Kallon ta ta ke a tsorace ta ce. “Lafiya Halima na gan ki haka, ko wani ne babu lafiya a gida.”
“Mtsw! Kowa ƙalau na zo ne na ba ki haƙuri a kan abin da ya faru.”
“Wani abin ne ya faru?” Kawar da kanta gefe ta yi ta na faɗin,
“Ni ba na zo ne mu yi dugon zance ba, na je gida ne Mama ta sa na mata alƙawarin zan nemi yafiyar ki, kuma sai har idan kin tabbatar da kin haƙura sannan ita ma za ta haƙura.” Da murmushi a fuskarta ta ce,
“Ai ni tun farko ban ɗauki auren ki da Yaya Hafiz da zafi ba, tun a allon ƙaddarar mu Allah ya rubutu ba ni ce matarsa ba ke ce matarsa, to me zai sa na ɗauka da zafi. A’a har cikin raina ba na fushi da ke wallahi.”
Halima ta kaɗa kafaɗa ta na faɗin “koma ki na fushin ko ba kya yi ruwan ki, kuskure dai ba nawa ba ne kin sa ni na sani kuskure na ki ne tun farko.”
Shiru Zhara ta mata kiran Mama ta yi a waya ta bayan ta ɗaga ta miƙewa Zhara,
“Ga Maman” karɓa ta yi “Ina wuni Mama?”
“Lafiya lau Zhara ya gida ya karatun?”
“Wallahi AlhamdulilLah. Ya Baba”
“Ya na nan lafiya lau” su ka ɗan yi shiru, Mama ta katse shirun.
“Ina mai ƙara ba ki haƙuri a kan abin da Halima ta ma ki.”
“Haba Mama ni wallahi ba ta mini komai ba, kuma ni ban riƙi ta a rai ba. Da ga ni har ita babu wanda ya isa ya canza ƙaddarar sa, don Allah ki daina fushi da ita.”
Ajiyar zuciya Mama ta yi “Na ji daɗin jin haka Allah ya yi ma ki albarka, Ubangiji ya ma ki sauyi ma fi alkhairi. Don Allah kar faruwar hakan ya yan ki zumuncinku da ku ka ta su da shi tun ƙurciya.”
Kallon Halima Zhara ta yi wacce ta ke a tsaye ta haɗi gabas da yamma kamar wacce a ka aikuwa da saƙon mutuwa.
“Uhm! Insha’Allah Mama ba abin da zai sauya.” Su ka yi sai da safe ta bata wayar fizgar wayar ta yi ta juya za ta fita “Halima” ta kira ta da sanyin murya, juyowa ta yi su na kallon juna. “Me yasa ki ke son yanki alakarmu ta ƙarfi ne? Me na ma ki da zafi har ki ke iya yi mini wannan hukuncin Halima? Sam ba na jin daɗin hakan wallahi.”
Kafeta ta yi da idanu kafin ta ce. “Ba ki mini komai ba Zhara, sai dai kuma ba zan ɓoye ma ki ba tun ranar da ki ka sa ƙafa ki ka dawo gidan nan da zama ban saki jin natsuwa a raina ba saboda ina tsoron auren ki da Baby ya yu.”
“Humm Halima kenan sheɗan ne kawai ya ke kitsa ma ki hakan zuciyar ki na ɗauka, har abada aurena da Yaya Hafiz ya haramta kamar yadda kishi da ƙanwata Hassana ya haramta hakan kema.”
“Ta ya zan aminta da hakan bayan na san har gobe ki na son shi, sannan kuma Dadyn Baby ya na son ki a kwai son haɗin auren a zuciyarsa tun da har ya ɗauko ki ya kawo ki gidan sa.”
“Idan na ma ki alƙawari za ki yarda da ni?” Gyaɗa kanta Halima ta yi ta na faɗin “bari ki ji abu ɗaya ne zai sa na yarda da ke na kuma cire tunanin za ki iya auren mijina shi ne ranar da na ga kin zama matar wani ba mijina ba.”
Ta na gama faɗa tasa kai ta fita sai kuma ta dawo ta na faɗin “Yawwa na manta na faɗa ma ki sati mai zuwa za mu bar ƙasar nan tare da Baby za mu je yawon amarci.”
Murmushi ta yi ta ce. “Madallah na taya ki murna, Allah ya tsare ya kai ku lafiya ya dawo da ku lafiya.”
“Amin idan har addu’ar ta kai har zuci” ta faɗa fuska a mere tare da ficewa tabar Zhara da tagumi.
“Ikon Allah rayuwa kenan, wai duk ƙaunar da mu ke yi wa juna yau Halima ta rikiɗe ta mayar da ita ƙiyayya, sannan ban da rigima ta rashin hujja ita da ta ci duduniyarta ba ta yi fushi ba sai ita ce za ta yi fushi. Hum.!”
Ta samu su na fira kamar yadda ta barsu zama ta yi kusa da Khadija fuskarta a sake kamar ba abin da ya faru, “ina Zhara ɗin?” Ya mata tambayar idanunsa a kanta, “ta ce karatu ta ke shi yasa ba ta fito ba” gyaɗa kansa ya yi. “Matar Yaya ina alƙawarina?”
“Ai na faɗa ma ki ba zan kawo ma ki ba har sai idan kin zo da kan ki sai ki karɓa” ta ɗan yamutsa fuska “Don Allah dai ki ba Yaya gobe ya kawo mini, ni fa fitar ce ta ke mini wahala wallahi”
“Ashe kuwa ba kya so”
“Shi kenan na ji zan zo ɗin, Allah dan dai na ta neman sa ban samu ba da ba za ki yi mini jan rai ba”
“Wai mene ne ku ke ta magana a kansa?” Khadija ta ɗan yunƙuru ta na fadin “sirri ne Momy”
“Humm ku ku ka sani. Yawwa Hafiz yaushe ne tafiyar ka” ɗagowa ya yi da ga kallon wayar da ya ke ya na faɗin “sati mai zuwa Insha’allah”
“Nan za ka kawo matar ka idan za ku tafi ko, kasan zaman kaɗai ce ba shi da daɗi” kallon Halima ya yi a ka yi daidai da ta ɗago suka haɗa idanu ya yin da zuciyarta ta bada rass! Kawar da kallon sa ya yi da ga kan ta zuwa wajan Momy ya na faɗin “a’a tare ai za mu tafi, kin manta da na faɗa ma ki.”
“To su Matar Yaya za a hau jirgi ashe, to wallahi kar ki je ki yi wa Yaya ƙauyanci dan na san idan ba a waya ba ba ki taɓa ganin jirgi ba bare har ki shiga.”
Ta yi maganar ta na yi mata dariya, duk sai ta ji ta mozanta, murmushin ƙarfin hali kawai ta yi, harararta ya yi.
“Khadija zan ɓata ma ki rai fa.”
“Ni me na yi Yaya da ga wasa.”
“Haka a ke wasa a gidan ku?” Shiru ta yi ta na turo baki gaba.
“Ka ga ai gaskiya ta faɗa kar ka wani yi mata faɗa ko kin taɓa ganin jirgi ne Halima?” Ta mata tambayar ta na kallonta da murmushi a fuskarta, dariyar haƙora ta yi da a ka ce ya fi ya ƙi ciwo, “a’a Momy”
“To ka ji ba. Sannan maganar tafiya da ita sam babu ta, duka yaushe a ka yi auren da har za ka fara tafiya da ita. Sannan ai ba sabawa ta yi da fita waje ba ‘yan ban da son ɗorawa kai lalura.”
Dib ‘yar fara’ar da ta ke fuskarta ta ɗauki ya yin da zuciyarta ta shiga dukan uku-uku. Marairaici fuska ya yi “Don Allah Mom… Ɗaga masa hannu ta yi.
“Ka ga na riga da na gama magana ka kuma sani ba sauya wa zan yi ba.” Ta miƙe tsaye ta fara tafiya kafin ta juyo ta ce. “Ka same ni ɗaki.”
Jiki a sanyaye ya bi bayanta. Khadija ta kalleta “ya dai matar Yaya na ga kin yi ɗib kamar wutar nepa ta ɗauke” murmushin ƙarfin hali ta yi “Ba komai.”
Tashi tsaye ta yi tare da ɗaukar wayarta “mene ne ma abin damuwa dan ba a tafi da ke ba, dama ai ba saban ba ko” uffan Halima ba ta ce da ita ba har ta haura sama.
Sun yi tsaye a tsakiyar ɗaki fuskarta babu annuri ta ce. “Ka daina ganin na ja baki na yi shiru ka yi tunanin auren ka ya wani ɗaɗa ni da ƙasa Hafiz, na so auren ka da Halima ne saboda abu ɗaya zuwa biyu, fasa auren ka da Zhara, sannan kuma na sani dole zuciyar uwar Zhara ta yi ƙona a na gobe ɗaura aure a ce an fasa auren, wannan ne kaɗai yasa ni yarda da auren ka da Halima.”
Ta zauna gefen gado ajiyar zuciya ya yi tare da zama ƙasa dab da ƙafafunta ya riƙo hannunta.
“Don Allah Momy ki daina irin wannan sam bai dace ba, kuma kin ga ba daɗi na sa ma ta rai da tafiyar nan na zo na ce ba za ta ba.”
“Ni uwar ka na ce ba za ka je da ita ba, in ban da rashin tunani irin na ka shi talaka an faɗa ma ka a na zure masa ne irin haka, idan har ta samu dama komai za ta iya yi tun da ba arziƙi su ka sani ba, ai Khadija ta faɗa mini komai a she yarinyar nan ba ‘yar kowa ba ce ɓoye mini gaskiya ka yi.”
“Da mai kudi da talaka duka Allah ya yi su fa, sannan kuma an … “Ai sai ka faɗa mini tun da ga jahila ka samu ba” duk yadda ya so lallaɓata ta tuɓure a kan maganar ta haka su ka bar gidan zuciyoyin su babu daɗi.
Tun da su ka dawo gida ta sa shi gaba da kuka da meta “humm na sa ni dama ya za a yi a gidan ku a so ne, na gama fahimtar har da haɗin bakin ka ma a ka yi mini wannan wulaƙancin, daɗin ta dai kai ne ka na ce ka na sona har duk abinda ya faru ya faru bare a ce kwaɗaye ne ya sa na aure ka.”
Mamaki ya cika shi ya mata zuru da idanu sautin kukan ta ya karu komai bai ce da ita ba dan wani irin ɓacin rai ya ke ji a zuciyarsa ga ɓacin ran hukuncin Momy sannan sun dawo gida ita ma kuma ta ƙara masa wani wanda tabbas idan har ya yi magana abin ba zai yi daɗi ba. Washegari ya fito cikin shirin fita ya duba dani wayam babu komai ya shiga ɗakinta ta na kwance ta na dannar waya, tsayawa ya yi kanta ya na faɗin “ya na duba dani babu komai.”
“Ban girka ba” ta bashi amsa ba tare da ta kalleshi ba” ransa a ɓace ya ce. “Ki na ganin wannan matakin da ki ka ɗauka shi ne daidai ko? To shi kenan bisimillah Allah ya ba ki sa’a” ya fice ransa a ɓace ta raka shi da tsaki, ya na jiyo ta gyaɗa kansa kawai ya yi ba tare da ko ya juyo ba bare har ya tanka mata.
Hawaye masu zafi su ka ciko mata idanu babban damuwarta gami da fashin tafiyar nan biyu ne, a cikin group ɗin su na makaranta ta gama yamuɗiɗin tafiyar nan, sannan ga maganar da ta faɗa wa Zhara a jiya, yanzu duk ya za ta yi da wannan abin kunya? “Kai uwar miji ko masifa! Wallahi da gaskiyar masu faɗin da uwar miji gwanda kishiya idan har kishiya ce ta ma isa!” Ta yi maganar a zafafi.
Tafe su ke cikin motar Anwar Hafiz da ya ke zaune a kan kujerar mai zaman banza ya na waya “Ok ba damuwa idan har ka gyara motar kawai ka kawo mini gida dan ni har na bar office ɗin.”
“Ok an gama Oga” tsinki kiran ya yi ya kalle Anwar “wai ka san Momy ta sauke tafiya ta da Halima.”
“To me yasa?” Ya yi tambayar da mamaki, fuskarsa ciki da damuwa ya ce. “Ka san Momy ai ita ba wai so ta ke harka da talaka ba, ka san jiya mun je garin su Halima tare da Khadija na sa ni dama za ta zo ta faɗa wa Momy iyayen Halima talakawa ne shi yasa ban so na tafi da ita ba ita kuma Momy ta ce sai tare za mu tafi, wannan fushin ne yasa ta ce babu in da zan tafi da ita.”
Gyaɗa kansa Anwar ya yi ya na faɗin “Babban magana, sai haƙuri tun da har ta yanki hukunci ai ka san ba sauya wa za ta yi ba.”
“Na so na kira Dady na sa ya mata magana ta amince ita kuma ta zo ta ɓata mini rai…” Ya bashi labarin abin da ta masa, murmushi Anwar ya yi ya na faɗin “to kai meye abin damuwa wayayyir mace kuma matar so ai ba sa yin laifi komai su ka yi daidai ne” harararsa ya yi ya na faɗin “manta wa ma na yi na ma ka maganar, mtsw.”
“To meye na ɗaukar zafi da ga faɗar gaskiya.”
“Riƙi Kayan ka ba na so!”
“Ka da Allah yasa ka so ɗin” dukan su suka yi shiru na ‘yan daƙiko Anwar ya kawar da shirun “ni fa na samu matar aure.”
“Wai da gaske ka ke?” Gyaɗa kansa ya yi ya na faɗin “da gaske na ke?”
“Hafsat ko Rahama”
“Ba ko ɗaya da ga cikin su wata dai ce daban.”
“Kai fa ɗan iska ne yanzu duk yaudarar su za ka yi dama” harararsa Anwar ya yi kafin daga bisani ya ce. “dama na taɓa cewa zan aure su ne bare har na yaudare su, su ne su ke ta shirmen su ka kuma sa ni kawai son ɗora mini laifi ka ke.”
“To na ji wace ce wacce ka tsayar ɗin?” Shiru ya yi fuskarsa ɗauki da murmushi “gaggawar me ka ke ka ƙara haƙuri lokacin faɗa ma ka bai yi ba, sai ka dawo da ga tafiya za ka ji ko wace ce.”
“Banza ka san ba za ka faɗa mini ko wace ce ba to dan me ma za ka fara yi mini maganar.”
“Koma dai me za ka ce ba zan faɗa ma ka yanzu ba”
“Kar Allah yasa ka faɗa ɗin idan ka isa ma har a yi auren kar ka faɗa.”
“Hahaha shawara mai kyau Hafizu nawa” banza ya masa ya ɗauki wayarsa ya na danna, Anwar ya yi dariya bai kuma ce da shi uffan ba har ya ajiye shi a gida su ka yi sallama shi kuma ya juya zuwa gida.
Zaman lafiya ya yi ƙaranci a tsakaninsu sam ta daina shiga sabgarsa tun ya na share ta har abun ya zo ya fara damunsa da dare ya sameta ɗaki a kwance zuwa ya yi ya kwanta ta bayanta ya rungumeta ta dinga ƙoƙarin kwace kanta ta kasa dole ta haƙura “hukuncin ya isa haka, ina mai ba ki haƙuri, ki yi haƙuri don Allah ki daina azabtar da ni da nisanta kan ki da ni.”
“Ai dama hakan ka ke so ba kaima share ni ka yi ba” ta yi maganar cikin muryar kuka, “ban isa ba ai, kawai na ga kin ɗauka da zafi ne shi yasa na ɗaga ma ki ƙafa har zuciyar ki ta yi sanyi amma duk wani motsi na kina raina” ajiyar zuciya ta yi idanunta na zubar da hawaye ta ce. “Yanzu shi kenan tafiya za ka yi ka barni” juyo da ita ya yi su na fuskantar juna ya na yawo da yatsun sa a fuskarta.
“Ki yi haƙuri ni ma ba hakan na so ba sai dai kin sa ni dule na yi biyayya wa Momy, amma na ma ki alƙawari ina dawowa ba da jimawa ba zan shirya mana tafiya kuma Insha’allah ba za ta hana ba.”
“Uhm! Shi kenan Allah ya kaimu.”
“Amin. Na ji daɗi da ki ka haƙura hakan zai sa na yi tafiyar cikin natsuwa.”
“Zan yi kewar ka sosai.”
“Nawa kewar har sai ta fi ta ki, dan ni na fara tun yanzu. Kin ga jibi ne tafiyar za ki je gidan Momy har na dawo?”
“A’a ba in da zan tafi” ta bashi amsa da sauri murmushi ya yi tare da janyota jikinsa “to ko Zhara ta zo ku zauna tare?” Wani irin abu ta ji ya daki zuciyarta ita ta rasa dalilin da yasa ya ke son yi mata maganar Zhara
“Kin yi shiru”
“A’a ba na so” ta bashi amsa a taƙaici “yadda ki ke so hakan za a yi sarauniyata.”
Daren da zai tafi ya zo ya yi wa Momy sallama ya so ganin Zhara ta ce da Kande da ya aiko ta faɗa masa ta yi bacci, haka ya tafi ransa bai so ba. Washegari da yamma ta fito cikin shiri ba ta samu kowa falo ba ta haura sama ta samu Momy na waya tsayawa ta yi daga bakin ƙofar har sai bayan da ta gama wayar ta kalleta ta na faɗin,
“Lafiya ki ka zo ki ka mini tsaye”
“Dama Yaya Anwar ne ya zo ya ce na raka shi unguwa.”
“To ni mene nawa a ciki da za ki zo ki faɗa mini idan ma hotel za ki raka shi ku kwana ruwan ki ne bai shafe ni ba.”
Hawaye su ka ciko mata idanu har cikin ranta ba ta ji daɗin wannan furucin ba, “tsayen me kuma ki ke yi” jiki ba ƙwari ta fice su ka yi Kiciɓis da Khadija da ta ke ƙoƙarin shigowa ɗakin ta mata kallon ƙasa da sama ta na yatsinin fuska ta ce. “Dama ina ganin Anwar a waje na san ke ya zo ɗauka, an ga ɗan shawalwalin saurayi ɗan birni ga ƙurciya ga naira shi yasa a ke ta ƙoƙarin cusa kai tun da an yi kwantai a wajan Yayana” ƙasa ta yi da kanta ta bi ta gefen ta ta wuce ta na ji a ranta kamar kar ta fita sai dai ta na jin nauyin sa, idan har taki zuwa dole ya nemi jin dalili ita kuma ba za ta iya faɗa masa ba, haka ta fita zuciyarta babu daɗi.
Can’t wait for the next chapter 🔥🔥🔥