Skip to content
Part 36 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

A firgici ya matsu wajan yana tambayar abin da ya faru Halima ta kasa magana sai ihu take tana riƙi da cikinta “Zhara mene ne wai ina tambaya kun mini shiru!” Yayi maganar yana mai kafeta da idanu, kawar da kanta tayi daga kansa tana kallon ɗaya ɓarin “ni ma dai ban sani ba ka tambaye ta ka ji gatanan a gaban ka.”

“Ina zamana ina kallo kawai ta zo ta sani gaba da duka a ciki saboda kawai ta tambayeni abinci na ce yana kichin ban jin daɗi shi yasa ba zan iya ɗaukowa zuwa falo ba.”

“Lallai ma Halimar nan wallahi ke abokin ƙaryarki ma ba ya a raye” Halima ta yunƙura za ta tashi ta kasa ta koma ta zauna tana faɗin “cikina ji nake kamar zai fashe, kana gani fa a kaina ka sameta” ta ƙarasa maganar da ƙyar tana mayar da numfashi.

“Zhara meyasa za ki daketa? Me ya haɗa ku?” Kallon mamaki take yi masa tsabar gaskiyar tayi mata yawa har ma ta rasa me za ta ce masa. “Wato dai ina yabon ki sallah za ki kasa alwala ko, ke da nake yi maki kallon marar son fitina shi ne yanzu za ki sauya ki fara fitina, ko tausayinta ba kya ji saboda abinda yake cikinta!” Komai ba ta ce da shi ba ta juya zuwa ɗakinta “magana fa nake maki shi ne za ki tafi ki barni!!”

“Uhm! To ni me kake so na ce da kai?”
“Ki zo ki bata haƙuri, sannan daga wannan ranar kar na ji ko na sake ganin kin kai hannu jikinta da sunan duka” tana tafiya ta ce. “Ba zan bata haƙuri ba dan banga me nayi mata ba da har zan neme yafiyarta a kai” ganin za ta shiga ɗaki ya janyo ta da ƙarfi ya kai hannu zai mareta sai kuma ya janye yana ƙwafa, murmushin takaici tayi “me yasa ka fasa oya ga fuskar maza ka mare ni” Halima tana kuka tana yi mata gwalo a fakaice, “ki bata haƙuri na ce!” Shiru tayi tana nazari ‘bai kamata na tsaya ina sa’insa da shi a gabanta ba domin tayi hakan ne dan ta haddasa fitina a tsakaina da shi, bai kamata na bata damar yin nasara a kaina ba’ tunda zuciyarta ta bata magana bata wani yi jinkiri ba ta je ta riƙo hannun Halima tana faɗin “kiyi haƙuri kin san zuciya bata da ƙashi sannan duk ɗan halak kunnuwansa ba za su iya jurar jin ana zagin iyayensa yayi shiru ba tare da ɗaukar mataki ba, amma in sha Allah ba zan sake ba” tana faɗar hakan ta kaɗa kai ta wuce ta gaban shi da ya daskare a wajan.

“Wai da gaske zaginta kika yi?” Turo baki tayi tana faɗin “ai to dai ba Dady ne na zaga ba kuma ko Abban nata ba wai zagin shi nayi ba kawai ‘yar magana ce na faɗa wanda kowa ya ji ya san gaskiya na faɗa” kunnenta ya riƙi yana murɗawa “ki godewa Allah ki godewa abinda yake cikin ki wallahi da sai kin ji a jikin ki! Za ki raba ɗayan biyu ne a tsakanin shi Abban da Dady? Ko suna da banbanci ne a wajena har kike wani faɗin wai ai ba Dady ba ne yeyeyen iyee!!” Cikinta ya ɗuri ruwa ganin yadda ya ke magana cikin fushi ‘kar fa reshe ya juye da mujiya’ tayi maganar a zuciyarta idanunta a kan shi tana ƙoƙarin janye hannunta daga kan kunnenta dan har cikin ranta take jin zafin riƙon “kayi haƙuri don Allah ni wallahi ba zaginta nayi ba ita ce ta neme ni da rigima” tsaki ya yi ba tare da ya ce da ita komai ba ya wuce zuwa ɗakin Zhara.

“Uhm! Wai komai nayi sai ya dinga ƙoƙarin juyewa ya dawo kaina, Humm ba komai a dai juri zuwa rafi da sannu tulun zai fashe.!”

Zaune ya sameta a gefen gado tana dannar waya zama yayi gefenta cikin sanyin murya ya ce. “Me yasa ina tambayar ki ba za ki ba ni amsa ba sai dai ki ce wai na tambayeta” ajiye wayar tayi a gefenta ta juyo suna fuskantar juna “to ai kai ne Yaya dole na faɗi hakan magana kake cikin fushi ban tunanin ko na faɗama za ka yarda dani” hannunta ya riƙo yasa cikin na shi yana murzawa ahankali “a kan me zan ki yarda dake bayan ban taɓa kama ki da faɗar magana ɗaya ta rashin gaskiya, kawai dai raina ya ɓaci ne saboda yadda na same ki hannunki a jikinta”

“Kayi haƙuri ba zan sake kuskuren yin hakan ba, amma kayi mata magana ta daina taɓa iyayena akan komai zan jure amma banda taɓa mini martabar su, Dady fa ta zaga hakan yasa na kasa iya riƙi fushina na mareta bayan nan kuma babu a binda nayi mata kawai ƙarin maganarta ne” rungumeta yayi jikin shi “kiyi haƙuri ban san hakan abin ya ke ba shi yasa, zan mata magana ba za ta sake ba, amma wannan rigimar ba na sonta kin kuma sani.”

“Zan kiyaye In sha Allah” janyeta yayi jikin shi yana miƙewa tsaye “yunwa fa nake ji” tayi maganar fuska a marairace. “Yunwa kuma, to ina abincin da a ka girka ko ba kya ra’ayinsa ne.”

“A’a na duba babu ga shi ka ce idan ba girkin mutum ba ne ba shi ba shiga kichin, kuma ba tun yau ba in dai ba ni ke girki ba to banda abinci a gidan nan.”

“Zo mu tafi wajan Halimar na ji dalili” tashi tsaye tayi gabansa ta tsaya tare da riƙo hannunsa “ni fa ba na faɗama ne dan ranka ya ɓaci ba ko dan kayi mata faɗa, kawai na faɗa ma ne dan kayi mini izinin shiga kichin na dinga girkawa kaina” komai bai ce da ita ba ya bi ta gefenta ya wuce ta biyu bayan shi da sauri.

Ba kowa a falon Halima ya ce ta zauna ya kira Halima, jim kaɗan suka fito tare ta zauna a inda Hafiz ya zauna tana tunzuro baki “ke Halima meye dalilin da yasa ba kya ba Zhara abinci duk ranar girkin ki?” Har za ta musa kuma ta ga ai ba tsoranta take ba hakan yasa ta ce. “saboda ba baiwarta nake ba da zan dinga girkawa ina bata tana ci ta zuba a masai!” Nuna ta yayi da ɗan yatsa yana faɗin “na gama fahimtar ki sam ba kya so a zauna lafiya, to bari ki ji wallahi Allah kin ji na rantse idan har na sake ji ko gani kinyi girki ba ki bata ba za ki sha mamakin matakin da zan ɗauka, in banda rashin tunani ita da take girkawa ki buɗe ciki kina zuba wa bata ce komai ba sai ke da ba ki da ta ido!”

“Dama na sani kirana kayi dan ka ci mutuncina a gabanta tunda ita ɗin jinin ka ce sai ka nuna mini wariyar launin fata, ba komai akwai Allah ai!”

“Komai za ki faɗa ki faɗa girki dai ne ba zan taɓa raba shi ba, kuma duk ɗayan ku ya girka bai ba ɗaya ba wallahi zan ma ku hukumcin da har ku mutu ba za ku manta ba!” Haushi ya ƙumeta hakan yasa bata ce komai ba ta bar masu falon tayi shigewarta uwar ɗaki. “Ban san ranka zai ɓaci har hakan ba da ba zan faɗama ba, kayi haƙuri.”

“Rashin faɗa mini tamkar cutar da ni ne da kuma jefani a halaka tunda amanar ki na ɗauko idan har kika yi yunwa a gidana Allah ba zai barni ba, dan haka kar ma ki fara tunanin za ki ɓoye mini irin hakan idan ta faru” kanta kawai ta gyaɗa ta bar ɗakin bayan ya bata izinin hakan.

Kwance take a jikin shi yana wasa da kitson kanta “albishirin ki?” Ɗago da kanta tayi tana kallon shi ta ce. “fari ƙal ta samu ne?”

“Uhm to a bani goron nawa mana” tashi ta yi ta zauna a kan kujerar ta harɗe ƙafafuwan su tana faɗin “kai dai faɗi albishirin na ka goron da zan ba ka ba mamaki ko ma na ce na tabbatar da sai ya fi albishirin naka girma” ɗago haɓarta ya yi yana girgiza kai “uhm-um fa yarinyar nan kar fa ki mini wayo.”

“Ba fa zan ma wayo ba kai dai faɗi kawai ina sauraron ka” tayi maganar tana jan karan hancinsa. “Shi kenan na yarda, amma fa idan goron bai wani yi mini armashi ba za ki sani ne” gyaɗa kanta tayi alamar ta yarda dan ta ƙagu ta ji menene. “An sa ranar auren Yayan ki Anwar da Nabila”

“Kai AlhamdulilLah na ji daɗi sosai wallahi, ita ɗin ‘yar wani gari ce?”

“‘yar’uwarsa ce da take zaune a wajan Maman shi tun yarinta saboda ta taso da maraici tun tana yarinya iyayenta suka rasu, a gidansu ta girma in har ba mutum ya sani ba ba zai taɓa gane ba Mama ce ta haife ta ba”

“Ko ita ce kake bani labarin ta so ka kamar me?”

“Eh ita ɗin ce kuwa ba ki manta ba ashe” murmushi tayi tana faɗin “ina kuwa zan manta ko lokacin da muka je gidan gaida Mama ina ta jin haushin yadda take kalle mini kai babu ko ƙibta idanu, shi yasa idan na ji za ka tafi gidan sai na ji kamar na hana ka tafiya” dariya ya yi “kai mata kishin ku yayi yawa, ni sam ai ba ta gabana, Anwar fa ya jima yana sonta tun tana yarinya kawai dai ya ɓoye ne saboda ganin in da hankalinta ya karkata, ko yanzu ni ne na ga ji da ɓoyon na faɗawa Mama cikin sa’a ana tambayar yarinyar ta amince”

“Gaskiya na ji masa daɗi Ubangiji Allah ya sanya alkhairi yasa matarsa ce mutu ka raba.”

“Amin summa Amin. Oya ba ni goron.” murmushi tayi tana riƙo hannunshi ta ɗora a cikinta ta kai bakinta a kunnen shi “Sweet Baby zai zama Dadyn Baby” tana faɗa ta sunne kanta a ƙirjin shi. “Wai don Allah da gaske kike ko wasa dai ki ke”

“Allah da gaske nake, wata biyu banga al’adata ba hakan yasa na sai abin awo da zan tafi makaranta ina dawowa na yi awon ya nuna mun a kwai” rungumeta ya yi tsam a jikin shi “AlhamdulilLah! Allah na gode ma a shekara ɗaya zan zama baban ‘yan biyu ko huɗu ko ma takwas waƙila dukan ku bibiyu za ku ba ni, kai gaskiya ni ɗin jarumi ne” duka ƙirjin shi ta yi “kai ko haba ‘yan biyu ana zaune ƙalau.”

“Eh ni dai ina so Allah ba ni dan darajar Ya RasululLah (S.A.W) gaskiya ya kamata a jinjina mini na zama zakin maza” sake ɓoye kanta tayi tana dariya.

Tunda Halima ta ji Zhara na da ciki tabi ta tashi hankalinta tunanin mafita take, ita ba ƙawaye take da su a gari ba bare har ta nemi shawarar su, ba kuma za ta tunkari.

ƙawayensu na gida ba tunda duk tare suke da Zhara. Tana zaune ta miƙe ƙafafunta tana cin ɗan suɓul da tayi da garin rogo wayarta ta yi ƙara miƙa hannu tayi ta ɗauki wayar ganin sunan Momy a jiki yasa gabanta faɗuwa ɗaga kiran tayi cikin tsoro “Hello”

“Munufuka na ji an ce kinyi ciki shi ne yasa na kira ki dan na ba ki saƙo wajan uwarki ki faɗa mata na ce ta daina murnar karanta ya kama zaki, na tabbatar ma ku da duk abin da za ki haifa ba zai taɓa albarka ba domin ba na sonki ba na son auren ki da ɗana ku ne kuka yi abin da kuka yi har ku ka juyar da hankalin uba da ɗan shi a ka yi auren ki da shi saboda ku mallaki duniyar uba da ɗa, to matuƙar ina raye ba za ku taɓa yin nasara ba wallahi sai na karya alƙadarin ki da ga ke har uwar taki ko da tana tsafi da baƙar jaɓa!” Ƙit ta tsinki kiran zuba wa wayar idanu tayi hawaye masu zafi suna saukowa daga idanunta zuwa kumatu, Hafiz ya shigo ɗakin da sallama a bakin shi turus ya yi a bakin ƙofa yana kallonta sam ba ta ji shigowar sa ba har ya ƙarasu wajanta a jiye ledar da ya shigo da ita ya yi a ƙasa ya durƙusa gabanta yana ɗago haɓarta “lafiya” faɗawa tayi jikinsa tana ci gaba da kuka “kin tayar mini da hankali ki faɗa mini me ya same ki.”

“Kaina ne yake ciwo” ɗagota ya yi daga jikin shi yana ƙoƙarin sanya idanunsa a cikin nata “ciwon kai Sweet Baby? Har ciwon ciki kinyi a gidan nan banga kin yi kuka ba sai wannan, anya ba wani abun kike ɓoye mini ba? Ko dai Halima ce tayi maki wani abun?” Gyaɗa kanta tayi alamar a’a “shi kenan Allah ya sawwaƙi, bari na ɗauko maki magani”

“Na sha maganin” komai bai ce da ita ba sai gyara zaman sa da ya yi ta kwanta a jikin shi zuciyarta nayi ma ta zafi ‘wai ba za ta taɓa haifar ɗa mai albarka ba, sannan me zai sa daga ni har Mama zuwa neman magani ko son dukiyar su me muka nema muka rasa a duniyar nan daidai rufin asirin bawa’

Maganar sa ce ta dawo da ita da ga zancen zucin da take “ba na hana ki shan yaji har hakan ba, gaba ɗaya abinci ya sauya kala saboda masifar yaji”

“Kayi haƙuri na daina Allah, wannan ɗin ma dan ba zai ciwo idan babu yajin ba ne shi yasa”

“Ki dai dinga kiyayewa ko dan lafiyar ki” kanta kawai ta gyaɗa masa da har zuwa lokacin maganganun Momy dawo mata suke a cikin ƙwaƙwalwarta kamar a yanzu ne take faɗa mata su.

Da dare suna kwance a kan gado ruwan sama ake tamkar da bakin ƙwarya yanayin yana yi mata daɗi ta ƙara shigewa jikin shi “tafiya fa ta tasu mini zan tafi India zan yi wani course na wata uku” da sauri ta tashi tana faɗin “kai har wata uku, amma dai tare za mu tafi ko?” Zama ya yi ya rungumeta ta baya ya harɗe hannayen su tare da ɗora kanshi a kafaɗarta “zan so hakan sai dai ba zai yu ba, saboda idan na tafi da ke Halima fa? Hakan zai iya zuwa da matsala, da itama kuma Halima cikinta ya shiga wata takwas wata mai fita ne watan haihuwarta” hawaye suka ciko idanunta cikin ƙoƙarin mayar da kukan ta ce. “Hakan ne Allah ya kai ka lafiya ya dawo mana da kai lafiya, zan yi matuƙar kewar ka”

“Ni ma zan yi kewar ki koma na ce har ma na fara, da damar tafiya da ke tabbas ba zan barki ba sai dai babu damar yin hakan”

Juyowa tayi gaban shi ta zauna a kan shi tare da rungomo shi ta wuyan shi tayi shiru “ba dai kuka ba?” Girgiza masa kai tayi alamar a’a “kar fa kisa damuwa a ranki koyaushe kina a tare da ni ki sa hakan a ranki, duk wani abu da nake duk wani motsina da bugun numfashina kina a maƙali a ruhina” murmushin jin daɗi tayi “na ji daɗi sosai nima ina jin hakan a ko wani lokaci”

Kashe masu fitila yayi suka kwanta zuciyarta na saƙa mata wani abun murmushin gefen baki tayi tana jin gamsuwa da tunanin da zuciyarta ta saƙa mata.

Fulani

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 0 / 5. Rating: 0

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Waye? 35Kuskuren Waye? 37 >>

2 thoughts on “Kuskuren Waye 36”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×