Skip to content
Part 9 of 43 in the Series Kuskuren Waye? by Aisha Abdullahi Yabo

Lokacin biki sai daɗa tunkaruwa ya ke Dady ya gyara gidan da za su zauna ansa kayan ɗaki masu kyau da tsada an ƙawata gidan sosai ko ‘yar masu hannu da shuni sai hakan, ‘yan’uwa da abokan arziƙi sai zuwa su ke ganin kayan lefen da a ka kawo suna san barka.

Tunda Nabila ta ji labarin auren Hafiz har an kai komai gaba ɗaya hankalinta ya tashi shirya wa ta yi  ta ce da Mamanta za ta je gidan ƙawarta kai tsaye gidan su Hafiz ta nufa tana addu’a Allah yasa ya na gida ba su kuma tare da Yaya Anwar, tun da ta shiga harabar gidan ta ke rarraba idanunta ba ta ga motar Hafiz ba ta san da wahala ne idan har ta taki sa’ar samunsa a gida, jiki a sanyayi ta shiga cikin gidan Kahdija kawai ta samu zaune a cikin babban falo tana kallo, cikin fara’a Khadijah ta tashi ta rungumeta tana mata oyoyo, “ƙawata idonki kenan ko yaushe rabun ki da gidan nan?”

Sakin juna su ka yi Nabila ta harareta tana faɗin “kin ji ki da wani zancen ba har gara ni ba ina zuwa ke ɗin ai ko tuna yaushe rabon da ki je gidanmu ba za ki yi ba.” “Hahaha to na ji zo mu tafi ɗaki.”

“A’a nan ɗin ma ya yi ina Momy?” Ta yi tambayar tana zama a kan kujera, Khadijah ta zauna tana faɗin “Momy ta tafi unguwa, ya Mama da su Fatima?”

“Duk suna nan lafiya lau, yanzu bikin Yaya Hafiz za a yi shi ne ko ki faɗa mini sai dai na ji Mama da Yaya Anwar suna magana” riƙi kanta Khadijah ta yi tana faɗin “ki yi haƙuri Nabila wallahi sam na sha’afa na ɗauka munyi maganar da ke, kinga yau saura sati ɗaya biki ma, ki yi haƙuri” ajiyar zuciya Nabila ta yi idanunta sun ciko da hawaye cikin ƙoƙarin haɗiye kukan da ya zo ma ta ta ce; “ba komai Allah ya sanya Alkhairi.”

“Amin Ya Rabb” Hafiz ya shigo falon da sallama a bakinsa, zuciyar Nabila ta ba da dum! Ta zuba masa idanu kasancewar kujerar da ta ke a zaune tana kallon ƙofar shigowa, sonsa taji ya na ƙara fizgarta ƙarasa shigowa ya yi  Khadijah ta masa sannu da zuwa ya  amsa ma ta yana tambayarta Momy ta faɗa masa ta fita, cikin sanyin murya ta gaishe shi ya amsa da fara’a ya na tambayarta jikin Mama ta ce da shi “ta ji sauƙi, ai yanzu ta jima ba ta tasu mata ba tun da a ka yi mata wannan allurar da ka rubuta mata.”

“Ma Sha Allah, hakan ake so Allah ya ƙara sauƙi”
“Amin” ya zauna a kan kujera yana dannar waya ya ce; “Deji yau me a ka dafa a gidan nan” cikin shagwaɓa ta ce; “ni fa Yaya ba Deji ne sunana ba Khadijah za ka ce” yana harararta ya ce; “idan kuma na ƙi fa?” Ta yi shiru tana turo baki, “ni je ki kawo mini abinci.”

“Ya na a kan dani.”
“Na sani kawo min nan ɗin zan ci” tashi ta yi ta nufi wajan da dani ya ke, idanunta na kallon ƙasa ta ce; “dama wajan ka na zo Yaya Hafiz.”

Ajiye wayar ya yi a kan hannun kujera ya na mayar da hankalinsa a kanta ya ce; “wajena kuma?” Ta gyaɗa ma sa kai “ok. Ina sauraran ki” za ta yi magana Khadijah ta shigo riƙi da faranti madaidaici ta ɗora kula babba da ƙarama sai gorar ruwa faro, da cop, ta ajiye gabansa, ta juya  tana faɗin “Nabila bari na kawo ma ki abinci.”

“Barshi wallahi na gode” juyowa ta yi tana harararta ta ce; “kin ma isa” murmushi ta yi kafin ta ce; “Allah kuwa a ƙoshi na ke ai kin san ba zanyi fulatanci a gidan nan ba” Khadijah ta zauna tana faɗin “ai shi kenan kin kyauta”  so ta ke ta yi magana sai dai zaman Kadija a wajan ba za ta iya cewa komai ba, kula da hakan da ya yi ya sa ya kalle Kadija ya ce; “ji ki gyara mini ɗakina” cikin turo baki ta ce; “Yaya gyaran ɗaki kuma? To ina Hashimu da ya ke gyara maka ɗaki?”

“Shin za ki tashi ki je ki yi aikin da na saka ki ko kuma sai na tasu na ɓaɓɓalaki!?” Cikin jin haushi ta tashi tana faɗin “ina zuwa Nabila” ta bar falon tana ƙurrafi a ranta tana faɗin ‘kawai a hana mutum sakewa a gaban baƙuwa zai ta sakani aiki idan kuma na ce mu je tare shigen fi’ili masifa zai yi tunda ba kowa ya ke yadda ya shigar masa ɗaki ba’ ta yi ƙwafa tare da ƙarasa fita falon, ya ce da Nabila ya na saurarinta, duk da ta ji daɗin yadda ya fahimci ta har ya yi dabarar sa wa Nabila ta fita ɗakin sai kuma ta kasa yin magana ta rasa ta ina za ta suma, “kinyi shiru” ajiyar zuciya ta yi cikin sanyin murya ta ce;  “am dama  dama a kan maganar auren ka ne, na ce idan har za ka amince ni ko bayan auren ka ne zan iya zuwa a matsayin matar ka ta biyu don Allah Yaya Hafiz” zuba ma ta idanu ya yi aransa ya na mamakin  yadda a kayi mata su ka ajiye kunya irin wacce a kasan ‘ya’yan hausa fulani suna da ita, wai mace ta zo gaban namiji tana magiyar ya aure su.

Gyara zamansa ya yi kafin daga bisani ya ce; “duk na ji abinda ki ka faɗa Nabila sai dai ina so ki bani aron hankalin ki nan” ya zuba ma ta idanu ta yi ƙasa da kanta tana wasa da zoben hannunta,  “Nabila maganar soyayya ba ta taɓa haɗani da ke ba, kamar koyaushe na sha faɗa ma ki ke ɗin ƙanwata ce kamar dai Kadija, dan haka ki a jiye zancen so ko aure gefe ki bari mu cigaba da yin zumuncin mu ba tare da an samu tangarɗa ba.” Hawayen da tun ɗazun take hana su zuba ne wannan karon riƙon su ya gagareta har sai da suka zubo mata, ji take kamar ta zubi gaban sa ta sake ruƙonsa alfarma sai dai ina ba za ta iya ba kar yada kan ya yi ya wa duk da ko yanzu ta san ta riga da ta gama yada kanta, tausayinta ne ya cika masa zuciya, tabbas ya san so da irin raɗaɗin da zuciya ke shiga a yayin da kake ganin abin da ka ke so ya na shirin suɓuce maka, cikin lallashi ya ce; “ki yi haƙuri Nabila kinga ke ƙanwar abokina ce ba zan so a ce na yaudare ki da abinda babu shi a zuciyata ba tamkar cin amanar abotaka ce, abinda kawai zan iya ce wa da ke shi ne ki bar wa Allah komai ki cigaba da addu’a ya ma ki zaɓi mafi Alkhairi  In Sha Allah idan har ki ka yi haƙuri ki ka bar wa Allah zaɓi zai ba ki miji wanda ya fini nagarta da komai.”

Komai ba ta iya cewa da shi ba ta ɗauki jakarta ta miƙe tsaye cikin muryar kuka ta ce; “shi kenan Yaya Hafiz zan yi abinda ka ce zanyi haƙuri ba dan na so ba sai dan banda yadda zanyi, zan kuma yi addu’a kamar yadda ka ce, sai dai ina so ka sani ba zan iya hana zuciyata sonka ba kamar yadda na ke so ka ajiye wannan a ranka ko me ya sameni sanadin sonka ne kai ne sila” ido a rufe ta bar falon, bin ƙofar da ta fita ya yi da kallo, gaba ɗaya jikinsa ya yi sanyi wata irin damuwa ta rufe zuciyarsa abincin da bai iya ci ba kenan, ya nufi sashinsa ya samu Kadija tana kakkaɓi zanen gado ya ce ta barshi kawai ta ɗago za ta yi magana yanayin da ta tagani a fuskarsa ya sa ta haɗiye maganar tare da barin ɗakin kamar yadda ya umurce ta. Kwanciya ya yi a kan gado gaba ke ɗaya maganganunta sun dagula masa lissafi, sam ba ya so wani ya shiga damuwa saboda shi bare kuma jinin Anwar anya kuwa ya kyauta wa Nabila da amininsa?

Kadija tana zuwa ta samu Nabila ba ta nan ta kirata a waya haƙuri Nabila ta ba ta da faɗa mata wani uzurin ne ya ta so ma ta hakan yasa ta tafi ba tare da sunyi sallama ba, ba dan ta gamsu ba ta ajiye wayar ta cigaba da sabgoginta.

*****
Dangi ta ko ina sun fara tururuwar zuwa Jigawa gidansu Zhara ya cika babu masaƙar tsinki kasancewar gobe asabar ne ɗauren auren, Dady da mutanensa duk sun sauka a birnin Jigawa wanda ya kama hotel-hotel,  sai hada-hada a ke ga abinci na  alfarma da Dady ya bada oder ayi, Ango tare da angayar abokansa duk sun hallara sai ɗaiɗaikon jama’a ne za su shigo da safe kafin ɗauren auren kasancewar ƙarfe goma na safe za a yi ɗauren auren.   

Da dare Halima tana zaune ƙarshen katifa ta cure jikinta waje ɗaya kuka ta ke marar sauti, yayin da take jin wani irin ciyo a zuciyarta, Aunty Laila da ta zo tun safe anan za ta kwana har Kano za ta raka amarya,  ta zo ta sameta cikin wani yanayi zama ta yi kusa da Halima ta dafa kafaɗarta kafin daga bisani ta ce;  “anya kuwa Halima kewar Zhara kaɗai ke damun ki wannan kukan ya yi yawa. Yaya ta ce tunda bikin ya ƙaratu kullum cikin kuka ki ke me ya ke damun ki Halima?”


Ita kanta ba ta ce ga abinda ya ke damunta abu ɗaya ta sani a ƙuntace take jin zuciyarta, sake jiho mata tambayar Aunty Laila ta yi lumshi idanunta Halima ta yi hawaye masu zafi suna cigaba da zarya a fuskarta, kwantar da kanta ta yi jikin Aunty Laila cikin muryar kuka ta ce; “ni kaina ban san me ya ke damuna ba Aunty Laila amma ina jin wani irin nauyi a kan zuciyata tamkar an ɗora mini babban dutsi a kanta.”

“Ikon Allah to ki dage da addu’a ba mamaki shaƙuwar da ku ka yi da Zhara ne tun kuna yara koyaushe kuna tare yanzu kuma aure zai raba ku, ki yi haƙuri a hankali za ki saba.” gyaɗa kanta kwai ta iya yi,  Aunty Laila tana fita ɗakin kiran Hafiz ya shigo wayarta ta zura wa wayar idanu zuciyarta na dukan uku uku har kiran ya tsinki ta kasa tsayar da tunaninta guri ɗaya ta ɗaga ko ta cigaba da ƙin ɗauka kamar yadda ta ke masa kwana biyun nan, saƙo ne ya shigo wayarta da sauri ta ɗauki wayar tana duba wa kamar yadda ta yi tsammani shi ɗinne ta fara karanta saƙon nasa.

Ki fito ina ƙofar gidan ku, idan har kuma ki ka ƙi fitowa tabbas zan je na faɗawa Zhara gaskiya.

Saukar da gwarron numfashi ta yi ba ta da mafita da ya wuce ta fita ɗin domin ta san idan har taƙi fita zai aikata abinda ya faɗa ɗin, jiki a sanyayi ta miƙe tsaye Hijab ɗin da ta yi sallah isha tasa ta fita  cikin sanɗa cikin sa’a har ta fita babu motsin kowa a cikin falon tsaye ta same shi cikin suro gidansu, sallama kawai ta iya yi masa ta tsaya gefe tare da sunkuyar da kanta ƙasa juyowa ya yi yana fuskantar ta cikin wani irin yanayi ya ce; “Baby me ya sa ki ke wahalar da zukatanmu a kan abinda Allah bai haramta ba?”

Kukan da take ƙoƙarin hana fitowar sa ne ya fito cikin sauti kallonta ya ke hankalinsa a matuƙar tashi har ma ya rasa me zai ce da ita. Zhara ta fito ɗakinta tare da Nafisa ‘yar ƙanwar Mama da su ke sa’anni da juna Mama da take fitowa daga kichen ta kallesu tana faɗin “ina kuma za ku je da daren nan”?  “Mama za mu je wajan Halima ne ina ta kiran wayarta ba ta ɗaga ba ga shi munyi za ta zo, shi ne za mu duba ta.”

“Humm ai kam dai akwai aiki gobe idan kin tafi ban san ya za ku yi ba daga ke har ita.” murmushin ƙarfin hali Zhara ta yi tare da riƙo hannun Nafisa su ka tafi tana jin zuciyarta a ƙuntace  Allah ne kaɗai ya san irin kewar da take ji na ƙawarta da iyayenta tun kan ta tafi. Hafiz ya kalleta cikin tausasa murya ya ce; “Halima ina so zan tambaye ki kuma ki faɗa mini gaskiyar abinda ya ke ranki, shin kina sona har yanzu ko kuma kin daina sona”? Shiru ta masa “idan za mu kwana tsaye a wajan nan ba zan tafi ba har sai kin bani amsata” ɗago kanta ta yi tana kallonsa cikin raunin muryar da ta ci kuka ta ce; “ko da har yanzu ina sonka Hafiz babu amfanin da hakan zai mini gobe kamar wannan lokacin kana tare da ƙawata matarka, don Allah Hafiz ka fahimcini mu haƙura da juna shi ne kawai mafita.”

“Ki bani amsata kina sona ko ba kya sona”? “Ina sonka Hafiz sai dai kuma ya zama dole mu rabu dan banda idanun da zan kalle Zhara na faɗa mata ina sonka ko kuma zan aure ka mu yi zaman kisantaka da ita” murmushi ya yi kafin daga bisani ya ce; “ban damu da me Zhara za ta faɗa ko duniya za su faɗa abinda kawai na sani ina sonki kuma Allah bai haramta aurena da ke ba.”

“Uhm! Ni gaskiya ina tsoron bakin mutane da duniya ma, dole mu haƙura da juna Hafiz.” kallonta ya ke cikin tabbatar mata da abinda zai faɗa daga zuciyarsa ne ya ce; “Halima Allah bai haramta aurenmu ba,  dan haka ba zan haramtawa kaina abinda na ke so kuma ya ke halat ne a gare ni, kuma ki sani ko duk duniya za su taru su ƙalubalance ni a kan auren ki ba zan taɓa canza ra’ayina na auren ki ba, ina so ki san da wannan” juya wa ya yi ya ce da ita yana zuwa, jim kaɗan ya dawo tana nan tsaye a inda ya barta kamar an dasa icce, babbar ledar da take hannunsa ya miƙa ma ta kallon ledar ta yi kafin daga bisani ta mayar da kallonta gare shi tana faɗin “me ye”?

“Ki karɓa mana kafin ki yi mini tambaya” hannu biyu tasa ta karɓa idanunta a kansa tana jiran amsar tambayarta, gyara tsayuwarsa ya yi tare da sa hannayensa cikin aljihun wandonsa ya ce; “kayan zuwa Dena ne gobe idan an kai Amarya abokaina sun shirya mana Dena, iri ɗaya ne da na Zhara launin ne kawai ya bambanta itama yanzu zan je na kai mata na ta” ta girgiza kai za ta yi magana ya yi saurin taran numfashinta ya ce; “bana son jin komai Baby dole ki karɓi kayan nan kuma dole ki sa bana son musu, akwai kuɗi na sa ma ki a cikin jaka” ya na gama faɗa ya sa kai ya fita, jiki a sanyayi ta shiga gida, ta ma rasa wani kalar tunani ko hukunci za ta yanke wa kanta.

*****

Ɗakin Mama ta shiga tana zaune cikin dangi ana ta fira ciki da farin cikin haɗuwa da juna, Mama ta kalleta ta ce; “aa har kun dawo”?

Zhara ta ce; “ba mu je ba muna hanya Yaya Hafiz ya kirani a waya ya ce zai zo shi ya sa mu ka dawo.”

“To ina Nafisa”? “Tana tsakar gida waya take” Inna Suwaiba Yayar Mama ta kalle Zhara tana faɗin “wai ma kuwa kinci abinci”?
“Ina fa ta ci tunda bikin nan ya ƙaratu ba ta son cin abinci kullum sai kuka da baƙin rai” cewar Mama, Inna ta ce; “laifin ki ne ai da sai ki dinga sa ta gaba tana ci yarinya duk ta rame ko so ki ke a kaiwa angon ki ke a ƙyamushi” rufi fuskarta ta yi tana dariya, Inna tasa a ka kawo mata tuwon Samo da miyar kuɓewa haka ta ci abincin ba dan tana jin daɗin sa ba sai dan ba ta so ta ma ta musu, kiran Hafiz ya shigo wayarta ta daƙili kiran tare da kashi wayar gaba ɗaya, kaɗan ta ci ta tashi Inna na ta faɗa komai ba ta ce da ita ba ta bar ɗakin.

Dare ya raba waɗan da su ke ɗaki ɗaya duk sunyi bacci, sai hayaniyar ‘yan’uwa da ka ke ji a tsakar gida ana ta haɗa abincin ‘yan ɗaurin aure, a kwance take bacci ya ƙauracewa idanunta so ta ke ta yi kuka ko za ta ji sanyi a zuciyarta sai dai sam kukan ya ƙi ya ba ta haɗin kai tashi ta yi ta zauna tare da dafa saitin zuciyarta da take mata barazanar fashewa saboda azabar ciyon da take mata, zubar ta yi ta tashi tsaye kamar wacce a ka muntsina ta je wajan da ta ajiye wayar ta ta ɗauka number Dadyn Hafiz ta lalubu ta danna kiran aranta tana addu’ar Allah ya sa ya ɗaga cikin sa’a kiran na shiga ya ɗaga yana faɗin,

“Mamana ba ki yi bacci ba” tana jin muryarsa kuka mai ƙarfi ya zo ma ta, cikin tashin hankali ya ce; “SubhanalLah! Lafiya Mamana”? Ta kasa cewa da shi uffan sai kuka take da sauri ya ya yi bargon da ya rufa da shi tare da tsinki kiran yana fitowa  ɗakin ya kira drebansa ya ce ya tashi za su fita, hakan su ka bar hotel su ka nufi gidan ɗan’uwansa zuciyarsa ciki da tsoro idan ba wani abun ya samu ɗan’uwan nasa ba.

Bookmark
ClosePlease login

No account yet? Register

Rate the story.

Average: 3.5 / 5. Rating: 4

As you found it interesting...

Follow us to see more!

<< Kuskuren Waye? 8Kuskuren Waye? 10 >>

4 thoughts on “Kuskuren Waye? 9”

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
3
Free daily stories remaining!
×