Skip to content

Kuskuren Wasu | Babi Na Uku

4.5
(2)

<< Previous

Wata Ƙaddara

Tun farfaɗowar Yaya Kulu bayan ƙaramin ɗanta ya yayafa mata ruwa ta tsunduma tunani kan yadda zata shawo matsalar data tunkarosu. Babban baƙin cikinta asarar data tafka na maƙudan kuɗaɗɗan da tana da tabbaci kan ba lallai ta sake samun kamarsu ba. Musamman yadda al’amuran plaza ɗinta suka ja baya sossai akan shekarun da suka shuɗe. Wayarta ta ɗauka jiki babu ƙwari ta dana kira. Bayan ƴan gaishe-gaishe ta ɗora da,

“Malam matsalar…”

“Buƙatarki ta iso tun tsayin lokuta, abu uku muke buƙata daga gareki shi ne. Za ki sayi baƙar saniya a yankata. Wanda zai yi yankan zai saka fararen kaya, a tara jinin a roba in ya gama a cire kayan a tsomasu a jinin. A je gidan tururuwa a yi rami ko suri a saka a ciki. Akwai layu guda biyu kan katangarku ta waje, kisa a ɗauko za ki sami tarwaɗa a cire kan ki buɗe ki saka a ciki kisa wani abu ki ɗaure bakin tarwaɗan. Bakin Khadija zai rufe ruf kan batun ɗiyarta amma sai kin kula sossai. Domin a yanzu haka ɗiyarta nada kusanci da ku sossai tana nan cikin Katsina kuma tana buƙatar agaji kadda ki kuskura su yi gamo da juna.”

“Malam babu yadda za ayi tabar garin?”

“Ƙaddararta na zama cikin garin me girma ce, akwai tashin hankali ga duk wanda ya yi yunƙurin datse igiyar data yi naɗi wa zaren ƙaddararta.”

“Na gode Malam zaka ga saƙo!”

“Mun riga mun ɗauki saƙonmu, ki duba inda kika ajiye wata kaddara taki me girma anan muka zari kasanmu bama aikin banza.”

Ras gabanta ya faɗi data tuna da sarƙarta ta miliyan biyu da rabi. Baki na rawa ta yi nufin yi masa magana amma tsawar da ya daka ta dakatar da ita.

“Musunki na nufin ɓata aikinki”

Ɗif wayar ta ɗauke, runtse idanu ta yi ga mamakinta sai ga ƙwalla. Wata tsana me girma ta sake ƙabura a zuciyarta game da Maryam tana jin da tasan zata zamo tarnaƙi ga rayuwarta da sun kauda ita tun kafin zuwanta duniya kamar yadda wasun su suka bayar da shawara tun a baya. Kai tsaye ɗakinta ta nufa ta soma binciken wajen da ta ajiye sarƙar. Sai dai sama ko ƙasa babu sarƙa babu dalilinta. Hannu ta ɗora aka tamkar zata tsala ihu, sai dai shigowar babbar ‘yarta a yanayin da ya ja hankalinta ya sa ta maida hankalinta kanta.

“Kausar daga ina ki ke?”

Sai da ta yatsina fusk kamar ba zata tanka ba, sai kuma ta fuske.

“Gidansu Naja’atu na je na karɓi na saƙo!”

Kamar zata sake jefa mata wata tambayar, amma bata bata damar hakan ba. Ta yi saurin kara waya a kunnant kamar an kirata. Wayar ƙarya ta kama yi a haka ta shige ɗakin tana satar kallon mahaifiyarta ta. Tana shiga ta danna sakata tare da zaro kwalaban maganinta. Ɗaya bayan ɗaya ta soma gwamutsa na gwamutswa tana jinta kamar wadda aka yi wa bushara da gidan aljannah.

*****

“Abba sannu da zuwa”

Yaran suka furta suna dubansa a ɗan tsorace. Kauda kai ya yi yana cin magani. Daidai lokacin data ajiye taɓaryar hannunta tana kwashe yajin data dakawa maƙotansu aka biyata.

“Ahmad maza zo ka kaiwa Indo dakanta, idan ta baka kuɗin ka siyo muku gari da ƙuli da mai a zo aci lokacin shiga karatu na ƙaratowa.”

Bata kali inda yake ba, har yaron ya yi abinda ta umarceshi. Hakan be dameshi ba burinsa kawai ta haɗa garin da shi. Yana kallo ta share zufa tare da sake ɗaukar masarar da aƙala ta kai tiya ɗaya ta juye cikin babban turmin ta soma surfawa.

“Ke Maryama!”

Bata amsa ba, amma ta dakata tare da zuba masa idanu alamar ina saurarenka. Tsaki ya ja tare da faɗin,

“Kin maidani ɗan iska saboda kin soma kama mutsabai ko?”

Takaici da mamaki ne suka nemi kasheta. Idonta ya sauka kan Afnan da ta lura tana gunguni tare da aikawa mahaifin nata harara. Wani tsoro me girma ya ɗarsu a ranta tana gudun a sake maimaita kuskuren baya.

“Me kake buƙata?”

“Abinci”

Ya faɗa kai tsaye, galala ta yi tana dubansa, a saninta rabon da ya bata sisi harta manta. Yaranta kuwa har tausayi suke bata. Hatta da sallah basu san su saka sababin kaya ba sai dai kwance tsawan rayuwarsu. Ballantana ita kanta, bata taɓa ganin miji me ƙyashi da hassadar mijinta ba, ita kam ba dan tsananin rabo ba bata jin zata haifi waɗanan ƴaƴan da suka haifa tare kodan gudun rayuwar ƙaskancin da tun ba yau ba ta karanceta a idanunsa. Amma ƙaddara ta riga fata.

“Ka jira Ahmad ya dawo”

Ta furta tana ƙoƙarin maida ƙwallar idanunta,

“Wallahil azim Mamma ba zai ci shi ba, ki nema da guminki kuma ki ba wani ƙato? Ki ci da shi ki ci da ƴaƴansa amma a wofince!”

Saubahn ne ya yi furucin da murya me zurfi, ga wata ƙwalla kwance a idanunsa. Ido ta zuba masa a tsorace, bakinta har rawa yake yi. Tasan halin Saubahn sarai. Akanta zai iya da kowa amma bata hango ɗa me ido a fafatawarsa da Nuhu. Humaira kuwa dake gefe, hannu ta ɗaga masa alamar jinjinawa.

“Lallai wuyanka ya isa yanka Sauban ni kake cewa ƙato? Kin gani ko Maryama kin ga abin da kika haifa ko? Lallai ne koda yake babu haufi ga mutumin da ba asan asalinsa ba. Ai tsintaciyar magge bata magge. Dangin dangiroro ne ba haufi.”

Wani ƙaton ramine ya sake buɗewa a zuciyar Sauban, ya ɗago da kai idanunsa jajir, tamkar ɗan bududugin kwaɗo a ruwan barkono.

“Ba asan asalinmu ba amma ana manne damu ana cin arziƙi…”

“Sauban dan ubanka zo ka bar gidan nan kafin raina ya ɓaci in nakasa ka!”

Ta yi furucin wani marayan kuka na taho mata. Da mamaki cikin knsa yake dubanta. Zuciyarsa na tunasar da shi, “wannan jarumar uwa ce fa, ita ce take iƙirarin ya fita ya bar gidan da da guminsa a cikinsa. Da tabbatuwar yadda furucinta ke samun mazauni a zuciyarsa yana sake jadadda masa kamar furucin na yi masa nuni ne da ta ga ji da shi a cikin ahalinta. A karo na barkatai ya dake jinjina girman fifita mijinta akan kansa. Ba yau ne farau ba, amma duk da ƙanƙantar shekarunsa da take hangowa yana mamakin yadda makantar son rai take gindaya tunaninta.

Kallon Mamman yake da dukkan zuciyarsa, wasu shafukane suke sake buɗe masa tare da ajiye manyan taban da be san ranar cikar gurbinsu ba. Be yi aune ba ya soma jin saukar duka ajikinsa, dukansa take badan bata sansa ba, sai dan guje masa baƙar zuciya irin ta Nuhu. Ita take dukan amma ciwukan a zuciyarta take jin saukarsu. Yanayin da take kai hannu kansa kaɗai ya isa tabbatarwa me hankali ciwon daga zuciya yake.

Tsaye ya yi yana kallonta tana dukansa, bai ko motsa ba kuma ba shi da niyyar hakan. So yake tabunan dake zuciyarta su ƙara kumburin da za su asassa ciwon da zai buɗe idanunta daga makanta kan mutumin da ba komai ba ne arayuwarsu. Wannan alaƙar yake san datsewa, yana so ta rayu a bigiren da babu nauyin maha’incin mutum kamar mijinta. Ya alla koba komai ƙuncinsu zai sauƙaƙa fiye da kowa.

“Ka fita ko in maka baki Sauban!”

Duk wasu notika na jikinsa sai da suka daina aiki! Dubanta ya ke yi amma idanunsa na lalluban idanunta dan san gasgata furucinta,

“Eh! Ka tafi ka yi nisa da rayuwarmu bama buƙatarka!”

Malam Nuhu kansa da kullum burinsa ganin ya nesanta ta da Sauban ɗin ne sai da ya girgiza. Be taɓa tsamanin ranar zata zo masa a kusa ba, amma bazai bari damar ta kuɓuce masa ba,

“Me ka ke jira ba ka ji abinda ta ce bane?”

“Na ji Baba kuma zan tafi ba anjima ba yanzu ma kuwa”

Karon farko a rayuwarsa ya kirashi da Baba tun bayan kashedin da ya yi masa kan kuskuren aikata hakan,

“Kadda ka sake kirana da babanka ni ban haifi ɗan iska irinka ba. Shege me idanjn mayyu”

Shi ne furucin da ya shata layi tsakaninsu a baya dan haka be taɓa kuskuren sake kiransa da kalmar ba. A fusace yake da shi dan haka ya ci gaba,

“Mamma zan tafi zan yi nisa da ku, ba kuma zaki sake gani na ba har sai lokacin da ki ka gajiya wajen neman inda nake. Ina fatan kadda ki makara!”

Daga haka ya juya da sassarfa yana barin tsakar gidan akan duga-dugansa. Tafiya ya ke kan ƙafafunsa amma zuciyarsa ce take motsawa. Tana matsewa da wata irin kewa na ahalinsa. Yasani Mamma ta yi hukunci ne dan gudun abin da zai faru gareshi amma be taɓa tsamanin zata iya nesanta shi da ahalinsa ba. Me ya sa zata zaɓi alawa ta yasar da zinare? Bayan yana da yaƙinin zaƙinta ba zai dawwama a kan harshanta ba.

Kai tsaye tasha ya nufa. Ba shi da tabbaci kan garin da zai nufa dan haka motar data rage na neman cikon mutum guda ita ya nufa kai tsaye ta tashi da shi zuwa garin da zata nufa.

Lokacin da Ahmad ya dawo ba ƙaramin mamaki ya yi ba ganin su Afnan na kuka. Tambayar duniya sunƙi bashi amsa sai shassheƙa da ajiyar zuciya. Kasancewarsa mutum me zuciya tu ni ya cika ya yi fam ganin hakan yasa Humaira da suke kira da Afra ta daure ta yi masa bayanin abin da ya faru.

Badan yasan Humaira ba zai iya cewa ƙarya take, duka dai gata shekarunta ba masu ya wa bane amma yana da tabbacin ba zata yi wa mahaifiyarsu ƙarya ba. Da wani irin ɓacin rai yake kallon mahaifiyar tasu sai dai ba shi da ƙumajin tanka mata dan haka ya ajiye ledar garin jiki a sanyaye ya juya ya bar gidan. Babu inda be zaga ba a tashar amma be ga ko me kama da yayansu ba. Zuciyarsa ta cika da ƙunci yayinda kansa ya soma barazanar buɗewa. Me yasa Mamma zata yi musu wani giɓin a rayuwarsu? Bata san Sauban shi ne bangon rayuwarsu ba? Wace irin rayuwa take buƙatar su yi? Ba shi ya koma gida ba sai goma na dare. Zuwa lokacin gaba ɗaya ƙannan na shi sun yi zuru-zuru. Da gudu Afnan ta rungumeshi tana kuka,

“Baka ganshi ba ko?”

Ba shi da karsashin bata amsa dan haka ya jinjina kai kawai yana bubbuga bayanta,

‘La illah illalahu Maryama me zan gani zo ki ga yadda ɗanki ya ƙwaƙumemun ƴa dama zaluntata kuke?”

Jinkita babu inda ba ya rawa tsabar tashin hankali, domin ta gama fassara inda kalamansa suka nufa. Musamman yadda ya buɗe murya maƙota na ji. Ahmad kuwa tsabar takaici sai ya sake matse Afnan a ƙirjinsa so yake sai ya gwadawa mutumin nan iyakarsa.

“Ahmad ka cikata idan ba so kake baƙin ciki ya ƙarasani ba!”

“Mamma ke kika siyi tikitinsa da kanki saboda ai kinsan zaɓin da kika yi rayuwarki ba shi ki ka zaɓa ba. Shi ki ka zaɓa akan gobanmu?”

Ya faɗa yana nunashi da yatse tare da danne mikin kewar ɗan uwansa,

“Zamu barki da shi Mamma. Zamu barki da shi da halins..”

“Ba zamu barta da shi ba Ahmad”

Abdallah ya furta yana auna masa mugun kallo,

“ai hakan yake buƙata tare da muƙarabansa ya kasheta har lahira. Ni zan koya masa hankali zan nuna masa mu ma ƙarfinmu ya kawo…”

Gabanta ne ya faɗi tasan halinsa. Ya fi kowa zuciya cikin yaranta yana da haƙuri da shanye abubuwa amma be iya fushi ba. Basu yi aune ba ya ɗagashi ya buga da kasa, gaba ɗaya suka yi kansan. Amma ban da dukansa babu abin da yake yi. Malam Nuhu kuwa gaba ɗaya ya fita hayacinsa, amma kuma a ƙasan zuciyarsa babu nadama ko ɓurɓushinta. Da ƙyar aka ƙawaceshi a hannunsa dan sai da ya yi masa dukkan kawo wuƙa. Nan ya ta shi yana bambami tare da aibata mata yara kamar yadda ya saba, abu na farko da ya fi komai ƙona mata rai. Kuma take jin ko shi kaɗai ya isa shata layi a zamantakewarsu. Amma ta rasa wai shin menene yake riƙeta? Wace irin kaifaffar igiya ce ta yi mata ɗaurin talala a rayuwarta da ta Nuhu.

Baki a fashe, yana ɗingishi haka ya dinga ratsa majalisu yana faɗa musu ƙarya da gaskiya. Daga nan ya nufi babbar majalisar unguwar wato gidan me unguwa. Nan ya zauna ya rattaba masa ƙarya da gaskiya, aka tarkato Mamma da iyalanta. Cikin ƙasƙanci da nuna tsagwaron rashin mutunci ya saki baki ya dinga zuba musu shari. Mamma ta yi kuka, ta yi kuka kamar ba gobe. Ta yi nadamar data san cewa ita ce tushenta. Jiki a sanyayye suka baro wajen, domin dai buƙatarsa ta biya duniya ta aibata mata yara.

Washegari haka suka raɓata duk suka fice gaisuwa ce kawai ta haɗasu. Ahmad ya sake ninkawa tasha da fatan ganin Sauban. Yayinda ƴan matan suka wuce zuwa makaranta rai babu daɗi. Abdallah kuwa shi ya zauna tare da ita kasancewar ya zana jarrabawar barin sakandire sakammako suke jira shi da Ahmad. Haka suka yini babu daɗi. Sai da Ahmad ya shafe kwana biyar kullum tasha yake yini yana aikin dako duk ba ba ya ra’ayinsa, yana kuma yaƙinin zai ga yayansa amma shiru maƙatau babu labarinsa.

*****

Tun daga ranar Mamma bata sake ganin dariyar Ahmad ba, iyakarta da shi gaisuwa. Maigidan kuwa be sake samun ƙimar gaisuwa ta ratsa tsakaninsu ba. Su Afnan su ne abokan hirarsa. Idan ya fahimci Mamma zata shiga sai ya yi gum. Duk inda yake tunanin zai ga ɗan uwansa ya bincika amma babu labarinsa. Ƙarshe ya samu tabbacin an ganshi a tasha ya hau mota, daga ranar ya sakawa ransa sallama ya ci gaba da yi masa addu’ar kasancewa a hannu nagari.

Sai dai Mammarsu ta dasa wani ciwo me girma a zuƙatansu. Ta haifar da giɓin da ya zamo masu bame warkewa ba. A hankali sai hidima ta soma hawa kan Ahmad ɗin. Karatunsa ya tsaya cak, islamiyyarma sai Asabar da Lahadi yake yakicewa ya je, shi ne tasha shi ne jari bola haka.a Abdallah ya fantsama bakin titi saida ruwan leda. Facin takalmi da sauransu. Sannu-sannu sai suka soma zama kamar wasu almajirai. Basu damu da wanki ba, saɓanin da da duk sati yayansu zai haɗasu su wanke hadda na Mamma. Su Afnan kuma su yi guga.

Ahmad na takaicin rayuwar da suke yi, har baya jin shayin gwaɓawa Mamma magana saboda zafin da zuciyarsa take yi masa. Ta sani, sun sani Sauban shi ne ƙarfinsu. Duka-Duka Sauban ɗin shekarunsa goma sha takwas ne dan dai yana da tsayi da garin jiki. Ahmad kuwa sha biyar gareshi shi da Abdallah kasancewarsu tagwaye. Sai Afnan da Humaira masu shekara goma sha biy biyu cif a duniya suma tagwaye ne. Takacin Ahmad be wuce na yadda ba shi da ƙumajin rungumar ƙanansa kamr yayansu ba.

Tunda ya zamana babu Sauban sai Mamma ta ƙara ƙaimi wajen faffutukar nema musu abin da zasu saka a bakin salati. Sai dai kamar rufe ƙofofin ake a gareta. Gaba ɗaya surfenma ya daina samuwa. Wankau idan ta karɓa ruwan wankin wahala yake mata saboda babu me ƙarfin jido ruwa kamar Sauban. Sai yanzu ne take jin ta tafka babban kuskure karo na uku a rayuwarta. A hankali damuwa ta soma nuƙurƙusarta, ciwon kai da ƙirji suka zama abokanta sannu-sannu ta soma kwanciya yau ta miƙe gobe ta kwanta. Ciwo ne me girma yake cin zuciyarta sai dai duka tana ɗora alhakin wahalhalun rayuwarta akan baiwar Allah Khadija. Matar da ta wofintar da bigiren tushan samar mata da nagartar ƙuruciya.

How much do you like this story?

As you found this story interesting...

Follow us on social media to see more!

Leave a Comment

Your email address will not be published.

You cannot copy content of this page.

CLICK HERE TO INSTALL THE APP
×