Amma ban da dukansa babu abin da yake yi. Duk iya ƙoƙarin su sun kasa ƙwatarsa.
Malam Nuhu kuwa gaba ɗaya ya fita hayacinsa, ban da ihu da kururuwa babu abin da yake yi. Sai dai kuma a ƙasan zuciyarsa babu nadama ko ɓurɓushinta. Da ƙyar aka ƙawace shi a hannunsa sai da ya yi masa dukkan kawo wuƙa. Tukuna da taimakon Mamma ya samu ya kuɓuta.
Nan ya ta shi yana bambami tare da aiba ta mata yara kamar yadda ya saba, abu na farko da ya fi komai ƙona mata rai. Kuma take jin. . .