Lokaci-zuwa lokaci takan shirya ta ziyarci gidan su duk da ba wai wani nishaɗi zuwan yake ba ta ba. Sai dai ta fahimci sauyi sosai a mutanen gidan. Mahaifinta ya rage sakin mata, sannan Mama Sumayye ta sami rauni ta ɓangaren juya matan gidan. Haka kuma yaran gidan manya akwai tausayi tsakanin su da ƙananan saɓanin baya.
Su Sa’ade da take ɗan rarrabawa Omo kan su yanzu ta fahimci akwai nutsuwa a tare da su. Kuma da damar su sun koma islamiyya. Sai dai halin Mama Sumaye ne sai ubangijinta domin babu abin da ta rage na daga ɗabi’unta.
Shekarar su ɗaya da aure ta haifi Saubahn. Sosai suke ƙaunar yaron. Yana da shekara ɗaya da rabi ta haifi tagwayenta maza guda biyu aka saka musu suna Ahmad da Abdallah. Amma Ahmad ɗin suna kiransa da sunan Madu.
“Abu Saubahn gaskiya a bar shi da Ahmad ɗin sa amma mene ne wani Madu”
Shi ne furucin da Maryam ta yi masa lokacin da aka sanya sunan. Murmushi ya yi wanda ya taso masa da wani miki,
“Maryama rashin sanin wane ne Tasi’u shi ya sa har ki ƙalubantar sunan Madu a cikin yaranki. Amma tabbas Madu wani jigo ne na rayuwata.”
“Amma me ya sa ka ke ɓoye mini waye kai?”
“Ba ɓoye miki nake ba, ina gudun ku faɗa irin ƙalubalan dana faɗa ne. Kinga rayuwar gidanku Maryam ba komai ba ce akan rayuwar gidanmu da ƙabilata. Don haka ki sa a ranki rashin sanin asalina gata ne gareku da kuma kwanciyar hankalinku.”
“Ba ƙalubalantar nake ba, amma ka san duk daran daɗewa danginka su ne ado wa goben rayuwarmu.”
“Na sani, amma wani adon guba ne a rayuwar bawa komai nagartarsa.”
“Amm….”
“Mubari Maryama mu bar batun.”
Ya roƙeta. A lokacin ta so ya ba ta labarin danginsa amma ya nuna mata akwai sauran lokaci. Karon farko da sa’insa ta gindaya tsakanin su a zamantakewarsu. Rigima har gaban Malam babba malamin su amma dai shi ma haƙuri ya ba ta. Domin ya tabbatar mata shi kansa wayar gari ya yi ya ga Tasi’u cikin almijransa. Domin ba ya daga cikin waɗanda iyaye ne suka kawo shi. Ganin fushi ba zai kai ta ya sa ta tattara ta haƙura ta sauko ta rungumi yaranta suka ci gaba da rayuwa.
Yarinta da rashin sanin yadda za ta kula da kanta musamman a matakin kwanika ya sanya rayuwar ta soma yi mata wahala. Hakan ya sanya Tasi ya soma yi mata kwaɗayin tazarar haihuwa. Wanda ita kuma Maryam ta ɗauka a ya soma tsanar haihuwa ne ƙiri-ƙiri ta fito ta nuna masa ba za su yi tazarar haihuwa ba. Shi kuma kafe kan sai ta yi. A nan ma sun so samun saɓani, sai daga baya ne da ya zauna ya fahimtar da ita dalilinsa ta fahimce shi. Daga ƙarshe ma sai ta fahimci ashe ita yake son yi wa gata.
Maryam ba wai gudun haihuwa nake ba. Ina guje miki wahalar raino ne musamman ke da ki ke yarinya……”
“Shi ke nan Baban su Madu na amince.”
“Ki kira ni da Abu Saubahn ɗina ya wadatar.”
Dariya ta yi kawai. Washegari kuwa ya ɗauke ta suka nufi asibitin Katsina, tun shigar su garin ya fahimci yadda ta tsare gida. Ya san haka yana da nasaba da kadda ya yi mata batun zuwa gidan kakanta Baduku ne. Don haka be ma soma yi mata batun ba.
Suna nan zaune har layi ya zo kanta ta miƙe ta shiga ofishin. Ba ta fi minti biyu da shiga ba ta fito, shi ta nema ya shiga suka shiga tare, da sallama suka shiga aka amsa musu.
“Ka yi haƙuri ta ce mana tare ku ke shi ya sa muka nemi ganinka.”
Matashiyar ta furta tana murmushi,
“Sanin ƙa’idar aiki ne shi ya sa.”
Abokin aikinta ya tayata, kai Tasi ya kaɗa yana gamsuwa da hujjarsu,
“Da sanina za ta yi, ni ma na Sakata ta yi.”
“Ko kana da hujja?”
“Ƙwarai kuwa, Maryama ƙaramar yarinya ce, sannan kuma duka yaronta shekararsa ɗaya da rabi ta sake haihuwar wannan na bayanta. Ina guje mata ta sake maimaita hakan shi ya sa na ga ya dace ta ɗauki mataki.”
“Daga wane gari kuka zo, saboda ta ce mini daga wani ƙauye ku ka zo kuma sai na ga kamar kai ɗin kana da alamun wayewa……”
“Dr Asiya likita wai ko jarida?”
Abokin aikinta ya tambaya. Wani kallo ta watsa masa, sai dai kafin ta sake magana wani masinja ya shigo kiranta daga ofishin ogansu. Tilas ta fita amma kuma tana yi tana waiwaye don ba haka ranta ya so ba. Abokin aikinta ne ya juya yana duban su,
“To kamar dai yadda ku ka sani tsarin iyali abu ne mai kyau. Ko na ce ba da tazara tsakanin haihuwa da kuma haihuwa. Sanan kuma shi bayar da wannan tazara yana da hanyoyi daban-daban.
Ku sani ire-iren hanyoyin aiwatar da tazarar haihuwa na wucin gadi yana da alfanu da kuma haɗurra…”
Ido Maryam ta zaro,
“Ka ji ko?
Ta faɗa tana ƙure shi da idanu. Shi kuwa gaba ɗaya ba ta ita yake ba ya ƙagu su bar wurin saboda Dr Asiya. Ba ya muradin ta dawo ta same shi domin ya lura wani kallon ƙurilla takewa fuskarsa musamman ƙasan haɓarsa. Ras! Gabansa ya faɗi tunawa da tambarin dake nuna ƙabila da ahalinsu.
Ɗazun a sace ya kai kallonsa kan tata haɓar. Ba ƙaramun kaɗawa gabansa ya yi ba saboda ganin irin nasa tambarin sak. Yana da yaƙinin ko ita wace ce jininsa ce.
“Yi haƙuri ƙanwata, ai haɗɗuran ba irin wanda ki ke tunanin bane. Amma zan miki bayani dala-dala idan bai gamsheki ba sai ki sauya shawara. Sai dai bara na fara miki da shawarwarin.
Kamar yadda aka san mace da yin jinin haila ko wane wata, ƙyankyasar ƙwan haihuwarta ne ke kaiwa ga zubar jinin haila. Kowane wata ƙwai ɗaya ke nuna daga jakar kwayayen haihuwar ’ya mace, idan ƙwan haihuwar ya gama nuna sai a ƙyanƙyashe shi, ya bi hanya zuwa mahaifa. Da zarar an ƙyanƙyashe kwan haihuwar mace, to lokacin cikar yabanyarta ya fara ke nan.
Ƙwan haihuwar mace yakan ɗauki kwana uku zuwa biyar kafin ya isa mahaifa. A lokacin da ƙwan ke tafiya, shimfiɗar mahaifa za ta cika, ta ƙara kauri, don bayar da dama ga ƙwan haihuwar namiji saukin isa ga kwan haihuwar ’ya mace.
Idan ibadar aure ta faru a wannan lokaci, in Allah Ya so kuma aka samu shigar ciki, shi ke nan sai cikin ya kafu a cikin mahaifa, ya ci gaba da girma. Idan kuma ba a samu shigar ciki ba, ƙwan zai ci gaba da zama na tsawon kwana uku zuwa biyar, kafin shimfiɗar mahaifar ta narke, sai a fitar da ita tare da ƙwan, wannan shi ne jinin haila.
Idan mace ta tantance ranar da ƙwan haihuwarta ke ƙyanƙyasa, sai ta kiyaye waɗannan ranaku, ta kididdige ranar maimaituwarsa a kowane wata, don kauce wa ibadar aure ko daukar wata hanyar hana shigar ciki a wadannan ranaku.
Hanyoyin hana ɗaukar ciki kuwa muna da su da dama, akwai allura akwai kuma tsinke. Sai kuma ƙwayar magani. Allura akwai ta wata biyu akwai ta wata uku. Magani kuwa shi shan sa kullum ne kuma a daidai lokacin da aka soma shan sa ba a saɓawa. Idan takwas na dare aka soma sha to kullum sai takwas ɗin nan za a sha shi. Sai kuma tsinke da ake sakawa a damtsen hannu. Baya ga su akwai hanyoyin hana ɗaukar ciki kamar su:
Lura da yanayin jiki ko al’ada: wannan ya ƙunshi tsananta lura da sa ido ga canzawar yanayin jiki da ke bayyana lokacin gabatowar jinin haila, haka mace za ta rika lura har ta gano ranakun yabanyarta, waɗanda idan mijinta ya kusance a waɗannan ranakun, lallai za ta samu shigar ciki. Idan aka tabbatar da waɗannan ranaku, sai ma’aurata su riƙaa tsallake waɗannan ranakun wajen ibadar aure, ko kuma su yi mafani da wata hanyar hana shigar ciki a wadannan ranaku na cikar yabanya.
Kiyaye Canzawar dumin Jiki: Mace kullum za ta ɗauki ɗumin jikinta da tsinken auna ɗumin jiki (thermometer), ana ɗaukar ɗumin jikin ne kullum idan an tashi daga barci kafin a sauka daga wajen kwanciya. Duk ranar da ta ga ɗumin ya ƙaru sama da na kullum, to ranar ƙwan haihuwarta na wannan wata zai ƙyanƙyashe.
Canzawar ruwan maziyyi: Mace za ta sa ido ga yanayin ruwan maziyyinta. Maziyyin da ke fita lokacin ƙyanƙyasar ƙwan haihuwa fari ne, mai kauri, mai lema kuma mai laudi, yana taimakawa ga yiwuwar haɗuwar ƙwan haihuwar mace da namiji cikin mahaifa.
Amma maziyyi kafin kyankyasar kwan haihuwa, da kuma gab da gabatowar jinin haila mai launin ɗorawa ne, sannan ba shi da kauri kuma ba shi da lema. Sai dai yawan shan kayan da’a da wasu matan ke yi na iya sa yawan zubar ruwan maziyyi, don haka zai yi wuya su iya tantance ranakun kyankyasar kwan haihuwarsu ta wannan hanya.
Tsinken IUD Don Hana Shigar Ciki: IUD wani siririn tsinke ne mai siffar harafin T, yana da siririn zare a kowane bangare, ana sanya shi cikin mahaifar mace don hana shigar ciki, ko idan cikin ya shiga ya hana tsiruwarsa cikin mahaifa.
IUD iri biyu ne, akwai wanda ke dauke da sinadarin copper, wanda a hankali zai rika turara cikin mahaifa, yana hana ƙwayayen haihuwar namiji isa ga ƙwan haihuwar mace ballantana har a samu ciki. Sannan akwai sabon samfurin wannan tsinken da ake kira da IUS, shi kuma yana ɗauke da sinadarin ’yanmatanci progestin, wanda shi ma a hankali sinadarin ke turara cikin mahaifa, ya hana shigar ciki ko kafuwarsa cikin mahaifa. Yana ɗaukar tsawon shekara biyar zuwa goma yana aikin hana shigar ciki, ya danganta da samfurin da aka yi amfani da shi.
Matsalolinsa:
•Babbar matsalarsa ita ce, akwai yiwuwar a samu shigar ciki alhali yana cikin mahaifa, wanda hakan na iya sa wa cikin ya zube lokacin da ya kai wata huɗu zuwa shida. Zubar da cikin da ya kai wata huɗu kuwa haramun ne a shari’a.
•Haka kuma akwai yiwuwar a samu tsiruwar ciki a wajen mahaifa, wanda hakan zai iya zama barazana ga lafiya da kuma rayuwar uwar da ke dauke da cikin, da kuma abin da za ta haifa.
•Yakan sa yawan zubar jini tsakanin wannan haila zuwa wata, kuma yana sa jinin hailar ya kara yawa da nauyi.
• Akwai yiwuwar tsinken IUD ya lume cikin mahaifa, kuma sinadarin copper da ke cikin IUD yana iya huɗa mahaifa.
• Sannan yana sa yaduwar ƙwayoyin cuta a mara da ’yanmatanci da mahaifa”
Gaba ɗaya tsit suka yi, musamman Tasi da shi ya jagoranci zuwan na su don haka jiki a sanyaye ya miƙa masa hannu,
“Dr ina ga mun haƙura kawai”
Ya faɗa yana aje ƙwarin gwiwa a saitinta domin ya lura cewarsa kawai take jira. Take kuwa ya ga ta saki wata irin ajiyar zuciya. Tausayinta ne ya kama shi. Wato har ga Allah ba ta so amma kuma cewarsa ne togonsa. Sai ya soma zargin kansa da kadda ya shiga haƙƙinta.
Tunawa da Asiya ya sa ya yi saurin tashi suka bar wurin bayan ya yi wa Dr ɗin godiya. Suna tafe tana lura da yadda yake waiwaye har da tuntuɓe. A haka suka hau napep sai lokacin ta ga ya saki ajiyar zuciya. Murmushi ta yi kawai a ranta tana ƙudurce duk ranar da ta shigo Katsina sai ta nemi asibitin ta kuma nemi wannan baiwar Allahr don ta lura kamar kallon sani take masa.
Ko bayan sun koma gida sai da ta yi masa ƙorafi.
“Abu Saubahn kamar matar nan ta sanka?”
“Wace haka?”
“Ta asibiti”
Jim ya yi. Kamar kuma wanda aka mintsina sai ya hauta da faɗa. Ba don tabyarda da furucinsa ba na cewa irin ƴan matan nan ne masu neman mazan aure ba ta haƙura.
Sam ko kaɗan ba ta ji cewar Asiyan ta yi kama da hakan ba don dai ya ƙi ba ta dama ne. Ba ta so hakan ba matuƙa, wani tsoro na ɗarsuwa a ranta game da rayuwarsu. Sau tari idan ta yi wa Tasi maganar Ahali takan ga canji a tare da shi baya maraba da hakan ko kaɗan. Amma shi ɗin gwani ne wajen nuna mata ta ziyarci dangin Mamarta.
Ya sha ɗaukarta da kansa ya kaita duk da babu wata mutuntaka da suke samu mahaifiyarta kuwa babu damar ganinta ko kaɗan. Sau biyu suna haɗuwa a zuwan da su ka yi da sallah lokacin Saubahn na da shekara uku su Abdallah ɗaya da rabi.
Sosai ta zage ta zageta tas tare da yi mata korar kare daga lokacin ta sake gina katanga mai tsayi tsakaninta da mahaifiyarta. Gidan su kuwa takan je lokaci zuwa lokaci da ƙunshin alkhairinta ga mahaifinta. Matansa babu ruwanta da su iyakatarta su gaisa.
Tun daga ranar aka rufe batun tazarar haihuwa. Domin daga ita har shi ba su cewa za su iya ba.
Shekarar Bakin Ciki
Suna shekarar su ta uku da aure gwanin ban sha’awa. Rayuwa ta miƙa sosai suke kulawa da junansu. Lokaci zuwa lokaci Tasi kan ce mata zai je gida amma be taɓa karambanin ya je da ita ba, ita ma ba ta taɓa nuna masa tana san zuwa ba tunda ta ga baya so. Ta rungumi yaranta tare da maida hankali kan sana’arta.
A shekarar ne Tasi ya yi abin da ya ƙara ƙima da mutuntakarsa a zuciyar Maryam. A asirce ba tare da saninta ba ya tara kuɗinsa ya shiga cuku-cukun nema mata gurbin zana jarrabawa. Sai da ya gama komai sannan ya sanar da ita muradinsa na son ya maida ita makaranta . Ba ƙaramin farin ciki ta yi ba da abin da ya aikata. Mafarkan da take tunanin ba za su samu gareta ba ashe suna tafe.
Cikin ikon Allah ta zana jarrabawa sakammako ya fito, kuma tana cikin ɗaliban da su ka yi nasara. A lokacin an samu wayewa sosai a ƙauyen su ta fanin karatu da kansa ya nema mata gurbi a wata makarantar matan aure ta yaƙi da jahilci wadda suke ɗaukan masu matakin karatun primary kamarta. Kasancewar akwai ƙwararrun malamai masu tsayawa tsayin daka. Duka shekara uku kowane ɗalibi yake yi yi sai su zana jarrabawar NECO da WAEC.
Maryam ta dage sosai ta maida hankalinta kan karatu, cikin tsakanin ne mijinta ya gina musu gida madaidaici nesa da unguwarsu. Domin wanda suke ciki na malaminsa ne. Gida ya yi masha Allah ginin bulo da bulo ya sha shafe da siminti mul-mul.
Su Mama Sumayye ba ƙaramin baƙin ciki su ka yi ba, domin dai Maryam ba ta rasa komai ba sai ma cigaba da ta samu. Haka su ka tare su ka cigaba da gudanar da rayuwar su. Sai ya zamana ta nesanta kanta da gidan su sosai tun daga lokacin.
Ba ta zuwa kwata-kwata tun wani zuwa da ta yi aka ji wa Madu rauni kasancewarsa yaro me na ci da kafiya idan ana faɗa da shi. Amma lokaci zuwa lokacin ta kan samu aiken gaisuwa daga bakin mijinta in ji mahaifinta.