"Na lallace ban ci jarrabawa ba, shi ke nan wuyar ginin da na ci a banza!"
Ɗif ta yi shiru tana raba idanu komai ya soma zaga mata cikin kanta, wuyar ɗaukar ƙasa yana gewaye ƙwaƙwalwarta. A hankali ta lumshe idanu tana tuna ta rasa duk wani buri nata kenan? Dariyar Mama Sumaye ta jiyo tana faɗin,
"An ƙi sharar masallaci an yi ta kasuwa. An ƙi cin biri an ci dila. Yau dai ƙarshen boko ya zo a gidan nan sai a zo a zaɓi aure kamar kowace cikakkiyar ɗiya..."
"Baba don Allah kai wa Manzon. . .