Hawaye ne su ka ciko a idanunta, ta lumshi idanunta tana tuna maganar yayanta kafin ya fita. Ta fito cikin shiri tana sanyi da dogowar riga ta les baƙi mai ratsin duwatsu, ta sa ƙaramin mayafi ta yafa a kafaɗarta, tana riƙi da jaka ta shiga ɗakin Mama ta samu Mama na kwance a kan gado, zama ta yi gefen gado tana faɗin “Mama ba dai jikin ba?”
Tashi Mama ta yi ta zuru ƙafafunta ƙasa ta ce, “Jiki kam Alhamdulillah ya yi sauƙi sai ɗan abinda ba a rasa ba, na dai kwanta ne numfashin nawa ne har yanzu bana jinsa daidai.” cikin damuwa ta ce; “Ubangiji Allah ya ƙara lafiya Mama”
“Amin ya Rabb, ina zuwa naga kin shirya?”
“Mama kin manta da safe na faɗa maki zan je gidan su Yaya Hafiz wajan Khadija?”
“Eh na manta sam, Allah ya tsare ki gaida momyn ta su.” ta miƙe tsaye tana faɗin “za ta ji Mama.” ta juya za ta fita su ka yi ido biyu da Yaya Anwar da ya ke a tsaye bakin ƙofa ya watsa mata wani kallo da sai da taji hanjin cikinta sun ya mutsa, ƙasa da idanunta ta yi ta ce; “ina wuni Yaya”
“Lafiya” ya amsa mata a gajirce, sumai-sumai ta yi tabi ta gefen shi za ta fita ya ce; “ki jirani a falo” rintsi idanunta ta yi a ranta tana faɗin ‘shi kenan sarkin takura yanzu sai ya hanani fitar nan’ zuwa ta yi ta zauna a falo, Fatima tana zaune a kan kafet tana kallon tv, bai jima ba ya fito zama ya yi a kan kujerar da take fuskantar ta ya kafeta da idanu fuskar shi babu annuri ya ce; “yanzu Nabila wunyan ki har ya yi kaurin da za ki dinga zuwa wajan saurayi?” Fito da idanunta ta yi cikin tsoro ta ce; “ni Yaya waye ya faɗama wajan saurayi zan tafi, wallahi ko waye ya faɗama sharri ya min” yana harararta ya ce; “sakaryar banza yanzu me na ji kina faɗawa Mama“? Shiru ta yi tare da yin ƙasa da kanta, “ba tambayar ki na ke ba“! Fatima ta ragi muryar tv ta mayar da hankalinta a kansu ta kasa kunne dan jin abinda a ke faɗa, “ka yi haƙuri Yaya gidan su Yaya Hafiz na ce zan je amma ni ba wajan shi zan je ba wajan Khadija zanje“ gyara zaman shi ya yi kafin ya ce; “Nabila ke mace ce ki riƙi mutuncin ki na ‘ya mace, ballagazar mace ce marar ta ido ita ce take bibiyar namiji a duk inda ya ke ko da yana sonta bare ke da ba kya ma gaban shi” ya numfasa kafin ya ci-gaba da magana “Hafiz abokina ne mutumin kirki ne tabbas nagartaccen mutum ne da zan so a ce auren ki da shi ya yo amma fa idan shi ne ya ce yana sonki ba wai ke ki dinga zubar da darajar ki kina bin shi ba, dan haka daga yanzu na hanaki bibiyar shi ciki kuwa har da kiran waya, idan da rana ɗaya naji kin neme shi ko kinje gidan su ke ko ta ina ne wallahi ranki in ya yi dubu sai ya ɓaci!” Ya miƙe tsaye ya je gabanta ya murɗa kunnenta ta ritsi idanunta da ƙarfi saboda azabar zafi da ta ji, “kin dai ji me na faɗa maki ko?“ Cikin muryar kuka-kuka ta ce, “Eh na ji zan kiyaye.“
“Yawwa kin taimaki kanki“ ya wuce ɗakin shi, ta tashi ta bar wajan da gudu ta bar falon, Fatima tabita da kallo tana girgiza kanta aranta ta ce; ‘iska na wahalar da mai kayan kara, Allah karka jarabcemu da abinda ba za mu iya ba’ ta ɗauki remot ta ƙara muryar tv ta ci-gaba da kallonta. Tana zuwa ɗaki ta faɗa kan gado ta kwanta rigingini sai da ta yi kukan ta mai isarta, ji take kamar zuciyarta za ta fashe wani irin so take wa Hafiz tana ji a ranta idan har ta rasa shi za ta iya rasa ranta, tashi ta yi ta sauya tufafin jikinta ta dawo ta kwanta ta ɗauki wayarta tana duba hotonan Fatima ta shigo ɗakin ta zauna a kan kujera tana dannar waya, Rufaida ta shigo ta faɗa mata zuwan Yaya Hafiz.
Taja numfashi ta furzar juyawa ta yi ta koma ɗaki zuciyarta na mata wani irin zafi, suka bi bayanta zuciyar Fatima ciki da tausayin ‘yar’uwarta. “Ya Allah ka rabamu da son ma so wani.”
“Amin dai ai kam Aunty Nabila tana fama da aiki son cusa kai babu kwarjni,” Rufaida ta yi maganar ƙasa-ƙasa, Fatima ta harareta ta ce, “Ai koma miye laifinki ne tana zaman zamanta kika zo ki ka faɗa mata da ba ki faɗa ba da har ya tafi bata ko san ya zo ba, yanzu kin zo kin ƙara mata damuwa.“
Tana yatsina fuska ta ce, “To kanwa uwar haɗi, ni me ye nawa dan naga abinda ta ke so ta gani na zo na faɗa mata, shi ne ki ke so ki yi munafunci“ cikin masifa Fatima ta ce, “Ni kike kira da kanwa uwar haɗi munafuka?“
“Eh ɗin ko ƙarya na faɗa“ ta yi maganar cikin gatsini “wallahi ni kin san ko wa ya ci tuwo dani, tabbas miya ya sha, kin sani dani da ke kar ta san kar ne, wallahi yanzu sai na naɗa maki na jaki!”
“Hihihi!! Wallahi sai dai mu naɗawa juna na jaki ki daina ganin wannan jikin naki ki ɗauka za ki ɗibi wani abun a jikina ƙarfi ba daga jiki bane abun a zuciya ya ke.”
“Dalla can! Ku fitar min a ɗaki banzaye koyaushe ba ku da aiki sai faɗa kamar wasu kaji!“ Rufaida ta kaiwa Fatima duka ta arce na kare ta fita ɗakin a guje, “Bala’i! Ni ki ka daka, wallahi za ki sani bari su Yaya su bar gidan nan sai jikin ki ya faɗa maki!“ ta yi maganar ranta a ɓaci ta koma ta zauna a kan kujera, ko ta kansu Nabila bata dake bi ba ta koma ta kwanta a kan gado a ƙuntaci take jin zuciyarta.
*****
Shiga office ɗin nasa ya yi a gajiya ya zauna a kan kujera ya yi miƙa ya ɗauki wayar sa yaga kira sosai ciki harda wata number da har ta zafara zama a kansa saboda yawan kiran da a ke ma sa da ita, tun yana ɗauka ana masa shiru har ya gaji ya daina ɗauka, ya buɗe WhatsApp ɗinsa kai tsayi saƙon number da a ka kirashi da ita ya fara buɗewa ciki da zaƙuwa ya rasa me ya sa ya ke matuƙar zaƙuwa da ta turo masa saƙo abinda kawai ya sani saƙonninta suna matuƙar saka shi farin ciki duk da bai santa ba bai taɓa jin muryarta ba bai taɓa ganinta a zahiri ba sai dai a hotonan ta da take turo masa, kyakyawa ce tana da diri irin kalar macen da ya ke da burin aure kenan, cikin shauƙi ya fara karanta saƙon.
“Ina Son ka My Noor, zan kuma ci-gaba da sonka har a bada abadan da’iman. Ina ciki da shauƙin kasancewa a tare da kai a matsayin miji da mata, ina addu’a Allah ya sa ka zama mijina uban ‘ya’yana, haƙiƙa da na fi ko wace mace sa’a da samun Nagartaccen miji kamar ka wanda ya ke matuƙar wahala a wannan zamanin. Ina SON KA da dukan raina My Noor”
Lumshi idanunsa ya yi ya kwantar da kansa jikin kujera yana jin wani irin bugun zuciya da bai taɓa jinsa a ransa ba a kan mace, ya buɗe su a hankali ya buɗe hotonan da ta turo ma sa, da video tana bin waƙa cikin natsuwa da shauƙi ba rawa take ba a zaune take a kan kujera tana juya idanunta haɗi da lumshi su tana buɗewa a hankali da murmushin ta mai ɗaukar hankali sosai ta tafi da imaninsa wannan ita ce sak irin macen da ya ke siffantawa da kuma mafarkin sa, wani saƙonne ya shigo da sauri ya fara karantawa
“Amincin Allah ya tabbata a gare ka My Noor. Ina fatan kana cikin ƙoshin lafiya? Gaskiya na ji damuwa sosai har sai da idaniyata su ka zubar da hawaye saboda gaba ɗaya yau bangan ka a online ba, kuma na kira wayar ka baka ɗaga ba, har na fara jin tsoron ko Lafiya, ina fatan kan cikin ƙoshin lafiya? Ka kularmin da kanka Annurin Zuciyata.”
Yana so ya tura mata amsa sai dai tuna baikon ‘yar’uwar shi Zhara ya kan katse mashi hanzari hakan ya sa duk saƙon da take turo ma shi iya ya karanta amma daidai da rana ɗaya bai taɓa bata amsa ba. Ci gaba ya yi da kallon videon yana jin wani irin abu na fizgar zuciyar shi gami da ita, shigowar nos ne ya dawo da shi daga duniyar da ya ke cikin mutuntawa ta ce; “Doctor a kwai marar lafiya da yawa da su ke jiran fitowar ka ɗakin tiyata tun ɗazun fa.“
“Uhm! Ba na ce ki tura su wajan su Doctor Mujahid ba.”
“Na tura na safe waɗannan daga baya su ka zo.”
Ya duba agogon da ya ke maƙali a hannunsa kafin ya dawo da duban shi a kanta ya ce, “Sister Rabi lokacin sallah ya gabata amma bari na duba ko mutum biyu ne sai na je nayi sallah azahar idan na dawo sai na ƙara sa duba sauran.”
“Ok Doctor, “ ta fita ya ajiye wayar yana mai yin ajiyar zuciya.
*****
“In kaga ruƙumi kaga akala, daga ina haka?” Zhara da Halima su kayi dariya Halima ta ce; “Aunty Laila daga gida zuwa nan.” Hankaɗa labulen ɗakin ta yi tana faɗin, “Lallai yau kuma aljannun yawon gidana suka cilloku?”
Karasa shiga suka zauna bayan sun gaisa ta je ta kawo ma su ruwa da ɗan wake yaji manja da yaji da yaji kayan haɗi bajewa su kayi suna ci suna santi Zhara ta ce, “Shi ya sa mu ke son zuwa gidan nan Aunty Laila ba kya rabu da abun dancikin.” dariya ta ce, “Allah ya shirye ku, kamar kun san ina neman ku.“ Har haɗa baki su ka yi wajan faɗin “Ta samu kenan Aunty?“
“Shaƙiyancin ku sai ku“ suna gama cin abinci Halima ta ce, “Aunty faɗa mana wani labarinne?“
“Sarkin son jin labari kamar ‘yar jarida wai Halima ba za ki fasa karantar lauya ba ki dawo jarida.”
“Banda abinki Aunty Laila ai dai kusan duk abu ɗaya ne tunda lauya ma ai sai ya nemi labari ta yanda zai fahimci shari’ar gaban shi, yanzu dai faɗa mana mene ne?“ cikin dariya Zhara ta ce, “Oh Halima son jin gulma kamar kamar bazawara.“
“Ni fa makirci ne bana so idan aka tuna zuciyar ki na tabbatar kinma fini zaƙuwa ki ji.”
“To sarakan musu ya isa hakan, dama tun ranar da kuka zo gidan nan a kan hanyar ku ta fita idan za ku tuna kun haɗu da Abban Yasmeen tare da abokin shi?”
“Tab mun manta wallahi, jiki kan maganar ki kawai Aunty Laila.” Halima ta faɗa tana gyara zamanta, murmushi Aunty Laila ta yi kafin ta ce, “To abokinne ya mun maganar yana son ɗaya daga cikin ku ya ta min bayani na kasa ganewa tunda kaya iri ɗaya kuka sa, sai da ya ce min mai Hijab na gane Zhara ya ke nufi tunda a cikin ku biyun dama ita kaɗai take yawo da Hijab, da farko dai na ƙyaleshi sanin halinku na rashin kula samari tunda ga su nan suna bibiyar ku kuna yaƙince su ta ƙarfi, to sai matsin number ya ke min hakan ya sa na ce ya bari zan neme ku.”
Dukan su suka ƙyalƙyace da dariya tana hararsu ta ce, “Au dariya ma na baku ko?“ Halima ta ce, “Ba hakan bane Aunty Laila aradu ki faɗa masa ya makaro dan Zhara kam anyi baikon ta.“ Kallon Zhara ta yi tana faɗin “Wai haka Zhara da gaske anyi maki Baiko?“ cikin murmushi Zhara ta ce, “Da gaske Aunty Laila, saura wata ɗaya biki.”
“Ikon Allah shi ne banji ga kowa ba.”
“Kin san kin kwana biyu baki ke gida ba, mu ma ba mu zo ba, zuwan da mu ka yi mu faɗa maki kenan.” Halima ta faɗa tana ƙoƙarin miƙewa danyin alwala.
“Allah ya sanya Alkhairi, waye wannan da ya ciri tutar Zhara mai tsoron maza?“ cikin dariya Halima ta ce; “Yayanta ne auren zumunci ne.“
“Ma sha Allah, Allah ya sanya Alkhairi, bari na ce ya dawo wajanki ku daidaita“ har ta sa ƙafarta waje ta dawo da sauri ta ce, “To da farko dai Amin. Sai zancen ya dawo wajena Allah Aunty karma ki suma, ni karatu na sa a gaba ba aure ko soyayya ba.“
“Sannu Mango pak! bari na je wajan Yaya na ji idan ita ce ta ɗaure maki gindin rashin auren sai na ji ta da toshe.“ Ta ɓata rai kafin ta ce, “Aunty Laila karki sa nayi dana-sanin zuwa gidan nan na kuma ɗauki ƙafata da gidan-nan fa.”
“Allah ya baki sa’a, idan kin sake dawowa ma ban gode ba marar kunya kawai.“ za ta yi magana Zhara ta je da sauri ta turata waje tana faɗin “ji ki yi alwala mu yi sallah mu tafi kin dai ance kar mu daɗe.“ bayan fitar Halima Zhara ta dawo kusa da Aunty Laila ta ce; “dan Allah Aunty Laila ki yi haƙuri“ tsaki ta yi kafin ta ce, “Halima na da matsala riginarta ta yi yawa ba dama a zauna da ita bata ɓatawa mutum rai ba, ai da sai ta bari idan tagan shi bai mata ba sai ta ce bai mata ba.“
Haƙuri kawai Zhara ta bata, suna yin Sallah su ka mata sallama, a hanya sai meta Halima take tana faɗin “kaji rigima irin ta Aunty Laila kawai ta kwasu wani gara da ƙilama yana fama da kayan tumbi kamar an dasa masa ‘ya’ya goma kamar tulilin mijinta ta ce wai na so shi“ dariya Zhara ta yi tana faɗin “Allah ya shirye ki Halima“
“Allah ta ban haushi ne, idan na koma zuwa gidan ta yi abinda ma ya fi wannan.”
“Oh! Halima meta Halima rigima Dan Allah ya isa haka magana ta wuce tunda dai kin faɗa mata bakya yi ɗin.” bata dai daina me ta ba tafiya kaɗan sai ta yi maganar sanin hali ya sa Zhara ba ta sake cewa da ita komai ba.
*****
Da dare bayan ta gama tilawa ta ɗauki wayar ta ta kunna data tana shiga watspp saƙon shi ta fara dubawa gaisuwa ce da tambayar ya ta wuni, fuskarta da murmushi ta ba shi amsa, yana online suna magana sama-sama dan firar bata ma sa wani armashi tunda ta kasa sakin jikinta da shi, anan ya nemi da ta turo ma shi hotonanta ba musu ta turo ma sa ma su yawa ko wanne tana sanyi da Hijab wani kuma da mayafi,
“Ke ba kya hoto ne ba mayafi”?
Shiru ta yi tana nanata karanta saƙon, tabbas tana da hoto marar mayafi amma kuma ba za ta iya tura ma sa ba gaskiya ta rubuta ma sa.
“Eh Yaya, duk haka nake hoto”
Jim kaɗan ya dawo da amsa “Ok ki ɗauka yanzu ki turo min, kuma ayanda ki ke da kayan da ya ke jikin ki nake so ki ɗauka ki turo min“ tana karantarwa tana fito da idanu, ta duba jikin ta kayan bacci ne jikinta rigar iya gwiwarta take, ga rigar ana ganin jikinta Kasancewar ana zafi shi ya sa ta sa ta, kuma ita kaɗai take kwana a ɗakin ‘yan biyu ɗakin Mama su ke kwana, kiranta ya yi ta WhatsApp cikin sanyin jiki kamar marar lakka ta ɗaga kiran “Yaya“
“Na’am, me ya sa ki ka yi shiru“?
“Ba komai Yaya“
“To ina jiranki ki turomin“ ɗora hannunta ta yi a kan goshinta ta ma rasa me za ta ce ma shi, “Kinyi shiru“
“Yanzu zan ɗauka“ ta bashi amsa tana miƙewa tsaye, a ranta tana tunanin kawai ta yi sauri ta sauya kaya sai tayi hoton, kamar ya san tunanin da ta ke ya ce; a yanda kike na ce ki ɗauka idan har ki ka sauya kayan jikin ki ko ki ka turo wanda kika jima da yi zan gane“
Turus ta yi ta tsaya da tafiyar da take a ranta tana faɗin ‘wayyo Allah shi kenan ya ganota mutum kamar aljani, tsinki kiran ta ji ya yi ta janye wayar daga kunninta tana kallon wayar kamar za ta samu amsar ya za ta yi daga cikin wayar ne.
Allah yabada sa’a
Labari Yana dadi sosai.
Allah ya Kara basira
Masha Allah labari yayi dadin,Allah yakara basira
Ubangiji Allah ya qara basira momcy, wallahi Ina yinki
Ma sha allah 👍
Labari fa yana ba da citta Indo Aisha.
A ci gaba da gashi👍👍👍
Gaskiya ne Fulani labarin yana dadi sosai Allah kara basira
Masha Allah
09168687167
Ma sha Allah
Madalla da ke Fulani