Skip to content
Part 1 of 1 in the Series Kwamin Nadama by Rasheedat Usman

“Ina bazai saɓu ba.!! Da kamar wuya Gurguwa da auren nesa. Tabbas na yarda ungulu bata san kuɗin sabulu ba dole idan ta samu ta ɓarnata, yo Astagafurullah Kabiru ai ni ba kalar matar da za’a yiwa kishiya ba ce.! Wallahi ba ka isa ka ƙara Aure ba idan kuma ka ce sai ka ƙara to kuwa za ka ga masifa da bala’in da baka taɓa gani ba a cikin gidanka dan wallahi sai na cinnawa gidan nan wuta kowa ya mutu. Ni ma yaushe ka gama sauke mini haƙƙina da Allah ya ɗaura ma ka? Idan Ban da ƙaddara ma ai ni ba sa’ar auren ka ba ce idan dai Allah ya yanka maka kazar wahala ne dole sai ka fige ta.”

  Kinci ƙwal ubanki Ladiyo shegiya mai kai kamar shantu. Idan Banda iya shege da tsiya mijin naki za ki zaga shegiya mai kai kamar kwallon goruba. Da uwar me Kabirun ya rageki?”

   Iyatu ta feso min wannan baƙar maganar da ga sauƙe mugun zaren da ya ke tsuƙuƙƙuye a ƙarjina. Runtse idanuna nayi ina kallon Iyatu da ta kanne idanunta masu kama da na ƙiya tana shiga abinda bai shafeta ba saboda ɗiɗiri da shiga sharo ba shanu.

  “Sannu Iyatu ishashiya ‘yar Iya har wani mai kai kamar ƙwallon goruba ki ke kirana, yo ai gara goruba ba’a rasata da ƙananan gashi, ke kuwa naki kan ai sai dai a kirasa da ƙwallon ƙoƙiya. Ƙarya na masa ne ko ya sauke mini haƙƙina da Allah ya ɗaura masa ne. A hakan nayi haƙuri na zauna da shi cikin wannan talaucin sannan ya ce wani aure zai jajiɓo, saboda kawai kaga ina sonka ina haƙuri da talaucin ka, to wallahi uwar kuturu ma tayi kaɗan ballantana ta makaho ni da kai mutu ka raba takalmin kaza babu shegiyar da ta isa ta shigo gidan nan da sunan aure har ta amsa sunan matarka, danni kaɗai aka halliceka kuma da ni za ka ƙare rayuwar ka.”

    Dirar sautin muryar Kabiru a ma’aunin tantancen jin kunnuwana sai da yasa zuciyata bugawa da ƙarfin gaske tabbas maganar da Hausawa ke cewa na miji tabarmar ƙashi ya tabbata akan Kabiru.

   “Ba ki isa ki hanani ƙara aure ba Ladiyo ni ba ni daga cikin shashashun mazan da matan su ke juya su, kishi ai ba hauka ba ne da za ki fara ba ni umarni. meye ki ke yiwa kanki ina dai sutura ce kawai da har za ki mini gori komai talauci na dai ban taɓa bari kin kwana da yunwa ba, aure kuma ba fashi kamar da ƙasa sai anyi.”

   Tsalle nayi na dire tare da cakumar wuyan sa idanuna suka rufe raina ya yi mungun ɓaci cikin ƙaraji da ɗaga murya na ce wa Kabiru.

    “Idan ka cika ɗan halak a cikin uwarka ka sake ni Kabiru tunda ba fitar kashin awaki mu ka yi da kai ba, idan kuma ba ka sake ni ba to kai ba ɗan halak ba ne.”

   Salati Iyatu ta sauke tana zura mini idanu wani irin duhu ne ya rufe mini danuna jiri ya kwashe ni nayi tangal tangal zan faɗi nayi saurin dafe gini jin amon muryar kabiru.

   “Na sake ki saki biyu Ladiyo tabbas ni ɗan halak ne a cikin uwata. Ki tafi ki barni ki gani idan zan mutu, aure ne bazan fasa ba, zan yi aure na kuma ci gaba da rayuwata ki sani na haifu a cikin uwata.”

  Ihu na kurma ina dafe kaina tare da riƙo Iyatu wacce take kaka a wajen Kabiru .

    “Kabiru ka sake ni fa kace? Iyatu kina jinsa fa.”

  “Yo to dama ai mutum bai iya mugunta ba sai ya yiwa kansa, ba dai kince za ki hana ƴar wani aure ba humm!! Tabbas inda rai da rabo wata rana ɗan sarki kan iya zama sarki. Ga shi dai Allah ya yi aure da marar kwabo, ‘ya dai sai ta shigo ke kuma ya sake ki sai muga ta yadda za ki hana auren yanzu. ni cikani da ma ai idan za ka gina ramin mugunta ginasa daidai tsawonka.”

    Wani irin danasanin cakwamar kwalar rigar Kabiru nayi hawaye ya gangaro daga idanuna, sai yanzu na dawo hayyacina jin kalmar saki na ce.

    “Kabiru ka sake ni? Dan girman Allah Iyatu ki ce ya fasa wannan auren ya mayar da ni ɗakina.?”

   Cikin shewa Iyatu ta kallini tana mini kallon uku saura kwata ta ce da ni.

    “Wai ni ɗin? Na sa ya mayar da ke ɗakin ki a’a ba da ni ba sa lallen kaza.”

    “Na shiga uku.”

   Na yi maganar cikin ƙunar zuciya da baƙin ciki na kasance cikin matan da ke da mungun kishi ko kaɗan bana son ganin mace ta raɓi mijina ko da kuwa ƙanwata da muka fito ciki ɗaya, duk da mijina talaka ne wanda sai ya nemo da ƙyar muci ina matuƙar ƙaunarsa, a haka na ke haƙuri da talaucin sa ina ɗauke kaina akan duk wani abun da zai kawo saɓani gare mu, shi yasa na dage da sana’ar da zan rufawa kaina asiri sai dai ina da mugun kishin da bazan yarda mijina ya ƙara aure ba muddun ina numfashi, na gwammaci ganin mutuwata da dai na ga ranar da mjina zai mini kishiya sai ga shi yau an wayi gari ya sake ni saboda wata ina kuma numfashi zan gansa tare da wata ba ni ba, to meye amfanin alwashin da naci tabbas cakwamar kwalar mijina shine danasanina, baƙin kishina ya kaini ga danasani.

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.