Skip to content
Part 30 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Murmushi ƙarfin hali Zhara ta yi tana faɗin “sannu da zuwa kin tsaya daga ƙofa shigo mana.”
“Ina wuni Aunty Halima” ƙarasa shigowa ta yi ta tsaya gefen Hasana “lafiya lau Hasana ina Husaini.”
“Ya fita” Mama ta fito kichen kallon ta take cikin mamaki “ikon Allah Halima yau ki ce a gidan namu.”
“Wallahi kuwa Mama ina wuni.”

“Lafiya lau, ya gidan, kin tsaya ki zauna mana, ke kuma Zhara kin barta a tsaye.”
“Na ce ta zauna ita ce dai ta tsaya” har cikin ranta ba ta so ta samu Mama a gidan ba shi yasa ma ta yi ta addu’a Allah yasa ba ta nan, ajiyar zuciya ta yi kafin daga bisani ta ce. “Ba komai ina sauri ne na ce bari na zo mu gaisa ashe ma Zhara tana gida.”

“Kin kyauta ai, itama ba ta jima da zuwa ba” Zhara ta miƙe tsaye tana faɗin “mu je ɗaki” ba musu ta bi bayanta zuwa ɗaki ta tsaya daga tsakiyar ɗakin duk da tayin wajan zaman da Zhara ta yi ma ta. Dukan su suka yi shiru suna tuna rayuwar su ta baya musamman wasu abubuwa da suka faru a cikin ɗakin a rayuwar su ta baya. “Ki zauna mana” Zhara ta katse shirun tana nuna mata katifa, “ba abin da ya kawo ni kenan ba, na zo ne mu yi magana akan maganar auren ki da Mijina” cikin ƙarfin hali Zhara ta ce da ita tana saurarenta.

“Ina mai ba ki haƙuri a kan abin da ya faru a baya, na yarda nayi kuskure amma duk da hakan idan har da adalci bancancanci wannan hukuncin daga gare ki ba, domin tun a farko na yi iya ƙoƙarina wajan ganin na guje masa na kuma gujewa auren shi, amma ki ka na ce har sai da ki ka ga auren ya tabbata ba tare da sanina ba. Kin ga kenan ai ba laifina ba ne, ba kuma kuskurena ba ne hakan Kuskuren na ki ne” ta yi shiru tana jan numfashi, Zhara ta zuba mata idanu tana saurarenta “ina so ki dubi tarayyar mu abin kunya ne a ce wai ni da ke mu aure miji ɗaya tsakani da Allah ke ba za ki ji hakan wani barbarakau ba wai namiji da sauran Hajara?”
Ganin Zhara ba ta ce da ita komai ba sai kallonta da take yi, “ina ta magana kinyi shiru” gyara zamanta ta yi tana faɗin “ai sauraren ki nake, idan kuma kin gama faɗar abin da za ki faɗa ne sai naji”

“Humm ai abin faɗa yawan su ya wuce na gama, shin za ki sanya almakashi ne ki yanki amintar mu kamar yadda ki ka ɗauki hanyar yi ko kuwa za ki fasa auren mijina ne domin ci gaba da amintar mu?” Dariya Zhara ta yi marar sauti tana kawar da kanta daga kan Halima ta yi tana kallon wani gefen tana faɗin “kuskurena ne ko kuskuren ki ne kuma dai Kuskuren waye duk mu ajiye wannan a gefe, domin komai da ya riga da ya faru na riga da na yarda da cewar ke ɗin matar Yaya Hafiz ce tun a luhulmahafuz cikin mu babu wanda ya isa ya canza ƙudurar Ubangiji.

“Me kike so ki ce da ni kenan.”
“Ina so na faɗa ma ki kamar yadda ba mu isa mu ka hana Allah ikon sa a kan auren ki da Yaya Hafiz ba haka ban isa na hana Allah ikon sa a kan nawa auren da Yaya Hafiz ba, kawai abin da zan iya cewa da ke shi ne mu bar wa Allah komai duk hukuncin da ya yi mu ɗauke shi da hannu bibbiyu. Amintar mu idan har kin so ba za ta taɓa yankewa ba ni dai a wajena ban san kuma na ki hukuncin ba”

“Mtsw! Dama ai na sani ta ya za ki ƙi amincewa da auren sa bayan kin rasa mijin aure shi yasa a ka shiga a ka fita har sai da tsohun shi ya manna masa ke wanda na san ko shi tsohun nasa ba a banza a ka barshi ba” ta nuna ta da ɗan yatsa tana magana cikin kausasa murya “wallahi ina mai gargaɗin ki da kar ki kuskura ki ce za ki aure mijina domin yin hakan tamkar kin sai tikitin ɗin mutuwar ki ne” kallon Halima take da matuƙar mamaki domin ko a mafarki a ka ce wai za ta sauya har hakan kai tsaye za ta musa har da ƙarin rantsuwa ma za ta yi. Amma gaba ɗaya namiji yasa ta sauya “magana nake kin mini banza!”

“To me ki ke so na faɗa maki, ba fa tsoron ki nake ba kawai fitinar ce ba na so saboda ba ta da amfani, sannan ina duba amintar mu shi yasa nake ɗaga maki ƙafa kina yi mini yadda kika so. Sannan kin fi kowa sanin idan har masoya suna yawa to ni sun ma mini yawa kin san wannan, dan haka na fi ƙarfin zama gaban malami dan janyo zuciyar namiji, ba mamaki ke ce kika gaza ta wani fannin har hakan yasa ya gano ashe fa ya tashi yi wa kansa sakkiyar da ba ta da ruwa shi yasa ya yi saurin dawowa.” Ta yi shiru tana murmushi “yawwa ki ka ce tikitin ɗin mutuwa na saya? To shi kenan ai sai mu zuba mu gani, gidan Hafiz dai ne sai na shigo a matsayin matarsa kamar yadda ki ka shiga, babu kuma wanda zai kalle aurena da shi a matsayin cin amana matuƙar ba a kira na ƙi auren da hakan ba” Halima ta cakumo wuyan rigar Zhara “ai kuwa auren ki da mijina shi ne cikakkin auren cin amana ba nawa ba” magana take tana kaiwa mata duka, a fusace Zhara ta kaita ƙasa tana mayar mata da duka Mama ta shigo ɗakin da sauri tana faɗin “SubhanalilLah me ya ke faruwa? Kun yi hauka ne dambe kamar wasu ƙananan yara!” Magana take tana ƙoƙarin raba su amma ta kasa janye Zhara daga jikin Halima tsawa ta daka mata tana faɗin “za ki ɗagata ko sai na nuna ma ki fushina ne!?”

Janyewa ta yi ta koma gefe tana mayar da numfashi “ke har kin isa ki ce za ki sameni a gidan ubana ki dake ni! Shiru-shiru ai ba tsoro ba ne gudun magana ne!”
“Zhara ki mini shiru na ce! Me ya haɗa ku?”
“Wai gargaɗe na take da kar na aure Yaya Hafiz ita har ta isa, ni ban yi kishin da auren ta da shi ba a lokacin da ni zai aure na haƙura na taya ta yaƙin cikar burinta sai ni ce za ta yi kishi da ni saboda ƙwaƙwalwarta ta kife ce!”

“Isa ce tasa na aure shi a lokacin na ki auren domin ni ce zaɓin shi shi yasa ya ɗaukini ya bar ki duk da tarin mutanen da kuka tara. Aure da Hafiz kuma Bismillah ina jiran ki ki shigo ki gani idan har za ki ci riba, Allah na tuba wanda ba sonki yake ba ya kuma nunawa duniya hakan ki shigo ki ga ni idan za ki samu farin ciki!”

“Ai kuwa zan shigo sai kuma na tabbatar ma ki da duniyar cewar ni ce zaɓin nasa sai na tabbatar ma ki da ina gaban ki a zuciyar Hafiz!”

“Ina jiran ki ki zo ɗin! Sannan ba dai ni kika daka ba sai kin san shaye ruwa ne wallahi sai kin yaba wa aya zaƙinta!!” Zhara za ta yi magana Mama ta dalla mata hannu a bakin “idan na ji kin sake cewa tak wallahi sai ranki ya ɓaci, kun dai ji haushi kun ji kunya wallahi, kun ta shi tun yarinta tamkar ‘yan biyu komai a tare kuke yin sa saboda namiji ya shigo rayuwar ku rana tsaka kuna shirin mayar da amintar ku ƙiyayya” dafa kafaɗar Halima ta yi ta buɗe baki za ta yi magana Halima ta gauci daga dafar da ta yi mata tana yin tsaki “ni ba ki da abin da za ki faɗa mini ai da haɗin bakin ki a ka yi komai” sakin baki ta yi tana kallonta ita Halima take faɗa wa magana harda tsaki ficewa Halima ta yi tana yaɓa masu magana takaici ya rufe Zhara tana so ta yi magana Mama ta hana ta yin magana.

Bayan fitar ta Mama ta ce. “Iri-irin waɗan-nan matsalolin nake duba ma ki Zhara amma ya na iya tunda kin ce kin ji kin gani ai sai dai na bi ki da addu’a kawai Allah ya kare ki daga kaidin su”
“Ni fa ba ni ce na nace wa auren nan ba shi ne da kuma Abba da Dady ba kuma zan iya cewa da su a’a ba kin san haka, kiyi haƙuri.”

“Ni daina ba ni haƙuri ba ki mini komai ba, Allah dai ya kyauta kawai. Amma ki sani wannan shirmin kar ki kuskura ki ce za ki yi shi idan anyi aure dambi ko sa’insa da kishiya zubar da ƙima ne a wajan miji, ke dai yi ƙoƙari ki ga kin kyautata masa biyayya haƙuri shi ne kishi na ainahi da muka gada a wajan matan Ma’aiki SallalLahu Alaihi Wa Alihi WasalLam. Ki kuma tsalkaki zuciyar ki” shiru ta yi tana sauraren nasihar Mama har Mama ta gama ta bar ɗakin ba ta ce komai ba dan haushi take ji da ba a barta ta lallasa ta ba, “mahaifiyata take yi wa tsaki!”

Jidda ta janye tagumin da ta yi bayan ta gama sauraren Halima da ta gama kora mata bayani ajiyar zuciya ta yi tana faɗin “ni wallahi har ma na rasa ma me zance, maganar gaskiya tun farko Kuskuren ki ne Halima gaskiya zan faɗa ma ki yardar da Zhara ta maki ne yasa ta haɗa ki da Hafiz dan ki gwada shi, ke kuma sai ki ka biye wa sheɗan ya fitsare maki zuciya kika manta amintar ku da komai kika karɓi soyayyar shi har kuka kai ga aure.”
“Na yarda na so shi na kuma ba shi damar da ya so ni ɗin, amma ai na ce ba zan aure shi ba ita ce tasa ya aure ni sannan kuma yanzu sai ta dawo ta ce za ta aure shi cin amana ya wuce wannan!”

“Ni gaskiya zan faɗa maki kiyi haƙuri ki ajiye komai ki tsalkaki zuciyar ki ku zauna lafiya tunda dai har Allah ya riga da ya tsara hakan, kuma maganar Allah Zhara ba ta ci amanar ki ba, kawai ki… Ɗaga mata hannu ta yi “Kinga Jidda ni ban zo nan dan ki wani yi mini wa’azi ba na ɗauka idan ki ka ji za ki bani wata shawarar da zan samu mafita amma sai wani zuba kike mtsw!” Duk yadda ta so ta saurareta taƙi sai ma tafiyarta da ta yi. “Yau na ga ikon Allah ke ba a kira auren ku cin amana ba sai dan ita da kowa yasan tun farko da ita a ka yi maganar auren yanzu za ta aure shi sai ki ce za ki yi kishi ai kuwa iska na wahalar da mai kayan kara” Jidda ta yi maganar tana mai tashi dama aiki take Halima ta shigo.

Zaune take akan tabarma ta tasa abinci gaba ta kasa ci ji take kamar zuciyarta za ta fashe saboda baƙin ciki da takaicin abin da Zhara ta yi mata. Har Mama ta zauna kusa da ita ba ta sani ba janye hannun Halima daga tagumin da ta yi Mama ta yi tana faɗin “lafiyar ki kuwa?” Ajiyar zuciya ta yi “lafiya lau.”

“Humm da dai kin fito kin faɗi abin da ke zuciyar ki dan nuƙu-nuƙu ba zai ma ki rana ba” kuka ta fashe da shi tana magana cikin ƙunar zuci “Mama wai Hafiz ne zai aure Zhara!” Murmushi ta yi kafin daga bisani ta ce. “Kenan wannan dalilin ne yasa ki ka kwaso jiki kika zo gida? To mu yi maki me? Ai Halima duk tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwan kan duka, kuma kowa ya sai rariya yasan za ta yi masa zuba. Dama na san wannan ranar za ta zo” shigowar Baba ne yasa ta yi shiru tana amsa masa sallama, zama ya yi a kan tabarma da mamaki a fuskar shi “baƙuwa muka yi babu sanarwa.”

“Humm aikuwa dai gata nan, sannu da dawowa ya kasuwar.”
“AlhamdulilLah”

“Sannu da dawowa Baba” idanunsa a kanta ya amsa gaisuwar yana tambayar lafiya yaga kamar kuka take.? “Bari na kawo ma abinci kar ka daka ta wannan yarinyar.”
“Wani abincin zan ci bayan alamu sun nuna da a kwai matsala faɗa mini me ya ke faruwa?” Kallon Halima tayi tana Murmushi ta ce. “Ba fa wani abun ba ne wai mijinta ne zai aure Zhara shi ne take wannan kukan wanda ni na rasa dalilin yin na sa” cikin fara’a ya ce. “AlhamdulilLah wallahi na ji daɗin wannan al’amarin koyaushe addu’ar da nake ta yi kenan Allah ya tabbatar da auren nan domin har ga Allah na ji ciwon abin da ya faru a baya kuma duk ta sanadin ‘yar da muka haifa” kasaki ta yi tana sauraren shi da matuƙar mamaki ‘wato ma duk murna suke shi Baban da kanshi har addu’a yake yi.’

Maganar Mama ce ta dawo da ita daga zancen zucin da take “nima dai kar ka tona zuciyata kaga irin farin cikin da nake wallahi, sannan in banda shirmen ki da a je wani wajan a ɗauko ma ki wacce ba ki san halinta ba ba gara Zhara da kin fi kowa sanin halinta ba. Sannan in dai kina da ta ido ai ba kya nuna kishi ko baƙin ciki da wannan auren ba tunda dama can ita ce asalin zaɓin rana tsaka ki ka zo ki ka yi masu kutse” ji take kamar ta fasa ihu, ko abincin kasa ci tayi ta bar masu wajan.

Bin bayanta ta yi da kallo ta saukar da ajiyar zuciya “wato ita ta manta da abin da ta yi a baya sai a yanzu da za a yi mata ne za ta ji ciwo.”
“To halin ƙurciya fa Allah dai ya kyauta.”
“Amin. Bari na ɗauko ma abinci” ta faɗa tana meƙewa tsaye.

Tun bayan da ta koma gida gaba ɗaya ta daina shiga lamarin sa ya yi lallashi har ga ji ya zuba mata idanu. Ana saura kwana uku biki yana ɗaki yana shirin fita dan Anwar yana gida yana jiran shi za su je unguwa. Shiga ɗakin tayi babu ko sallama ta masa tsaye a kai daina ɗaure maɗaurin takalmin ya yi ya ɗago yana kallonta “mene kuma? Kin shigo ba ko sallama kamar ba ‘yar musulmi ba.”
“Sa himma dai ka kira iyayena da kafirai” riƙi kansa ya yi cikin damuwa ya ce. “SubhanalilLah! Allah ya tsare ni da hakan, rigima kike ji ba kuma zan biye ma ki ba. Don Allah ki zo ki fita ina da abin yi”riƙi ƙugu tayi tana faɗin “ai kuwa ka so rigima dan ka saya da kuɗin ka tunda har ka ce za ka ƙara aure. Ni abin da ya kawo ni me kake nufi a ina za ka ajiye amaryar taka ne? Na ga babu wani shiri da a ka yi wa gidan nan” ƙarasa sa takalminsa ya yi ya mike tsaye yana sa agogo a tsintsiyar hannunsa “magana nake yi fa.”

“Ba a nan za a ajiye ta ba, gidan ta daban” lailayu ashar ta yi ta zunduma masa “tunkan a ɗaura auren har za a fara nuna mini rashin adalci wato ita danƙara mata gida ka yi ni kuma za ka barni a wannan gidan!”
“Halima dan na raba ma ku gida hakan ba zai sa a kira ni da marar adalci ba domin na yi hakan ne saboda zaman lafiya na tabbatar da idan har na haɗe ku waje ɗaya fitina ce kawai zan haɗa, sannan mene ne matsalar gidan nan ne, duka yaushe ki ka zo, babu wanda zai ga gidan nan ya ga wani aibun sa domin kamar sabo yake.”

“Wallahi ni ba zan yarda ba ko dai ka haɗe mu waje ɗaya ko kuma ni ma ka mini wani sabon gidan na bar wannan ɗin” zuba mata idanu ya yi shi har ma ya rasa me zai ce da Halima domin rigimarta ta masa yawa gaba ɗaya halinta ya sauya ta zo masa da ba zata. “Ba wai kallona za ka tsaya kana yi ba faɗa mini wanne za ka yi daga cikin biyun?”
“Shi kenan idan na fita zan turo ma’aikata su sabunta fintin gidan idan har kayan ɗakin ma kina da buƙatar a canza maki In sha Allah duka za a yi.”
“Ni ba hakan na ce ina so ba ko dai ta zauna a gidan nan tare da ni ko kuma nima ka ba ni wani gidan daban.”

“Ko ɗayan ba zan yi ba har fintin ma an fasa, haba! Wai kin ɗauka tsoron ki nake ne? Kawai ina lallaɓa ki ne da yi ma ki uzuri cewar duk macen da za a yi wa abokiyar zama dole sai ta ji ba daɗi a ranta, amma na ga sam kin gagara fahimtar haƙurin da nake maki. Ki je kiyi duk abin da za ki yi ɗin!!” Ƙwafa ta yi tare da barin ɗakin fau! Kamar kububuwa. Tsaki ya yi ransa a ɓaci ya ƙarasa shirin sa ya fito filo ya sameta riƙi da galan ɗin da yake sayen man fetur na ingin da kuma ashana riƙi a hannunta kawar da kanshi ya yi daga kanta ya nufi ƙofa zai fita ta sha gaban shi da sauri tana huci “wallahi in har ba za ka yi abin da na ce ba zan zuba mana fetur ɗin-nan kowa ma ya mutu sai na ga ni idan da gawa za a ɗaura auren.!!” Bude galan ɗin ta yi ta fara watsa shi cikin falon. Kallonta yake cikin wani yanayi mai wuyar fassarawa.

Fulani

<< Kuskuren Waye? 29Kuskuren Waye? 31 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×