Skip to content
Part 42 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Sakin wuyan ta ya yi yana huci “maza faɗa mini ina sauraren ki!” Shafa wuyanta tayi tana mayar da numfashi “wallahi ni ban ma ta komai ba, Momy ce ta zo bayan tafiyar ka” ta faɗa masa komai komawa ya yi kan kujera ya zauna diɓis yana riƙi kanshi da yake yi masa ciwo kamar zai cire.

Da ƙyar ta iya jan ƙafa ta ƙarasa gaban shi ta rusuna “kayi baƙuri haƙiƙa na san nayi rashin kyautata wa ga Zhara amma wallahi ban san komai a kan ɓatan ta ba, kuma nayi nadamar duk abubuwan da na dinga yi ma ta a baya.”

“Kinga Halima ki tattara ina ki -ina ki ki bar gidan nan, ki ɗauka rashin ganin Zhara tamkar rasa mazuƙunni ne a gidana!” A tsoraci ta kai dubanta gare shi wanda har ya bar kujerar ya suma tafiya zuwa ɗakin shi “Hafiz me kake nufi da ni ne, na tafi gida kake nufi?” Ba kya buƙatar sake maimaici domin kin ji me na faɗa” ta kasa ko da motsa ɗan yatsanta har ya shiga ɗakinsa, ƙarar rufe ƙofarsa ne yasa ta zabura ta nufi ɗakinta tana kuka.

Bayan sallah isha dukan su suna zaune tsakar gida kan babbar tabarmar da Mama ta shimfiɗa Baba ya kai dubansa gareta yana faɗin “kukan me za ki sa mu gaba kina yi, ko me ya faru ai tun farko ke ce ki ka janyo faruwar sa Halima.”

“A to nima dai Malam abinda na faɗa mata kenan, ke kin aure mata miji a ranar auren ta kinsa an fasa da ita duk hakan bai sa ta ƙulance a rai ba sai ke ce za ki ƙulanceta saboda alƙalamin ƙaddarar ku yasa za ku rayu a inuwa ɗaya.” bayan hannunta tasa tana share hawayen da suke kwaranyowa a fuskarta tana faɗin “to amma ai nayi nadama, sannan ya ba ni damar na ba shi haƙuri na kuma gyara kuskurena ya ƙi.”

“Ai kin kuma riga da kin makaro da kin gyara tun kan hakan ta faru da ba ki tsinci kanki a wannan yanayin ba. Kuma ni wallahi ba zan taɓa kiran sa domin ya mayar da ke ɗakin ki ba, dan kin riga da kin zubar mana da girma a cikin a danunsu duk da Allah ya gani daga ni har mahaifiyar ki ba mu ɗora ki kan wannan turbar ba kin dai biyewa zuciya da sheɗan da suke ɗora ki a keken ɓera yau ga inda ya jibge ki.”

Washegari sallah asuba kawai suka yi suka bar garin Kano saboda kiran da mahaifin Halima ya yi wa Dady. Tsaye suke ƙofar gidan su Halima tare da matashi Nura ɗan unguwar yana yi masu bayani “na san ɗan a-dai-daita-sahun da suka shiga dan ina wajan suka shiga, sai dai gaskiya ban san gidan su ba, muna haɗuwa ne a majalisarmu.”

“Ko za ka kaimu majalisar ne mu tambaya don Allah?” Hafiz yayi masa tambayar cikin zaƙuwa “ai sai dare muke haɗuwa yanzu kowa yana wajan nema” riƙi kansa Hafiz ya yi ji yake kamar ya fasa ihu ko zai ji sassauci a zuciyarsa. Cikin jan numfashi Dady ya ce. “Shi kenan za mu jira zuwa dare don Allah sai ka zo ka rakamu majalisar ta ku.”

“In sha Allah ana yin sallar magarib zan zo mu tafi” godiya suka yi masa bayan tafiyarsa Dady ya kai dubansa ga Baba yana faɗin “mun gode fa.”

“Haba dai ba komai ai ni ma nauyi ne da ya rataya a kaina” Dady ya nufi mota yana faɗin”za mu je wajan ‘yan-san-da mu ji ko a kwai wani labari daga nan sai mu tafi masauki, idan yaron ya dawo dan Allah sai ku same mu a masauki ko ma dai ku kira sai mu zo mu tafi.”

“Shi kenan Allah ya tsare, Allah kuma ya taƙaita mana yasa a dace” Hafiz bai iya cewa komai ba sai mota da ya nufa. Yana daga ƙofar gida har motarsu ta ɓacewa ganinsa ajiyar zuciya yayi tare da juyawa zuwa cikin gidan jikinsa a sanyaye. Kichen ya samu Mama tana haɗa masu karin kumallo “yanzu nake ta ƙoƙarin na gama dan a kai masu karin kumallon”
“Har ma sun tafi, na so su karya Alhajin ya ce a’a sun yi a hanya.”

“Ayya. To ya labarin su Zhara?” A takaice ya mata bayanin komai yana gama faɗa mata ya juya zuwa ɗakin shi “amma ba su yi ma maganar Halima ba?” Juyowa yayi yana kallonta kafin daga bisani ya ce” ba su yi mini ba, kamar ma ba abinda ya faru, koma dai meye ita ce ta janyo wa kanta.”

“Uhm! Allah ya kyauta.”

“Amin ya Allah. Bari na yi shirin fita rana ta soma ɗagawa.” Halima da take kwance ɗakin Mama zazzaɓi ya rufeta ta lumshi idanunta tana zubar da hawaye masu zafi. Ko a lissafi-lissafin mafarki ba ta taɓa tsammanin Hafiz zai juya mata baya har hakan ba.

Zaune suki a bayan mota dreba na jan motar “sai yanzu nake tunanin ina ma mun ce ya tuntuɓe ɗai daga cikin waɗan da suke zama a majalisar tunda ba za a rasa wanda ya sani ba, ga shi ko number wayarsa ba mu karɓa ba” riƙi hannunsa ya yi “ka kwantar da hankalin ka ko bayanin nan da muka samu ma nasara ce, mu barwa anjima in sha Allah za a gan su. Mu dai ta addu’a ” gyaɗa kansa yayi tare da kwantar da kansa jikin Dady idanunsa a lumshi. Ana sallah Azahar Anwar ya ƙarasu masaukin su. Zaune yake gaban Dady “kayi haƙuri sam ban taɓa kawo hakan zai faru ba wallahi da ba zan bar garin ba har sai kun ƙaraso.” gyara zaman sa yayi yana faɗin “Anwar sam ba ka da laifi abu ne da Allah ya riga da ya nufa sai ya faru babu wand ya isa ya hana faruwar hakan.

Fatana kawai duk inda suke Allah yasa suna cikin aminci ya kuma bayyana mana su cikin ƙoshin lafiya.”

“Amin. In sha Allah za a gansu”
“Ka je ka lallaɓa ɗan’uwan na ka ko abinci yaƙi ci yana cikin damuwa sosai” miƙewa yayi yana faɗin zan ba shi ba ki in sha Allah.”
Kwance ya same shi lulluɓe da bargo kamar yadda ya barshi “wai ba ka tashi ka kayi wankan ba” yayi maganar yana yayi bargon hannunsa ya kai jikin Hafiz “SubhanalilLah! Hafiz ba ka da lafiya ne jikin ka zafi kamar wuta.”

“Tun jiya nake jin zazzaɓi” yayi maganar yana ƙara janyo bargon ya lulluɓe. Zama yayi gefen gadon yana faɗin “Hafiz damuwa fa ba ta maganin matsala sai ma ƙara janyo wata matsala, don Allah ka cire damuwa a ranka mu yi ta addu’a na tabbatar da izinin Ubangiji za a gansu” da ƙyar ya iya tashi ya zauna tare da jingina bayansa jikin kan gado yana faɗin “taya zan iya hana kaina damuwa Anwar, kaf dangin mu da na mamanta mun zaga an kira wayoyi amma ba su je ba, to suna ina? Kuma a ce wai mahaifiyata ce silar hakan. Maganar nan da nake yi ma Dady ya saki Momy.”

“Innalillahi wa Inna ilahi raji’un! Saki dai? Kai lamarin bai yi daɗi ba sam, Allah ya sawwaƙa. Kayi haƙuri komai zai daidaita in sha Allah” miƙewa yayi yana faɗin bari na haɗa ma ruwan wanka don Allah ka daure kayi sai mu tafi asibiti” kai kawai ya gyaɗa masa. Bayan ya fito wanka yasa shi gaba sai da ya ci abincin da yasa a ka kawo da ƙyar ya ci kaɗan sannan suka fito zuwa asibiti.

Ana idar da sallar magarib daga masallaci suka wuce unguwar su Zhara sai dai har a ka yi sallah isha ɗan rakiyar na su bai dawo ba “anya zai zo kuwa?” Hafiz yayi tambayar idanunsa na a kan baban Halima. “Zai zo mahaifin sa ya ce shi ne ya aike shi mu ƙara haƙuri dai” ko rufi baki bai yi ba sai ga shi ya ƙarasu cikin girmamawa ya gaishe su bayan sun gaisa ya ce “kuyi haƙuri Baba ne ya aike ni shi yasa kuka ji ni shiru.”

“Ba komai, ai sai mu tafi dama kai kaɗai muke jira” motar Anwar Hafiz da Nura suka shiga, Dady da Baba suka shiga ɗaya motar. Suna zuwa Nura ya fita jim kaɗan ya dawo yana faɗin “sun ce kwana biyu bai zo ba, sai dai an samu wanda ya san gidan su.”

“A to ai ta zo gidan sauƙi kai Hafiz ku je ku roƙe shi ya raka mu” Hafiz da yake tsaye gefen motar Dady ya amsa da to tare suka je suka roƙi alfarmar ya raka su, kallonsu yayi a ɗan tsorace “me ya yi ne ake neman sa? Kar na zo na kai ko wani abun ya faru kun ga ni ma na sa kaina a matsala” dafa kafaɗarsa Nura yayi yana faɗin “KB ba fa wani abun ba ne ni na san su, kuma ka san ba zan jefa ka a matsala ba ka yarda da ni.”

“Humm! Hakan ne, ka san rayuwar nan ta lalace ta zama abin tsoro, ba damuwa mu tafi” riƙo hannunsa Hafiz yayi yana faɗin “kana da gaskiya sai dai sam ba abinda kake tunani ba ne” cikin gamsuwa ya bi su suka shiga mota.

Tsaye suke ƙofar gida suna neman ɗan aikin da zai sallama masu shi sai ga wata matashiya ta fito tana riƙi da kular abinci “anya kuwa Yaya za mu samu abin hawa ka san da dare yayi unguwar nan tana wahalar abin hawa” janyo ƙofar yayi yana faɗin “ai laifin ki ne da ba ki gama girkin da wuri ba”

“Yaya faɗa kawai kake yi mini amma wallahi nayi iya ƙoƙarina itacen ne ba su ci ɗanyu ne kasan wahalar wutar damuna kuwa” tsaki yayi Anwar da Hafiz suka ƙarasa wajan su “salamu alaikum” “Amin alaiku Salam” ya amsa masu sallamar fuskarsa na nuna rashin sanin ko su waye, K.B ya ƙarasa yana faɗin “don Allah muna neman Shafi’u ne?”

“Lafiya kuwa?” Yayi tambaya da mamaki a fuskarsa Dady ya matsa kusa da shi yana faɗin “Lafiya lau, don Allah a kwai wasu da ya ɗauka shi ne muke so mu ji wani wajan ya a jiye su saboda mun neme su mun rasa. Allah yasa shi wannan” ya nuna Nura yana mai ci gaba da faɗin yaga sanda suka shiga abin hawan shi wannan ɗin ya ma sunan nasa?”
“Shafi’u” Nura ya ba shi amsa. “Uhm! Na fahimta sai dai maganar nan da nake ma ku ba ya da lafiya yanzu haka fitowar nan da muka yi asibiti za mu je mu kai ma su abinci.”

“Assha me ya same shi?”
“To AlhamdulilLah yau dai mun ga sauƙi tunda har ya farfaɗo daga suman da yayi, hatsari ne suka yi wata babban mota ta hau kan abin hawan nasa.”

“Tun yaushe abin ya faru?” Hafiz ya jeho masa tambayar a ruɗe. “Yau kwana biyu kenan da faruwar hatsarin” Hafiz ya yi low! zai faɗi Anwar ya yi saurin riƙo shi yana faɗin “haba don Allah ka kwantar da hankalin ka ba fa ce ma aka yi tare da su hakan na faru ba” shiru yayi ya kasa ko da motsi tsoro ne fal a zuciyar sa. Cikin ƙarfin hali Dady ya ce “Allah ya ba shi lafiya ya kuma kiyaye gaba. Amma sanda abin ya faru shi kaɗai ne ko kuma yana tare da wasu?” Shiru yayi cikin nazari kafin daga bisani ya ce”eh to ni ma dai kiran mu a ka yi a waya asibiti muka same shi tare da ‘yan-san-dan da suka kai shi, yanayin da muka tarar da shi wallahi ban iya tsayawa na ji shi kaɗai ne ko har da wasu ba.”

“Idan ba damuwa don Allah mu je asibitin sai mu bincika mu ji.”

“Eh za mu iya tafiya.” Suka rankaya zuwa asibitin zuciyoyin su ciki da tararraɗen abin da za su tarar. suna isa suka tarar da wata dattijuwa tana kuka sai namijin da yake gefe yana bata haƙuri yana share hawaye da sauri ya ƙarasa gaban su “Inna lafiya, Baba me ya faru ina Shafi’un?”

“Shafi’u ya tafi wanda ya fi mu son sa ya karɓi abunsa Dukansu suka sa salati, kan Hafiz yayi wani irin saraawa da yasa shi sunkuyawa a wajan yana riƙi kanshi. Ganin yadda suke maganar inda za su samu kuɗi su biya kuɗin asibiti da kuma motar da za ta ɗauki gawar kasancewar su masu ƙaramin ƙarfi, Dady ya shiga maganar yatsaya kan komai har ɗaukar gawar zuwa gida. Suna ajiye su suka tafi da alƙawarin za su dawo da safe ayi jana’iza da su. Daga gidan asibiti suka koma zuciyoyinsu ciki da tararraɗen me za su tarar. Cikin sa’a suka samu Likitan da ya gani a sanda ake cuku-cukun karɓar gawar ya na shirin fita, sallama Dady yayi masa da fara’a ya amsa masa kafin daga bisani Dady ya ce. “Don Allah taimako nake nema daga wajan ka? “Na’am ina sauraren ka” Likitan yayi magana idanunsa akan Dady. “Yanzu ba jimawa mun tafi da wani mamaci wanda hatsari ya rutsa da shi ban sani ba ko ka gane shi.”

“Eh to na gane shi, duk da mutum uku ne suka rasu da daren nan sai dai shi kaɗai ne wanda hatsari ne yayi silar zuwan sa asibitin nan a ka kuma tafi da shi gida, wani abun ne ya faru?” Ajiyar zuciya yayi kafin ya ce. “Shi mamacin ya kasance ɗan a-dai-daita-sahu ne, a jiyan da abin zai faru ya ɗauki ahalina a ciki ga shi mun neme su mun rasa, shi ne muke tunanin ko da su al’amarin ya rutsa, hakan yasa muka dawo mu bincika” gyaɗa kansa yayi yana faɗin “tabbas su huɗu ne aka kawo su ukun ko da aka kawo su sun rasu, suna ɗakin a jiyar gawa, dama ana cigiyar ‘yan’uwansu” jikin Hafiz ya dinga kirma zama yayi a wajan yana gumi. Anwar ya kafe likitan da idanu da matuƙar tashin hankali ya ce. “Kuma mata ne?” Cikin gyaɗa kai ya ce. “Eh akwai dattjai biyu sai matashiya ɗaya, mu dai je ku gansu dan ku tabbatar ko su ɗinne” Hafiz kasa tashi yayi daga wajan sai da Anwar ya tallafu shi ya miƙe tsaye cikin tararraɗi suka bi bayan likita zuciyoyinsu ciki da tsoron abin da za su je su ga ni. Sanda suka sanya ƙafafunsu cikin ɗakin Hafiz ya juya zai fita Dady ya riƙo hannunsa yana faɗin,

“Ina kuma za ka tafi?”

“Zan jira ku a waje ba zan iya ƙarasawa ba, ina jin tsoron abinda idaniyata za su gane mini, ba zan iya jura ba” bubbuga kafaɗar sa ya yi “mi muka isa mu yi bayan karɓar ƙaddarar da duk ta zo mana mai daɗi ko a kasin hakan, dukan mu ba mu isa mu sauya abinda dama can an rubuta zai faru, dan haka ka zama mai dakiya a kan komai” janyo shi yayi sauka ƙarasa shiga ciki likitan na faɗin “idan har su ne waɗan da kuke nema a kwai buƙatar mu kira ‘yan-san-da wanda su ne suka kawo su asibitin”

“Ba damuwa likita za a yi duk abinda ya da ce In sha Allah” Dady yayi maganar yana mai tsayawa kusa da likitan da yake ƙoƙarin buɗe ma’ajiyar gawar.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 5 / 5. Rating: 1

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Waye? 41Kuskuren Waye? 43 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×