Skip to content
Part 8 of 23 in the Series Kuskuren Wasu by Sanah Matazu

“Na lallace ban ci jarrabawa ba, shi ke nan wuyar ginin da na ci a banza!”

Ɗif ta yi shiru tana raba idanu komai ya soma zaga mata cikin kanta, wuyar ɗaukar ƙasa yana gewaye ƙwaƙwalwarta. A hankali ta lumshe idanu tana tuna ta rasa duk wani buri nata kenan? Dariyar Mama Sumaye ta jiyo tana faɗin,

“An ƙi sharar masallaci an yi ta kasuwa. An ƙi cin biri an ci dila. Yau dai ƙarshen boko ya zo a gidan nan sai a zo a zaɓi aure kamar kowace cikakkiyar ɗiya…”

“Baba don Allah kai wa Manzon Allah ka siya mini, an ce ana siya. Ba zan iya tara kuɗin da zan siya ba don Allah Ba…”

Wani bahagon duka ya kai mata da ƙafa, ya yi nasarar samunta a gefen idonta, ta dafe wurin tana jin wani yummm! A cikin ƙwaƙwalwarta yayin da ganinta ya ɗauke. Zuciyarta ta tsinke,

‘Idan na makance fa?’

Ta tambayi kanta, ba ta yi aune ba ya shiga dukanta kamar wata jaka,

“Irin jarraba irin masifa, kaicona da auren uwarki bai tsinanamin komai ba sai tashin hankali. Kaicon son ran da ya gindaya alaƙa tsakanina da jininku.”

Iya dakuwa ta daku, ga mari ga tsinka jaka. Ga rashin nasara, ga rashin cikar buri ga kuma duka. Ranar ta sake tabbatarwa ba ta da gata, aka rasa wanda zai ƙwaceta a gidan. Har sai da ya gaji don kansa ya barta.

Rarrafawa ta yi da ƙyar ta koma ɗakin da suke kwana. Kafin ka ce kwabo zazzaɓi ya rufeta, sai rawar ɗari ta ke yi. Haƙoranta na haɗuwa gab-gab. A haka ta yini babu wanda ya leƙota. Ga yunwa ga kuma tashin hankalin da take ciki. Sai zuwa la’asar ta samu ta fito da haɗa hanya ta nufi wajen Baba magini.

Ba ƙaramin tausaya mata ya yi ba, abinci ya siya mata ta ci daga nan ya yi mata nasiha kan ba komai bawa yake samu ba a rayuwa. Ita dama jarrabawa ta danganci haka, sa ace ƙoƙari da jajjircewa ba shi ne yake ba mutum ba face hukuncin Allah.

Ya jinjina rayuwarta tare da takaicin rashin kasancewarsa wani nata ko wani mai faɗa a ji, tabbas da yana ɗaya cikin bisa biyun babu abin da zai hana shi cikawa Maryam burinta.

Tun daga wannan rana ta haƙura da burinta na son karatu baki ɗaya. Cikin ikon Allah ta maida hankalinta kan karatun allo a haka ta yi saukar alƙura’ani da wasu littatafai irunsu ƙawadi da ahalari.

Daga baya ta ɗora da hadda, a makarantar da take zuwa akwai wani almajiri buzu, ta sha jin wasu na kiransa da ba’arewa ce amma babu wanda zai ce takamaiman inda ya fito. Sun shaƙu da Maryam sosai.

Almajirin mai suna Tasi’u wasu na kiransa da Tasi. Suna mutunci da ita sosai, shi ne malamin su na ajami, kuma yana ko ya mata karatun boko duk da da farko ƙi ta yi saboda haushin faɗuwarta jarrabawa.

A hankali ya dinga ribatarta da nasiha da shawarwari har ta amince. Ta saki jiki matuƙa da shi, musamman yadda ya gwada mata tausayi da jin ƙai matuƙa. Sannu a hankali alaƙarsu ta juye zuwa soyayya.

Tun tana ɗari-ɗari har ta saki jiki, babu irin habaicin da ba ayi mata ba amma ta toshe kunnuwanta. Babban ƙalubalan da ya so taɓa zuciyarta shi ne, yadda su Mama Sumaye su ka dinga kwarzanta ba shi da asali.

Ba’asn asalinsa ba, da fari abin ya ɗan dameta. Amma daga bisani sai ta yi tunanin to ita ina nata asalin? Ba ta da abin nunawa ta ce shi ne abin tinƙahonta don haka auren Tasi shi ne rufin asirinta. Dan haka babu musu ta amince masa ya fito aka yi bikinsu.

Ba wata uwa mahaifinta ya tsinana mata ba, daga katifa sai fululluka da abin da ba arasa ba. A ranar ta ƙara yin kukan rashin uwa fiye da tunaninta. Su Mama Sumayye kuwa bidiri su ka yi sossai domin auran yara huɗu aka yi a gidan, Zainab da Kulu yaran Asabe da kuma Laminde da Kande yaran Barira.

*****
Rayuwar Maryam a gidan Tasi rayuwa ce mai kyau da inganci, tattashinta ya ke yi kamar ƙwai. Suna wata biyar da aure, ya ɗauketa ya kaita dangin mahaifiyarta ba dan ranta ya so ba. Ta hanyar kwatancen da mahaifinta ya ba su bayan ya gama gasa musu baƙaƙƙen maganganu.

Don ma dai yana jin kunyar Tasin ne saboda duk Juma’a zai zo ya gaishe shi tare da ɗan hasafin na goro. Hakan ya sa yake shakkarsa matuƙa, sai dai zuwan na su bai ƙarawa Maryam komai ba face takaici da danasani.

Basu sami wata tarbar arziƙi ba, sakammakon tun asali basa ƙaunar auren mahaifinta da kuma mahaifiyartata. Kasancewar tun a baya ɗan’uwanta ne ya so aurent ta ƙi, saboda mahaifin Maryam ɗin ya riga shi fitowa nemanta, Allah ne ya haɗa su ƙaddarar rabon haihuwarta ya zamo tsani.

Sun haɗu ne a kasuwar cikin gari, ‘yar kutungu, shi ya kawo wakensa na suya da ya noma ita kuma ta shiga siyaya saboda ƙaratowar azumi. Tsautsayi ya sa jakar kuɗinsa faɗuwa, kuɗi ne masu yawa a lokacin, kuma a yadda yake da maƙo hankalinsa ba ƙaramin tashi ya yi ba. A lokacin da ta tsinci jakar ba ta yi gaggawar kai wa sarkin kasuwa ba, ta dai riƙeta a hannunta ta cigaba da siyan bin da ta zo nema.

Har zuwa lokacin da ta ji ana cigiya, bayan tambayoyi aka tabbatar da mallakinsa ce, har gida ya rakata yana yi wa mahaifinta godiya tare da yaba tarbiyar da ta samu. Mahaifinta Mal Audu baduku, sana’arsa ke nan ɗinkin takalma da kuma layu da ɗinkin ƙwarya. Yana da matar aure guda ɗaya wato mahaifiyar su Baba Harira. Mace mai sauƙin kai da kawaici. Tana sana’ar sayar da tubani.

Mal Audu baduku mutum ne mai ƙaramin ƙarfi, sai dai kuma jajjirtacen mutum ne mai neman na kansa mai kuma gudun wulaƙanci tare da magana kaifi ɗaya. Duk da kasantuwarsa mai ƙaramin, yana ƙoƙari wurin ganin yaransa sun wadatu ilmi daidai gwargwado.

Kama daga karatun addini har zuwa karatun primary da kuma na secondary, daga nan sai ya aurar da su, daga bisani idan mai gidanki na da ra’ayi sai ki cigaba a gidansa. Duk yaran sa daga kammala S.S.C.E ba sa wuce wata biyar ko shekara ya aurar da su.
Khadija ita ce ɗiyar shi ta farko da ta shafe shekara biyu da kammala karatu, sai dai ubangiji bai bata mijin aure ba, sa’o’inta a dangi da maƙota daga masu yara biyu sai uku. Hakan ya damu mahaifinta matuƙa da gaske, mahaifiyarta na nuna masa komai hukuncin Allah ne.

A haka aka sake shafe shekara guda, ba nacin da ba ta yi ba Mal Audu ya bar ta ta cigaba da karatu shi kuma ya dage kan sai ta fitar da mijin aure. Tun abin ba ya damunta har ya soma damunta, ta rage walwala da kuzari ko cikin dangi.

Ana haka kwatsam ƙaddarar haɗuwarta da Tukur ta gindaya, tun daga lokacin sai ya zamana duk san da ya shigo kasuwa sai ya zo sun gaisa da Mal Audu da ‘yar tsarabarsa. Cikin ƙanƙanin lokaci ya zama ɗan gida.

Khadija kan saki fuska su gaisa sosai idan ya zo, har ma ya soma ba ta ajiya na wasu kuɗaɗensa, idan ya dawo ranar kasuwa ya karɓa. Kafin ka ce kwabo shaƙuwa ta shiga tsakanin su. Tun tana kaucewa har ta saki jiki.

Abin da Khadija ba ta fuskanta ba, Mal Tukur ya yi dumu-dumu cikin ƙaunarta, tashin farko bai shawara da kowa ba ya tunkari mahaifinta. Shi kuma bai jinkirta ba ya amsa buƙatarsa. Lokacin da Khadija ta samu labari take ta yanke jiki ta faɗi, domin a lokacin ta soma soyayya da ɗan yayar mahaifiyarta sai dai daga ita sai Yaya Kulu da Yaya Iro suka san da batun. Ko da ta farfaɗo atabau ta ce ba za ta aure shi ba, mahaifinta kuwa ya lashi takobin ƙarya ne ta mayar da shi mai magana biyu.

Hasalima gani yake kawai ta raina masa hankali babu wata soyayya da suke da ɗan yayar Innarta ta, shekararta nawa a gida amma basu sn hakan ba. Wannan shi ne asalin abin da ya ƙula gaba tsakaninta da shi. Nan da nan Khadija ta fita hayacinta ta rame, tun suna ɗaukar abun wasa har abun ya soma damun mahaifanta. Da kuka da komai take roƙonsa,

“Baba ka da ka ba ni shi, bana son sa garin su ƙauye ne.”

“Uwata ƙauye ba ya hana mace ta samu aljannah ƙarƙashin inuwar aure ke dai ki yi biyaya ki kuma karɓi ƙaddara. Ni kaina ban san dalilin zabar Tukur matsayin wanda za ki rayu da shi ba amma ki bar wa Allah.”

Wannan shi ne furucin daya rabata da mahaifinta. Mahaifiyarta ta zauna ta nusar da shi, ƙwarai ya gamsu ya yi kuskure, sai dai kuma ya ba ta haƙuri tare da nuna mata shi mutum ne mai magana ɗaya, ba zai zubar da girmansa a wurin Tukur da danginsa ba.
Nan fa hankalinta ya sake tashi, ‘yan uwanta da yawa gani suke asiri ya yi wa mahaifin su. Maimakon su tausheta sai suka ƙara rurawa abun wuta. Musamman da suka ji asalin garin da Tukur yake zaune can cikin ƙauyen Malumfashi ne. Ba su da wuta, ba su da ruwa kuma ba su da hanya mai kyau bare makarantun boko.

Yaya Kulu ta fi kowa zugata, har ɓoye ta suka yi, sai da suka ga ran mahaifin su ya ɓaci har ta kai shi ga yanke jiki ya faɗi sannam suka shiga hankalim su, su ka fito da ita. Gaba ɗaya ‘yan uwa da dangi su ka nemi yi masa bore kan labarin auren, amma kuma bai sare ba haka ya ɗauketa ya ba wa Tukur aurenta domin cikar mutuntakarsa.

Wannan ya sa gaba ɗaya ‘yan uwanta su ka tsani auren. Gashi ƙarin haushinsu wanda taƙi aure shi ne mai arziƙin ahalin su kuma tun daga lokacin ya janye wajen yi musu hidima. Bayan auren da ɗan lokaci ne, Khadija ta saduda ta miƙawa ubangiji lamuranta, sai take ganin kamar ubangiji ya yi nufinta zuwa garin ne domin ta zamo haske ga wasu al’umma.

Domin ta fuskanci tarin kura-kurai da yawa tattare da su, haka kuma ƙarancin ilmi da rashin wadatar tarbiya. Nan ta shiga nunawa su Yaya Kulu ita fa sai yanzu ta fahimci wani babban rabo ne ke tattare da ita idan ta yi haƙuri.

*****
“Tabbas ƙaddarar da ta jefo ni gidan Tukur mai girma ce.”

Shi ne furucin da ta yi wa Yaya Kulu a wata ziyara da ta kawo musu, suka fahimci tana da shigar cikin Maryam ƙarami. Aikuwa ina wuta su jefa ta, ta inda suke shiga ba ta nan suke fita ba. Amma atabau Khadija ta nuna musu ita fa ta ga wurin zama. Kuma za ta rungumi ƙaddara a duk yadda ta zo mata.

To fa wannan ya tunzura zuƙatan ‘yan uwanta, da ma ko bayan auren ba ziyartarta suke ba, haka kuma sau tari za ayi abu a dangi ba ta sani sai dai idan mahaifinta ya ziyarceta. Domin waya ma ba samuwa take ba, saboda ba su da service. Mahaifiyarta kuma ba mace ba ce mai zuwa gidan ‘ya’ya. Allah da ikonsa mahaifin su ya faɗi ya mutu shi ke nan su ka sake mantawa da lamarinta baki ɗaya.

Haka Khadija ta cigaba da rayuwa a gidan Tukur da daɗi babu daɗi, kasantuwarta macen da yake ƙauna sai ta zamo saniyar ware a cikin matan. Uwa uba sauyin da ta zo da shi a garin gaba ɗaya ya ƙara mata ƙima da wata irin mutuntawa. A haka ta cigaba da rainon cikinta har Allah Ya sauketa lafiya.

Gata da kulawa sun same shi a wurin Tukur ita da abin da ta haifa, ranar suna yarinya ta ci sunan Maryam haka suka cigaba da rainonta cikin so da kulawa. Maryam tana da shekara ɗaya a duniya mummunar ƙaddara ta gindaya tsakanin mahaifanta.

Haka kawai babu siɗi ba saɗaɗa Tukur ya yi wa Khadija saki uku. Wannan takaicin sakin ba tare da hujja ba ya sanyata yasar da tatsitsiyar ɗiyarta ta bar masa gidan. Haka ta tattara ta dawo gida ranta babu daɗi.

Lokacin da auranta ya mutu danginta kamar su zuba ruwa a ƙasa su sha haka su ka ji, musamman mahaifiyarta. Nan da nan aka soma rige-rigen kaiwa Alhaji Salisu labari wanda a lokacin yana da matar aurensa da yaran su tagwaye guda biyu Hussain da Hassan. Sai dai kuma lokaci ɗaya su ka fuskanci Khadijan za ta ba su matsala, ta hanyar nun ƙulafucinta kan abin da ta haifa ta kuma baro a gidan auranta.

Tun sun ɗaukar abin da wasa har su ka soma tattaunaw kansa, dan haka ba su yi wata-wata ba su ka ɗauki matakin da suke ganin ya dace su ka yi mata farraƙu da ɗiyarta da kuma tuna garin da ta barota gaba ɗaya.

Wannan shi ne musababbin da ba ta ƙara waiwaitar rayuwar Maryam ba. Aka sha bikinta da masoyinta ya ɗauketa su ka lula Kaduna ya haɗe su da uwargidansa. Sai dai ba su san cewa sun kai Khadija makasarta bane, domin da ita da babu duk ɗaya su ka koma a wajen Salisu. Domin dai Hajiya Hauwa ita take shimfiɗa mulki san ranta a cikin gidan.

*****

Dalilin baƙin Khadija da Maryam ke gani kuwa ya samo asali ne kan ranar da su ka je da maigidanta, a ranar mahaifiyarta ta zo, sai dai ga mamakin Maryar maimakon ta ga rawar jiki ko murnar ganinta musamman shekarun da aka shuɗa sai ma taga kamar ƙyamatarta take yi. Haka su ka dawo gida zuƙatan su babu daɗi, ita dai tsabar takaici hawaye ma ya ƙafe a idanunta.

Tun daga lokacin ta ɗauki alwashin ba ita babu mahaifiyarta har abada. Babu yadda Tasi bai gwada mata ba, amma fafur ta ce atabau ita ta haƙura da su. Ƴan uwanta na gidan su sun isheta ta nuna ta ce ga danginta ko da babu zumunta tsakanin su. A haka su ka cigaba da zaman su, gwanin ban sha’awa.

Wanki da hidimar gida duka tare suke yi, daga bisani ya shirya ya tafi aikin gininsa kafin ya dawo ta shirya masa lafiyayyen abinci. Rayuwa suke cikin godiyar ubangiji, wata rana a fita a samo wata rana kuma a dawo haka. ba ta taɓa nun masa gazawart ba sai dai ajizanci irin na ɗan Adam.

Maryam ta so soma sana’a ko don tallafa masa da wasu hidindimu na gidan. Amma ya nuna mata sam baya buƙata. Rashin sabo da zaman banza ya sanya take jinta a matuƙar takure. Sai ta yanke shawarar soma yin fanke da safe. Da farko Tasi ya nuna mata ɓacin ransa amma daga bidami da ya fahimci manufarta sai ya ƙyaleta. Sosai hakan ya taimaka mata, idan ana wata hidima haka ta biki ko suna ba ruwanta da tambayarsa. Haka kuma ƙananun yara na gidansu musamman mata masu tasowa marasa mahaifa ta kan ɗan siyi omo da sabulu ta danƙa musu domin su amfana.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 3

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Wasu 7Kuskuren Wasu 9 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×