Skip to content
Part 37 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Tsaye take a kichen tana wanke kajin da za tayi masa dambun nama kamar a mafarki ta jiyo muryar Kande mai aikin Momy da sauri ta fito falo “wai mafarki nake ne Aunty Kandala ce a gidan nan?” Tayi maganar tana murza idanu “hahaha to ko dai na mintsine ki ne dan ki tabbatar” rungumeta tayi tana dariya. Zama suka yi a kan kujera bayan sun gaisa ta kawo mata ruwa da abinci “wai har da abinci ni da ba daɗewa zan yi ba” zama tayi gefenta tana faɗin “ai kuwa sai kin ci, ni da fushi ma nake da ke ko sau ɗaya ba ki taɓa zuwa ba tunda na zo gidan nan.”

“Kiyi haƙuri wallahi ina so na zo sai dai kin san halin Momyn ta ku, yanzun ma cefane zan je nayi sa’a direba baya nan ta ce na shiga napep shi ne fa na ce bari na biyu a gaisa” murmushi Zhara tayi tana faɗin “Momy kenan, haka ta hana Khadija zuwa sai sau ɗaya ta zo da ta tambaya a gaban Dady. Allah dai ya kyauta.”

“Amin Ya Allah, sai haƙuri watarana komai zai wuce idan anyi hakuri. Ina Halima?”
“Ta je duba Babanta da bai da lafiya, da tare za mu tafi kuma wani uzurin yasa ban samu na bita ba.”

“Ayya Allah ya ba shi lafiya. Ashe Yallaɓai tafiya ta tashi” tayi maganar tana cin abinci “wallahi kuwa sati na samu sai tafiya In sha Allah” sun jima suna fira kafin ta mata sallama ta bata kuɗi da ƙyar ta karɓa sai bayan tafiyarta ta shiga kichin ta ci gaba da aikinta. Bayan ta kammala tayi wanka sallah la’asar tayi ta zauna tasa wayarta a gaba tana tunanin ta ina za ta fara ajiyar zuciya tayi kafin daga bisani ta danna kiran ba tare da ta tantanci me za ta faɗa masa ba. “Mamana.”

“Na’am Dady, ina wuni?”

“Lafiya lau, fatan kuna lafiya”

“Lafiya lau muki sai kewan ka da muke tayi wannan karon ka jima ba ka dawo ba”
“Kuyi haƙuri kuna raina yanayin aikin ne ya riƙi ni.”

“Ba komai Allah ya dawo da ku lafiya, Khadija ma ta faɗa mini tare za su zo da Yaya saboda matsalar idanunta.”

“Eh ta ce da ni idanun kwana biyu suna damunta, shi yasa na ce ta biyu Hafiz ɗin sai suga likita, ni ma sati mai zuwa zan bar Pakistan sai mu haɗe da su a India ba mamaki ma mu dawo tare da Khadija ɗin. Ko za ki rako su ne?” Ji tayi kamar tayi tsalle dan murna cikin dakiya ta ce. “Da na ce zan biyo su ɗin, to amma Halima kar a barta ita kaɗai” murmushi yayi kafin daga bisani ya ce. “Ki shirya ku zo tare zan yi wa Hafiz magana sai a kawo mata wata daga cikin ‘yan’uwa ta taya ta zama, ko ta dawo wajan Momyn ta ku ta zauna tunda na ji an ce ta kusa haihuwa” farin ciki kamar za ta rungume shi ta wayar “na gode Dady Allah ya ƙara lafiya.”

“Amin Ya Allah, zan turo ma ki kuɗi ta account ɗinki sai ki yi shiri” godiya ta shiga yi masa suka rabu zuciyarta fal da farin ciki. Dare ya yi tana sauraren ya yi mata maganar tafiya shiru bai ce da ita komai ba, ta kuma sani sarai Dady yayi masa maganar kawai maganar ne ba zai mata ba, zuba masa idanu tayi tana ci gaba da shirin tafiyarta a ɓoye.

A na saura kwana uku tafiya yana shirin tafiya office tana sanya masa maɓallin riga ya ce. “Kin kai ni ƙara wajan Baban ki ko?” Fito da idanu tayi tana faɗin “ƙara kuma ni ɗin kuma?”
“Daina yi kamar ba ki sani ba a kan tafiyar mu ce” murmushi tayi tana ƙarasa saka masa maɓallin ta ce. “Ni ba ƙara na kai ka ba, kawai dai ya tambaye ni ko ina so na biyu ku ne, ni kuma na ce masa eh sai dai kar abar Halima ita kaɗai..” ta faɗa masa yadda suka yi ta ƙara da cewa “ka ga ai ba ƙara ce na kai ba ko?”

“Ai fa ya na iya ko ƙarar ne ko ba ƙarar ba ne ai kun gama shirya komai dole kuma na bi, zama ya yi gefen gado tare da zaunar da ita a kan cinyoyinsa yana faɗin “zan fi kowa farin ciki idan har na tafi da ke, banƙi mu kasance a tare a ko wani lokaci ba har bayan ba numfashi na Zharana, sai dai ina tunanin rigimar Halima ba lallai ne ta iya fahimta ta ba” lumshi idanunta tayi kafin daga bisani ta buɗe su tana kallon sa “na fahimci ka tun a ranar, kayi haƙuri Allah ba ni ce na ce da Dady zan bi ka ba, amma bari zan kira shi na san me zan faɗa masa sai a janye maganar tafiyar tawa” jan karan hancinta ya yi “kar ma ki fara ki janyo mini faɗan Dady, za mu tafi ɗin kawai Allah ya kaɗe duk wata fitina.”

“Allah ba zai yi faɗa ba nasan me zan faɗa masa.”

“A’a kar ki ce masa komai, ki dai shirya kawai komai na riga da na kammala komai na fitar ki ƙasar waje.” Ba ta wani ja ba dan dama ba ta shirya fasa tafiyar ba.

Saura kwana biyu tafiyar su girkin Halima ne suna kwance a kan gado da dare yana wasa da yatsun hannunta ya ma rasa ta ina zai suma yi mata maganar tafiyar shi da Zhara “ka ce kana so ka faɗa mini wata maganar kuma ka yi shiru.”

“Uhm! Ba shiru nayi ba kawai dai ina tunanin yadda za ki karɓi maganar ne”
“Kasa jikina ya yi sanyi ko wani abun ne ya samu Baba?” Tashi ya yi ya zauna itama ta tashi ta zauna a gaban shi suna fuskantar juna “don Allah mene?”

“Ba abinda ya samu Baba, wata alfarma ce dai nake nema a wajan ki”

“Alfarmar ce har sai ka ta wani yin ɗar-ɗar? Wace irin alfarma ce da ba zan iya yi ma ita ba a duniyar nan. Ka faɗa mini ko meye zan ma” hannunta ya riƙo yasa cikin na shi “don Allah ina so ki fahimci ni ki kuma yarda da ni ba na yi hakan ba ne dan na baƙanta ma ki rai, ina so ne dama na faɗa ma ki tare da Zhara za mu yi wannan tafiyar” kallon shi take babu ƙyabtawa “hum him dama na ji a raina hakan ce za ta faru tun sanda ka fara maganar tafiyar, tabbas na sani raina mini hankali kayi da na ce zan bi ka ka ce a’a ko ɗayan mu ba za ka da shi ba.”

“Ki fahimci ni har ga Allah babu niyar tafiya da ita kaw… “Kawai me? Ni ba ka da abin da za ka faɗa mini gaskiyar Mama kowa ya sai rariya dole ya san za ta yi masa zuba. Ni ce na fara neman ka na fara kawo kaina a wajan ka, sannan na aure zuciyar da ba ni take so ba wata daban take so, sannan ita ɗin dangin ka ce dole ka nuna mini fifiko a kan komai na ta!” Murza hannunta ya shiga yi ta fizge ajiyar zuciya ya yi kafin daga bisani ya ce. “Kar ki yi mini gurguwar fahimta, kar kuma ɓacin rai yasa zuciyar ki yi ma ki saki-saƙin abin da ba hakan ba. Da ba na sonki kina tunanin zan yarda na zaɓe ki a matsayin abokinyar rayuwata uwar ‘ya’yana. Dan Zhara tana ‘yar’uwata hakan ba ya na nufin zan fifita ta a kan ki ba, dukan ku abu ɗaya ne a wajena auren ku nake babu wani banbanci. Kema da a ce cikin ki bai tsufa ba sai na tafi da ku gaba ɗaya dan dai a zauna lafiya, amma cikin ki ya ts…

“Ka ga Hafiz don Allah ka fitar mini a ɗaki ban bukatar jin wani suki burutsun ka, da yake a can ɗin babu masu haihuwa ko jirgin ne ba ya ɗaukar mai ciki oho! kawai ka fitar mun a ɗaki!!” Duk yadda ya so ya lallashi ta hakan ya ci tura dole ya bar mata ɗaki ya tafi nasa ɗakin zuciyarsa a ƙuntaci.

Da safe ko buɗe ɗakinta ba ta yi ba bare har ta haɗa masu karin kumallo sai Zhara yasa ta haɗa masa karin kumallon bayan ya kimtsa ya fita zuwa wajan ɗauren auren wani abokin sa. Fitowa ta yi wajan wanka tana goge jikinta da ƙaramin tawol Halima ta shigo ɗakin “Halima an tashi lafiya?”

“Da ban tashi lafiya ba za ki ganni ne!”

“Oh to Allah ya huci zuciyar ki uwar gida sarautar mata” tsaki Halima tayi tana faɗin “na ji an ce wai da ke za a tafi, ba dai tafiya ba bismillah wallahi na tabbatar ma ki da sai kin yi da-na-sanin tafiyar nan, ba za ki taɓa samun farin ciki ba har ku je ku dawo ki rubuta wannan ki a jiye a allon zuciyar ki!!” Dariya Zhara tayi “me kika isa ki mun? Wallahi babu abinda kika isa ki yi mini sai abinda Allah ya nufa. Dan haka na riƙi Allah na kuma tabbatar da zai tsare ni da dukan sharrin masharranta.”

Ta dafa kafaɗarta ta na ci gaba da magana “kin san dama hausawa na faɗin ramau tafi farau daɗi, kina tunanin fashin da kika yi mini a ranar girkina na ƙaryar ciwon mijina ya kwana a ɗakin ki kin ci bilis. Humm dama na ƙudirta a raina sai na rama lokacin ramuwar ne kuma ya zo fashin kwana ɗaya kika yi ni kuma zan kasance da shi tsawon wata uku idan na so ma fin hakan. Dan haka tafiya ba fashi da yardar Allah sai dai ki haɗiye zuciya ki mutu.”

“Oh hakan ne ashe? Hum kin ba ni dariya wallahi, yaro man kaza bai san wuta ba har sai ya faɗa. Mu zuba mu gani tsakanin ni da ke!” Ba ta jira jin me Zhara za ta faɗa ba ta fice, tsaki tayi tana faɗin “na gane idan har ina yi maki shiru ba ƙaramin raini ne zai shiga tsakanina da ke ba.!” Mayafi kawai tasa ta ɗauki key ɗin mota a guji ta bar gidan “wannan fita Allah dai yasa ta lafiya ce ya kuma tsare hanya wannan gudu kamar za ta tashi sama” mai gadi ya yi maganar yana rufe gyet.

Zaune take gaban Momy tana kuka “wai shi Hafiz ɗin ne ya faɗa ma ki tare za su tafi da Zhara, anya kuwa kunnenki ya jiye maki daidai?”

“Wallahi hakan ya faɗa mini kuma ita ma ta tabbatar mini da hakan. Ni fa cewa ya yi ba za ya da kowa ba kawai sai ga shi ya ce zai je da ita, ni wallahi ina zargin ko wani abun suka yi masa saboda yadda yake maganar sam ba ya a hayacin shi, sannan da kunnena na ji tana waya da gida tana faɗin ai aikin ya yi kyau sosai, iya dai abin da na ji ta faɗa kenan tana ganina ta kashe kiran. Sannan ta je gida kwananta ɗaya a can”
Cikin huci ta ce. “Ya yi kyau zai zo ne ya sameni ne, ji ki sama ki ɗauko mini wayata!” Da sauri ta je ta ɗauko ma ta bayan ta kawo ma ta “Momy kar fa ki faɗa masa na zo nan ko kuma ni na faɗa ma ki.”

“Ke dai Allah dai ya yi ma ki albarka da kika zo ki ka faɗa mini da ba zan sani ba har su tafi. Ba zan faɗa masa ba” sallama ta yi wa Momy ta bar ta tana ta faɗa a bakin ƙofar shigowa suka haɗe da Khadija da take dawowa daga unguwa “tauraruwa mai wutsiya ganinki ba alkhairi ba.”

“Fito da idanu ta yi cikin takaici “Khadija ni kike faɗawa magana?”
“Faɗar magana ko faɗar gaskiya, na tabbatar da wani abun ne ya kawo ki dan tun da a ka yi auren Aunty Zhara da Yaya Hafiz ba ki sake zuwa gidan nan da alkhairi ba sai dai idan wani munafuncin ne ya kawo ki” numfashi ta ja ta furzar ji take kamar ta kamata da duka sai dai ta haɗiye ɓacin ran gudun kar ta ɓata rawarta da tsalle “Humm ya yi na kuma gode” ta bi ta gefenta ta fita. Ƙarasa shiga falon tayi ta samu Momy na waya “komai kake ka zo ina jiran ka yanzu nan” tana gama faɗa ta tsinki kiran zama tayi kusa da ita tana faɗin “ya naga ranki a ɓaci?”

“Ni da Yayan ki mana wai ashe da Zhara yake shirin tafiyar nan ni ban sani ba”
“To mene ne a ciki Momy in banda ɗorawa kai damuwa matarsa ce fa…..”

“Ai dama na san kin sani faɗa ne dai ba ki yi ba, ita kuma ɗaya matar tasa me yasa ba za shi da ita ba?”

“Wallahi dama tunda na ganta sai da jikina ya ba ni wata fitinar ce ta zo ta saƙa. Ita ɗin fa ciki ne da ita haihuwa yau ko gobe, idan har tayi haƙuri idan zai wata tafiyar ba sai ya yi da ita ba mene ne a ciki”

“Ba za ki taɓa fahimtar abin da nake hange ba, dan haka in har ba za ki tayani yaƙi ba kar na sake jin kin sa mini baki a maganata” ɗaukar jakarta ta yi ta haura sama tana mamakin yadda Momy ta zama tamkar hawainiya a da bata son Halima amma yanzu saboda a taru a ƙuntatawa Zhara shi ne take nunawa Halima so da goyon bayanta a kan komai. “Humm ai shi kenan a dai yi mu gani idan har tusa za ta hura wuta.” Ta ƙarasa maganar tana ƙarasa wa ɗakinta.

Sai dare ya samu ya je gidan Momy a ɗakinta ya sameta ta idar da sallah isha zama ya yi gaban ta yana gaishe ta ba ta ko amsa masa ba ta hau faɗa “wato saboda ka nuna mini ban isa da kai ba tun ɗazun na kira na ce da kai ina neman ka sai yanzu ka ga damar zuwa ko ma na ce ta ga damar ta bar ka ka zo!”

“Ba hakan ba ne wallahi ni rabona da gida tun safe da na fito ban koma gida ba, sanda kika kira ni a lokacin zan shiga ɗakin tiyata, aiki bai barni ba sai yanzu, kuma na ta kiran wayar ki na yi ma ki bayani ba ki ɗaga ba. Ki yi haƙuri don Allah Momy” tsaki ta yi tana harararshi “idan har ban yi haƙuri ba zan dake ka ne. Wai Hafiz dan ka raina ni ka shirya tafiya da matar ka har jibi ne tafiyar amma ba za ka faɗa mini ba, sai dai na ji a wani wajan!” Riƙi kanshi yayi cikin damuwa ya ce. “Wallahi ina da niyar faɗa ma ki, dama na bari ne yau idan na zo sai na faɗa maki.”

“Ba gaskiya ba ne in har kana da niyar faɗa mini ai da ba za ka kai har yau ba ka faɗa ba, su iyayenta da suka fi ni muhimmanci ba ka kaita ta yi sallama da su ba”
“Ba ni na kai ta ba direba ne ya kai ta. Amma ina mai ba ki haƙuri na yi kuskure ba za a sake ba.”

“Ka ma sake ɗin idan har ka samu damar yin hakan. Ka ji ni da kyau in dai wannan tafiyar ce in har ka ga ka yi ta da Zhara ka tabbatar da babu numfashi a tare da ni, idan kun dawo daga kai ni maƙabarta sai ka ɗauki matar ka ku tafi” cikin tashin hankali ya ce. “SubhanalilLah! Momy me ya yi zafi don All… “Wuta ne ba zafi ba dan uban ka! Wallahi wallahi ba za ka tafi da Zhara ba idan har ka tafi da ita yau sai na yafewa Zhara da uwarta kai!!” Idanunsa suka yi jawor ya kasa cewa uffan.

Fulani.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Waye 36Kuskuren Waye? 38 >>

1 thought on “Kuskuren Waye? 37”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×