Ganin yana shirin buɗe ƙofa yasa ta saurin riƙi hannun shi cikin zubar da hawaye ta ce. "Don Allah dai ka yi haƙuri kar ka cutar da ni, ni fa 'yar'uwar ka ce kai mai kare mutuncina ne a inda a ke ƙoƙarin kawar mini da shi. Don Allah Yaya ka mayar da ni gida" kallonta kawai ya yi na 'yan sakanni kafin daga bisani ya kawar da kanshi daga kanta ba tare da ya ce da ita komai ba ya buɗe ƙofa zai fita hakan ya tunzura zuciyarta ta fara magana cikin fushi. . .
Allah ya kara basira
Masha Allah