Skip to content
Part 33 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Momy ce tsaye a bakin ƙofar shigowa falon murmushi ƙarfin hali tayi “sannu da zuwa Momy ƙara so kin tsaya daga bakin ƙofa.”

“Dama ai jiran ki nake Hajiya mai gida ki mini izinin shigowa gudun kar rashin izinin na ki ya janyo mini matsala” ta yi maganar cikin gatsale, jikinta ya yi matuƙar sanyi komai ba ta ce ba sai tsayawa tayi daga gefe, zama ta yi a kan kujera Halima ta fito ɗakinta fuskarta ciki da fara’a sannu da zuwa”

“Yawwa Halima ai na ɗauka ko ba kya nan”

“Ai tun ɗazun na dawo, bari na kawo maki abin sha”

“A’a dawo ki zauna na gode” ba musu ta zauna a kusa da Momy. “Ina wuni”
“Da ban wuni ba za ki ganni ne, wato dan samun wuri har ni za ki zaga kice me na isa na yi sai dai nayi iko da gidana amma ba dai gidan ki ba” mamaki ya bayyana a kan fuskarta gaba ɗaya ta kasa fahimtar me Momy take faɗa “magana nake maki kinyi shiru ko isar ce za ki nuna mini ne?”

“Uhm kiyi haƙuri ni wallahi ban san na faɗi hakan ga kowa ba ko a cikin raina ma bare kuma na furtawa wani”

“Haba ke kuwa Zhara kar ki ce za ki sauya zance dan kin ganta a gaban ki. Ɗazun na faɗa maki zan je wajan awo amma zan biya na duba Momy kwana biyu tayi fama da ciwon ƙafa ki ka ce ba za ki ba dan ke makaranta za ki tafi, da na nuna maki hakan ba daidai ba ne dan uwa darajarta tafi ta komai a duniyar nan me kika ce da ni?” Ta mata tambayar tana mai zuba mata idanu “ni yaushe ma muka yi hakan da ke don Allah”
“Kai Momy kin ga halinta na munafuncin ba wai dubeta yi take kamar ba ta san komai ba, cewa fa ki ka yi ba za ki ba dan karatun ki ya fiye maki komai ba za ki rasa karatun ki saboda wata can ba, shi ne na ce wacce ta haifa ma ki mijin ce wata can ai idan da tunani bai kamata ki faɗi hakan a kanta ba dan in yanzu ta ce ɗanta ya barki magana ta zauna, kika ko ce ba ta isa ba gidanta ne take da iko ba dai a gidan ki ba” sakin baki tayi tana kallon Halima kamar wata doluwa mamaki ya cika ta yadda Halima take ta zuba zancen ƙarya babu kunya babu tsoron Allah da ƙyar ta iya buɗe baki ta ce. “Ki ji tsoron Allah halima yaushe muka yi hakan da ke don Allah fa? Ni da gaba ɗaya wunin yau ba mu haɗu da ke ba”

“Idan ban ji tsoron Allah ba tsoron ki zan ji ne? Na ce tsoron ki zan ji ne? Zan iya rantsuwa da ƙur’ani a kan munyi wannan maganar da ita Momy idan har hakan zai sa ki gamsu da ta faɗa ɗin” ta ƙarasa maganar idanunta a kan Momy “wallahi na yarda a kawo ƙur’anin nima zan rantse sai a tabbatar da mai gaskiya a tsakanin ni da ita” shigowar Hafiz ne ya sa ta mayar da hankalin ta a wajan shi ba tare da ta ba Zhara amsar maganarta da tayi niya ba.

“Yawwa dama kai nake jira tun ɗazun ƙara so zauna”

“Me ya faru ne Momy? Tun da kika kirani cewar na zo hankalina yaƙi kwanciya”
“Yanzu ai sai ya kwanta tunda ka samu ba a tsikare ‘yar gwal ɗin taka ba” kai duban sa yayi ga Zhara da tayi tsuru komai bai iya cewa da ita ba sai zaman da ya yi zuciyarsa na dukan uku-uku dan ya tabbatar da banza ba ta kai Zomo kasuwa sai da dalili, zuwan Momy gidan sa ba a banza ba ne kuma ba ya jin hakan alkhairi ne. “Zuwa nayi na tabbatar wa da matarka na isa da gidan nan domin kai da take taƙama da shi ikona ne kai, ina so na nuna mata har yanzu ruwa na maganin dauda, dan duk da ka girma ka mallaki hankalin kanka manyan gidaje motoci da kuma asibiti uwa dai uwa ce kuma in har ana so a gama da duniya lafiya dole a bi duk wani umurninta so da ƙafa”

“Wai me ya faru ne? Me ya janyo duk waɗan nan maganganun?”

“Idan har kayi haƙuri ba ka sanya garaji ba ai da sannu amsar tambayar ka za ta fito, daga yanzu na rushe tafiyar Zhara makaranta ma’ana babu ita babu makaranta tayi zaman aure kamar ko wace mace tagari firgice Zhara ta kalleta “kalleni da kyau makaranta ce dai ba za ki sake zuwanta ba” murmushin Halima tayi tana ɗagawa Zhara gira a fakaice “duk me ya kawo hakan Momy?”

Ya yi tambayar murya a sanyaye”

“Saboda ta nuna ni ba kowa ba ce a wajan ka ban isa da kai ba, sannan ta nuna karatu ya fini muhimmanci shi yasa nake so na tabbatar mata da matsayin da nake da shi a wajan ka!” Cikin ɗaga murya ta faɗa masa duk abinda Halima ta sameta ta faɗa mata a gida” kallon Halima yake da matuƙar takaici harma ya rasa me zai ce “magana za kayi ba wai kallon mutane na kira ka yi ba”

“Haba don Allah kawai saboda ta zo ta tsara maki zance sai ki yarda da ita, wannan fa duk shafcin gizo ne babu yadda za a yi Zhara ta faɗa maki hakan kawai d… “Da kai da ita Zharan duk ku karɓi wannan na ce ku karɓi wannan!” Ta masu daƙƙuwa “idan kai ta shanye ka ni garas nake a buɗe nake ganin komai, magana dai ba zan sauya ba kai kayi ta zama a cikin makantar har sanda Allah zai yaye ma ka ina nan ina ta yi ma addu’a”

“Kin ga ni ba ita ce mai gaskiya komai na faɗa ba yarda yake yi da ni ba shi yasa duk abin da take nake zuba mata idanu tunda ko faɗa masa nayi ba yarda yake ba”

“Ke dai Allah ya yi ma ki albarka da kika zo ki ka faɗa mini, bata san dama a ciki nake da ita ba na zuba mata idanu kawai” kallonsu take tana zubar da hawaye domin a duniyar nan a yanzun dai bata da wani buri da ya wuce karatun ta shi ne a ke ƙoƙarin hanata saboda kawai basa son ganinta cikin farin ciki.

“Hakan ba adalci ba ne Momy me na tsare maki ne kike ƙoƙarin ganin bayan duk wani farin cikina, ki tuna kina da ‘ya mace a gaban ki kuma gidan wani za ta tafi wallahi duk abin da kika mini sai an mata linkin hakan dan Allah ba azzalumin baw… Marin da Hafiz ya kifa mata ne yasa ta haɗiye sauran maganar dafi kuncinta tayi tana kallonsa da tsananin mamaki “marina fa kayi”

“Abinda ya fi mari ma sai na yi maki ko za ki rama ne? Mahaifiyata kike faɗa wa magana saboda ba ki da kunya!”

Farin ciki ya cika zuciyar Halima ji take kamar ta tashi ta taka rawa, murmushin farin ciki Momy tayi tana faɗin “ka faranta zuciyata Allah ya yi maka albarka” ta mayar da kallonta ga Zhara da take zubar da hawaye “ko yanzu na tabbatar da kin fahimci irin matsayin da uwa take da shi a wajan ɗan kirki” barin wajan tayi cikin sassarfa ta shige ɗakinta tare da rufe ƙofar zama yayi diɓis a kan kujerar zuciyarsa babu daɗi “ka dai ji me na faɗa ma ko matuƙar na ji labarin ta tafi makaranta wallahi Hafiz za ka sha mamakina, ko kuma na ji ita ko kai kun yi wa Alhaji maganar Allah ranka in yayi dubu sai ya ɓaci!”

“Kiyi haƙuri in sha Allah babu ko ɗaya da za a yi” ta tashi tafiya Halima ta raka ta iya ƙofar falon ta dawo Hafiz ya rakata wajan mota sai bayan sun tafi ya dawo cikin gidan ya tarar duk sun rufe ƙofa da key, zama ya yi dirshin a kan kafet gaba ɗaya ya rasa me ya ke yi masa daɗi haka ya gama zamansa ya bar gidan cikin ɓacin rai. Tun da ta shiga ɗaki take kwance a kan gado Husna sai kiran wayarta take taƙi ɗagawa ƙarshe ma kashe wayar tayi gaba ɗaya. Halima tana jin tashin motar shi ta fito ta kunna waƙa tare da sa murya tana rawa yau farin ciki take ji tamkar daren sallah.

Da dare wajajan ƙarfe goma ya dawo gidan ya tarar gidan shiru, wajan Halima ya tafi cikin sa’a ya tarar da ƙofar a buɗe, a falo ya sameta zaune a kan kujera tana dannar waya, zuciyarta ta dinga bugawa fat! Fat!! Fat!!! har ga Allah ta ɗauka ta rufe ƙofa ashe a buɗe ta barta sam ba ta shirya haɗuwa da shi a wannan lokacin ba. Zama ya yi a kan ɗaya daga cikin kujerar da suke fuskantar juna fuskewa ta yi kamar ba komai da fara’a a fuskarta “sannu da dawowa Sweety”

“Da izinin wa ki ka tafi gidan Momy?” Ya yi mata tambayar yana mai kafeta da idanu “to ai naga dai gidan iyayenka ne dan na je ban faɗa ma ba hakan ba zai zama laifi ba, kawai naje dubata ne saboda na ji kuna waya kana tambayarta hukunta. Sannan kuma ai ba fita nayi kai tsaye ba daga asibiti na fito”

“Dalilin kenan da yasa kika ce za ki je asibiti da mota ta ni na zauna nayi aiki ki dawo da kanki gida? Hakan da kika yi daidai ne, haka kawai saboda ban amince da karatun ki ba shi ne za ki yi ƙoƙarin zuwa ki rusa mata nata karatun sannan ki kuma haɗa da yi mata ƙaryar abin da bata faɗa ba” cikin jin haushi ta ce. “ni ban san yaushe na zama maƙaryaciya ba a wajan ka ba, idan har ba ta faɗa ba zan je na ce ta ce ne haba” gyaɗa kansa ya yi kafin daga bisani ya ce. “kin kyauta kin haddasa rigimar da kike so ki ga kinyi sai ki zuba ruwa ƙasa kisha. Ɗauko mini key ɗin motata” tana tunzure-tunzure ta je ɗakin baccinta ta ɗauko masa fizga ya yi yana miƙewa tsaye wayarta da take a jiye akan kujerar ya ɗauka “ba ni wayata”

“Ba zan bayar ba, daga yanzu ko bakin gyet naji kin je wallahi in ranki yayi dubu sai ya ɓaci, waya kuma na ƙwace sai naga da me za ki kirata ɗin!”

“Wannan ai rashin adalci ne ai ita ya kamata kaje kayi wa wannan hukuncin ba ni ba, iyee wannan ai shi ake kira da Kura da shan duka gardi da ƙwacen kuɗi, to wallahi ba za ta saɓu ba wai bindiga a ruwa dole ka bani wayata!” Bai bi ta kanta ba ya fice ta biyo shi tana masifa bai tanka mata ba sai bugun ƙofar Zhara da yake tana jinsa ta masa banza dan za ta iya jurar komai amma banda duka ko a kan rashin gaskiya ne bare kuma da gaskiyarta wai kuma mari. Jiki a sanyaye ya juya zuwa ɗakin shi zai rufe ƙofa Halima ta riƙi ƙofaf kallon da ya watsa mata ne yasa ta saki ƙofar rufe wa ya yi da ƙarfi, haka ta juya ɗaki tana zancen zuci, ‘idan fa na yi wasa ina ji ina gani reshe zai juye da mujiya.’

“Dole ne nasan abin yi.!”

Washe gari da sassafe ya sake komawa har yanzun dai ba ta buɗe ƙofa ba, da zai fita wajan aiki ya yi ta buga mata ƙofa ta masa banza, tsoro ne ya shige shi “kar dai wani abun ya samu ‘yar mutane fa. Zhara don Allah ki buɗe mu yi magana, kina jina kuwa?” Shiru babu amsa ko motsinta ya kasa ji bare har yasa rai da za ta buɗe ɗin, haka ya fita wajan aiki zuciyarsa ba daɗi, ko ta kan Halima bai bi ba tashin motarsa kawai ta ji ƙwafa tayi wato da gasken dai yake ba zai bata wayarta ba.

Office ɗin Anwar ya je ya samu zuwansa kenan zama ya yi a kan kujera “ango ka sha ƙamshi na Halima da Zhara ba da kanka asare” tsaki yayi “kai ba ka fahimtar lokacin wasa da wanda ba na wasa ba” ajiye fayel ɗin hannunsa ya yi ya zauna a kan kujerar da take kusa da ta Hafiz yana faɗin “me ya faru ne?” Kallon hannunsa ya yi cikin damuwa ya ce. “Da wannan hannun nasa na Mari Zhara”
“Mari! Kai kuwa me yayi zafi haka har ya kai ga duka?”

“Uhm! Halima ce ta haddasa rigimar nan ita ce silar faruwar komai” a taƙaici yayi masa bayanin abin da ya faru “oh Allah banji daɗin hakan ba, ko me za ta yi bai kamata ka daketa ba dukan mace ba abu ne mai amfani ba musamman a wajan miji, duk da bata kyauta ba faɗar maganar da tayi amma tsakani da Allah idan za mu yi duba ta sigar adalci an mata abin da ba lallai ne ta iya jurar yin shiru ba”

“Amma ai koma meye da tayi haƙuri taga me zanyi amma kasan ba zan iya jurar ganin tana faɗa wa mahaifiyata magana na kuma ja baki nayi shiru ko da kuwa ita ce ba ta da gaskiya”

“Yanzu dai ko ma meye ya riga da ya faru ka yi ƙoƙarin bata haƙuri, idan ya so daga baya ko ni zan iya taya ka roƙar Momy har ta amince ta janye maganar rashin zuwan Zhara makaranta” tsaki ya yi kafin daga bisani ya ce. “Ba na jin zan iya bata haƙuri idan har ita a matsayinta na matar da nake aure ba za ta iya sauke girman kanta ta bani ba, damuwata ita ce rashin jin motsinta da banyi ba, ban san a wani halin take ba”

“Ai kuwa dole ka bata haƙuri domin marin da kayi mata shi ne babban laifin ka kuma ba ko wace mace ce za ta jurewa hakan ba, sannan idan da adalci ya kamata kayi mata uzuri domin bata taɓa yi ma wani abu kwatancin hakan ba. Ka tashi mu je gidan In sha Allah za ta buɗe ƙofar, amma don Allah ka dinga sarrafa fushin ka dukan mace ko musulunci bai yarda da hakan ba, ka kuma sani” jinjina kansa kawai yayi. A tare suka fito kowa ya shiga motarsa.

Halima tana zaune a kan kujera tana kallon wani Film ɗin India a ka ɗauki nepa tayi tsaki ” ‘yan rainin hankali sun ɗauki wutar, kallon da yake ɗebe wa mutum kewa sun wani ɗauke wutar, shi kuma ɗan baƙin ciki ya hanani wayata mtsw.”

“Assalamu alaikum” juyawa tayi kallo ɗaya ta mata ta gane wace ce dan satin farko na zuwan Zhara ta zo da yaranta ta wuni, hakan yasa ta juya da kanta ba tare da ta amsa mata sallamar ba “au ashe kina nan na ji ina sallama shiru, an tashi lafiya?” Halima ta mata shiru “Zhara kuwa na nan?”

“Ga ta nan a kaina!” Riƙi baki Aunty Husna tayi “ikon Allah abun ba na faɗa ba ne Allah ya ba ki haƙuri” tayi maganar tana tafiya tana jin Halima na yi mata tsaki komai ba ta ce da ita ba ta tura ƙofa taji a rufe buga ƙofar tayi tana kiran sunanta, Zhara da take kwance zazzaɓi ya rufeta ta jiyo muryar Aunty Husna hakan yasa ta tasu da sauri ta buɗe mata.

Tun da ta zauna take bin Zhara da kallo “me ya same ki naga kin rame?”
“Zazzaɓi nake fama da shi kwana biyu”

“Ayya sannu Allah ya sawwaƙe, wallahi duk hankalina ya tashi na ji ki shiru, kuma ina kiran wayar ki ba ta zuwa”

“Na kashe wayar ne shiyasa, kuma ma na daina zuwa makaranta”

“A kan me ko duk ciwon ne” cikin zubar da hawaye ta faɗa mata abin da ya faru “ikon Allah amma kuwa Halima ba ta kyauta ba, Allah na tuba yanzu ai anwaye an daina irin wannan kishin na hauka da sharri, amma fa kema ba ki kyauta ba wallahi uwa uwa ce komai lalacewarta, dole ya ji zafin faɗa mata maganar da kika yi” riƙo hannunta tayi ta riƙi “rufe kanki a cikin ɗaki hakan ba mafita ba ce ki ba mijinki haƙuri komai ya wuce”
“Haba Aunty Husna mari na fa yayi, ni zan iya jurar komai amma wallahi banda duka kuma a kan gaskiyata, sannan saboda kawai su ƙuntata mini shi ne za su hanani karatuna da nake matuƙar so”

“Eh ai na faɗa bai kyauta ba, amma abin da za ki yi tunani shi ɗin ɗan’uwanki ne ko ba shi ki ke aure ba idan har kika yi ba daidai ba yana da hurumin dukan ki bare kuma kina auren sa, duk da dai hakan ba hujja ba ne, amma na fi son ki kalle hakan ta sigar waye shi a wajan ki ko babu aure, sannan idan har kika ce za ki yi fushi da shi ai kin faranta ransu kuma burinsu ya cika dama ai daga ita Momyn har Halima sunyi hakan ne dan su ƙuntata maki su kuma shiga tsakanin ki da mijinki, to ki nuna masu basu isa ba ki yi ƙoƙarin dawo da farin cikin ki a tsakanin ki da mijin ki”

Shiru tayi tana kallon Zhara ganin babu alamar ta sauko yasa ta dafa kafaɗarta “Zhara kiyi haƙuri ki daina tuna marin nan hakan kawai zai sa komai ya daidaita, yin fushi da shi hakan na nuna da sunyi nasara akan ki, shi kuma maƙiyi karka yarda ya gano lagunka ko baƙin cikin ka, koyaushe murmushi ya kamata mu dinga haska makiyan mu da shi a matsayin takobi”

Ajiyar zuciya tayi tana faɗin “shi kenan zan yi ƙoƙarin yin hakan”

“Yawwa don Allah ki manta komai ki janyo mijinki a jikin ki, ki kuma kiyaye faɗawa mahaifiyarsa magana ko me za ta yi maki kiyi haƙuri matuƙar kina so ku zauna lafiya da ɗanta” tashi tayi tana ɗaukar jakarta “ni zan tafi tare muka zo da Abban Fati zai kaini makaranta na ce mu biyu na duba ki, ki ci gaba da addu’a In sha Allah za ki dawo ki ci gaba da karatun ki”

“Allah yasa, na gode sosai” za ta rakata tace ta yi zamanta ta yafe har ta kai ƙofa ta ce. “Ki dai samu abinci ki ci dan alamu sun nuna ba kya cin abinci” murmushi kawai tayi dan kam rabunta da abinci tun dare shekaranjiya lemo kawai take sha. Bayan tafiyar Aunty Husna ta yi wa ƙofar key ta zauna gefen gado tana tunani ko ta so zuciyarta ta karɓi shawaran Aunty Husna idan ta tuna marin da ya mata gaba ɗaya sai ta ji sam ba za ta iya ba shi haƙuri ba.

Fulani

<< Kuskuren Waye? 32Kuskuren Waye? 34 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×