ita ma tana ɗauke da miki irin na su. Dalilin da ya ƙara masa jin tausayin ahalin Tasi’u a ransa ke nan yana da tabbacin rayuwarsu cike take da ƙalubale.

Kai tsaye kuwa gidansu suka yi wa tsinke, lokacin da motocin suka tsaya ne hankalin Yaya Kulu ya dawo kan bakin ƙofar. Wadda take tsaye kamar kumurci tana huci. Tun jiya yake fama da ita akan a kira wayar Khadijan ta hana, ya rasa dalili sai dai da yawa daga cikin ‘yan uwanta da suka san dalili sun saka musu ido kawai. Domin da yawansu da haɗin bakin su a lamarin saboda tana basu kuɗi.

Ƙure motocin da idanu suka yi yayin da ƙirjin Yaya Kulu yake ta harɓawa kamar mai gudun mutuwa.
“Nan ne bara na yi muku iso!”
Muryarta ta ratso kunnuwansu,
“Assalamu alaikum”
Ai Yaya Kulu sai ta maƙale kamar gunki,
“Ta faru ta ƙare”
Furucin ya yo futar burgu daga bakinta tamkar suɓucewar bulo a hannun magini. Da idanu suka rakata daga ita har yayansu hakan ya sa ta tsaraka ta wayance,
“To yaya Isah ai ga ta nan musu ya ƙare!”
“Eh! Ga ta nan fa sai baƙin ciki ya kashe mutum”
Ya faɗa yana kama hannunta kamar wata yarinya, ita kuwa sai ta bi shi jikinta yana rawa domin ta sadaƙar wani abu ne ya faru ake ɓoye mata.
“Yauwa Baba ga ta nan!”
Sauran ‘yan uwanta suka haɗa baki wurin furtawa yayinda ƙafarta ta ƙarasa shiga gidan. Zuciyart ce ta tsinke a raunane ta furta,
“Wai lafiya?”
“Khadija ke ce?”
Muryar mahaifiyarta ta ratso kunnuwanta,
“Ni ce Baba wai lafiya na ga duk kun haɗu. Baba mene ne ya faru ki ke nemana haka na ga duka watana biyu da zuwa ganinki!”
“A to ni ma haka na gani ai ake ganin laifina”
Cewar Yaya Kulu,
“Hmmm!”
Hajara mai binta ta furta tana barin wurin.
“Yau duk dare Khadija sai kin kai ni Malumfashi na gano takwarata ɗaukar haƙƙin ya isa haka”
Wata ƙwalla ta share tare da furta,
“Allahu akbar Baba ai ba sai mun kai ga hakan ba. Maryama dai da ki ke magana kanta tan cikin garin nan. Kuma yanzu haka dalili mai ƙarfi ne ya kawo ni garin nan dalilin kuwa na haɗu da yaronta na fari. Shi kuma dalilin Fatima maƙociyarmu ya haɗu da dangin mahaifinsa da ita kanta Maryaman ba ta san su ba”
“Ba ta san su ba kamar ya?”
Cewar Yaya Isah wanda ke nufar waje domin tarar baƙi. Yaya Kulu kuwa banɗaki ta faɗa saboda suɓucewar wani mahaukacin zawo da ya yi mata futar burgu. A waje Yaya Isah ne ya tari su Appah tare da buɗe gaton garejin gidan, kasancewar an samu sauyi sosai mazan gidan sun taso an gyara gidan yadda ya kamata.
Ruwa aka kawo musu na sha da na alwala. Bayan sauke farali ne kuma aka shiga gaggaisawa. Daidai lokacin daga cikin gida aka jiyo kururuwar Yaya Kulu,
“Shi ke nan na shiga uku na lalace, tunda Maryama ta bayyana ƙarshe na ya zo daga wannan masifa sai wannan. Wannan yarinya annoba ce a garemu”
“Ki ga annoba a kanki Kulu”
Mahaifiyar su ta faɗa tana kwaɗeta da mahuci, ai kuwa ta sake saka ihu mai ƙarfi,
“Baba jiya asarar duhu ɗari biyar yau kuma plaza ta ta ƙone kuma duk ita ce sila…”
Ɗauketa Yaya Isah ya yi da mari, yana niyyar ƙara mata da mangari mahaifin Fatima da ya biyo shi ya dakatar da shi
“Ku bar shi ya daketa ƙila za ta yi bayanin ƙulin da ta ƙula yake ƙule mata ciki”
Hajara ta faɗa tana share ƙwala, duk sai aka zuba mata idanu.
“Yaya Kulu ki tona kanki idan ba haka ba wallahi zan fasa”
Hajarar ta furta tana tuna ranar da ta san komai game da abin da Kulun ta yi dalilin laɓewa da ta yi ta ji hirar su da aminiyarta. Sai dai kuma barazanar da Kulun ta yi mata na dakatar da karatun ɗiyarta da ta ɗauki nauyi ya sa take ta dakon abun a ranta.
“Kulu da ke ake!”
Yayansu ya furta yana sake nufarta ta ɓuya bayan mahaifin Fatima,
“Zan faɗa amma sai an zo da ita nan wurin”
“Ita wa?”
“Maryam ɗiyar Tukur maƙo”
Murmushi ne ya suɓucewa Haj Khadija haka ma Saubahn da ya ji sunan da aka kira kakansa da shi. Don haka suka ɗunguma gaba ɗaya. Saubahn shi ya faɗa musu unguwar da suke zaune, kasancewar Yaya Isah ɗan gari shi ya karɓi tuƙin suna tafiya Saubahn na nuna hanya har suka isa.
Daidai lokacin da suka isa ƙofar gidan Mamma na hura wuta za ta ɗora kasko, saboda sun soma yin doya da ƙwai da yamma. Amma ba ta barin su Afnan su yi aikin ita take siyarwa su suna ciki suna aikin gida.
Ɗago kanta ta yi tana ƙarewa motocin kallo. Idonta ne ya soma wani irin hazo-hazo lokacin da ta yi katari da mazan gidan su Tasi’u masu kama da juna. Duk da Tasi’u wahalar rayuwa ta sa shi baƙi amma gado ba ƙarya ba.
Ƙirjinta ne ya cigaba da bugawa lokacin da idanunta suka ci gaba da shawagi a wurin har suka sauka kan fuskoki ukun da ko da za ta mutu sau saba’in ta dawo ba za ta manta da su ba.
Saubahn, Yaya Kulu, da kuma mahaifiyarta.
Komai tsayin lokaci ba ta za mance wannan fuskar ba. To ta ma tuna fuskar Yaya Kulu bare kuma mahaifiyata. Zuciyarta ta yi wani irin tsale ta doka, fuskokin mazan da take kallo ne ya ɗaga hankalinta. Ƙyam ta tsayar da idanunta akan fuskar Appah tabbas ta taɓa ganin hoton tsohon a hannun mijinta. Wata irin juwa ce ta ɗauketa. Hakan ya yi daidai da ɗaukewar numfashinta ta tafi luu ta nufi cikin man da ta ɗora wanda ya gama yin zafi.
*****
“Samir ni ba ɗan iska ba ne da za ka je ka wulaƙanta iyayen yarinya sannan kum ka zo ni na nem naka bikonta! Ina ce ba ni na nema maka auran ba saboda? Nan ni da kai na saka maka sharaɗin matuƙar kana son yarinyar ka sauya ɗabi’unka amma sai mahaifiyarka ta ɗaurema ƙugu. Har tutuya ta yi mini duk munin namiji ko munin halinsa ba ya rasa matar aure yanzu wa ya gari ya waya?”
Mahaifin Samir ke nan yake ta faɗa, tun bayan da ya samu labarin abin da ya faru. Mahaifiyars kuwa ta yi tsuru-tsuru domin komai da yake ita ta ɓata shi, kuma babu abin da ba ta sani ba game da muzgunawa Fatiman da yake yi. Sai dai kunya da takaicin abokan zamanta na jin tijarar da ake mata ya hanata kataɓus.
Sai yanzu take dana sani da takaicin rayuwar da ta jefe yaron. Kiri-ƙiri ta nuna mahaifinsa bai isa komai a kan rayuwarsa ba. Don lokacin auran ma yayanta ne ya shige masa gaba. Komai yake so kuma ita take masa saboda mahaifinta na da rufin asiri. Sai dai Samir ya ba ta mamaki duk wata kaddara ta ta ya ƙarar da ita ba tare da saninta ba. Ɗimbin gadon da aka ba ta lokacin rasuwar mahaifinta duk babu shi.

<< Kuskuren Wasu 20Kuskuren Wasu 22 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×