Skip to content
Part 13 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Tun bayan da suka isa take zaune a cikin Babban falon mai aikin gidan kawai ce take ta zirga-zirga. Tayi tagumi tana kallon jakar kayanta har a cikin zuciyarta bata son zaman gidan nan kawai dai dan babu yadda za tayi ne. “bari na je na sake faɗa mata babu mamaki ta manta ne” mai aikin ta faɗa tana haurawa sama, ita dai komai ba ta ce da ita ba. Ta samu suna zaune tare da baƙuwa falon sama.

“mene ne?”

“Hajiya baƙuwar da na faɗa maki ta zo n … Tsawar da ta daka mata ne ya hanata ƙarasa maganar.

“idan har kika sake zuwa mini da zancen yarinyar nan sai na ɓalla ƙafafun sai naga da wace ƙafar za ki zo ki dameni!”

“Kiyi haƙuri” tayi maganar a tsoraci tare da ficewa. Tsaki Momy tayi  “wai wace ce ne?”
“barni da abin haushi, wai yarinyar nan ce da Hafiz ya fasa aure shi ne saboda iya yi na Alhaji ya ɗauko mana ita wai za ta yi karatu a nan ɗin sai ka ce garin nan ne kawai ke da makaranta.”

“Ikon Allah lallai Alhaji a kwai neman magana, anya ba so yake sai anyi auren nan ba. Idan har ba wannan ne dalili ba banga abinda zai sa ya ɗaukota daga gaban iyayenta ya dawo da ita nan ɗin ba.” 

“Bar wannan zancen Hajjagana wallahi bai isa ba kin kuwa san yadda na tsani yarinyar nan kuwa?”

“To wai duk me ya janyo hakan yarinyar ba ta da halin kirki ne?”

“A’a ba na ce ba, kawai dai yadda Alhaji yake fifita sonta ne fiye da ‘ya’yan cikinsa ne yake ƙona mini zuciya. Haka uwarta sanda muke zaune a gida ɗaya tare da sarakuwarmu komai a ka tashi uwarta ake sa wa a gaba a kan duk wata hidimar gidan.  Kowa ya buɗe baki ita yake yaba wa. Ke wani lokacin ma fa sai nayi girki wallahi Alhaji yaƙi ci ya ce tuwonta yake so, mahaifiyar su Alhaji kuwa bata san ina za ta ajiyeta ba da ƙaunar da take mata ta wuce duk yadda zan faɗa maki. Idan nayi ƙorrafi a ce ba halinmu ɗaya ba, ita kuwa shigen iyayi har wanki ita take yi wa Inna da gyaran ɗaki kirki take mata na masifa tsabagin kissa matar nan ta iya.

Ni kuma Allah ya gani ba zan iya wannan munafuncin ba. Ai kuwa na ga ‘yan ubanci da baƙin hali  a zamana da ita shi yasa wallahi tun a wancan lokacin na tsaneta.”

“Lallai kya tsaneta wallahi. Ke ni fa ba na ɗaukar wulaƙancin uwar miji bare kuma iskancin matan sauri wallahi ai kin ma yi ƙoƙarin zama da ita ni da tuni zan sa a raba mana gida.”

“Tab Inna ai ba za ta yarda ba kin ga yadda na so barin gidan taƙi amincewar shi ma kuma Alhaji da kafiyar masifa. Sai bayan  da rasu da likkafa ta cigaba shi ne fa muka canza har gari. Kin ga tunda mijinta bai yi kuɗin nawa mijin ba take ƙoƙarin sai ta cusa wa ɗana ‘yarta a ci banza” tashi tayi tana faɗin “karki yarda da wannan kam, dan ba mamaki ma da wata ƙulalliyar a ka turo ta.”

“Barni da su wallahi walki nake na ishi ƙugun kowa, na fi ƙarfin duk wani siddabarun su. Na ga kin tashi kar dai tafiya za kiyi?”

“Eh tafiya zan yi dama na ce bari na zo nai maki Allah ya sanya alkhairi an yi aure ban ƙasar.”
“Ai na ji ba daɗi da ba kya nan. Ya kamata ki je ki ga amarya.”

Ta faɗa tare da tashi tsaye suna tafiya Hajjagana ta ce. “zan sa lokaci ai mu tafi na ga sarakuwar tamu…..”

Suna saukowa ta zame daga kan kujera kaɗan ta gaishe su, sai Hajjagana ce ta amsa mata fuska babu yabo ba fallasa, suka wuce ta ta gyara zamanta jikinta ya ƙara yin sanyi. Momy ta dawo daga wajan rakiya ta zauna a falon tana kallo “ina so zan yi sallah, ina ne ban ɗaki?”

“Ga shi a kaina!” Shiru tayi tare da sunkuyar da kanta ƙasa, Kadija ta shigo ta jefar da jakarta tare da kwanciya a kan kujera tana faɗin “washh Allana! Yau na ɗebo gajiya wallahi.”

“Sannu Kadina ya karatun?” tashi tayi ta zauna tana faɗin “karatu ba daɗi fa Momy. Kande! Kande!!”

“Na’am!” ta amsa tare da shigowa falon da sauri “Sai ai ta kiranki ba kya amsa wa mutane.”

“Ki yi haƙuri ban ji ba ne wallahi.”

Mtsww! Ni don Allah ɗauko mini ruwa a firij ki kuma kawo mini abinci.”

“Abincin yana a kan dani ai.”

“Na ce a nan nake so na ci ko!” Tayi maganar a fusace haƙuri ta bata tare da barin wajan. Ta buɗe firij ta ɗauko mata ruwa bayan ta kawo mata ta je ta kawo mata abinci ta zuba mata a filet  shinkafa da miya ne da ya ji naman kaji ta baje ƙasan kafet tana ci idanunta suka kai kan Zhara ta fito da idanu. “Au baƙuwa muka yi, saukar yaushe?”

“Ban jima da zuwa ba” ta bata amsa a taƙaici. “Oh sannu da zuwa to” ta faɗa cikin nuna ko oho tare da ci gaba da cin abinci. Tana gamawa ta haura sama Momy tabi bayanta. Ta kalle Kande da take gyara wajan da Kadija taci abinci tana faɗin “Don Allah ina ne banɗaki” kallon sama tayi a ɗan tsoraci kafin ta dawo da dubanta kan Zhara “Sai dai idan ɗakina zan kai ki.”
“Eh kai ne ko can ɗin ne, na gode.”

Bayan ta idar da sallolinta ta kawo mata abinci tana faɗin “ga abinci kiyi haƙuri mutanen gidan hakan suke da jiji da kai. Alhaji ne sai Dr Hafiz su ne masu son mutane ba kamar uwa da ‘yarta ba” murmushi kawai Zhara tayi mata ta janyo abincin tana ci dan yunwar gaske take ji.

*****

Da dare suna zaune a dani za su ci abinci Dady ya ce. “Ke Kadija ina Mamana?” Tsuru tayi da idanu ita har ga Allah ta manta da akwai wata a gidan, nan fa ta fara in da in da “um in t… “bari a kirata, ji ki ki kirata” da sauri ta tashi ta tafi kallon tuhuma yake yi wa Momy sai dai bata yarda ta haɗa idanu da shi ba ta fara cin abinci. Suna ƙarasuwa ya ja kujerar da take kusa da shi da murmushi a fuskarsa “Mamana zo ki zauna a nan”  zuwa tayi kusa da shi ta durƙusa har ƙasa “Ina wuni Dady?”

“Lafiya lau, fatan kin zo lafiya, ya su Maman naki?”

“Duk suna nan lafiya lau. Sun ce a gaisheku” tayi magana tare da zama kan kujerar, da kan shi ya zuba mata tuwon samo miyar kuɓewa tana faɗin “bar shi na zuba” komai bai ce da ita ba ya zuba mata tare da tura mata gabanta “maza ki ci” kallon juna Momy da Kadija suka yi tare da taɓi baki.

Bayan sun gama suka dawo cikin falo suna fira “za ki zauna ɗakin Kadija ko kin fi so a baki naki ɗakin?”

Kallon Kadija tayi da itama ita ɗin take kallo, in son samunta ne kam ta zauna ɗakinta daban dan za ta fi sakewa. Amma kuma ba za ta iya faɗa masa bata son zama da Kadija ba. “Dady zan zauna ɗakin Kadija.”

“Kadija ga ‘yar’uwarki nan sai ku zauna a tare” murmushin ƙarfin hali tayi tana faɗin “to Dady.” bayan yayi masu sai da safe Kadija ta tashi a zuciye ta haura sama tana magana ƙasa-ƙasa “kawai a zo a takura mutum ni gaskiya bana son takura” Zhara ta bita da kallo har ta ɓacewa ganinta “ke!” kallon Momy tayi a tsoraci “ba wani ɗakin Kadija da za ki zauna ki zauna tare da ‘yar aikin gidan nan dama kin fi dacewa da can ɗin dan ba wani banbanci ne ba a tsakaninku” to kawai ta ce tare da tashi tabar falon jiki a sanyaye kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki. Momy ta bita da harara.

Gaba ɗaya ba ta jin daɗin zaman gidan masu gidan sam basa yinta in har ka ganta a falon gidan to Dady ne yake dab da dawowa  Momy za ta sa a kirata yana  komawa sashinsa za ta korata. Da Kande kawai take samu suyi fira ko kuma wayarta tana chat su ne abokan firarta.  Tana kwance a kan katifar Kande tana chat a wayarta Kande ta shigo ɗakin “Aunty Zhara Hajiya na kiranki”

“Don Allah ki daina kirana da Aunty nan kin fa girmeni.”

“To ai ba zan iya kiran sunan naki ba ne amma bari na dinga kiranki da Maman masu gida tunda hakan na ji Alhaji na faɗa” murmushi kawai Zhara tayi tare da miƙewa ta ɗauki Hijab ɗinta tasa tare da zura takalmi a ƙafafunta ta fita ɗakin.

Ta samu tana waya Kadija kuma tana dannar waya. waje ta samu ta zauna ɗan nesa da su. “ina wuni Kadija?”

“Lafiya” ta amsa mata a taƙaici ba tare da ko ɗago kanta tayi ba daga kan wayarta. Shiru tayi ta mayar da dubanta ga tv tana kallo. Bayan ta idar da wayar ta kalle Zhara a wulaƙanci ta ce. “na ga ki na so ki mayar da gida wajan hutawar ki iya kici ki kwanta to ni ba zan ɗauki hakan ba. Daga yanzu girkin gidan nan ya dawo kanki, har sauran ayukan gidan ki dinga yi tare da Kande.”

“To Momy”

“Shi kenan kiran jiki ku ɗora girkin dare” bayan fitarta Kadija tayi tsaki “wallahi na mugun tsanarta sanda ba ta gidan nan ban wani damu da ita ba sai zuwanta. Sam Dady baya wani kulani da zarar ya dawo ita ce abokiyar firarsa Mamana Mamana yenyen!”

“Ki ma daina sa ta aranki ki barni da ita aikin wahala zan dinga sa wa tana yi ta yadda za ta gudu da ƙafafunta” shigowar Hafiz ne yasa suka bar zancen a ka faɗa wani zancen. “Yaya yaushe za ka kawo mana Aunty Halima ne?”

“Ke ba za ki je ba sai dai ita ta zo to ba za ta zo ba” yayi maganar yana harararta
“Allah sarki Yaya ka ga ni makaranta ta sani a gaba banda lokaci sosai shi yasa, yau ma dan yana asabar ne na samu na zauna a gida.”

“Sannu alhudada sarkin karatu”

“koma dai me za ka ce ta ji ɗin. Ai ya kamata dai a ce ka kawota tun zuwanta zuwa ɗaya kawai tayi”

“Zan kawota In Sha Allah Momy. Yawwa ni kam ba an ce Zhara ta zo ba ne amma duk zuwan da nake bana ganinta.”

“Ina ruwanka da zuwanta me za ta yi maka idan ka ganta ne?” tayi masa tambayar cikin faɗa. “kiyi haƙuri Momy ni ba wani abun nake nufi ba kawai dai na ga ya kamata mu gaisa.”

“Mtsww! Tashi ka bar gidan nan, kuma daga yanzu in har ka san saboda ka ganta ne kake zuwa gidan mun yafe ka daina zuwa” murmushi yayi idanunsa a kan Momy ya ce. “fushin duk a kan nayi maganar Zhara ne. To kiyi haƙuri har gobe ban taɓa jin sonta a zuciyata ba ni Momy na ma manta da waccan maganar. Ita ɗin ƙanwata ce kamar dai Kadija.”

“Tab Allah ya tsare gatari da saran shoka. Ni wallahi a daina wani haɗani da ita dan na fita ta ko ina” harararta yayi zai yi magana Momy tayi saurin taran numfashinsa “ka ga don Allah tashi ka tafi gidanka bana son neman rigima” sallama yayi masu ransa a ɓaci dan har ga Allah ya ji haushin maganar Kadija.

Zhara da take kichen tasa bayan hannunta tana share hawayen da suka zubo mata duk abinda suke faɗa a kunnenta maganar Hafiz ce ta dinga dawo mata a kunnenta “har gobe ban taɓa jin sonta a zuciyata ba. Ni Momy na ma manta da wancan maganar!”

lumshi idanunta tayi hawaye suka sake kwararowa daga cikin kurmin idanunta zuwa fuskarta.   ‘Ya Allah ka rabani da son ma so wani ƙoshi wahala. Ubangiji ka cire mini son abinda ba zai zama rabona ba alfarmar Annabi (S.A.W)’ jin motsin Kande ne yasa ta saurin kai hannunta a fuskarta tana goge hawayen da ya ɓata mata fuska.

“Maman masu gida ki zauna kawai ni zan yi girkin.”

“Aa ki bar shi zan yi dama na gaji da zaman babu abin yi, ina so na fito nayi aikin ina tsoron kar nayi laifi a wajan masu gidan. Kin ga tunda ta bani dama shi kenan faɗuwa ta zo daidai da zama.”

“Uhm! Shi kenan bari na tayaki aikin. Ki dai ci gaba da haƙuri tabbas abinda suke basa kyautawa wallahi” murmushi kawai Zhara tayi ba tare da ta ce da ita uffan ba.

*****

Kwance suke a kan gado tana kwance a kan ƙirjinsa yana wasa da sabon kitson da yake kanta. “Baby yaushe za ka kai ne gida Allah ina kewar su Hajiya”

“Duka kwananki nawa da zuwa da har za ki fara tafiya gida.”

“Haba dai gida ne fa ba wani wajan ba. Ka fa san yadda na bar gida kuma har yanzu Hajiya fushi take dani bata ɗaga kirana tun bayan da na kirata da sabon layina ta fahimci ni ce bata sake ɗaga wa ba, Baba ne kawai muke magana har Yaya Mahamod baya ɗaga kirana. Ina so na bata haƙuri.” ta ƙarasa maganar tana zubar da hawaye. Tashi yayi ya jingina bayansa ga kan gado tare da sake janyota jikinsa ya kusanto fuskarta da tashi yana share mata hawayen da hannunsa yana magana cikin lallashi “kiyi haƙuri In Sha Allah wani satin za mu je mu bata haƙuri kuma na tabbatar za ta haƙura, ki kwantar da hankalinki kin ji Babyna.”

Murmushin jin daɗi tayi ta mayar da kanta a ƙirjinsa tana shaƙar ƙamshin jikinsa.  “kuna waya da Zhara kuwa?” ɗaguwa tayi ta zuba masa idanu gabanta na dukan uku-uku. Me yasa zai mata zancen Zhara ita fa ko sunan ba ta so ta ji a bakinsa. “wannan kallon fa?” Yayi mata tambayar yana ɗaga mata gira. Murmushi tayi tana gyaɗa kanta ta ce. “ba komai. Ka san banda numberta kuma ina ta so na tambayeka number sai ina sha’afa.”

“Tana gari idan kun haɗu sai ki karɓi number a hannunta.”

“Kamar ya tana gari ban fahimta ba.”

“Eh ta dawo nan da zama nake nufi yanzu haka tana gidanmu za ta ci gaba da karatunta a nan ɗin” sosai maganar ta daki zuciyarta har ta kasa ɓoye abinda yake zuciyarta fuskarta babu annuri “Hum ta zo tayi karatu fa ka ce?”

“Eh hakan Dady ya ce za tayi karatunta a nan ɗin” ta yamatsu fuska “wani munafuncin dai ne yasa a ka dawo da ita nan ɗin dama na ji a raina dole watarana sai an yi ƙoƙarin sake cusa maka ita tunda ita ɗin ‘yar gwal ɗin Dadynka ce na sani tabbas sai an nuna mini ‘yan ubanci!”

Kallonta yake da tsananin mamaki “Halima kanki ɗaya kuwa? Waye yake yin munafuncin kenan Dadyna ne munafukin?”

<< Kuskuren Waye? 12Kuskuren Waye 14 >>

3 thoughts on “Kuskuren Waye? 13”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×