Skip to content
Part 24 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Ƙara sunkuyar da kanta ƙasa ta yi yayin da bugun zuciyarta yake ƙaruwa, ahankali ta ɗago kai ta kai duban ta ga Momy da tun ɗazun take aika mata da harara ta kawar da kanta da sauri tana duban Hafiz da ya langaɓar da kai yana yi mata magiya da idanun sa. Abba ya kalleta cikin faɗa ya ce.

“Ya ana yi ma ki magana kin yi wa mutane shiru sai wani kalle-kalle ki ke yi kamar makauniyar da idanunta suka fara gani yau, ki buɗe baki kiyi magana tunda dai duk nan babu sa’an ki!”

“Ka ga ba na son rigima ka yi mata sannu.”

Kallon Zhara ya yi da ya fahimci tsoron da yake zuciyarta da har ya bayyana a kan fuskarta wanda daga kallon da yaga tana yi wa Hafiz da Momy ya fahimci da akwai wata a ƙasan hakan yasa ya ji bari kawai ya yi na shi hukuncin.

“Shi kenan na ma gama fahimtar komai ba sai kin yi magana ba kawai ki tafi na san me zan yi” ajiyar zuciya ta saukar da har sai da kowa na wajan ya ji sai ta ba Dady tausayi.

Hafiz da sauri ya ce wa Dady “amma Da…”

“Ba na son wata magana Zhara ce zaɓin da na yi ma tun farko amma ka watsa mini ƙasa a ido ka nuna wa duniya ban isa da kai ba, dan haka tunda har ka aure zaɓin ka shi kenan ka barta ita ma ta samu na ta zaɓin tunda ba rasa ma su sonta ta yi ba bare har ka dinga yin ƙwallo da rayuwarta.”

Kicin-kicin Hafiz ya yi da rai me yasa Dady zai masa haka ai ya ji ya sani ya yi laifi amma ai ya ce a yi haƙuri ko. Ya ja numfashi ya furzar cikin huci ya tashi Abba ya ɗago ya kalleshi kawai har ya fita bai ce da shi komai ba.

“Wannan hukuncin ba daidai ba ne Yaya tunda har ya ba da haƙuri bai kamata a dinga ja masa rai ba don Allah kayi haƙuri komai ya wuce ka sake ba shi dama karo na biyu.”

“Ka ji ni da Husaini a sake ba shi dama ko dai a sake ba ku damar da kuke ganin kun rasa a baya? A da ya ce ba ya son ‘yar ku saboda baƙin cikin kun rasa hanyar arziƙin ku shi ne kuka je kuka yi ƙulla-kullarku ku kai yadda ya dawo baya ji ba ya gani a kan ‘yar ku. To ku faɗa ko nawa ku ke so zan ba ku ni dai ku sakar mini ƙurwar ɗana.”

Dady zai yi magana ya ga Abba ya yi dariya hakan yasa ya yi shiru yana kallon Abba.

“To banda abin ki Turai su waɗan nan kuɗin da ki ke ta magana idan ma su na so ai ba laifi ba ne tunda kuɗi nan dai naga na Yayana ne da kai da kaya kuma ai duk mallakar wuya ne, duk kuɗin nan dai da ki ke ta taƙama da fankama da su na Yayana ne idan yanzu ya baki read card dole a nan ɗin dai za ki bar kuɗaɗin ki koma rayuwar ruga babu mamaki ma wannan tallar ta fura da nono da muka taimaka muka raba ki da ita ki dawo mata.”

Ya ɗan sihirta yana kallon ta wacce ta cika ƙiris ya rage ta fashe ya ci gaba da faɗin.

“Ko da ya ke naga ba laifi suma dangin duk an saka su cikin rigar arzikin na mu.”

“Kana jin sa fa Alhaji magana yake faɗa mini!”

“To ke ba maganar ki ka faɗa masa ba dan kuma ya ba ki amsa sai ki ji zafi.”

Miƙewa tayi tsaye cikin kumfar baki ta ce.

“Eh dama na sani ai duka bakin ku ɗaya dama me za ka ji dan ya faɗa mini magana tunda ga dukan alama daga ɗan har uban duk sun shanye ku!!”

Ta juya kan Abba idanu a ƙankanci ta ce. “Kai kuma na dawo kan ka da ka ke cewa da an bani read card shi kenan na bar kuɗi ai wallahi ko kura ta mutu ta wuce a kira ta da Allah sarki. Tunda Allah ya bani arziƙin haihuwa ai na riga da na gama da Alhaji sai dai ni na sallama ku kuyi gaba zama daram kujerar tsakar gida!”

Ji ta yi kamar tasa ihu wani irin abu mai nauyi ya zo ya tukare mata zuciya duk ji take babu daɗi duk a sanadin ta manya suke faɗa in faɗa irin hakan, musamman Abba da ta sani mutum mai haƙuri yau shi ne yake sa’insa da Momy tashi ta yi ta fita da sauri tana zubar da hawaye duk sai take jin ta tsani kanta.

Dady ya bi ta da idanu har ta fice juyo da kallon shi ya yi kan Abba da ya ke faɗin.

“Wata kujerar ba wata kam idan ta …

“Ya isa haka kana namiji za ka zauna kana biye wa shirmin mata. Kema kar na sake jin bakin ki.”

“Hakan ma za ka ce ko wato duk rashin mutuncin da ya yi mini ko a jikin ka bare har ka yi wa abin tufka ba.”

“Ba wai na ce kar na sake jin kince wani abu ba! Ko me ya yi ma ki ai ke ce ki ka janyo wa kan ki da kin kama girman ki zai ma ki ne? Sannan ai an daɗe ana ruwa ƙasa na shanyewa ba tun yau ba na san duk irin abin da ki ke yi masu kawai ina kawar da kaina ne, dan haka dan yau tura ta kai bango ya mayar ma ki da magana ba zan masa magana ba tunda ke ki ka janyo wa kanki!” Fau ta fice daga falon kamar kububuwa.

Tsaki Abba ya yi yana faɗin “ka yi haƙuri Yaya kawai na ji ba zan iya haɗiyewa ba ne, ina matuƙar jin ciwon yadda take tunanin wai kuɗi ne ya sa muke son haɗa Mamana da Hafiz.”

“Kar ka damu kai dai ku ci gaba da haƙuri da halin Turai abu ne na shekara da shekaru ba wai yau a ka fara ba ya kamata a ce kun saba da halinta. Kuma In sha Allah zan yi wa lamarin tufka.”

“Uhm! Allah ya kyauta amma don Allah Yaya ka yi haƙuri ka bar Hafiz ya aure Zhara don Allah ina mai ƙara ba ka haƙuri a madadin sa.”

Na riga da na gama magana ba kuma zan sauya ba, na rufe wannan zancen. Am ya maganar da muka yi gami da wannan filin na bayan ku?”

Ba yadda ya iya dole ya bar zancen suka faɗa zancen fili.

Tana fitowa ta same shi tsaye bakin ƙofa fuskar sa a haɗe kallo ɗaya ta masa ta kawar da kanta da sauri ta nufi hanyar da za ta sada su da ƙofa janyo ta ya yi ta faɗa ƙirjin shi yasa hannu ta bayanta ya rungomota haɗe fuskokin su ya yi har suna jin numfashin juna “komai za ki yi mini a matsayin hukuncin laifin da na yi ma ki ko da kuwa duka da zagi ne a shirye nake da na karɓi wannan hukuncin amma ban da gujewa aure na ba zan iya jurar hakan ba ya kamata ki fahimci hakan” kicin-kicin ƙwaci kanta ta shiga yi sai dai ta kasa sai ma ƙara matseta da ya yi a jikin shi da ko motsin kirki ta kasa yi.

“Ni ka sake ni.”


“Ba zan yi ba har sai idan kin mini alƙawarin yanzun nan za ki tafi ki faɗa wa Dady kin amince za ki aure ni. Ko da yake alkawarin ɗazun ma ai ba ki cika ba.”

“Ko ɗazun ɗin ai alƙawarin dole ne kasa ni yi, kuma ni me ka ji na faɗa Dady ne da kan shi ya yi hukunci kuma ni ban da ja a kan duk wani hukunci na sa, kawai ka yi haƙuri ka riƙi matar ka ta gida da dama can ita ce zaɓin ka. Nima kuma babu jima wa zan fito da nawa zaɓin ” tsaki ya yi haɗe da kawar da kansa yana kallon gefen wasu shukoki jin muryar Momy yasa ya janye ta jikin shi yana riƙi da hannunta ya ce. “Zo mu tafi.”

Fizgi hannunta ta yi “ni ba in da zan tafi ka ƙyalini na yi tafiya ta” ya yunkura zai riƙota ta arci na kare ta gudu binta ya yi da kallo har ta ɓaciwa ganin sa, ajiyar zuciyar sa ta yi daidai da fitowar Momy ta watsa masa wani kallo ta zo ta tsaya gabansa tana faɗa kamar za ta dake shi “wato Hafiz ni ka ke so ka kunyata a idon makiyana ko. Yau duk saboda kai ubanta ya hayayyaƙo mini yana faɗa mini son ransa kamar ma zai dake ni.”

“Ki yi haƙuri na sani Abba ba zai taɓa yi ma ki hakan ba domin shi ɗin mutum ne mai haƙuri, idan kuma har ya yi na tabbata kin kai shi bango ne da dole sai ya yi.”

Salati tasa tana tafa hannu “ah ta tabbata kuwa Maryam da Husaini sun riga da sun mallake ku daga kai har uban na ka wato laifina ma kake gani? To koma dai mene ne ka dinga tuna ni mahaifiyar ka ce kuma matuƙar ina raye ba za ka taɓa auren Zhara ba?”

Ta yi maganar tana mai barin wajan ya sha gaban ta da sauri cikin damuwa ya ce.
“Kar ki yi mini hakan wallahi ina sonta zan iya rasa raina idan har na rasa ta taɓa kiji.”

Janyo hannunta ya yi ya ɗora saitin zuciyar shi “kin ji yadda zuciyata take bugawa wallahi komai zai iya faruwa da ni idan har na rasa Zhara” janye hannunta ta yi tana harararsa “na ji sai kuma me saura ta faso ƙirjin ta fito ta yadda zan tabbatar da soyayyar ta ka Sharukan.! Tafiyarta ta yi ta bar shi a wajan kamar ya yi ihu hakan ya ke ji a ransa dunƙule hannayensa ya yi ya hauri iska.

Tana zuwa ɗaki ta faɗa kan gado kwanciya yi wani irin son Hafiz take ji kamar ma a yau ta suma ji take kamar ta je ta faɗa wa Dady ya yi haƙuri za ta aure shi, sai dai idan ta tuna abin da ya faru a baya, ta tuna ga masifar Momy uwa uba kuma kusancinta da Halima duk sai ta ji auren na shi ya fice mata a rai.

Abba na shiga masaukin shi ya samu Hafiz zaune “ikon Allah Hafiz wai dama kana nan ba ka tafi ba?”

Zamowa ya yi daga kujera ya durƙusa gaban Abba da yake a tsaye riƙi ƙafafun shi ya yi yana zubar da hawaye “don Allah Abba ka lallaɓa Dady ya amince ni fa ko a baya ban ce ba na sonta ba na yarda na yi kuskure da na aure ƙwarta am…

“Ya isa hakan auren Halima ba zai zama kuskure ba Allah ya riga da ya nufa matar ka ce dan haka babu wanda ya isa ya hana tabbatuwar hukuncin Ubangiji.”

zama ya yi a kan kujera Hafiz ya ɗora kansa a kan cinyoyin Abba shafa kansa ya yi cikin lallashi ya ce. “Ka kwantar da hankalin ka ka kuma sa a ranka matuƙar Zhara matar ka ce babu makawa sai ka aure ta. Dan haka ka natsu ka cire damuwa mu ci gaba da addu’a kawai, mu kuma ba shi lokaci zan sake tunkarar sa da maganar amma yanzu mu saurara masa.” Haka ya yi ta tausasa zuciyar sa da kalmar kwantar da hankali har sai da yaga ya samu natsuwa sannan ya raka shi mota.

Halima na kwance a kan kujera bacci ya fara ɗaukar ta shigowar shi ce na tashe ta.

“Sannu da dawowa.” ta yi maganar tana miƙa hadi da mika “Yawwa sannu” zama ya yi kusa da ita yana shafa cikinta cikin kulawa “fatan da ke da Babyna kuna lafiya?”

“Uhm! Lafiya lau, sai kewar ka. Ina ta kiran wayar ka ba ka ɗaga ba.”

“Ki yi haƙuri na manta wayar ne a mota” miƙewa ya yi “bari na je na yi wanka” biyu bayan shi ta yi tana faɗin “yau ka daɗi ko duk aikin ne.”

“Ina gida ne muna tare da su Dady mun ɗan yi wani meeting ne shi yasa na jima ban dawo ba” gyaɗa kanta kawai ta yi. Bayan ya fito wanka ta taya shi shiri, yana kammala shirin suka fito filo. Suna zaune a kan daning yasa abinci a gaba “wai me ya ke faruwa ne naga kamar kana cikin damuwa, ga abinci kasa gaba kana ta kallo ba ka ci ba.”

“Mtsw! Ba komai kawai gajiya ce. Yawwa Zhara ɗauko mini wayata” sakin baki ta yi tana kallon shi da matuƙar tsoro da mamaki hakan yasa ya ce. “Me ya faru?”

“Oh tambayata ma ka ke me ya faru humm yau ni ce na zama zhara ni kake kira da Zhara” riƙi kanshi ya yi ya na ɗan fito da idanu ‘ya salam wai me ya ke damuna ne’ ajiyar zuciya ya yi kafin daga bisani ya ce. “ki yi haƙuri ba a sani na ba ne kuma ba mamaki dan mun ɗan wannan da ita ne har sunan ya tsaya mun a baki” a fusace ta tashi tsaye tana buga daning “kar ka wani raina mini hankali Hafiz kun ɗan wannan shi wannan ɗin me kenan!? Dama na sani wannan lokacin zai zo, kuma tun da na ji ka ce wai kun yi meeting na ji a jikina wata tsiyar ce a ke ƙullawa, amma ba laifin ka ba ne laifina ne da har na yarda na aure ka bayan na san ita ɗin ‘yar’uwar ka ce koyaushe za a iya nuna mini fifiko da son kai a kanta.”

“Kinga Halima abun da fa ki ke zato sam ba hakan ba ne kawai…

“Kawai me!? Kawai so ka ke ka auro ta ko na ce so a ke a cusa ma ka ita saboda ni ba jinin ku ba ce a ji daɗin wulaƙanta ni, to wallahi daga kai har su babu wanda ya isa yasa na yi zaman kishi da Zhara dole ka zaɓa ko ni ko ita!!” Ransa ne ya suma ɓaci hakan yasa ya ture abincin ya miƙe tsaye ya suma tafiya shan gaban shi ta yi “na ce ka zaɓa ko ni ko ita!”

“Shin dan kawai na yi kuskuren kiran ki da sunan ta shi kenan sai kiyi tunanin wani abun ne?”

“Idan har babu rame me zai kawo zancen sa? Ai wallahi na jima da jin hakan a raina dan haka kai nake jira ni ko ita” girgiza kansa ya yi yana murmushi “gaskiya ne jikin ki ya faɗa maki daidai auren zhara zan yi kamar dai yadda na aure ki. Sannan ba zan ɗauki ɗaya na bar ɗaya ba saboda dukan ku ina son ku.”

“Ai wallahi ba ka isa ba wannan ai cin amana ne ko kishiya kake so kayi mini ka rasa wacce za ka auro sai Zhara saboda cin amana!”

“Idan har ba a kira auren ki da nayi da auren cin amana ba tabbas ko auren zhara da zan yi ba za a kira da cin amana ba dan hakan don Allah na roƙe ki da ki barni na huta ki barni na ji da abin da ya ke gabana.”

Taja numfashi ta furzar cikin huci ta ce. “Ka faɗa mini duk abin da ka ga dama kuskure na ne da har na aminci na aure ka duk da na san irin wannan ranar za ta iya zuwa” janyo ta ya yi jikin shi ganin ta fara kuka ya suma lallashin ta sai dai kamar yana ƙara tunzarata dukan shi ta shiga yi tana yakushi duk da hakan bai sake ta ba hakan yasa ta gantsara masa cizon da yasa shi sakin ta babu shiru.

Ranar ko kaɗan ba ta barshi sun rintsa cikin daɗin rai ba kwana ta yi tana matsifa da zage-zage.

Washegsri wuraren sha ɗaya Zhara ta fito lakca tana tare da Aunty Husna suna fira jama’a sai kai da kawo suke cikin harabar makarantar. “Aunty Husna kin ƙi ki kawo mini Baby Amrah k… Ji tayi an watsa mata mari kafin ta dawo hayacinta an sake watsa mata wani marin da ya fi na farkon zafi jinta ne ya ɗauke ɗib wani irin duhu ya wanzu a idanunta…

Fulani

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Waye? 23Kuskuren Waye? 25 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×