Sakin wuyan ta ya yi yana huci "maza faɗa mini ina sauraren ki!" Shafa wuyanta tayi tana mayar da numfashi "wallahi ni ban ma ta komai ba, Momy ce ta zo bayan tafiyar ka" ta faɗa masa komai komawa ya yi kan kujera ya zauna diɓis yana riƙi kanshi da yake yi masa ciwo kamar zai cire.
Da ƙyar ta iya jan ƙafa ta ƙarasa gaban shi ta rusuna "kayi baƙuri haƙiƙa na san nayi rashin kyautata wa ga Zhara amma wallahi ban san komai a kan ɓatan ta ba, kuma nayi nadamar. . .