Skip to content
Part 5 of 23 in the Series Kuskuren Wasu by Sanah Matazu

Amma ban da dukansa babu abin da yake yi. Duk iya ƙoƙarin su sun kasa ƙwatarsa. Malam Nuhu kuwa gaba ɗaya ya fita hayacinsa, ban da ihu da kururuwa babu abin da yake yi. Sai dai kuma a ƙasan zuciyarsa babu nadama ko ɓurɓushinta. Da ƙyar aka ƙawace shi a hannunsa sai da ya yi masa dukkan kawo wuƙa. Tukuna da taimakon Mamma ya samu ya kuɓuta.

Nan ya ta shi yana bambami tare da aiba ta mata yara kamar yadda ya saba, abu na farko da ya fi komai ƙona mata rai. Kuma take jin ko shi kaɗai ya isa shata layi a zamantakewarsu. Amma ta rasa wai shin mene ne yake riƙeta? Wace irin kaifaffar igiya ce ta yi mata ɗaurin talala a rayuwarta da ta Nuhu?

Baki a fashe, yana ɗingishi haka ya dinga ratsa majalisu yana faɗa musu ƙarya da gaskiya.’Ya’yan matarsa sun haɗu sun yi masa duka, saboda ya kama ɗayan su na ƙoƙarin lalata masa ɗiya.

“Yanzu kai sai ka ƙyale shi Nuhu?”

Abokinsa Mal Isya mai tureda ya furta cike da munafurci.

“To me zan yi Mal Isya, kana ganin fa yadda suka haɗu suka tumurmusa ni kamar sun sami ƙaton ɓarawo. Ni sai na ke ganin ma kamar munafurci ne ya sa mahaifiyr ta su kuka duk yadda aka yi ita ta sanya su dake ni. Saboda na zame mata ƙarfen ƙafa.”

“Babu shakka za ta aikata, ai da ganinta wannan wannan matar taka idanunta a buɗe suke.”

Mal Isya ya sake furtwa yana jin wani ɗaci a ransa. Ba don komai ba sai don yadda ya tsani Saubahn a ransa. Kuma hakan ya samo asali ne saboda nuna buƙatuwarsu wurin yin mu’amalar banza da shi. Shi kuma ya runtse idanu ya ci mutuncin yadda ba sa zato. Babban takaicinsa yadda Shamsu ya saka musu kuɗi masu yawa domin su ja hankalin Saubahn ɗin amma abun ya faskara.

Tun daga lokacin ya ɗauki karon tsana ya ɗora masa, haka kuma ya ɗaura ɗamarar tunzura Nuhu ya yi musu tijara yadda ya ga dama. Abin ka da mai neman kuka aka jefe shi da kashin awaki. Sai ya ƙara ƙaimi tujarar yau daban ta gobe daban. Duk abin da Isya ya ɗora shi a kai bi yake yi saboda yana ba shi mai dan maiƙo ya ci. Shi kuma in dai kwaɗayi ne to shi da ƙuda ba a banbance gwani.

Don haka cike da neman agaji ya sake dubansa.

“Yanzu me ya kamata na yi?”

“Ƙara za ka kai su kawai!”

“Ƙara kuma Isya?”

“Eh mana ko so ka ke su sake kilarka gobe kamar ɗan da suka haifa?”

“Ko da wasa, amma dai kasan ba ni da sisin zuwa wurin ‘yan sanda ni tsoron su ma nake ji!”

Wata dariya Isyan ya kwashe da ita, har da buga ƙafa,

“Amma dai Nuhu sai yau na sake tabbatarwa kai baƙauye ne, duk iskancinka kana tsoron kwalawa ke nan? To ba wurin su nake nufi ka je ba. Nufina wurin mai unguwa.”

Washe baki ya yi, kamar tsohon da aka yi wa alƙawarin budurwa. Tabbas tunanin hakan bai zo masa ba ko da wasa. Da zama kuwa ya miƙe nan ya nufi babbar majalisar unguwar wato gidan me unguwa. Nan ya zauna ya rattaba masa ƙarya da gaskiya, aka tarkato Mamma da iyalanta. Cikin ƙasƙanci da nuna tsagwaron rashin mutunci ya saki baki ya dinga zuba musu shari.

Mamma ta yi kuka, ta yi kuka kamar ba gobe. Ta yi nadamar da ta san cewa ita ce tushenta. Jiki a sanyayye su ka baro wajen, domin dai buƙatarsa ta biya duniya ta aiba ta mata yara.

*****

Haka suka kwana zuƙata babu daɗi, ga Madu kuwa kewa da tunanin wurin da Saubahn ya fake yake yi. Baya son zuciyarsa ta amince da tunanin hukuncin da ya yanke amma yana da tabbaci haƙuri irin na yayansu sai dai bai iya yanke hukunci ba idan ya kai maƙura.

Washegari haka su ka raɓata duk su ka fice gaisuwa ce kawai ta haɗa su. Madu ya sake ninkawa tasha da fatan ganin Sauban. Yayinda ƴan matan su ka wuce zuwa makaranta rai babu daɗi. Abdallah kuwa shi ya zauna tare da ita kasancewar ya zana jarrabawar barin sakandire sakammako suke jira shi da Madu. Haka su ka yini babu daɗi.

Kwana ɗaya, biyu uku huɗu amma babu batun Saubahn. Duk inda suke tunanin sun je amma babu labarinsa. Sai da Madu ya shafe kwana biyar kullum tasha yake yini yana aikin dako duk ba ba ya ra’ayinsa, yana kuma yaƙinin zai ga yayansa amma shiru maƙatau babu labarinsa.

Hakan ya sanya ya rungumi ƙaddara ya ci gaba da kula da aikin da yayansu ya soma na inganta rayuwar su. Ya sani wani nauyi ne mai girma ya hau kansa. Kuma yana da tabbacin ba zai ɗauki abin da ya ɗauka ba.

*****

Tun daga ranar Mamma ba ta sake ganin dariyar Madu ba, iyakarta da shi gaisuwa. Maigidan kuwa be sake samun ƙimar gaisuwa ta ratsa tsakanin su ba. Su Afnan su ne abokan hirarsa. Idan ya fahimci Mamma za ta shiga sai ya yi gum.

Duk inda yake tunanin zai ga ɗan uwansa ya bincika amma babu labarinsa. Ƙarshe ya samu tabbacin an ganshi a tasha ya hau mota, daga ranar ya sakawa ransa sallama ya ci gaba da yi masa addu’ar kasancewa a hannu nagari.

Sai dai Mammar su ta dasa wani ciwo me girma a zuƙatan su. Ta haifar da giɓin da ya zamo masu bame warkewa ba. A hankali sai hidima ta soma hawa kan Madu ɗin.

Karatunsa ya tsaya cak, islamiyyarma sai Asabar da Lahadi yake yakicewa ya je, shi ne tasha shi ne jari bola haka ma Abdallah ya fantsama bakin titi saida ruwan leda.

Facin takalmi da sauran su. Sannu-sannu sai su ka soma zama kamar wasu almajirai. Ba su damu da wanki ba, saɓanin da da duk sati yayansu zai haɗa su su wanke hadda na Mamma. Su Afnan kuma su yi guga.

Madu na takaicin rayuwar da suke yi, har baya jin shayin gwaɓawa Mamma magana saboda zafin da zuciyarsa take yi masa. Ta sani, sun sani Sauban shi ne ƙarfin su.

Duka-Duka Sauban ɗin shekarunsa goma sha takwas ne dan dai yana da tsayi da garin jiki.

Madu kuwa sha biyar gareshi shi da Abdallah kasancewar su tagwaye. Sai Afnan da Humaira masu shekara goma sha biy biyu cif a duniya suma tagwaye ne. Takacin Madu be wuce na yadda ba shi da ƙumajin rungumar ƙanansa kamar yayansu ba.

Tunda ya zamana babu Sauban sai Mamma ta ƙara ƙaimi wajen faffutukar nema musu abin da zasu saka a bakin salati. Sai dai kamar rufe ƙofofin ake a gareta. Gaba ɗaya surfenma ya daina samuwa. Wankau idan ta karɓa ruwan wankin wahala yake mata saboda babu me ƙarfin jido ruwa kamar Sauban.

Sai yanzu ne take jin ta tafka babban kuskure karo na uku a rayuwarta. A hankali damuwa ta soma nuƙurƙusarta, ciwon kai da ƙirji su ka zama abokanta sannu-sannu ta soma kwanciya yau ta miƙe gobe ta kwanta.

Ciwo ne me girma yake cin zuciyarta sai dai duka tana ɗora alhakin wahalhalun rayuwarta akan baiwar Allah Khadija. Matar da ta wofintar da bigiren tushan samar mata da nagartar ƙuruciya.

*****

Lokacin da mota ta sauka a tashar Kaduna gaba ɗaya sai Saubahn ya rasa ina zai nufa. Babu abin da yake yawo a zuciyarsa sai yanzu me ƙannensa suke yi? Sun ci abinci? Nemansa suke yi ko kuwa Mamma ta hana su nemansa? A wane yanayi gidan na su yake? Ya kai aƙala awa ɗaya da rabi yana zaune har tashar ta soma watsewa kasancewar an kira magarba. Lallaɓawa ya yi ya shiga masallacin dake ciki ya yi alwala tare da gaba tar da sallah la’asar da magarba. Be tashi ba ya cigaba da istigifari yana jin sanyi na ratsa zuciyarsa.

Babu komai a ransa sai mahaifiyarsu, ya sani sarai ba ta da cikakkiyar nutsuwa saboda rashin sanin halin da ya ke ciki. Amma kuma hukuncinta ya yi masa tsaurin da ya asassa taurarewar zuciyarsa. Hakan ya sa ya amince cewa, nisa da su shi ne mafita a garesu duk da hakan ba zai basu sallamar zuƙata ba.

A hankali ya soma rawar sanyi, ga yunwa na faman juya hanjinsa. Sannu-sannu aka soma fita daga masallacin ɗaya bayan ɗaya. Ya zamana babu mutane sai ɗaiɗaiku. Sanyin da ya ke kaɗawa ya sa ya soma curewa a waje ɗaya saboda kayan jikinsa ba wasu masu nauyi bane. Sai yanzu batun kaya ya faɗo ransa.

Gabansa ya yi mummunar dokawa, musamman da ya tuna baya iya kwana biyu yana maimaita saka kaya ko da a yanayin sanyi ne. Mamma har faɗa take yi masa,

“Saubahn ka ki ya yi kanka da shiga ruwa. Ko tsoron mura baka yi, sai ka ce jinin ƙwaɗi!”

“Mamma!”

“Saubahn!!”

“Mamma mana dan Allah!”

Kwalla ya shiga sharewa, yayinda wata irin kewa mai kaifi ta danne ƙasussuwan ƙirjinsa. Numfashinsa ya soma fin ƙarfin hunhunsa. A hankali y sulale a wajen, ba shi da maraba da matace. Be sake sanin abin da yake faruwa ba.

*****

Tsayin kwanaki uku ke nan take fama da ciwon kai me tsanani, ko ɗaga kai ba ta iya yi. Malam Nuhu, kuwa tun ranar da ya tabbatar ta kori Saubahn, kuma ya ga tabbacin babu shi ya soma yunƙurin ganin ya ƙaddamar da abin da yake muradi a kanta.

Safiyar Asabar ne ya shirya ya ce mata zai je Malumfashi, yadda kanta yake mata barazanar darewa ne ya sa ko ta kansa ba ta bi ba har ya gama kara kainarsa ya tafi. Ya lura da tun lokacin da ya tunzurata ta kori Saubahn, take ƙule da shi. Ba don haka ba da ita zai tambaya kuɗin mota, dan haka bakinsa alaikum ya ja samarin ƙafafunsa ya kama hanyarsa cike da mugun nufi.

Tun fitarsa take juyi, a sama take jinta tun tana ganewa har idanunta su ka soma rufewa. Afnan da Humaira sun tafi islamiyya gidan ba kowa, duk da suma ɗin a ɗaure suke yi mata komai ba kamar yadda su ka saba ba.

Tana hango tuhuma a idanun su amma sun kasa tunkararta. Miƙewa ta yi saboda ƙishirwar da take adabarta, sai dai kafin ta kai inda randa take ta yanke jiki ta faɗi hakan ya yi daidai da shigowar Madu gidan.

***

“Wai lafiyarki ne na ga sai cika ki ke kina batsewa”

“Ina fa lafiya Hajiya Zali wannan tarnaƙin nawa ne zai dawo ni kuma zai takura ni ne kawai!”

Sai da ta yi mata duban tsaf sannan ta kwashe da dariya,

“Ni na ɗauka ma wani abun kirki ne ki ke ɓata ranki ashe ba haka bane. Yo sai me idan zai dawo ki tattaro kayanki ki dawo nan bayan kin ba shi tabbacin kin fita italia shigo da wasu kaya da kika yi order na kasuwancinki. Daga nan sai ki kashe wayarki na tsayin adadin kwanakin da zai yi ya juya ba sai kun haɗu ba. Tunda ko kun haɗu ba shi da wani amfanin da zai miki bayan ɓarin kuɗi.”

Dukkan wasa ta kai mata tare da furta,

“Lalai ke shegiyar gari ce.”

Cikin ƙanƙanin lokaci ta ware ta shiga gudanar da harkokinta yadda ta saba. Da yammaci su ka fita tare da sabon yaron da ta samu ɗan ƙuda. Har mamaki take yi, ga shi dai yaro ƙarami amma kuma yadda ya juya akalar rayuwarta lokaci ɗaya ya ɗimautata. Kuɗi take sakar masa tamkar ba ta san ciwonsu ba.

A ranta tana da ƙudurin siya masa mota, sai dai Hajiya Zali ta dakatar da ita, tare da ba ta shawarar ta siya masa machine saboda kadda ya fi ƙarfinta nan gaba. Sosai take jin daɗin yaron domin ya iya buga ƙwallo a raga.

Ga shi matashi mai jini a jika duka-duka be haura shekara ashirin da shida ba. Dan haka ta saki jiki take masa ɓarin kuɗi da jiki da zuciyarta. Ba ta fatan wata cikin tawagar su ta ƙyala idanu ta karɓe mata shi.

*****

Lokacin da Saubahn ya faɗi ƙasa a lokacin limamin masallacin ya shigo, domin ɗaukar wasu manyan littatafai da ya manta. Idannunsa akan Saubahn dake shimfiɗe tamkar gawa. Da sauri ya ƙarasa wajen tare da juya shi. Fahimtar yana numfashi ne ya sa ya hanzarta fita tare da samo yara su ka ɗauke shi aka fita da shi.

Kai tsaye gida aka wuce da shi, ruwa mai rangwamen sanyi ya sa aka samo, saboda yadda jikinsa ya ɗauki zafi rau kamar wuta. Take ya sa aka samo ya sa yara matasa kamarsa su ka soma goge masa jikinsa. Ban da kaɗawa babu abin da jikinsa yake yi. Sannu a hankali numfashinsa ya soma daidaita, a hankali ya soma motsawa har ya samu ya zauna da mazaunansa.

“Abinci! Yunwa na ke ji!”

Ya furta da muryar raɗa. Da hanzari Malam Liman ya tashi wani cikin matasan. Ruwan shayi ya sa aka kawo wanda ya wadatu da citta da kayan ƙamshi aka jingina shi da bango aka soma ba shi. Kurɓa ɗaya ya yi sai amai. Gaba ɗaya ya ba ta jikinsa da wajen,

“Mtsss!”

Wani cikin matasan ya yi tsaki, ganin yadda Saubahn ɗin ya ɓata wajen da amai yellowa shar.

“Kul Mahmuda, baka ganin a lalura yake? Kai ma baka fi ƙarfin ka samu kanka a wannan yanayin ba. Babu abu mai girma da darajar da ya kai ɗan Adam. Dan haka baka da ƙimar wulaƙanta mutuntakarsa.”

Jiki a sanyaye yake ba shi haƙuri, Saubahn kuwa jinjina kamalan malamin yake. Duk da yana cikin yanayin ciwo ya tabbatar hannu nagari ya faɗo. Gyara masa jikinsa aka yi tare da ba shi ruwa ya ɗauraye jikinsa.

Daga bisani Malam Liman ya sake sawa aka kawo masa wani ruwan shayin ya sake sha. Babu laifi jikinsa ya yi ƙarfi har ya miƙe ya jingina da bango. Ɗaya bayan ɗaya yake kallon yaran Malam ɗin kowa na ƙoƙarin yin abin da ya kamata. Lumshe idanu ya yi yayinda Madu ya faɗo masa a rai,

‘Ko me suke yi yanzu?’

Ya yi furucin a zuciyarsa. Surin buɗe idanu ya yi a ƙoƙarinsa na fatattakar tunanin daga zuciyarsa, sai dai hakan be hana zuciyarsa matsewa da tunanin jininsa ba. Zuciyarsa na sake yin zafi bisa hukuncin mahaifiyarsu a ransa ya furta,

‘Allah sarki Mamma kin kasa fahimtar cewa ita yanyawa tunkiyar ware take farmaka. Kamar hakane girma da martabar kasantuwarka cikin ahali take bayyana kanta. Domin su ɗin wani ɓangarene da zai girmama mutuntakarka. Ko da ba su baka komai ba za su iya zamo maka tagomashin kariya. Na tabbata da a a gida nake da tuni ƙannena na zagaye da ni.’

Wasu ƙwalla ya shiga sharewa ba tare da tuna cewa ga wajen da ya ke ba.

<< Kuskuren Wasu 4Kuskuren Wasu 6 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×