A hanzar ce ya shigo gidan a soro ya yi kiciɓus da Abban su, ya rusuna ya gaishe shi. Maimakon ya amsa sai auna masa ta maguzawa da ya yi tare da yin waje ya bar shi a nan shanye da baki. Juyawa ya yi da sassarfa yana gwamma numfashi ya shiga gidan, da hanzari ta miƙe tana tambayar,
"Sauban lafiya?"
Ledar hannunsa ya miƙa mata,
"Mamma ku ci wannan zan koma tashar motar yanzun nan!"
Kai ta kaɗa tana dubansa,
"Aa Sauban bana ƙaunar zaman tashar nan wallahi..."
"Dola ce ta saka, ki yi ha. . .