Zuciyarta ta dinga bugawa fat! Fat!! Fat!!! "Daina kallona da idanun na ki masu kama da na mayu!" Kawar da idanunta ta yi tana murmushi "sannu da zuwa Momy ina kwana" "Da ban kwana ba za ki ganni ne" tayi maganar tana ƙarasuwa ciki ta tsaya tsakiyar ɗakin tana faɗin "ina wayar ki?"
"Na sa ta caji"
"Ɗauko mini" jiki a sanyaye ta je ta ciro wayar caji mika ma ta tayi fizga tayi tana faɗin "daga yanzu na ji ko na zo naga ƙafarki ta fita daga gidan nan tabbas a bakin auren ki ko da kuwa. . .