Skip to content
Part 12 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Tun da suka isa Kano kai tsaye gidan Iyayen Hafiz aka wuce da ita wanda yake ciki tindim da ‘yan biki ‘yan’uwa da abokan arziƙi. Ɗakin baƙi aka sauki amarya da ‘yan rakiya bayan sun idar da salolinsu suka ci abincin da aka kawo masu wanda sai da Maman Zhara tayi da gaske sannan Halima ta ɗan tsakure kaɗan taci,  Aunty Sumayya ‘yar’uwar su Dady ce ta shigo ɗakin bayan ta sake gaida baƙin ta kira Maman Zhara suka fito falon baƙi suka zauna akan kujera cikin damuwa Aunty Sumayya ta ce.

“Ina ta ƙoƙarin na gama aikin da Yaya ya sani da wuri sai nayi sammakon tafiya wajanku tare da su Yaya Nuratu kawai sai Yaya Babba (Dadyn Hafiz) ya kirani wai ba sai mun zo ba, bayan ya zo ne yake faɗa mana duk yadda aka yi. Gaskiya ba mu ji daɗin faruwar hakan ba. Muna murna za a yi haɗin zumunci sai kuma lamari ya zo da sauyin da ba mu yi tsammani ba.”

“Haka Allah ya nufa babu yadda za mu yi bayan mu karɓi hukuncin nasa hannu bibbiyu. Kowa hakan abun ya zo masa a bazata” Mama tayi maganar tana murmushi, “Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, amma Hafiz bai kyauta mana ba. Ina Zhara?”

“Amin Ya Rabbi. Ku daina ganin  laifinsa  wallahi matar mutum ai ƙabarinsa. Zhara na gida bata zo ba” Afra ‘yar ƙanwar Momy ta shigo tana faɗin “Aunty Momy na kiranki.” 
“Ok ki ce da ita ina zuwa, bari na tafi, Allah ya fito mata da wani mafi alkhairi.”

“Amin dan Isar Annabi (S.A.W) bari na biyu ki ai mu gaisa da jama’ar gidan” ta yi maganar tana mai tashi tsaye.

“Wai ina kika shiga ne tun ɗazun ina ta nemanki.”
“Na je mun gaisa da Maman Zhara ne” Momy ta ɗan yamutsa fuska tana faɗin “ki ce kin je kin jajanta masu a kan asarar a suka tabka.”

“Asara kuma?” Aunty Sumayya tayi tambayar cikin mamaki  Momy na murmushi ta ce.  “Asara mana  anga samu anga rashi duk a lokaci ɗaya” gyaɗa kai kawai ta yi dan sai yanzu ta fahimci ina ta dosa, ita ta rasa dalilin wannan ƙiyayyar ta Hajiya Turai da Maman Zhara. Murmushi Maman Zhara tayi tare da ƙarasa wa cikin ɗakin ta tsaya daga gefe “Ina wuninku?”

“Lafiya lau” wasu daga cikin ƙawayen Momy suka amsa,  “ana ta hidima to Allah ya sanya alkhairi ya basu zaman lafiya.”

“Amin idan har addu’ar ta kai zuci, dan nasan Allah kaɗai yasan irin baƙin cikin da yake ranki. Allah na tuba ka tara jama’a  ka gama shela kowa ya zo za ka aurar da ‘ya kawai ranar aure ta zo ango ya ce ya fasa baya so ƙawa ce zaɓinsa ai babu abinda ya kai wannan baƙin ciki da kunya.”

Ta nuna Mama tana faɗin “wannan ce uwar amaryar da Hafiz ya ce bai so akai kasuwa ya zaɓi ƙawarta saboda yana tunanin tafi tarbiya”

“Allah sarki abun ba daɗi wallahi, ai tayi ƙoƙari da har ta zo biki. Sannu kinji” aminiyar Hajiya tayi maganar idanunta akan Mama, murmushi kawai Mama tayi ta bar ɗakin ba tare da ta ce da su komai ba dama tun kan ta zo Abba ya gargaɗeta da kar yaji wata rigimar ta ɓullo. “Gaskiya Hajiya baki kyauta ba, sam wannan ba daidai ba ne, da Hafiz da Zhara duk abu ɗaya ne, sannan abun kunya ai bai wuce wanda Hafiz ya yi ba”

“A’a ba ɗaya ba dai kam, ɗana ya fi su ta ko ina ki ma daina haɗasu. Kuma babu ruwanki bai shafeki ba idan za ki iya ji ko gani to idan ba za ki iya ba ki kama gabanki”
Aunty Sumayya ta fita ɗakin ranta a ɓace.

Hafiz  yana zaune gaban Dady ya sunkuyar da kan shi  yana magana ciki da damuwa “ina mai neman afuwarka Dady haƙiƙa na sani abinda nayi ban kyauta ba, amma wallahi daidai da rana ɗaya ban taɓa faɗa wa Zhara ban sonta ba, haka ban taɓa tunanin faruwar hakan ba. Kayi haƙuri Dady.”

Zuba masa idanu Dady yayi fuskarsa babu yabo ba fallasa “Da kake ta wannan ban haƙurin shin na faɗa maka kayi mini laifi ne?

Ka sa ni auren Zhara da niyar daga baya ka aure ƙawarta ku taru ku cutar mini da ita shi ne laifi mafi muni da za ka aikata mini wanda ba zan taɓa yafe maka ba.

Ina matuƙar son Zhara ina jinta tamkar ‘yar da na haifa ba  wai a matsayin ‘yar ƙanena kawai ba, zanyi matuƙar farin ciki a ce ta kasance a gabana a matsayin matar ɗana har abada, wannan yasa nayi tunanin haɗa aurenku amma duk ka rushe wannan ƙudurin nawa. AlhamdulilLah da Allah yasa ba sai bayan auren naku bane na san da wannan gagarumin cin amanar da kake da ƙudurin yi mini domin ba Zhara kayi wa ba ni kayi wa.”

Ya kalle Dady da sauri Dady ya gyaɗa kai “Eh ni kayi wa ba ita ba, har ga Allah a nawa ƙudurin fasa auren gaba ɗaya kamar yadda za a fasa na Zhara itama ɗaya yarinyar ba za a aura maka ita ba, amma Abbanku ya matsa ya kuma fi karfina wannan yasa har aka yi auren, ina maku fatan alkhairi.  Za ka iya tafiya” ya buɗe baki zai yi magana Dady ya ɗaga masa hannu “ban buƙatar jin komai daga gareka ka je Allah ya baku zaman lafiya” ya  tashi jiki a sanyaye ya bar ɗakin.

Wuraren ƙarfe goma a ka kai amarya ɗakin Momy in da ta bata kyautar zinari mai matukar daraja, tana tasa wa auren albarka farin ciki baki har baka. An so a kaita wajan Dady sai dai koda a ka je a faɗa masa a ka samu ya rufe ƙofa har ya kwanta, hakan yasa aka tafi kaita gidanta.

Bayan an kaita gidanta ‘yan’uwa sun watse daga ita sai ƙawayenta da suka zo dan ganin ƙwam  “ma sha Allah Halima wannan ai shi ake kira da gobarar titi a Jos,  wallahi gara da a ka yi, kyakyawan miji kyakyawan gida ga kayan ɗaki masu kyau da tsada ko ‘yar shugaban ƙasa albarka” cewar Hajara,  “nima dai maganar da nake a zuciyata kenan, Allah sarki Zhara gaskiya tayi missing ɗin kyakyawan gida” ta dafa kafaɗar Halima tana  ci gaba da magana “ya kamata ki daina wannan kukan hakan, Allah ne ya maki gam da katar ni banga abin damuwa ba, wallahi ko ni na samu wannan damar tuni zan yi wuff da shi”

“Ah to faɗa mata dai, gaba ɗaya kin hana kanki sukuni” ta janye mayafin da ta rufa da shi tana ci gaba da kuka “na sani ina son  Hafiz amma cin amanar da nayi  wa Zhara yana damuna sai nake ji sam ba zan iya zama da shi ba.”

“Tabdijam wallahi karma ki suma wannan banzan tunanin, Allah ya baki dama a maimakon ki gode masa sai kuma ki butulci masa, wallahi kar ki suma ai ba a kanki farau ba bare ya zama ƙarau ba.”

“Gane mini hanya dai ke bari ki ji wallahi ko ita ce ta samu damar da kika samu tsab za ta maki hakan. Sannan ko me ya faru ai KUSKURENTA ne ba naku  ba”

“Hajara, Na’ima duk yadda zan faɗa maku ba za ku taɓa fahimta ba. Kawai dai abar zancen”
“Da dai yafi maki, kuma wallahi ki rungume mijinki hannu bibbiyu ki kwashe soyayya da kuma kuɗi riba biyu inji sauro” shigowar Nana Khadija ne ya katse masu firan, ta bata waya tana faɗin “Yaya ne ya ce na kawo maki waya ya yi ta kiran wayarki a rufe.”

Ita bata ma san inda ta jefar da wayar ba tana gida ta barta. Ta karɓa tare da kanna wayar a kunneta. “Hello” ya yi shiru, “Hello ba kya jina

“Barka da wuni” ta yi maganar cikin sanyin murya, ya saukar da ajiyar zuciya tare da lumshi idanu  dukansu suka yi shiru na ‘yan daƙiƙu kafin ya kawar da shirun “na aiko yaro zai kawo kaya ki shirya za a zo a ɗauke ku zuwa wajan dena”

“Ni dai da an bar denar nan” tayi maganar kamar za tayi kuka, “nima na so hakan amma abokaina sun matsa sai anyi” yana gama faɗa ya tsinki kiran. Tunda ta faɗa wa su Hajara suka dinga murna.

*****

Hankali tashi ya mayar da ita inda ya sameta ya je ya ɗebo ruwa ya yayyafa mata amma ko motsi da sauri ya koma ɗaki ya ɗauki  mukullin mota bayan ya fito da motar ya zo ya ɗauketa suka nufi asibiti mafi kusa. Suna zuwa aka karbeta  likitoci na a kanta yana tsaye daga gefe yana kallonsu  sai addu’a yake akan Allah ya tashi kafaɗarta, aka  rubuta masa wasu allurai da ruwan jiki yaje ya sayo ba jimawa ya dawo bayan an gama ɗaura mata ruwan jiki likita ya nemi da suje office jiki a sanyaye yabi bayan likitan. 

Bayan sun  zauna “likita ina fatan dai ba wata matsalar ba ce ko?”

“Ka damu Baba In Sha Allah za ta samu sauƙi. Dama tana da ciwon zuciya?”

“A’a gaskiya ban taɓa saninta da ciwon zuciya ba ko da wasa” Abba ya bashi amsa yana kaɗa kai, “ba matsala, da alama akwai abinda ta tsawaitawa ƙwaƙwalwarta tunani akan shi wanda har hakan ya janyo ta yanki jiki ta faɗi, zuwa gobe idan jikin nata ya ƙara sauki za mu turaku wajan hoton zuciya dan mu ƙara tabbatar da tunanin da muke”

“Uhm! Allah ya kaimu. Na gode.”  Ya dawo ɗakin da a ka kwantar da ita ya zauna akan kujerar roba ya zuba mata idanu zuciyarsa ciki da tausayinta ko bata faɗa ba ya sani tabbas tana son Hafiz kawai ta sadaukar da soyayyarta ne ga ƙawarta. Yana ji a ran shi daga Hafiz har Halima basu kyauta mata ba, ya kuma ji ciwon abun fiye da tunanin yana dannewa ne kawai saboda baya son zumuncinsa da ɗan’uwan shi ya lalace.

*****

Washegari tunda safe  su Mama suka yi mata sallama bayan sun ƙara yi mata nasiha gami da zaman aure. A ka barta daga ita sai halinta, tana zaune falo akan kujera  tayi tagumi tana tunani har ya shigo ya zauna dab da ita sam bata ji ba, janye tagumin da tayi yayi ta ɗago a tsoraci ganin shi da tayi yasa ta saukar da ajiyar zuciya,  “wani irin tunani ne kike haka har na zo na zauna baki ji ba” tayi narai,-narai da idanu muryarta na rawa kamar za tayi kuka “gani nake kamar mafarki nake  so nake na farka amma na gagara garkawa, shi kenan na ci amanar amintarmu da Zhara” ta fashe da kuka rungumeta yayi jikin shi yana bubbuga bayanta  ahankali

“Kiyi haƙuri kukan ya isa haka,  Allah ne shedarki kinyi iyakar ƙoƙarinki ganin hakan bai faru ba, sai dai ita ƙaddara rigan fata take ina kuma da tabbacin Zhara za tayi maki kyakyawan fahimta, ki daina damuwa komai zai wuce kamar ba a yi ba kinji ko”

Ƙasa magana tayi sai dai kukan da take ta daina, “ba zan ɓoye maki ba, duk da auren nan ya zo ba yadda na so ba amma hakan bai hanani farin cikin cikar muradinmu ba, sannu a hankali komai zai wuce kamar ba a yi ba. Dama Dady ne nake tsoron fushinsa AlhamdulilLah ya sanya wa aurenmu albarka, ahankali zai huce dan haka ki cire damuwar komai a zuciyarki mu fuskanci rayuwarmu”   ya tashi tsaye tare da miƙar da ita tsaye, “mu je mu yi karin kumallo Babyna” ta rufe fuskarta tana murmushi haɗi da hawaye, shima ɗin murmushi ya yi mata tare da riƙi hannunta suka nufi Dani.

*****

Mama tana zaune gefen gadon da aka kwantar da ita ta riƙi hannun Zhara tana mata sannu, “Abban Zhara me yasa baka faɗa mini tun jiya ba?”

“Meye amfanin faɗa maki tunda dai ba biyu dare zaki yi ki dawo ba dai sai dai hankalinki ya tashi” Abba da yake zaune a kan kujera ya bata amsa yana kallon Zhara,  “ya jikin naki?”

“Na ji sauƙi Abba” ta bashi amsa cikin muryar marar lafiya. “Mamana ”
“Na’am”

“Na ji daɗi sosai da kika yi ƙoƙarin danni duk abinda kike ji har a kayi taro a ka watse, sai abu na biyu kinga hoton da a ka yi ya tabbatar da kina da ciwon zuciya wanda kema tun daren jiya da kika farka kukan da kike mini kenan zuciyarki ciwo take ji kike kamar za ta fashe. Na fahimci kina son Hafiz to alfarmar nake nema ki yi mini” ya yi shiru tare da zuba mata idanu kafin daga bisani ya ci gaba da faɗin. 

“Ki yi ƙoƙarin cire tunaninsa ko tunanin abinda ya faru domin samun lafiyarki da kuma kwanciyar hankalinmu, domin likita ya faɗa cewar matuƙar kika cigaba da yawan tunani da sanya abin a ranki zuciyarki za ta iya samun matsala wanda ba ma fatan faruwan hakan.”

Don Allah ki taimake mu kar mu rasaki saboda wani namijin da shi yana can yana farin cikinsa.  Itama Halimar manta wa za ta yi da komai tayi farin cikinta, dan haka don Allah kema ki manta da su a rayuwarki, kiyi sabowar rayuwa” Mama ta ƙarasa maganar tana share hawayen dake zubo mata, ɗaya hannun da ba a sa wa ruwa ba ta kai kan fuskar Mama tana share mata hawaye cikin sanyin murya ta ce. “In sha Allah zanyi abinda kuke so zan manta da komai ku tayani da addu’a akan Allah ya dafa mini”

“In sha Allah za ki iya Mamana, Allah ya maki albarkar. In Sha Allah za ki samu mijin da ya fi shi wanda zai sanya ki farin ciki duniya da lahira” lumshi idanunta tayi tana murmushi haɗi da zubar da hawaye. Tana ji a ranta ko dan farin cikin iyayenta dole ne ta ɓoye damuwarta, amma manta Hafiz abu ne mai matuƙar wahala sonsa ba da wasa ya shigeta kamun kazar kuku ya yi mata. Abba ya masu sallama ya tafi akan sai zuwa dare zai dawo.

Da dare Hajiyan Zhara ta zo ta dubata tana ƙara basu haƙuri Mama ta nuna mata komai ya wuce.

BAYAN SATI BIYU

Tana zaune gefen gadon Mama tana haɗa kayanta cikin ƙaramar akwati tana yi tana share hawaye, Mama ta shigo ɗakin kallonta tayi tana faɗin “wai har yanzu ba ki daina kukan nan ba?”

“Mama bana son tafiyar nan, ni dai da an ƙyaleni”

Zama tayi gefenta ta dafa kafaɗarta “Zhara ba ke kaɗai ce ba kya son tafiyar nan ba har mu ba ma sonta, kawai dan babu yadda za mu yi ne. Daga ni har Abbanki babu wanda zai iya ja da hukuncin Yaya, tunda ya ce ki koma wajansa da zama a can za ki cigaba da karatu to kiyi haƙuri ki sa wa zuciyarki son tafiyar kawai kar ki janyo wa kanki wani ciwon mun samu kin samu sauƙi”

Gyaɗa kanta kawai tayi ta cigaba da shirya kayanta, Hassan ya shigo yana faɗin “Aunty Zhara Yaya Mahamod na kiranki.”

“Yaya Mahamod kum?”

“Eh na gidansu Aunty Halima.”

“Oh yaushe ya dawo?”

“Ban sani ba yanzu dai na gan shi ya zo ya ce na kiraki. Yana nan ƙofar gida.”

“Ok kace da shi ina zuwa” ta ɗauki Hijab ɗinta “Kar dai ki daɗi kinga tun ɗazun direba ke jiranki. Bari na ƙarasa haɗa maki kayan kin tsaya shiririta kin san da tafiya tun jiya amma shiri ya gagareki.” sai da ta wanki fuskarta sannan ta fita.

Da murmushi a fuskarta ta ƙarasa gaban shi “oyoyo Yaya Mahamod saukar yaushe?”
“Jiya da yamma, na so na shigo da dare sai dai wani uzurin ya hanani zuwa” ya bata amsa da murmushi a fuskarsa,

“Allah sarki ba komai wallahi, ina wuni. Fatan an dawo lafiya ya karatu?”

“Lafiya lau, ya su Mama?”

“Suna nan lafiya lau” shiru ya ziyarci wajan kafin daga bisani ya kawar da shirun “na ji duk abinda ya faru banji daɗi ba ko kaɗan, ina mai ƙara ba ki haƙuri.”

“Haba wallahi, komai ya riga da ya wuce, sannan haka Allah ya nufa dukan mu ba za mu wuce ƙaddararmu ba.”

“Gaskiya Allah yasa hakan ne mafi alkhairi”

“Amin dan Ya RasululLah. Yau zan tafi Kano dama Mama ta ce na je nayi wa Hajiya Sallama ba mamaki ko tana da saƙo wajan Halima”

 “Ana wata hidimar ne?”

“A’a zan koma can ne da zama” cikin sanyin jiki ya ce. “Allah yasa hakan ne mafi alkhairi, ki bani numberki  sai a dinga gaisawa” bayan ta bashi ta ce “me za ka bayar a kai wa Halima” ya ɗan yi tsaki ba tare da ya bata amsa ba ya yi mata sallama tare da alƙawarin zai kirata idan ta isa. Bayansa tabi ta tafi tayi wa Hajiya sallama, itama ɗin tana mata maganar Halima ta basar jiki a sanyaye tabar gidan Hajiya na ta yi mata addu’a da sanya mata albarka.

Hassana ta riƙo akwati suka fito tare da Mama da Abba Mama na faɗin “kin dai ji me na faɗa maki ki ki iya kanki karki sa kanki ga abinda bai shafeki ba, kuma don Allah ki kiyaye Hajiya Turai karki yi abinda duk kika san zai janyo maku matsala a tsakaninku, itama Halima ban ce ki daina hulɗa da ita ba amma kar ki shige masu bare har wata matsalar ta kunno kai kinji ko?”

“In Allah ya yarda Mama zan kiyaye duk abinda kika faɗa mini”
“Yawwa Allah ya yi maki albarkar”

“Wai duk maganr da a ka yi cikin gida bai isa ba sai kun zo nan kun dasa wata!” Abba da yake tsaye wajan motar yayi maganar cikin faɗa, da sauri ta ƙarasa wajan motar tana ƙoƙarin haɗiye kukan da ya zo mata. Haka suka yi sallama da su ta shiga mota ba tare da ta yarda sun sake haɗa idanu ba, motar na fara tafiya ta fashe da kuka kamar wacce a ka aikuwa da Manzon mutuwa. “Ki yi haƙuri ba daɗi kam rabuwa da iyaye sai an kai zuciya nesa” direban ya yi maganar cikin sigar  lallashi.

<< Kuskuren Waye 11Kuskuren Waye? 13 >>

1 thought on “Kuskuren Waye? 12”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×