Gabatarwa
Dukkan yabo ya tabbata ga Allah, ina neman taimakonKa, ina neman GafararKa, ina kuma neman tsarinKa daga sharrance-sharrancen rayukanmu da miyagun ayyukanmu. Na shaida babu abin bautawa da gaskiya sai Allah, Shi kadai wanda ba shi da abokin tarayya. Ina kuma shaida wa Annabi Muhammadu bawanSa ne, kuma manzonSa ne. Allah ya yi tsira a gare shi da alayensa da sahabbansa da wadanda suka bi su da kyakkyawan koyi har zuwa ranar kiyama.
Addu’a
Har kullum ban gajiya da yi muku addu’a iyayen kwarai, Alhaji Ashiru (Kocalla) Alhaji Haruna da, Alhaji Ashiru sauran ‘yan uwa musulmi. Ubangiji Ya haskaka muku kabarinku.
Abin Alfaharina
Mijina wanda ya zamto abin tinkahona, ina kara mika godiya ta a bisa kokarinka gare ni, ba ka taba kosawa da lamurana. Ina fatan Allah ya zama gatanka, Ya iya maka a dukkan lamuranka Abul Yusura. Ina nufin Auwal By Force Zage.
Fatan Alkhairi
Ga dukkan makarantana a duk inda suke, ina godiya da kulawarku, ina fatan Allah ya sa mu yi kyakkyawan karshe, amin.
Bugawa A Computer
Nura Sada Nasimat Kt
ABUJA
Tsarin unguwar tamkar a Turai, unguwa ce wadda karamin mai kudi ba zai taba iya mallakar muhalli a cikinta ba shahararrun masu kudi wadanda suka ci suka tada kai irin manyan ‘yan siyasa, kusoshin gwamnati, ministoci, ‘yan majalissu, sanatoci. Su ne suka yi sansani a cikin unguwar. Cikin unguwar da kewayenta ba za ka taba ganin kasa ba, kamshin unguwar kadai ma ya fita daban. Manyan gidaje masu dauke da wasu irin manyan get su suka fi yawa a nan. Kai kanka kana dosar unguwar za ka san ka zo unguwar masu gidan rana ta yadda tun daga nesa za ka hangi sojoji suna ta faman safa da marwa dauke da makamansu, kamar masu shirin fita yaki. Ko kadan babu mabukaci a cikin wannan unguwa, za ka gane hakan ne ta yadda za ka dinga ganin kaji a abin shara wadanda suka yi funfuna. Shiru-shirun unguwar ya fi komai dadada ma ‘yan cikinta. Idan kai kadai ne a gidanka sai ka mutu har ka rube babu wanda zai sani.
Akasari ‘yan cikin unguwar kansu kawai suka sani, babu wanda ya damu da shiga harkar wani. Ba kowane makoci ne ya taba ganin makocinsa ba, sabida kowanne gida garkame yake da get, tsakanin get din ma zuwa gidan sai an yi tafiya mai nisa, wanda ko da yanka ka za a yi in makogoronka zai tsago saboda ihu babu wanda zai ji ka. Akasarinsu ba su san me ake nufi da talauci ba, ba su san me ake nufi da sanyi ko zafi ba. Kullum suna cikin A.C, ba a taba dauke musu wuta, duk da suna amfani da solar ne, shirun unguwar tamkar ba a duniya ba, in ka ji hayaniya sai na motoci. Wannan kenan.
Yana zaune a babban sitroom idanunsa a kan akwatun talabijin, yadda ya ga talakawa na kukan farin ciki, tare da sanya masa albarka ya dinga jin tsigar jikinsa na tashi. Burinsa kullum ya ga ya sanya talakawa farin ciki, hakan ne kadai ke sanya shi nishadi. Daga can bayansa Hajiya Khadija ce wadda yake kira da Ummi, motsinta ya jiyo ya yi saurin mikewa ya karasa gare ta. Zai yi magana ta riga shi.
“Ka kalli yadda talakawa ke farin ciki, zuciyarsu fari kal! Deedat dina, kai ma Allah ya faranta maka”.
Ya riko hannunta.
“Ummina, duk ke ce. Komai na zama ke ce sila, ke ce ki ka dora ni a wannan turba. Na gode miki kwarai da gaske Ummina”.
Ya kwantar da kai a kafadarta. Ta shafa gashin kansa.
“Allah ya yi maka albarka”.
Komawa suka yi suka zauna, tare da sake maida hankali a kan akwatun talabijin. Daidai lokacin da wasu matasa ke rokon ya fito ya tsaya takarar kujerar gwamna.
Ummi ta dube shi, “Ko bayan raina ban amince ka tsaya takarar siyasa ba, ban ki ka yi ja-gaba gurin cicciba na gari ba har ya kai ga gaci kamar yadda ka ke yi, amma siyasa? Sam ban lamunta ba”.
Yana murmushi, “Ki kwantar da hankalinki, danki ba shi da wannan ra’ayin, burina da man a kada wannan gwamnan, kuma na ji dadi da ya fadi tun a primary election, na san gaba ma ba zai taba cin nasara ba”.
Ummi ta dinga kallonsa cike da wani irin tausayinsa.
“Ummina, kina tuna baya ko? Kada ki damu, da izinin Allah sai mun ga bayan wannan gwamnan”.
Ta dinga kada kai.
“Ka bi a hankali, ka dinga sassautawa…”
Kuka ne ke kokarin kwace mata, da sauri ta bar gurin.
*** *** ***
Gaba daya ‘yan jam’iyyar hankalinsu a tashe yake, cikin kakkausar murya Injiniya Usain yake magana.
“Ba mu san me ye dangantakanka da shi ba, mun sani ka sanshi, kai ne kadan ka san ta inda za mu gane waye shi, amma ka ki ba mu haske, yaro karami yana faman shigar mana hanci da kudundune. Ka gaya mana shi, mu batar da shege”.
Dr. Munir ya furzar da huci mai zafi, wani irin miki ne ke taso masa.
“Na kasa tantance shi din waye kun fi kowa sanin inda yake badda bami, shu’umi ne shi tamkar aljani”.
Ya sauke ajiyar zuciya, “Mu dai mu tsananta bincike”.
Ahmad Deedat kwance a kan wani faffadan gado lullube da wani lallausar bargo ruwan damusa. Idanunsa a lumshe shi ba bacci ba, ba kuma ido biyu ba, muryar Sudes cikin rairo Suratul Mulk ne ke tashi a hankali. Ya soma jin rurin wayarsa. Muskutawa ya yi cikin gyara kwanciyarsa ba shi da alamar kai wa wayar agaji har ta katse. Ba a dauki wani lokaci ba ta sake daukar ruri. Ya ja tsaki ya mike zaune, ya dubi windo yana kallon inda sojoji ke faman shawagi. Ya ja tsaki, “Idan mutuwa ta zo ba za ku hana ta dauke ni ba”. ya ce a ransa.
Ya mika hannu zai dauki wayar, ta sake katsewa. Ya maida kai ga kallon agogon da ke manne a jikin bango. Karfe shida na safe.
“AAZEEN!” ya fada a ransa.
Da sauri ya sake daukar wayar ya shiga jujjuya ta a hannunsa.
“Yau akwai rigima kenan”. Ya sake ayyanawa a ransa. Ya yi murmushi, daidai lokacin ya sake jin rurin wayar, ya yi saurin amsawa tare da karawa a kunne.
“Me ya sa ba za ka daga min waya ba”. dasasshiyar muryarta ta ratsa kunnensa, muryar da ya fi kauna fiye da kowacce murya, muryar da ta fi kowacce murya burge shi. Haka kawai sau tari yake kewar muryar bai san dalili ba idan bai ji muryar ba ya kan ji tamkar ya yi missing din wani abu mai muhimmanci.
Ta ci gaba da fada, “Jiya na kira ba ka yi picking ba, yau ma ba ka da niyya”. Ta wani takarkare.
Shi kuma sai murmushi yake, acting dinta na burge shi.
“Au ina ta magana ka kyale ni ko?”
Ya kunshe dariya a ciki.
“Ki yi hakuri kanwata, ba zan sake ba”.
Duk da bai san wace ce ita ba, amma ya gama karantar halayyarta, akwai kuruciya a tare da ita, haka ne ya sanya yake biye mata.
“Au? Ka ci gaba da shirun ko?”
“Kin ga ai na ga bai kamata ina katse ki a magana ba…”
“To gaya min”.
“Ba ni da lafiya ne shi ne na sha maganin bacci, wannan shi ne dalilin da ya hana in ji kiran wayar taki”.
Tausayinsa ta ji sosai har zuciyarta.
“Oh! I’m sorry, me ya sa ba ka sanar da ni ba?”
Ya fahimci akwai alamun rudewa a cikin maganarta.
“Ta ya ya zan sanar da ke? Kin mance dokar da ki ka saka min na cewar kada na kira, kuma da tuni sai dai ki ji na mutu, kin ga da a ce ma ina kiranki da yanzu na sanar da ke”.
“Sannu, yanzu me ke yi maka ciwo?”
Ya ce, “Ciki da zazzabi”.
Ta zaro ido kamar yana a gabanta.
“Tab! An fa ce ba a son namiji ya yi ciwon ciki”.
“Ai na ji sauki, na je kyamis…”
Ta katse shi a zabure, “Kana son mutuwa ne? Kada ka sake zuwa kyamis, asibiti za ka je a duba ka. Shi kyamis zuwa ake sayen magani, ko karbar taimakon gaggawa. Yanzu ka shirya ka je ka ji. Bara na turo maka kudi, sai ka je…”
Zai yi magana ya ji ta katse wayar.
Yana zaune a dinning room yana kallon inda Ummi da masu aikinta Dije da Dela suna ta sintiri daga kicin zuwa dinning room. In ka ga yadda ta yi kwalliya sai ka rantse wani gagarumin bikin ko taro za ta je, komai nata abin burgewa, ba ta yadda wani ya yi ma Deedat girki da duk abin da zai kai bakinsa, ba ta da yarda a kan Deedat. Ba ta lamunce kowa ya shige masa in ya wuce Salim da Sulaiman. Ita ke tsara masa komai tun yana yaro burinta ya zamo mutumin da za ta yi alfahari da shi, duk wani mai kyamarsa ya yi alfahari da shi ta koya masa dabaru, da duk wani salo, ga shi yanzu ya girma, Allah ya amsa mata dukkan addu’o’inta, ko yanzu ta koma ga Ubangiji ba za ta yi bakin ciki ba. Abin da kawai ya rage mata shi ne, ya yi aure ta ga jikanta.
Ummi ce ke wannan tunanin a takaice, kawai Deedat ya zuba mata ido, da alama ta yi nisa. Ya shafi gefen fuskarta. Ta yi firgigi tare da sauke ajiyar zuciya.
“Ummina, me ke damunki ne?”
Ta tabe baki hade da daga kafada.
“Me ko zai dame ni bayan ga ni ga ka?”
Ya yi murmushi, ya dan kurbi shayi.
Da sauri ya ajiye kofin saboda zafinsa.
“Oh God! Sannu”.
“Shi ke nan Ummi… da ma ina son zan je gurin Kabir, kuma…”
“Ya isa, ban amince ba”.
“Don Allah Ummi ki bar ni, babu abin da zai same ni”.
“Idan ka je ba da yawuna ba, in kuma ka ki ji ga hanya”.
Ya lura da yadda ranta ya baci. Ya mike ya karasa gabanta, ya dire a kan gwiwoyinsa.
“Afuwan, ba zan sake daga maganar ba”.
Ta dan saki fuska, ta sa hannunta biyu ta tallafi habarsa.
“Ka tabbata?”
Ya jinjina kai.
“That’s good! Na mance ban gaya maka ba, jibi Nabila za su dawo, Hajiya Aisha ta samu lafiya”.
Bai ce da ita komai ba, ya mike ya fice. Ta bi shi da kallo. Me yaron nan ke nufi haka? Ta koma ta jinjina kai kawai.
KANO
Tana da boyayyen kyau wanda ya sa ta ke jin cewar ita din wata ce, irin kyawunta ake kira da manyan kyau. Da an ga mutum za a ga ana da irin mugun kyau da an kura masa ido za a fahimci kyawun nasa bai wani shahara ba, hancinta bai cika tsayi ba, manyan idanunta sun taimaka gurin bayyanar kyauwnta. Ba wani haske ne can da ita ba, amma kasancewar tana hadawa da mai za ka zaci irin fara kwal ce. Ba za a saka ta cikin gajeru ba, haka ba ta da tsayi. ‘Yar kwalisa ce ta gaske, kullum cikin attach wato karin gashi, farce zako-zako tamkar rainon arna. Ba za ka taba ganinta da shiga na mutunci ba, daga doguwar riga, wadda ta bayyana surarta sai riga da wando. Akwai ta da mugun girman kai, in ta gama raina mutum kai kanka sai ka raina kanka saboda yanayin kallon wulakancin da ta ke maka, abin da ta fi tsana a rayuwarta hada hanya da talaka. Sam ba ta iya mu’amala ba, kallo daya za ka yi mata ka fahimci tantirancinta, duk girman ka idan ka shiga gonarta sai ta yaga ka. Da manyan gwasake ta ke mu’amalarta, suga Daddy da kusoshi. Tana da mugun son abin duniya, duk kuwa da su din masu shi ne, sam ba ta da godiyar Allah ko yaushe tana hangen sama ne.
Tunda ta isa ma’aikatan nasu kananun leburori ke faman kaucewa, tun daga get ake faman yi mata barka da shigowa. Kallo bai ishe su, a inda aka tanada don ajiye motoci ta yi parking daya daga cikin masu hidiman gurin ya tako da sauri zai karbi kayan hannunta. Ta dakatar da shi gurin watsa masa wani harara. Ya koma ya rakube gefe.
Ta ja tsaki ta shige. Ta tarar da ofis dinta a share, a goge, masinjanta ya shigo cikin risinawa.
“Ranki ya dade sannu da zuwa. Kina bukatar wani abin?”
Ta kai mintina biyu tana latsa waya,ita ba ta ce eh ba, ba kuma ta ce a’a ba, Bala masinja ya dinga la’antarta a zuciyarsa. Ta ja tsaki cikin daga murya.
“Wai kai Bala ko fita zan yi in bar maka ofis din, ka zo ka kafe ni da ido? Da Allah malam bace min da gani”.
Sum-sum ya mike jiki a sanyaye.
Aminu na hango Bala ya shiga tuntsira dariya.
“Yau abin a kanka ya sauka kenan?”
Cike da takaici, “Kai dai bari, insha Allah wannan la’ananniyar matar sai Allah ya kaskantar da ita, muguwa”.
“Kai ga Oga nan. Wallahi ka iya bakinka, Oga yana jinka ka zama korarre, ka san su ne masu daure mata gindi”.
Ya zo daf da su suka yi duf!
“Sannu da zuwa Oga”.
Dago musu hannu kawai ya yi, suna kallo ya shige ofis dinta.
“Tsinannu da izinin Allah wataran sai kun makale”.
Aminu ya tuntsire da dariya.