A firgici ya matsu wajan yana tambayar abin da ya faru Halima ta kasa magana sai ihu take tana riƙi da cikinta "Zhara mene ne wai ina tambaya kun mini shiru!" Yayi maganar yana mai kafeta da idanu, kawar da kanta tayi daga kansa tana kallon ɗaya ɓarin "ni ma dai ban sani ba ka tambaye ta ka ji gatanan a gaban ka."
"Ina zamana ina kallo kawai ta zo ta sani gaba da duka a ciki saboda kawai ta tambayeni abinci na ce yana kichin ban jin daɗi shi yasa ba zan iya ɗaukowa zuwa falo ba. . .
Allah ya Kara basira
MashaAllah