Yana zuwa gida ya yi paking a wajan ajiye motoci ya fito ciki da sassarfa ya ƙarasa babban falo Khadijah ce kawai ya tarar a falon tana waya, janye wayar ta yi daga kunnenta tana faɗin “sannu Yaya.”
“Yawwa, Momy fa”?
“Tana ɗakinta” bai sake cewa da ita komai ba ya haura sama matattakala a bakin ƙofar ɗakin ya tsaya yana sallama, daga ciki ta ce da shi ya shigo. Tashi ta yi daga kwanciyar da ta yi a kan gado na alfarma da ya sha shimfiɗa da tsadaddin zanin gado, zama ya yi kusa da ita bayan sun gaisa ya yi shiru yana tunanin ta inda zai fara, “ya a ka yi ne, ka sani gaba ka yi shiru.” Yana susa gashin bakinsa da key ɗin mota ya ce, “Momy dama magana na ke so mu yi.”
Gyara zamanta ta yi kafin daga bisani ta ce, “kai na ke saurari” ya ja numfashi ya furzar ahankali kafin ya ce, “Momy akan maganar Zhara ce.” ‘yar fara’ar da take a fuskarta ta ɗauke ɗib cikin faɗa-faɗa ta ce, “Hafiz ka fa san na tsani naji maganar yarinyar nan ko, na faɗama ka janye maganar auren ka da ita ka ƙi ji.”
“Ki kwantar da hankalin ki Momy dama dai abinda na ke so kenan na janye maganar auren nata saboda ni yanzu haka na samu wacce na ke so, to amma Daddy na ke ji ban san ta ina zan fara ba wajan fahimtar da shi ba tare da ya yi fushi dani ba.” ya ƙarasa maganar cikin damuwa, murmushi ta yi cikin farin ciki ta ce; “Hafiz ka sani farin ciki tunda a ka fara maganar auren nan na ke jin ƙunci da damuwa a zuciyata sai yanzu na fara samun natsuwa.”
Ta yi shiru na ‘yan daƙiƙu kafin ta ce, “ni kaina ina jin Dadyn ku, amma duk mai sauƙi ne ka je ka fara faɗa ma sa kai kana da wacce ka ke so, ni kuma zanji da shi, kai dai duk fushin da zai yi ka tsaya a matsayar ka na ka fasa ka san halin Baban ka baya tsaurara fushinsa musamman a kan ku ‘ya’yansa.” Maganar da su ka yi da Momy sai ta sanya masa natsuwa da jin ƙwarin gwauwa, ya tashi zai fita har ya kai ƙofa ta ce; “ah ba ka faɗa min ‘yar ina ba ce yarinyar.” Ya juyo da murmushi a fuskarsa ya ce; “Momy anan garin take bari na nuna ma ki hotonta.” ɗauko wayarsa ya yi ya je ya nuna mata hotonta tana kallo tana faɗin “Ma Sha Allah kyawawa son kowa ƙin wanda ya rasa gaskiya ka yi dace, Allah ya sa rabun ka ce.” cikin farin ciki ya ce, “amin Momyna” ya bar ɗakin zuciyarsa fis.
*****
Washegari da sassafe ya shiga ɗakin Dady da har ya shirya zai tafi Abuja, tanƙwashi ƙafafunsa ya yi gaban Dady da ya ke zaune a kan darduma yana shan shaye Momy tana a kan kujera tana haɗa masa kayan sa a cikin ‘yar ƙaramar jaka, “Bokan Turai yau sammakun fita za a yi ne?” Cikin murmushi ya ce; “Aa Daddy sai zuwa goma zan fita In Sha Allah, na dai zo ne mu yi sallama na ji ka ce za ka yi tafiya kuma sammaku za ka yi.”
“Hakanne dama kuma ina so na yi magana da kai, yanzu dai bisimillah mu karya tukunna sai mu yi magana ko”? Yana gyaɗa kai ya ce; “Dady sai zuwa Anjima dai zan karya”
“Oh na manta fa ku ‘yan boko ne ba kwa cin abinci da sassafe mu da ya ke ‘yan gargajiya ne ai munfi ganewa cika ciki da sassafe” cikin dariya Momy ta ce; “to Alhaji idan ba kai ba waye ya ke cin abinci da duhun asuba.”
“Ba ku san sirrin da ya ke cikin karin kumallo da safe bane shi ya sa, daga ke har yaran naki duk na fiku kwaliti ai saboda ina kiyayi cikina yanda ya kamata, dama a ce kina tuƙa min tuwon dawa da na gero ga miyar kuka tasha daddawa wai wa ya ganni da sai na fi hakan lafiya, amma kun barni da abincin nan na ku na ‘yan zamani” dukansu su ka yi dariya kafin Hafiz ya ce; “tuwon dawa da gero kuma Dady.”
“Eh yaro ba ma idan ka samu ɗumami an haɗa da miya wuri ɗaya iya daɗi ko nama albarka, shi ya sa na ke son zuwan Maman Zhara ko idan na je can na kan cika cikina sosai da tuwon garin ta mai daɗi.” Nan take dariyar Momy ta tsaya ta ɗauri fuska tamkar ba ta taɓa yin dariya ba, kula da hakan da Hafiz ya yi ya sa ya yi saurin sauya akalar zancen ta hanyar tambayar Dady, “yawwa Dady ka ce za mu yi Magana.”
A jiye cof ɗin hannunsa ya yi yasa tushu ya goge bakin shi kafin ya ce, “Eh maganar biki ne lokaci na daɗa kusantuwa, shin filin ka da ya ke Sharaɗa za ka gini ko kuma dai za ka ɗauki ɗaya daga cikin gidajena ne sai a yi masa gyaran da ya ke buƙata?”
Cikin sanyin jiki ya ce; “duk yanda ka ce Dady hakan za a yi.” “A’a yanda duk ka so dai ai kai ne za ka zauna dan haka zaɓi na a wajanka, ka yi shawara idan na dawo ko kuma ta waya sai ka faɗa min abinda ka yanki, sai kuma kayan lefe na tura wa Matar Mubasshar kuɗi za ta sayo komai a can Dubai, idan ta dawo duk abinda babu sai a saya a nan ɗin.”
So ya ke ya faɗi abinda ya ke zuciyarsa sai dai kuma bakinsa ya masa nauyi ya kasa buɗe baki ya yi magana, “ka yi shiru ko da wata matsala ne?” Gyada kansa ya yi yana faɗin “Aa Dady Allah ya saka da Alkhairi, Allah kuma ya ƙara lafiya da buɗi mai albarka.” Cikin jin daɗi ya amsa da “amin Hafiz Allah ya yi ma ka albarka, sosai na ji daɗin yanda ka faranta raina ka karɓi zaɓin da nai maka, yanda ka faranta min Allah ya faranta ma fiye da hakan, Allah ya baku ‘ya’ya nagari ma su biyayya da albarka.”
Jikinsa ya yi matuƙar sanyi yana mai godewa Ubangiji da ya haneshi da furta abinda ya ke ransa tabbas da ya yi rashin wannan kyakyawan addu’a da albarka, cikin murmushi da sanyin jiki ya ce, “Amin Dady, na gode” ya yi sallama da Dady jiki ba lakka ya bar ɗakin, ɓacin rai iya ɓacin rai Momy ta shiga sai harara take mannawa Hafiz har ya bar ɗakin, cikin ɓacin rai Momy ta juyo kan Dady tana faɗin “rashin darajar tawa har ta kai ba za a yi shawara dani a kan bikin ɗana ba sai dai matar abokin ka.”
Tashi ya yi ya je ya zauna kusa da ita ya riƙo hannunta ta fizgi murmushi ya yi kafin daga bisani ya ce; “ki yi haƙuri abinda ki ke tunani sam ba hakan bane, na farko dai Mubasshar tare da matarsa suna Dubai za su yi sayayyar bikin ‘yarsu, hakan ya sa na tura ma su kuɗin lefen Hafiz, babban dalilina kuma na yi hakan duk sanda zan maki maganar auren nan sai mun samu saɓani hakan ya sa na daina yi ma ki maganar kinga ba mun zauna lafiya ba.” Shiru ta yi ba ta ce da shi komai ba, cikin lallashi ya ce, “shi kenan ki yi haƙuri idan har kin sauya a yanzu kina son auren ni a shirye na ke da baki ragamar komai a hannun ki, dama akwai sayin kayan ɗaki sai na bar komai a hannunki.” Da sauri ta kalleshi ta ce, “Wai bayan gatan da ka ma ta na saya mata kayan sawa ƙasar waje har kayan ɗakin kai ne za ka mata? To su iyayen nata me ye amfaninsu?”
“Inaga Turai mantawa ki ke wace ce Zhara a wajena ko, ko da a ce ba Hafiz za ta aure ba ni ne na ke da alhakin yi ma ta komai na aure domin ni mahaifinta ne ‘yar ƙanena ce uwa ɗaya uba ɗaya ki dinga tuna hakan.” ya faɗa yana mai miƙewa tsaye, “ina so ka sani yaron nan dole za ka ma sa sam baya sonta yana da wacce ya ke so” ta yi maganar tana mai kafe shi da ido, “ni ban san hakan ba a wajanki dai na ji tunda ba kya son auren komaima faɗa za ki yi.”
“Idan har ba ka yarda da maganata ba ai sai ka kira shi ka tambaye shi ka ji.” Zuba mata idanu ya yi ciki da ɓacin rai ya ce, “Turai idan har kin san abinda za ki faɗa gami da auren nan ba alkhairi ne ba ko abinda zai faranta raina to dan Allah ki ja bakin ki ki tsuki ki kuma koma gefe ki yi kallo.” Yana gama faɗa ya ɗauki jakarsa tare da ajiye mata kuɗi ya sa kai ya fita ya barta tana huci. Tana jin tashin motar Dady ta fito ta nufi shashin Hafiz tana zuwa ta hankaɗa ƙofar ta samu yana zaune gefen gado ya yi tagumi harararsa ta yi tana faɗin, “Haka mu ka yi da kai?” “Ki yi haƙuri Momy ba zan iya karya masa ƙwarin gwauwar da ya ke da ita a kaina ba, kawai zan haƙura na aureta.”
“Wato kana gudun zuciyar ubanka amma ba ka gudun tawa zuciyar ko?” Tashi ya yi ya riƙo hannunta ya zaunar da ita a inda ya tashi ya sunkuya gabanta gwauwoyin shi a ƙasa cikin karyar da kai ya ce, “ba hakan ba ne Momy, na san ke za ki fahimcini fiye da yanda da Dady zai fahimcini, ki yi haƙuri ki bani dama na yi wa Dady abinda ransa ya ke so.” Kawar da kai ta yi gefe ya sa hannu ya juyo da fuskarta suna fuskantar juna ya dinga yi ma ta magiya ajiyar zuciya ta yi kafin ta ce, “Naji amma sai idan ka yi min alƙawarin bayan auren sai abinda na gindaya za ka yi.” Da sauri ya girgiza kai ya ce, “Na yi ma ki alƙawari Momy kuma ba zan karya ba In Sha Allah.” Murmushi ta yi ita kaɗai ta san abinda ta ke saƙawa a zuciyarta.
*****
Sosai ta shiga damuwa a kan rashin jin Hafiz ta sani yana lafiya kawai dai ya ƙyaleta ne ya manta da ita, tana matuƙar kewarsa haka za ta shige ɗaki ta yi kuka mai isarta musamman idan zuciyarta na faɗa mata Hafiz ba ya sonta shi ya sa ya manta da babinta, koyaushe sai ta yi yunƙurin kiransa sai ta fasa, ba ta dai sake maganar da Halima ba tabarwa zuciyarta damuwarta, ta ci-gaba da sha’aninta kamar ba komai duk da kuwa akwai damuwa a ƙasan zuciyarta. Dawowarta daga makaranta taga wata haɗaɗɗiyar mota a ƙofar gidansu, Halima ta ce; “wow!! Motar nan ta tafi da imanina wallahi, kai da gani za ta yi wuta.” Cikin dariya Zhara ta ce, “To rufi bakin dai kar ƙuji ya faɗa.”
“Ke fiye da hakan ma sai na yi kinji wani laushi.” Ta yi maganar tana shafa motar kallon Zhara ta yi da sauri tana faɗin “ke ko dai Yaya Hafiz ne ya zo” zuciyarta ta dinga bugawa fat-fat, dariya Halima ta tintsire da shi tana faɗin “kai Zhara kinga yanda ki ka yi daga maganar Yaya Hafiz har kin zama wata iri, wallahi kin bari son mutumin nan ya ma ki mugun kamun kazar kuku.” Duka ta kai ma ta tana faɗin “Dama ai tsiyar da ki ke so ki min kenan shi ya sa ki ka shatu ƙaryar ki ni kinga na yi nan.” Ta ƙarasa maganar tana kaiwa Halima dundu a baya ta arce a guje ta shige gida, “Kam bala’i wallahi kin ɗauki ba shi anjima za ki biya wallahi!” Ta tafi tana masifa a ranta na ɗan adaidaita da ya ƙi yi ma ta nasihar ƙarasawa da ita gida.
*****
Tana sa ƙafanta a soron gidan kunnenta ya jiyo ma ta hayaniya kamar faɗa gabanta ne ya yanki ya faɗi, Hassana ta gani tana tsaye daga ƙofar shiga cikin gidan tana leƙin cikin gidan dafa kafaɗan Hasana ta yi Hasana ta juyo a tsoraci ganin Zhara ya sa ta yi a jiyar zuciya Zhara ta yi ƙasa da murya ta ce, “Me ke faruwa su waye su ka zo”?
“uhm ni na manta sunanta wannan dai ta gidan su Dadyn Kano ce ta zo take ta yi wa Mama masifa kamar za ta dake Mama.”
Zhara ta buga ƙirjinta zuciyarta sai dakan uku-uku take kamar za ta faso ƙirjinta ta fito dan tsoro, “wayyo Allana me ya kawo Momyn Yaya Hafiz gidan-nan”? Ta yi wa kanta tambayar a hankali kamar wacce ƙwai ya fashewa a ciki ta ƙarasa shiga cikin gidan Hajiya Turai tana tsaye a tsakar gidan ya yinda Mama take tsaye daga ƙofar ɗaki tana sauraren Hajiya Turai da ta ke ta kumfar baki kamar ba gobe, “ke kin san ɗana ya fi ƙarfin ‘yar ki yo ina ma haɗin kefe da kaska, ai ko wace ƙwarya da abokin ɓurminta, dan haka gargaɗi na ƙarshe da zan ma ku duk hanyar da ku ka bi ku ka yi ƙulle-ƙullen haɗin auren nan dan aci kuɗin shi da na ubansa to ku je ku warware Hafiz ba zai taɓa auren Zhara ba idan kuma ku ka ƙi ji tabbas ba kwa ƙi gani ba!”
Murmushin takaici Mama ta yi kafin ta ce, “Hajiya Turai kenan kina tunanin idan har maganata wata a bace a cikin auren nan da zan yarda a yi shi ne, wallahi ni yanzu a ka ce an fasa auren nan sai na fi kowa farin ciki, dan haka ki ma daina tunanin ina so bare har na ɓata lokaci wajan neman a yi, ki je can wajan mijin ki ki faɗa masa ya janye ki gani idan za a yi.” Zhara hawaye su ka ciko ma ta idanu, ta yi sumai-sumai za ta shige ɗakinta Hajiya Turai ta janyota da ƙarfi har sai da kafaɗanta ta amsa idanunta su ka shiga cikin na Hajiya Turai “Bar kallona da waɗannan idanunki ma su kama da na mayu, yo wa ma ya sani ko an sha a nonon gada!” ta yi saurin yin ƙasa da idanunta jikinta ya fara karkarwa ta tabbatar yau idan matar nan ta fara dukanta ba za ta barta ba har sai taga ba numfashi a jikinta saboda irin tsanarta da ta gani a cikin ƙwayar idonta, cikin tsawa Hajiya Turai ta ce, “Kina jina ko yarona ya fi ƙarfin ki idan ma kina tunanin zai aureki to tun wuri ki farka daga wannan mafarkin, shi yana da wacce ya ke so, dubi ki dubi a kurkin gidan da ki ke.” Ta faɗa tana nuna Zhara da gidan Zhara kam iya tsoro ta tsorata ga shi ta ma ta wani irin wawan riƙo har cikin ƙashin kafaɗarta take jin azabar riƙon, “Ki jini da kyau! Hafiz ba sa’an auren ki ne ba, ƙwarya tabi ƙwarya ne idan har ta hau a kushi ba ta moruwa, dan haka ki je ki nemi talaka faƙiri irin tsohunki ki aura.” Ta saketa tare da ingizata har sai da ta faɗi ƙasa ta nuna Mama tana faɗin “Ina fatan kinji mai na ce idan har kayan aurenta ne ba ku da ko ni nan zan iya taimaka ma ku da komai na auren, idan kuma mijin aure ta rasa to za ku iya kai sunanta gidan rediyo idan an samu mai so ko masallaci ku ba da ita sadaka amma ba dai ɗana ba!”
“To zuri’ar gidan Ƙaruna ma su ado da Naira, duk rashin mutuncin da za ki yi ki yi iya iyawar ki ki tafi ni in dai a kan auren Zhara da ɗanki ne to ni bani a ciki idan har mahaifinta bai janye ba to ni mai biyayya ce, idan har an ɗaura auren a ka kawo ta idan kinga dama ki yanka ta dan ƙiyayya, idan kuma kin san kin isa da mijinki to ki je ki sa ya fasa.” Ta shige ɗaki tare da rufu ƙofa, Zhara da tun da ta faɗi ta ke zaune a wajan tana kuka ƙafa tasa ta mangareta ta fice gidan tana ta masifa, da ƙyar Zhara ta iya tashi ta faɗa ɗakinta kuka ta ke kamar ranta zai fita.
Please akara yawan page, novel din ya hadu ,Allah ya kara basira, amin
Amin. Na gode sosai In Sha Allah
Salaam, malama Aisha inason novel dinnan complete idan akwai a Kasa ,Ga number na 09062733061
Aunty Fulani muna godiya sosai.
Allah ya Kara basira.
Labarin ya tsaru sosai
Labarin yayi dadi Allah yakara basira
Masha Allah Ubangiji Allah ya qara lfy da Nisan kwana
Allah ya ƙara basira
Ubangiji Ya ƙara basira Fulanita
Ma sha Allah