Ƙara sunkuyar da kanta ƙasa ta yi yayin da bugun zuciyarta yake ƙaruwa, ahankali ta ɗago kai ta kai duban ta ga Momy da tun ɗazun take aika mata da harara ta kawar da kanta da sauri tana duban Hafiz da ya langaɓar da kai yana yi mata magiya da idanun sa. Abba ya kalleta cikin faɗa ya ce.
"Ya ana yi ma ki magana kin yi wa mutane shiru sai wani kalle-kalle ki ke yi kamar makauniyar da idanunta suka fara gani yau, ki buɗe baki kiyi magana tunda dai duk nan babu sa'an. . .