Skip to content
Part 28 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Ganin yana shirin buɗe ƙofa yasa ta saurin riƙi hannun shi cikin zubar da hawaye ta ce. “Don Allah dai ka yi haƙuri kar ka cutar da ni, ni fa ‘yar’uwar ka ce kai mai kare mutuncina ne a inda a ke ƙoƙarin kawar mini da shi. Don Allah Yaya ka mayar da ni gida” kallonta kawai ya yi na ‘yan sakanni kafin daga bisani ya kawar da kanshi daga kanta ba tare da ya ce da ita komai ba ya buɗe ƙofa zai fita hakan ya tunzura zuciyarta ta fara magana cikin fushi “eh dama ai ba tun yau ba na daɗe da sanin ba ni ka ke so ba jikina shi ne abin da ka ke so, shi yasa tun farko ka so na turoma asalin kaina ta hanyar hoto haushin ban turo ba yasa ka fasa aure na. A yanzun ma na tabbatar da saboda jikina ne yasa ka ce za ka aure ni ba wai asalin son na wa ne kake ba!” Jan numfashi ya yi ya furzar da ƙarfi fita ya yi da sauri duk da ihun kukan da take tana faɗa masa magana bai kulata ba sai ma rufe ƙofar da ya yi.

Tsayawa ya yi gefen motar ya kira wata number jim kaɗan a ka ɗaga “ka fito ina harabar hotel ɗin.”

“Ka shigo ciki mana.”

“A’a ba ni kaɗai ba ne, ina dai jiran ka.” Tsinki kiran ya yi ya jifa wayar aljihu hannunsa na a kan sajin fuskar shi yana shafawa. Sai ƙoƙarin buɗe ƙofar take amma ta kasa fashewa ta yi da kuka ta na sake maimaita “dama na sa ni ba zai taɓa sona ba yaudarar kaina ne kawai nake!”

Wani matashi ne ya ƙaraso gaban Hafiz suka yi musabaha cikin fara’a ya ce. “Ranka ya daɗi a mini afuwa wallahi muna da miting ne ga shi mu na fitowa zan tafi Abuja jirgin sha biyu, shi yasa na ce ka zo ka karɓa saboda babu lokacin da zan zo na same ka.”

“Haba Nasir kar ka damu, ya aikin?”

AlhamdulilLah. Ga kayan” karɓa wata ledar ya yi daga hannun Nasir yana yi masa godiya bayan sun yi sallama Nasir ya tafi bude motar ya yi ya shiga bayan ya jefa ledar a sit ɗin baya ya gyara zaman shi, sai a lokacin ya kai duban shi gareta har yanzu kukan take gyaɗa kanshi kawai ya yi yana mai yi wa motar key. Sanda ta ga sun fita daga hotel ɗin ta saukar da nannauyan ajiyar zuciya komai bai ce da ita ba sai ma kunna waƙar da ya yi, sai sharara gudun da yake ta yi. Duk da a tsoraci take da yanayin gudun amma bata yarda ta nuna masa hakan a fuskarta ba ko ba komai dai tun da har sun bar hotel ɗin hankalinta ya kwanta.

A bakin gyet ya tsayar da motar idanunsa na a kan sitarin motar ya ce. “Zhara a yadda ki ke zato sam ba hakan ba ne ko a lokacin da na ce ki turo mini hotonan ki ban ce na tsiraicin ki ba kawai a yadda ki ke na ce ki daukar mini babu mayafi, a tunanina hakan ba zai zama laifi ba, ban kuma yi tsammanin zuciyar ki za ta ba ki wani mummunan tunani har hakan ba. Ya murza sitarin motar ya na mai saukar da ajiyar zuciya kafin daga bisani ya ci gaba da faɗin “na sai wasu kaya ne a Turkia abokina zai shigo Nageria sai na ce ya zo mini da su uzurin aiki yasa da ya shigo Kano bai samu ya zo wajena ba sai dai ya faɗa mini masaukin shi, dama niya ta idan na a jiye ki na je na karɓo sai ga shi kuma kin fasa zuwan kuma an yi daidai da muna kusa da wajan. Dan haka sam ba abin da ki ke tunani ba ne, ko wata ta waje ban taɓa kawo wa a raina zan yi irin wannan abin da ki ke tunani bare kuma ke da ki ke jinina.”

Sunkuyar da kanta ta yi ƙasa wata irin kunya da da-na-sanin zargen da ta yi masa ta rufe ta “ka yi haƙuri” ta furta cikin sanyin murya. Buɗe mota ƙofa ya yi “za ki iya tafiya ina da marassa lafiya.”

“Don Allah ka yi haƙuri”

“Ki daina ba ni haƙuri ki na da damar da zuciyar ki za ta ba ki ko wani irin tunani a kaina, ba kuma zan ce dan me ba, dan haka ki yi tafiyar ki kawai” cikin sanyin jiki ta fita motar rufe ƙofar ya yi ya bar wajan a guje. Juyawa ta yi zuwa cikin gidan tana addu’ar Allah ya kai shi lafiya dan ta tsorata da irin gudun da ya ke. A harabar gidan suka haɗu da Khadija tana shirin shiga motar ta riƙi marfin motar ɗaya ƙafarta na a cikin motar ta ce.

“Ba dai har kun gama ba?”

“Sai gobe Malamin ba zai samu damar shiga ba yau.”

“Oh ni ma dai yau ba zan shiga makaranta ba zan je unguwa, ko za ki rakani?”

Murmushi ta yi tana faɗin “ba na jin daɗin jikina ne da na raka ki, ki yi haƙuri.”

“Humm ba komai, Allah ya ba ki lafiya” ta amsa da amin tare da shigewa ta gefen

Khadija zuwa cikin gidan ranta babu daɗi. Khadijah ta bi bayanta da kallo hakan kawai take ba ta tausayi. Jiki a sanyaye ta shiga mota.

Wunin ranar ta yi shi ne cikin rashin jin daɗi duk sai take jin haushin kanta me yasa za ta bari zuciyarta ta yi mata mummunan saƙa irin wannan a kan ɗan’uwanta, anya kuwa ta kyauta masa? Sau tari ta kan ɗauki wayarta dan ta kira ta ba shi haƙuri sai kuma ta kasa to me kuma za ta faɗa masa ai ta riga da ta ɓata rawarta da tsalle.

Tun zuwan shi office ya tarar da marar lafiya da yawa suna jiran shi, kallo ɗaya za ka yi masa ka fahimci ɓacin ran da yake ɓoye a ƙasan zuciyar shi duk da kuwa ƙoƙarin ɓoye hakan da yake sai dai fuskar shi ta riga da ta fallasa asirin zuciyar shi. Ana yin kiran sallah azahar ya samu ya zame ya bar asibitin bayan da ya yi sallah a masallacin asibitin. A mota ya bar wayar shi ya tarar da kiran da yawa, Anwar ya masa kira ya kai biyar hakan yasa ya kira shi.

“Likita bokan turai na Halima da Zhara ba da kanka a sare, ai ni har na cire rai da za ka ɗaga ko ka nemi ni” shafa sajen fuskar shi ya yi har yanzu damuwa na shimfiɗi a fuskar shi. “Yau kuma da shaƙiyancin da ka zo mini da shi, na bar wayar mota sai yanzu na ga kiran. Ya su Mama?”

“Ta na nan lafiya koyaushe sai mita take ka yada ita, ni kuma na faɗa ma ta ko ni ka zuba ni a kwandon shara” dariya marar sauti Hafiz ya yi ya na faɗin “sharri kawai ka yi mini wajan ta.”

“Sharri ko gaskiya. Yanzu dai ina so za mu yi wata magana, ya za a yi kana asibitin na zo na same ka ko kana gida?”

“Yanzu na fito asibiti ina hanya, kai kana ina ne?”

“Ina gida”

“Ok zan zo na same ka daga nan sai na gaisa da Mama” daga nan suka yi sallama a jiye wayar ya yi a kan kujerar mai zaman banza.

Hafiz ya tarar da su duk suna falo suna ciki abinci zama ya yi kusa da Mama “Barka da wuni Mama”

“Idon ka kenan ko Hafiz yaushe rabon da na ganka a gidan nan.”

Susa sumar kanshi ya yi yana murmushi “a yi haƙuri aiki ne yayi mini yawa amma kuna raina.”

“To ai shi kenan Allah ya taimaka, ya su Halima fatan su na lafiya?”

“Lafiya lau, In sha Allah zan kawo ta ku gaisa.”

“Idan ma rowarta kake mana ai zan zo ma da kaina na ganta, Anwar ne koyaushe cikin aiki ai da tuni mun je.”

“A yi haƙuri za mu zo In sha Allah”

“Ina wuni Yaya” suka gaishe shi kusan a tare. Da murmushi a fuskar shi ya amsa masu yana tambayar su yau ba makaranta ne ya gansu a gida. Fatima ta amsa masa da ba su jima da dawowa ba. Nabila da tun shigowar shi ta tsaya da cin abincin zuciyarta na dukan uku-uku, ta sani har abada wannan mikin ba zai taɓa ɓaciwa a zuciyarta ba sai dai kawai ta ci gaba da ba wa zuciyarta haƙuri kamar yadda ta saba. Anwar ya kalleta ya kawar da kanshi kawai yana mai miƙewa tsaye “mu je ɗaki, Fatima ki kawo mana abinci.”

“To Yaya” ta amsa tana mai meƙewa tsaye.

“Wai duk fushin ne yasa ba za ka ci abincin ba ne?”

“Mtsw! Kawai ba na jin daɗin jikina ne, ai girkin ba na ka ba ne da fushin ka zai shafe shi na Mamana ne.”

“Hahaha to na ji, yanzu dai kasan dalilin kiran na ka”? Cikin gyaɗa kai ya ce. “Sai ka faɗa” gyara zaman sa Anwar ya yi yana faɗin “maganar gaskiya a yadda kake tunanin tarayyata da Zhara sam ba hakan ba ne” zuba masa idanu ya yi tare da tattaro duk wata natsuwa yana sauraren shi. “Babu wata magana ta soyayya a tsakanina da ita ba mu taɓa makamanciyar wannan ba, kawai dai na san ina ɗaukar ta ne mu fita taga gari a ranar na nemi alfarmar ta yi mini alƙawarin ba za ta kula kowa ba har bayan ta kammala karatu ta tambaye ni dalili na ce zan faɗa mata amma ba a yanzu ba.

Na kan yi kamar soyayya muke da irin yadda nake ba ta kulawa duk a domin ka.”

“Saboda ni kamar ya kenan?”

“Na sani kana son Zhara sai dai wani dalili na ka ko na ce ra’ayin da ka kitsawa zuciyar ka yasa ka kasa fahimtar hakan, wannan yasa na dinga yin abubuwan da zai sa ka yi tunanin ina sonta ne ta hakan kawai zan iya zuburo da abin da ya ke binni a ƙasan zuciyar ka ta hanyar kishi. Ko ita Zharan ba ta san dalili ba kawai dai ta san ina ba ta kulawa.”

Shiru Hafiz ya yi kunya ta rufe shi har ma ya rasa me zai ce me yasa ya kasa fahimtar aminin na shi. Rungume Anwar ya yi “ban san me zan ce da kai ba ban san da wace kalmar zan gode ma ba, ka yi haƙuri da abin na yi ma.”

“Manta da wani haƙuri can, burina auren ka da Zhara ya tabbata AlhamdulilLah haƙata ta kusa cimma ruwa, ina yi ma fatan alkhairi.” sun rabu da Anwar cikin farin ciki yana ƙara girmama Anwar a zuciyar shi haƙika samun amini kamar sa a wannan zamanin a kwai wahala.

Wuraren goman dare ta tabbatar da ba zai zo ba kuma babu tabbas ɗin zai kira ta ɗin, ɗaukar wayarta ta yi ba tare da ta yi dogon nazari ba ta kira wayar shi tana fara ringing a ka ɗaga, “macijiya ba kya ramin kan ki ya dawo gida ma tsabar munafunci ba za ki bar shi ya sarara ba!” Da sauri ta janye wayar daga kunnenta ‘tabbas bai kamata na kira a irin wannan lokacin ba, me yasa na kasa iya riƙi kaina ne’? Maganar Halima ce ta dawo da ita daga zancen zucin da take.

“Na sani ki na jina.”

“Ki yi haƙuri.”

“Da ke da haƙurin duk kun ci … rintsi idanunta ta yi ranta a ɓaci ta ce. “Halima ni ki ke zagi?”

“An zage ki ɗin ko za ki rama ne?”

“Humm wai ke me ki ke ɗaukar kanki ne Halima? Shin dan kinga ina yi ma ki kara da alkunya shi yasa ki ke ganin za ki iya ɗauko duk wani shirgin sharar ki ki zuba a kaina.”

“To ashe kan mage ya waye har hakan.”

“Shiru-shiru fa ba tsoro ba ne gudun magana ne, sannan me ma ki kace ɗazun wai macijiya ba ta ramin kanta shin kin manta da wannan ramin da ki ke ciki asalin ramin nawa ne ki ka zo daga sama kika kutso kan ki? Kin ga ashe tunda mai wuri ta zo sai a mai tabarma a samu a naɗe dan mai wuri ta zo karɓar wurinta.”

“Ai isa ce take sa ka ka yi ƙwacin wajan da wani ya haƙa, sannan kar ki manta dai matar ture bata da wani armashi a wajan miji na sani kin sani duniyar mu kuma ta sheda ke ɗin ba zaɓin Hafiz ba ce zaɓin mahaifin shi ce ni ce zaɓin shi kuma ya nuna wa duniya hakan tunda a ranar ɗauren auren ki duk da tarin jama’ar da su ka taru ya nuna ba ya da ra’ayin ki ni ce zaɓin shi a she kenan na cire tuta” rintsi idanunta ta yi har cikin ranta ta ji ciwon maganar murmushin ƙarfin hali ta yi kafin daga bisani ta ce “har yanzu dai da sauran ki ki je ki tambayi mijin mu ki ji ta ya a ka yi auren ki da shi ya yu.

Sannan ki bi a sannu domin igiyar auren ki tamkar a hannuna take, idan yanzu na so tsinke ta ba za ki kwana da auren Hafiz ɗina ba” tana gama faɗa ta tsinki kiran ta koma ta kwanta haɗe da janyo bargo ta rufe jikinta gaba ɗaya.

A ranta tana jinjina sha’ani na rayuwa wai yau Halima ce suke ga maciji duk a sanadin ɗa namiji. Har ga Allah ba ta son irin wannan rayuwar sai dai ya za ta yi ta kaita maƙurar da dole sai ta magantu.

Hafiz da ya fito wanka ya tarar da ita a tsaye wayar shi a hannunta “lafiya na ga ranki a ɓaci ke da wa ku ke waya?”

Numfashi ta ja ta furzar da ƙarfi “har damar da ka ba Zhara ta kai hakan, saboda cin fuska duk abin da kuke yi bai isa ba sai ta biyu ka da kira a sanda kake gida, sannan ta faɗa mini magana son ranta!”

Miƙo ma ta hannun shi ya yi yana faɗin “ba ni wayata.”

“Oh ta wayar ka ma ka ke ko tambayata me ta faɗa mini ba za ka yi ba”

“Da ba ki ɗauka ba za ta faɗa ma ki ne, sannan na tabbatar da ko me ya faru ke ce ki ka fara dan dukan ku babu wanda ban san halin ta ba” jefa masa wayar ta yi saurin caɓewa ya yi yana faɗin “so kike ki fasa mini waya.”

“Ba waya ba ji nake har kai da ita ɗin na haɗa na fasa!” Ta yi maganar a fusace ta nufi ƙofar fita har ta buɗe ƙofa ta juyo a zuciye tana faɗin “ta ce igiyar aurena a hannunta take ina jira yau na kwana a gidanmu sai na tabbatar da lallai matsayin na ta ya kai”!! Ta fita tare da rufi ƙofar da ƙarfi.

Girgiza kanshi ya yi “kai mata idan ka daka ta ta su sai su fasa ma ka kwanyar kai da rigimar su” tsaki ya yi sai bayan da ya yi shirin bacci, sannan ya fito ya samu ta rufe ɗakinta da key jiyowa ya yi zuwa ɗakin shi ya yi kwanciyar shi, zuciyar shi babu daɗi Halima matsala Zhara ma da a ke yi masa domin ta itama ɗin ciwon kai take ba shi.

Kwana biyu Hafiz bai neme ta ba haka zalika duk yadda tasa idanunta ko za ta ji shigowar shi gidan shiru bai zo ba, hakan ya sanya ta shiga damuwa har ma ta rasa wani kalar tunani za ta yi.

Fulani

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 4.5 / 5. Rating: 2

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Waye? 27Kuskuren Waye? 29 >>

2 thoughts on “Kuskuren Waye? 28”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×