Kamar yadda rayuwa ta gadar game da zamantakewar auratayya a gidan malam Bahaushe haka ce ta kasance a gidansu Maryam. Kowa ce mace ita take ɗauke da ragamar ‘ya’yanta tun daga kan ci da sha da kuma sutura.
Tsakanin su da mahaifin su a sutura sai dai sallah. Ba damuwarsa ba ce ki ɗorawa ɗansa talla, abin da kawai ya sani shi ne zai baki tsabar hatsi don ki sarrafa abinci, ranar da yake ra'ayi ya ɗora kuɗin cefane ranar da baya yi ki nemo ko sata ce ki sarrafa ba damuwarsa ba ce.
Ɗa kuwa zai. . .