Ƙara ya dinga jiyowa na fitowa ta cikin falon hakan yasa da sauri ya ƙarasa shiga ciki da matuƙar tsoro a zuciyar shi. Suroro ya yi ya na mai kallon falon wanda duk ta ya mutsu shi ta faffasa kaya masu tsada da a ka ƙawata falon "mene ne haka Halima kin samu taɓin hank... Jifan da ta masa da gilas ɗin da a ka saka fulawa ne ya sa shi yin shiru ba tare da ya shirya wa hakan ba. Ya fasa masa goshi har jini ya fara fitowa hakan bai sa ya bi ta kan raunin. . .
Masha Allah! Allah yakara basira