Skip to content
Part 27 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Ƙara ya dinga jiyowa na fitowa ta cikin falon hakan yasa da sauri ya ƙarasa shiga ciki da matuƙar tsoro a zuciyar shi. Suroro ya yi ya na mai kallon falon wanda duk ta ya mutsu shi ta faffasa kaya masu tsada da a ka ƙawata falon “mene ne haka Halima kin samu taɓin hank… Jifan da ta masa da gilas ɗin da a ka saka fulawa ne ya sa shi yin shiru ba tare da ya shirya wa hakan ba. Ya fasa masa goshi har jini ya fara fitowa hakan bai sa ya bi ta kan raunin ba sai ma kallonta ya ke da matuƙar mamaki a fuskar shi. “Duka yaushe a ka yi auren mu shi ne dan kawai cin amana da son a nuna iyaka ta shi ne har za ka ƙara aure kuma wai Zhara saboda cin amana!!” Jiki a sanyaye ya nufi ɗakin shi ba tare da ya ce da ita uffan ba. Bin bayan shi ta yi da sauri ta sha gaban shi “wato ga mahaukaciya ba shi ne har ina yi ma magana za ka yi tafiyar ka ka barni a tsaye!!”

“Me ki ke so na ce da ke? Ba kin riga da kin ɗauki matakin da ki ke ganin ya fiye ma ki ba? Me kuma ki ke jira maza ki ƙarasa aikin na ki ki rusa har gidan idan kin gama farfasa kayan!” ya ƙarasa maganar yana mai ture ta ya shige ɗaki kafin ta shigo ya yi wa ƙofar key. Yana jiyo kukanta tana zage-zage da faɗin an cuceta an mayar da ita saniyar ware saboda ita ba ‘yar’uwar sa ba ce. Sosai ran sa ya ɓaci tabbas ya jinjina wa halin Zhara ya kuma ƙara kammama darajar ta da soyayyarta a zuciyar shi. Duk abin da ya faru ya yin fasa auren ta ko a fuska ba ta nuna ɓacin ranta ba bare har ta yi ma su wani rashin mutunci kamar yadda Halima ta ɗauko hanyar yi. Treatment ɗin wajan da ta masa rauni yayi, kwanciyar shi ya yi bayan ya gama. Ranshi a matuƙar ɓaci ya ke bai yi niyar koma wa asibiti ba sai dai kiran da a ke ta yi masa ne ya sa shi fitowa babu kowa a falon sai dai har yanzu ya na nan a yamutsan shi.

Da dare bayan ta idar da sallah isha tana a kan dardumar Anwar ya kira ta ya ce ta fito yana ƙofar gida. Dama da Hijab a jikinta dan haka wayar kawai ta a jiye ta fito cikin sanɗa tana addu’ar Allah yasa ba kowa a filon cikin sa’a bata tarar da kowa ba sai tv da ke Kunne. Da fara’a ta ƙarasa wajan shi “ina wuni Yaya Anwar?”

“Lafiya lau Zhara idon ki kenan ki dawo har ki kwana ba za ki kira ni ba.”

“Ayya ka yi haƙuri ban samu natsuwa ba ne shi yasa.”

“Shi kenan fatan kin dawo lafiya?”

“Lafiya lau AlhamdulilLah” gyara tsayuwar shi ya yi yana faɗin “me ya samu wayar ki ina ta kira ba ki ɗaga ba?”

“Na manta wayar ne kuma da na dawo ba ta da caji sai yau na yi ma ta cajin” fitilar motar Hafiz ta hasko su har sai da tasa Hijab tana rufe fuskarta. Murmushi Anwar ya yi “Yayan mu Hafiz” shi bai kashe fitilar ba bai kuma fito motar ba. Mayar da kallonta ta yi jikin motar Anwar ta ba hasken baya fuskantar ta ya yi yana kallonta ya ce. “Ɗazun sai ga kir… “Ke maza ki shiga gida!!” Da mamaki Anwar ya ce. “Haba ya za ka zo muna magana kawai ka kora mini ita”

“Na ce ki wuce ciki ko sai na sassaɓa ma ki!!” Da gudu ta bar wajan kamar ta yi kuka dan har ga Allah taji haushin yadda ya ma ta. Sai da ya ga ta shiga ciki sannan ya juyo kan Anwar “idan ba ka sani ba ina so a yanzun ka sani an riga da an tsayar da maganar aurena da Zhara dan haka daga yau sai yau kar na sake ganin ku a tare.”

“To ai tsayar da maganar a ka yi ba wai auren a ka ɗaura ba ko? Dan haka sai mu jira ranar da a ka ɗaura a sannan ne zan tabbatar da taka ce.”

“An ɗaura ko ba a ɗaura ba ita ɗin tawa ce matuƙar ba ka so mu samu matsala da juna to ka fita hanyarta” yana ƙarasa faɗar maganar ya tafiyar shi Anwar ya bi bayan shi da kallo har ya ɓaci wa ganin shi. Ajiyar zuciya ya yi motar shi ya shiga ya bar wajan ya na mai kaɗa kai.

Ƙiris ya rage su yi karo da Momy a tsoraci ta ja da baya “ki yi haƙuri ban san ki na zuwa ba ne.”

“Dalla can! Sakarya kawai ki na tafiya kamar ba mace ba sam babu tafiyar natsuwa a tare da ke. Ni matsa ki ba ni hanya” jiki a sanyaye ta ƙarasa sauka daga matattakalar ta tsaya a gefe duk da hakan sai da ta bangaje ta tana mai ya ma ta tsaki. Tana ganin Momy ta bar wajan saurin tafiya ɗakinta tayi. Hafiz ya ƙarasa shigowa falon samun su ya yi suna kallo “kai kuma me ka zo yi da dare nan.”

“Haba Momy sai ka ce wanda ya fara zuwa yau da ki ke yi mini wannan tambayar” ya yi maganar yana mai zama a kan kujerar da ta ke daga gefen Momy. “Ni ban son wani fi’ili in dai saboda ni ka ke zuwa to na yafe ka yi zaman ka a gida ba sai ka zo ba ko waya ne sai mu yi ya wadatar” dariya ya yi marar sauti rigimar Momy ta yi yawa sai ka ce ƙaramar yarinya. “Sannu da zuwa Yaya, ya aiki?”

“Yawwa sannu Kadin Momy AlhamdulilLah. Ina Zhara?”

“Tana ɗaki kasan ta da zaman ɗaki kamar wata amarya irin na da ɗin nan.”

“Laifin ki ne ai da tun farko kin ja ta a jiki da ba za ta koya wa kanta zaman ɗaki ba.”

ƙarasa faɗar maganar ya yi yana mai tashi tsaye “Humm ni ba ruwana dama can dai tsoron mutane ne da ita.” Komai bai ce da ita ba ya nufi hanyar sama “ina kuma za ka tafi?”

“Zan duba ta ne a kwai saƙon da zan ba ta ne” hararashi ta yi tana faɗin “ba na son wani munafunci dama na san ai zuwan ba wai ka yi shi ne saboda ni ba saboda waccan shashashar ce ka zo. Zo ka wuce!” Ta ƙarasa maganar tana nuna masa ƙofa langaɓar da kai ya yi “don Allah ki bari na je abu kawai zan bata”

“Ba ni saƙon sai ni na kai mata” riƙi kan shi ya yi har ga Allah ya na so ya ga Zhara amma ya tabbatar da ba za ta bar shi ba. Zuciyar shi babu daɗi ya juya zuwa ƙofa yana faɗin,

“Sai da safe.”

“Haifar ka na yi ai ba kai ne ka haifi ni ba bare har ka ce za ka mini wayo har yanzu a jaririn yaro nake kallon ka” komai bai ce da ita ba har ya fita ta raka shi da harara. “Momy ya kamata ki a jiye komai don Allah tunda dai kin san halin Dady ba wai zai fasa abin da ya yi niyar yi ba ne.”

“Kin san Allah Kadi idan na sa ke jin bakin ki a kan maganar yarinyar nan sai na fasa ma ki baki! Ji ni da yarinya dan kin ga girma ya taso ma ki shi ne ki ke neman ki rainani ko” wayarta ta ɗauka ta haura sama tana faɗin

“Allah ya ba ki haƙuri.”

“Uhm!! Lallai yaran nan sai na tashi tsaye nema su ke su fi ƙarfi na duk a kan waɗan nan matsiyatan!” Ta yi ƙwafa Kande ta kawo mata ruwan Lipton ɗin da ta ce ta kawo mata.

“Ke kuma sai yanzu ki ka ga damar kawo mini!”

‘Kai jama’a duka yaushe ta ce na kawo ma ta duk saurin nan da na yi amma ban tsira da faɗan na ta ba’ tsawar da ta daka mata ne yasa ta dawo daga zancen zucin da take. “Za ki ɓaci mini da gani ne ko tsayuwa za ki yi kina kallona da waɗan nan mitsatsun idanun nan na ki masu kama da na ƙiya!” Da sauri ta bar wajan tana mai jin haushin yadda koyaushe take ci mata fuska da idanunta da ba ita ta yi wa kanta su ba.

A mota ya yi ta kiran wayarta taƙi ɗagawa hakan yasa ranshi ya ɓaci wato ma ta ji haushi dan ya hana ta tsayuwa da Anwar shi ne take fushi da shi, buga sitarin motar ya y ya na tsaki ya ja motar a guje ya bar wajan.
Wuraren goma da wani abu ta shirya ɗakin Momy ta shiga ta samu ba ta nan har za ta fito ta ji motsi a banɗaki hakan yasa ta zauna a kan kafet tana jiran fitowar ta, ba ta jima da zama ba ta fito. “Lafiya ki ka zauna mini a ɗaki?”

“Dama zan tafi makaranta ne kuma na duba ba kya falo shi yasa na zo na duba ki anan ɗin.”

“Sai kuma me?” Miƙewa ta yi tsaye tana faɗin “na tafi”

“Mtsw! A kwai dai munafuncin da ya kawo ki. Kuma wallahi na fi ƙarfin duk wani surƙullen ku daga ke har uwar ki!” “Ki yi haƙuri” ta ƙarasa faɗa tana nufar ƙofa. Har ta buɗe ƙofar “tsaya!” Cikin tsoro ta tsaya tana mai juyowa “na a jiye kuɗi da sarƙoƙin da na saya jiya bari na duba na ga idan ba ki mini halin ɓera ba” rintsi idanunta ta yi duk abin da take yi mata ba ta taɓa jin ciwon sa ba irin yau, sata fa. Buɗe idanunta ta yi da suka sauya daga fari zuwa ja tana kallon Momy da ta buɗe wadrop tana dubi-dubi can ta juyo tana harararta ta ce. “Ai na ɗauka kin mini halin na ku na gadu tun da kin sha a nono, maza bace mini da gani!” Buɗe kofar ta yi da sassarfa ta fita tana jin wani irin tafasa a zuciyarta tabbas yau da ba Momy ba ce wallahi da sai sun daku sai ta faɗa mata abin wa suka taɓa sata a kuma wajan wa ta yi gadon.

A falo suka haɗu da Kande tana goge tv “a’a ba kin ce ba za ki tafi makaranta ba yau” cikin ƙoƙarin kawar da ɓacin ranta ta ce.

“Aunty Husna ce ta ke ta kira na muna da lakca ƙarfe sha ɗaya ga shi har goma da rabi ta yi”

“Ayya to Allah ya tsare sai kin dawo.”

“Amin.” Ta faɗa tana mai fita daga da ga falon.

“Ina kwana Baba”

“Lafiya Lau Fatima Zhara ta Ma’aiki.”

murmushi ta yi kafin daga bisani ta tambaye shi ina Direba ya faɗa mata an aike shi wajan cefane” duba agogon da yake ɗaure a tsintsiyar hannunta ta yi ƙarfe goma da talatin da biyar jiki a sanyaye ta yi wa Baba sallama ta fita tana addu’ar Allah yasa ta samu abin hawa da wuri. Tana fita bakin gyet motar Hafiz tana kunno kai kallo ɗaya ta yi wa motar ta kawar da kanta ta bar wajan da sauri duk da hon ɗin da yake danna mata ta yi biris da shi, bayanta ya biyo yana ƙara danna mata hon ta ɗan yi tsaki tare da tsayawa sauke gilas ɗin ya yi bayan ya tsaya gefen ta yana faɗin “ki na ji na shi ne za ki yi banza da ni ko?”

“Ni ban wani ji ka ba.”

“Humm shi kenan shigo mu tafi” har za ta musa masa ta tuna lokaci ya tafi babu kuma tabbas ɗin za ta samu abin hawa yadda unguwar take da wahala samun abin hawa hakan yasa ta shiga motar. Sai bayan da ya ɗauki hanya ya ɗan juyo ya kalleta “Ina dreban da ya ke kai ki makaranta ne?”

“Ya ta fi cefane” gyaɗa kanshi ya yi kafin daga bisani ya ce. “Kwanan baya mun yi magana da Dady za a saya ma ki mota zan sake tuntuɓar shi na ji idan har bai riga ya yi magana ba sai na sa a kawo ma ki.”

“Da ka bar shi ni kam”

“Dama ai ba shawarar ki na ke nema ba bare ki ce na bar shi” shiru ta masa ya ɗan kalleta yana murmushi “kin yi kyau” kawar da kanta gefe ta yi tana kallon wajan hanya ta jikin gilas ɗin ƙofar. “Me yasa ki ka ƙi ɗaga kirana tun jiya haka da safe ma na kira ki ba ki ɗaga ba”

“Ban kusa ne”

“Ba gaskiya ba ne, na sani ki na jin haushi na ne saboda na hana ki taɗi da Anwar shi yasa ki ke mini wannan hukuncin dan kin san ba zan iya jura ba ko.”

“Humm hakan dai ka ke gani amma ni sam ba hakan ba ne” shiru ya yi itama ta masa shiru na ‘yan daƙiƙu kafin daga bisani ya kawar da shirun “me ya ke damun ki na ga kamar ranki a ɓaci.”

“Ba komai”

“A’a akwai komai sai dai kawai idan ba za ki faɗa mini ba”

“Da gaske fa ba komai”

“Uhum! Shi kenan ina mai ƙara ba ki haƙuri da abin da Momy take yi In sha Allah komai zai wuce kamar ba a yi ba” gyaɗa kanta kawai ta yi. Wayarta ce ta yi ƙara Aunty Husna ce bayan ta ɗaga take faɗa mata malamin ya ce sai gobe wani uzurin yasa ba zai zo ba ɗan tsaki ta yi tana faɗin “kuma shi ne bai faɗa ba har sai da mu ka fito. Shi kenan sai goben tun da dama shi kaɗai muke da yau” tana faɗa ta tsinki kiran kallon shi ta yi tana faɗin Yaya Hafiz mu juya gida sai gobe wai malamin ya na da uzuri”

“Hakan ya mun daɗi dama ina so na samu lokaci a tare da ke.”

“A’a ni dai ka mayar da ni gida ka ga ban saba wani zuwa yawo ba.”

“Saboda ni ɗin baƙon ki ne ko kuma dan ba Anwar ba ne” kawar da kanta ta yi daga kan fuskarta ganin irin yadda ran shi ya ɓaci, sai kuma ciwon da ta gani a goshin shi hakan ya tashe hankalin ta tana ji kamar ta tambaye shi me ya faru da shi sai dai kuma kar yaga kamar ta wani damu da shi ne, hakan yasa ta ja baki ta tsuki. Jin sun tsaya yasa ta ɗagowa bakin gyet ɗin wani hotel taga sun tsaya, karbar ɗan ƙaramin kati ya yi idanunta a kan shi tana masa kallon tsoro da tuhuma har a ka ɗaga masu babban ƙarfin suka shiga harabar hotel ɗin ganin yana shirin yin pakeng yasa ta buɗe baki da matuƙar tsoro “me za mu yi anan ɗin?”

Ko kallonta bai yi ba har ya gyara parking ɗin motar shi “tambayar ka fa nake Yaya me za mu yi anan ɗin hotel ne fa.”

“Ai na ɗauka ko wata masaƙar mu ka so ai” ya ƙarasa maganar yana mai harararta. “Hotel ne fa Yaya!” Tsaki ya yi kafin daga bisani ya ce. “Kin san dai na fi ki sanin ko ina ne tunda ni na kawo mu ba wani ne ya kawo mu ba ko?” Ya ba ta amsa fuskar sa a haɗe kamar wanda bai taɓa dariya ba. Nan take hanjin cikinta suka fara ƙugi zuciyarta ta shiga dukan uku-uku.

Fulani

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Waye? 26Kuskuren Waye? 28 >>

1 thought on “Kuskuren Waye? 27”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×