Skip to content
Part 39 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Zuciyarta ta dinga bugawa fat! Fat!! Fat!!! “Daina kallona da idanun na ki masu kama da na mayu!” Kawar da idanunta ta yi tana murmushi “sannu da zuwa Momy ina kwana”
“Da ban kwana ba za ki ganni ne” tayi maganar tana ƙarasuwa ciki ta tsaya tsakiyar ɗakin tana faɗin “ina wayar ki?”

“Na sa ta caji”

“Ɗauko mini” jiki a sanyaye ta je ta ciro wayar caji mika ma ta tayi fizga tayi tana faɗin “daga yanzu na ji ko na zo naga ƙafarki ta fita daga gidan nan tabbas a bakin auren ki ko da kuwa makarant ne kin dai jini da kyau ko?”

“Eh” juyawa Momy tayi za ta fita ta sake juyowa tana faɗin “tun da har kika nace kika aure ɗana duk da kin san ban son hakan tabbas sai na sa kin yi da-na-sanin aurensa da kika yi, sai nasa kin ji a ran ki zaman ƙabari ya fiye maki kwanciyar hankali a kan zama a gidan ɗana!” Ta je ta bubbuɗe wadurop ɗin ɗakin “bari na duba idan da wasu kuɗin dan na tabbatar da ba za ki bar shi ya tafi ba har sai kin wawashe kuɗaɗin shi.”

Duk ‘yan kuɗaɗin da Zhara take da su ta kwashe har ATM ba ta barta da shi ba ta fita ta bar ta a tsaye tamkar iccen da a ka dasa. A falo ta samu Halima ta na tsaye “yawwa Halima kina ji na ko ki sanya mini idanu sosai a kanta idan har ta fita ko wani ya zo gidan kin ji na faɗa maki ko?”

“Tabbas kuwa zan sanya maki idanu a kanta, idan har naga abin da ban yarda da shi ba zan yi gaggawar sanar dake.”

“Kin kyauta mini kuwa, ni zan tafi, duk rintsi kar ki bari Hafiz ya yi magana da ita ko yasan wani abun da ya shafe ta” gyaɗa kanta ta yi tana mai tabbatar mata da za ta kiyaye. Rakata tayi har wajan Mota har ta zauna a baya Halima za ta rufe ƙofa “kira mini mai-gadi”

“To Momy” ta kai duban ta wajan gyet yana zaune a kan binci yana sauraren rediyo “kai Malam Idi!”

“Na’am Hajiya!”

“Zo nan!!” Da sauri ya a jiye rediyo ya zo cikin rusunawa ya ce. “Barka da fitowa Hajiya Babba ai sam ban ga fitowar ki ba.”

“Sannu, kana ji na ko ka sanya idanu sosai a kan masu shigowa gidan nan, matuƙar ba wajan Halima a ka zo ba kar ka bari a shiga.”

“To amma ita kuma Hajiya ƙarama fa?”

“Tunda ba ƙwaƙwalwar kifaye ne da kai ba ai tunda ka ji na ce Halima ina nufin ita kaɗai ba da watan ba, dan haka ka kiyaye ko Anwar ban yarda ka bar shi ya shiga gidan nan ba idan har ka barshi shiga wallahi ka tabbatar da ka rasa aikin ka har abada!”

“SubhanalilLahi ina mai ya yi zafi ai ko waye ma ba zan bar shi ya shigo ba yadda ki ka faɗa hakan za a yi babu ja” rufe motar tayi tare da saukar da gilashin motar tana faɗin “da ka taimake kan ka, sannan ka tabbatar da Zhara ba ta fita gidan nan ba, idan har ka yi Kuskuren faɗawa Hafiz ko kuma kaucewa ɗaya daga cikin umurnina ba rasa aikin ka kaɗai ba har rayuwar ka za ka iya jefawa a cikin hatsari ka ji na faɗama” saurin rufe bakinsa ya yi yana faɗin “ina ai bakina ƙanen ƙafata zan kiyaye”

“Mu je dreba”

“To Hajiya” mai-gadi ya je da sauri ya buɗe masu gyet bayan sun ɓacewa ganinta ta shiga gida tana jijjiga jiki da waƙa “ahaye nanaye duniya sabuwa, zanci duniyata bisa tsinki wata kuwa sai dai a haɗe zuciya.”

Zaman ‘yan buri tayi ji take kamar ta fasa ihu “tabbas a yanzun ne na fahimci mene ne Mama take guji mini. Innalillahi wa Inna ilahi raji’un! Me nayi ma ki ne Momy ki ke so ki mini kisan mummuƙe!?” Riƙi kanta tayi da yake matuƙar yi mata ciwo kamar zai rabu biyu ‘ya ilahi wannan rayuwar da take so na yi ai rayuwar kurkuku ma tafi shi ‘yanci tunda za su yi yawo a cikin gidan yarin idan an so a yi wasa da dariya ga jama’a fallan a ciki, ni kuma fa shi kenan hakan zan rayu tamkar mayyya a cikin gidan nan?’ kifa kanta ta yi jikin gado hawaye masu zafi suna zarya a kan fuskarta. Gaba ɗaya wunin ta yi shi ne cikin wani irin yanayi marar daɗi, sai bayan ta yi sallah la’asar ta fito dan ta samawa kanta abinda za ta ci ba kowa a falon ta duba daneng babu komai a kai, hakan yasa ta tafi kichen da niyar dafa ko taliya ce dan yunwar gaske take ji “ke ke tsaya ina za ki je?” Halima ta yi mata tambayar tana fitowa ɗakinta

Tsayawa ta yi cak tana lumshi idanunta ‘Allah ka ba ni ikon fin ƙarfin zuciyata kar kalaman ta su tunzura ni nayi abin da zai janyo mana matsala’ juyowa tayi da murmushi a fuskarta “zan ɗora girki ne”

“A kan wani dalili kin manta dokar da a kasa ne?”

“Ban manta ba, amma laifin ki ne da ba ki girka ba kin ga kuwa ai ba zai yu na zauna da yunwa ba dole na nemawa kaina mafita. Idan kuma har kin girka sai na koma gefe ki zubo mini nawa”
“Humm in dan girki ne kam na yi amma fa iya cikina na girka dan haka sai ki bari zuwa gobe da kike da dama sai ki girkawa kanki”

“Halima don Allah ki ƙyaleni na yi sha’ani na ba na so ki kai ga zuciyata don Allah” murmushin gefen baki tayi tana faɗin “Allah ko uwata. To ai zuciyar taki ce nake so na kai gareta sai na ga idan har tsire ni za ki yi a tsinkin tsere tsabar fusata!” Ajiyar zuciya ta yi ta juya zuwa ɗaki ba tare da ta ce da ita komai ba “hahaha a wuni ɗaya har wata ta zabgi haka, Allah sarki abin tausayi ba dole ba an sa rai da za a tafi yawon shaƙatawa da miji sai kuma abu ya juye ba a yadda a ka yi tsammani ko a ka so ba” kallonta Zhara tayi ji take kamar ta ba ta amsa sai dai ta danni zuciyarta ta shiga ɗaki da sauri ta rufe ƙofar tana mayar da numfashi. Wajan firij ta nufa ta ɗauko lemon juice ta sha ta koma ta kwanta. Washegari ta fito dan ɗora girki sai dai ta tarar da ƙofar kichen ɗin a rufe ta tura ta tura taƙi buɗewa ɗakin Halima ta tafi ta samu tana ƙaramin falonta tana kallo “lafiya za ki shigo mini ɗaki?”

“Ita ce ta kawo hakan, ina key ɗin kichen?”
“Yana wajena”
“Ba ni zan yi girki” gyara zamanta ta yi tana faɗin “idan har zan ba ki to mene fa’idar na rufe ɗin?” Da mamaki ta ce. “To a kan wani dalili ne zai sa ki rufe mini madafi?”
“Saboda gyatumar mijin ki ce ta yi umurnin hakan, idan kuma har kina so ki san dalili sai ki je ki tambayeta ko kuma kisa waya ki kirata” hannu tasa ta riƙi goshi tana mai jan numfashi “ko a mafarki ban taɓa tunanin a kwai wani abu a duniyar nan da zai sauya amintar mu da ƙaunar da muke yi wa juna ta zama ƙiyayyya ba. Humm! Da yake bawa bai da sanin abin da zai faru a rayuwar shi tabbas da nasan irin wannan lokacin zai zo wallahi da ban yi kuskuren sanya ki gwada ƙarfin soyayyar da Yaya Hafiz yake yi mini ba, da yake wake ɗaya shi yake ɓata gari, an kuma riga da an baro kyau tun ran halitta. Amma ina matuƙar da-na-sanin yin wannan kuskuren”
“Wallahi har kin ba ni bazawarar dariya, ya a ka iya ai dole a ce da mijin iya Baba, tunda har Allah ya yi matarsa ce ni kin isa ki hana Allah ikonsa ne? Ina kuma mai bugun gaba da wannan Kuskuren da kike tunanin kinyi ya zaɓi ni ya barki wanda rashin iya jurar hakan ne yasa a ka bi boka da Malam har a ka zama matar shige, kuma sai na tabbatar da ba ki ci ribar hakan ba kin tattara inaki-ina ki kin bar gidan nan an koma zaman zawarci a gida domin Hafiz nawa ne kowa ya sheda hakan tunda ya iya barin ki a ranar ɗauren auren ki ya aure ni”

“Har yau kin kasa ganewa ko kuma kin gane kina basarwa ne, da ba dan ni ba da ba ki kasance anan ɗin ba, sannan wallahi idan na so ƙarar da auren ki da Hafiz ko kwana ɗaya ba za ki yi ba. Wannan lokacin damar ku ce daga ke har wacce take ɗaure ma ki gindi, amma ina so kisa wannan a ranki ki kuma dinga tunawa ita kanta wacce kike taƙama da ita tana da wanda yake gaba da ita wanda ko kara ya gitta ba ta isa ta tsallake ba ni kuma ni ce gwal ɗinsa abar tattalinsa, ba ke da kike matar ɗansa ba ko uwar gayyar na so ta bar gidan tsab za ta bari cikin ruwan sanyi” tana faɗa ta juya za ta fita Halima ta tasu ta biyu bayanta ta juyo da ita da ƙarfi tana faɗin “za ki maimaita wannan maganar a gaban ta idan har ke ɗin isassa ce!!” Murmushi ta yi kafin daga bisani ta ce. “mene ne amfaninki idan har sai na faɗa ai ke ɗin kin zama Manzo a tsakanin ni da ita, albashi ne kawai ya yi saura a fara biyan ki sai ki faɗi farashin ki” zuba mata idanu Halima ta yi har ta ma rasa me za ta ce janye hannunta ta yi tana faɗin “tunda ba ki da abin faɗa ni bari na tafi dan ina da abin yi, idan kin gama yanki shawara sai ki faɗi farashin na ki ina jira.” Har Zhara ta fita ta kasa ko da motsa ƙafarta.

Tun da ta shiga ɗaki ta zauna a kan gado tana tunanin abin yi “zama da yunwa shi ne hure mafi muni wanda kuma ba zan iya jura ba. Mene ne abin yi?” Tashi ta yi da sauri tana dudduba jikikunan ta cikin sa’a ta samu dubu biyar da sauri ta ɗauki Hijab ta je wajan da take a jiye key ɗin mota ta neme shi sama ko ƙasa ta rasa riƙi ƙugo ta yi “ko shakka ba na yi har shi Momy ta ɗauka” cikin sanyin jiki ta fito bayan ta rufe ƙofarta da key. Halima da take zaune a falo ta biyu bayanta ta tsaya daga bakin ƙofa tana liƙen su. Ta tarar da mai-gadi yana ban ruwa ga shuki-shukin da a ka ƙawata harabar gidan da shi. Sam ba ta kula da shi ba hakan yasa kanta tsaye ta nufi ƙaramar ƙofa dan fita kamar an ce ya juyo yaga bayanta da sauri ya ajiye botar ban ruwan ya biyu bayanta “au ashe ke ce barka da fitowa Hajiya” ya yi maganar a lokacin da ya sha gabanta.
“Yawwa barka Malam Idi ya aiki”

“Da godiya Hajiya”

“To sai dai zan iya karɓar kuɗin a kwai samarin unguwar nan su biyu da muke mutunci da su, idan har ɗayan su ya zo sai na ba shi ya sayo ma ki tunda ba zai yu na bar aikina ba” kuɗin ta ciro cikin jaka ta ba shi bayan ya karɓa ta ce. “Don Allah ƙaramar waya nake so a sayo mini amma kar ka ba ni a cikin gida zan zo na karɓa da kaina ko zuwa dare ne”

“Ba damuwa In sha Allah zan bayar a sayo maki, zan kuma yi yadda kika ce” godiya ta yi masa tare da juyawa zuwa ciki. Bin bayanta ya yi da kallo, Halima ta yi saurin komawa ciki ta zauna a in da ta barta, ko kallonta ba ta yi ba buɗe ɗakinta tayi ta shiga.

“Allah sarki abin tausayi in banda ina tsoron kar na rasa aikina da me zai sa na hanata fita, ko meye fa’idar yi mata wannan hukuncin oho” sam bai ji zuwanta ba sai ji ya yi an warci kuɗin kallonta ya yi a tsoraci “oh wato da a ka ce a hanata fita shi ne kuma sai ka zama yaron aikinta”

“Ki yi haƙuri wallahi ba aikina ta yi ba” to mene ne idan ba aikin naka ta yi ba su kuɗin da naga ta ba ka na meye!?” Tunaninsa ya ce da ita kuɗin sa ne sai dai jin da ya yi ta ce ta ga ni babu mafita dole ya faɗa mata gaskiya. “To idan ta zo ka faɗa ma ta kuɗin suna hannuna” har ta shiga gida bai iya cewa da ita komai ba. Tausayin Zhara ya cika masa zuciya “wannan shi ake kira da kisan mummuƙe, Allah kaɗai yasan me mutanen nan suka shirya wa baiwar Allah nan, Allah ka yi ma ta mafita.”

Halima na zaune a kan kafet ɗin babban falo tana cin ɗan wake Zhara da ta fito wajan mai-gadi ta shigo a fusace tana faɗin “a kan me za ki karɓe mini kuɗina”

“A kan na isa! Idan kuma kika ce ki yi mini rashin kunya wallahi yanzu sai na kira Momy dan aikinta nake” har ta buɗe ba ki za ta yi magana sai kuma ta fasa kawai ta shiga ɗaki tana jin tsakin da Halima take yi mata ba ta kulata ba sai key ɗin da ta yi wa ƙofarta.

Yadda taga rana hakan taga dare ga yunwa ga ciwon kai da yasa ta gaba, ji take jikinta ya yi sanyi ko motsin kirki ba ta iya yi da ƙyar ta iya yin sallah asuba. Tana jin babu wanda take so ta ji muryarsa irin Abbanta ta faɗa masa halin da take ciki sai dai babu damar yin hakan, a kan dardumar da ta yi sallah bacci ya yi awon gaba da ita. Halima cikin bacci ta ji kira ya shigo wayarta da lalube ta ɗauki wayar da take bayan fillo ba tare da ta duba sunan ba ta ɗaga jin muryar Mamanta yasa ta saurin buɗe idanunta “Mama lafiya kika kira da asubar nan?”

“Ina fa lafiya Halima, ina Zhara ne tun jiya da yamma a ke kiran wayarta ba ta shiga sannan an kira wayarki ma ba ki ɗaga ba” cikin jin haushin dalilin da zai sa Mama ta wani damu da kishiyarta ta ce. “Ni ban san me ya samu wayarta ba, kuma ni jiya muna gama waya da Hafiz ban sake mayar da hankali kanta ba. Wai me ya faru ne na ji muryar ki wani iri?”

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Waye? 38Kuskuren Waye? 40 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×