*****
“Ba aiki ya kamata ki yi ba, hutawa za ki yi, ki bar ni da wannan uwar kwiyar”.
“Babu komai Anty, kin ga idan na saka hannu sai mu fi saurin gamawa”.
“Okey, shi ke nan tunda kin dage. Ga kaya can na dauko miki ki saka, kada ki bata na jikinki”.
“To Anti”. Nurat ta fada.
Ta koma daki ta sauya kaya. Kayan sun yi mata das tamkar nata. Ba ta daura dankwali ba, ta gyara tufkar gashinta ta fito. Kicin ta nufa inda ta samu Anti Aisha da kanwarta Yusra.
Anti Aisha ta bi ta da kallo, ba ta taba ganin Nurat ba sai yau, amma jinta ta ke yi kamar wadda suka shekara da ita. Wani irin kaunarta ce ta darsu a zuciyarta. Ta sauke ajiyar zuciya.
“Kawai ki tafi da kayan, da ma ban taba saka su ba, tunani nake yi kamar sun yi min kadan shi ya sa tuntuni na ki sakawa”.
Yusra ta ce, “Wallahi kin yi kyau”.
“Yanzu ki ci gaba da aikin, zan je na yi wanka, na san suna hanya kada su zo ban shirya ba. Oga ya yi min kashedin in yi kyau sosai, kada Ogansa ya raina shi”.
“Wai Yaya Aisha waye wannan din?”
Yusra ta tambaya tana kallonta.
‘Shi din na musamman ne. Takensa shi ne, in k sanshi shi ne, idan ba ka sanshi ba, to ba shi ba ne”.
“Okey, to me hakan ke nufi?”
“Ni kaina ban sani ba, a bakin Ogana nake jin wannan kirarin, na dai san mutum ne mai kirki. Da bazarsa muke rawa, ban taba ganin mutum irinsa ba, ya fi kowa kirki…”
Ringin din wayarta ne ya katse ta. Ta zaro ido.
“Kada dai sun iso?”
Jiki na rawa ta daga wayar.
“Da fatan kun gama shirya komai?” Deeni ya tambaya ta daya bangaren.
Ta ce, “Sauran kiris”.
‘Okey, shi ke nan. Mu ma ga mu nan mun nufo gidan, abu mafi muhimmnci ki bar su Yusra su karasa aikin ki je ki yi wanka”.
“An gama ranka ya dade”.
Da gudu ta fice ta nufi bathroom.
“Tunda ki ka ga Yayata na wannan rawar kafar ba karamin kudi za ta shaka ba, Deeni yana da son abin duniya, na tabbata ba karamin samu yake a gindin wannan bakon ba. shi fa mijin Yaya idan ya raina ma kura ko kallo ba ka ishe shi ba. Yana da girman kai, ya fi mu’amala da manyan mutane…”
“Kin ga Yusra ki bar wannan gulmar mu yi kokarin gama aikin nan tukunna’.
Sun gama komai, suna jidar kayan abincin zuwa dinning room, Aisha na can daki tana shirya kanta, Nurat ta dauko jug na glass ta nufi dinning room. Ita kuma Yusra na moping din kicin. Nurat ta dukufa tana shirya dinning table suka kutso kai. Sallama suka yi gaba daya su ukun idanunsu a kanta, ba su taba ganin kyakkyawar halitta irinta ba.
Zo ka ga kunya da tashin hankali, kam! Ta kame a gurin.
“Subhanallahi! Ya Allah, na shiga uku, ta ya ya zan iya ficewa?”
Ba ta iya amsa sallamarsu ba.
Shi kam Deedat gabansa ne ya shiga bugawa.
“Ba kya jin ana sallama?” Deeni ya fada.
“Amin”. Ta ce a takaice. Da kyar ta ke daga kafafunta ko gabanta ba ta gani saboda kunya. Juyawar da ta yi Salim da Deedat suka dubi juna. Da sauri ya boye kansa da wani irin sonta da ya shiga naso a dukkan sassan jikinsa. Ita din ma duk da ba ta waye da ko su waye ba, ai hijabinta kawai ta dauka ta yi waje ba tare da ta yi sallama da su Yusra ba.
Aisha ta fita daga daki cikin kayatacciyar shigar da ta sanya ma Deeni nutsuwa. Bayan sun zazzauna, Deeni ya dube ta.
‘Waccan bakuwar muka yi?”
“Ni ma yau na fara ganinta, kawar Yusra ce. Yarinyar kirki ba ruwanta, komai nata abin burgewa ne”.
‘Yaya ban ga Nurat ba fa, ina ta shiga?” Yusra da ke kokarin shigowa ta tambaya.
“Ki duba”.
Ta ce, “Ba ta nan, daga can nake”.
“To ina ta yi?” In ji Aisha.
“Shi ya sa ban so ta fio diining ba, ba ta son mutane. Ina zuwa”. Aisha ta ce.
Daki ta koma, inda ta tarar da kayan ta zube a kan gado ta dawo gurinsu.
“Wallahi ko tafiya ta yi, hijabinta kurum ta dauka ko kayan nata ba ta canza ba”.
Yusra ta yi murmushi, “Da alamar kacibus ku ka yi da ita cikin rashin sani kuma babu hijabi a jikinta ko?”
Da sauri deeni ya kada kai.
“Tab! Yaya ai ko ke da ganin Nurat Usman a gidanki za ki rina, ita din wata iri ce, kunyarta ta yi mata yawa, ai wannan din ustaziyya ce, ni fa na yi mamakin da ta amince ta sanya wannan riga da wandon, Nana ta ce min, ko a gidansu ba ta zama babu hijabi, idan ma ba a yi sa’a ba ko gidansu Nanan ba za ta koma ba, karshenta ma tana can tana kuka”.
“To ke ba ki san gidansu ba?”
“Ina zan sani, ni da ba ‘yar gari ba? Ni ma yau darajar Nanar ba ta nan ne ya sa ta shigo gidanmu. Ni kuma na rakito ta nan”.
Salim kam hankalinsa gaba daya ya dawo kan Deedat, tsantsar sonta ya dinga hange a idanunsa. Tabbas wannan din ce ta dace da rayuwar Deedat, ita ce macen da yake mafarkin mallaka. Da alamun an tada mishi mikin da ke kwance a zuciyarsa.
Gaisuwar Aisha ce ta katse masa tunani. Hira suka shiga yi tsakaninsu ban da Deedat, ba su wani damu da hakan ba sanin cewar shi din ba mai son magana ba ne. Tashin hankalinsu daya, ya ki cin abinci sai lemo kawai da ya sha. Karshe ma mikewa ya yi.
Suka bi shi da kallo.
“Sai ina?” Deeni ya tambaya.
“Ku ba ni minti goma zan dawo”.
Bai jira amsarsu ba ya yi waje.
Duk inda yake tunanin zai ganta ya duba babu alamarta, dole ya koma gidan duk hankalinsa a tashe. Yana son zama da Yusra domin tambayar inda ta ke, to amman yana jin wani irin nauyi, ba zai iya tsayawa yana tadin budurwa da ita ba, yana jin hakan bai dace ba, ko ba ma haka ba, hakan ba girmansa ba ne.
Sai bayan magriba suka bar gidan, inda Salim ya ajiye ma Aisha dubu dari biyu gen-gen, ya bai wa Yusra dubu hamsin. Farin ciki a gurinsu tamkar za su shide.
Bayan fitarsu Yusra ta dubi Aisha.
“Kin ga Nurat ta yi ma kanta, da tuni ta samu kudaden nan”.
“Amma dai ko ‘yar dubu goma kin ba ta?”
“Tab! Wai ma, wa ya ce ta tafi? Ko sisi ba zan ba ta ba”.
“Shi ke nan zan ba ki dubu goma ki ba ta”.
“Wannan kam in ki ka ba ni zan ba ta”.
Aisha ta kai mata duka.
“Mara mutunci”.
*** *** ***
Ta rungume shi ta baya, “Daddy kana sona da yawa, ba ni da tamkarka. Ina yinka wallahi ka fidda ni kunyar kawayena, zan nuna musu taka kyautar’.
Ya mirgino da ita gabansa yana murmushi.
“Rangida zan iya yin komai domin farin cikinki. Ba ma haka na so ba”.
“Dad taho mu je ku yi sallama da su, suna daki”.
Ta janyo hannunsa. Hajiya Rahma ta kawar da kai ba ta ma san suna yi ba, ita dai ko ba komai ta rabu da kaya.
Nurat ce ta shigo, ta bi ta da kallo.
“Ina kayanki?”
“Ammi na yi kyau ko? Kwata na fada shi ne na saka kayan kawata, makociyarsu ce, ina Yayata?”
“Tana can daki ita da kawayenta’.
“Okey, bari in je na ci abinci, yunwa nake ji”.
Ta yi waje, ta bi ta da kallo.
“Aazeen ina ma za ki zama kamar Nurat?”
Ta kada kai kawai.
Washegari da sassafe su Zee suka wuce, ranar Hajiya rahma ji ta yi kamar an sauke mata dutsen dala daga kanta.
Alhaji Usman ne ya shigo sitroom yana faman cika da batsewa. Ta yi kamar ba ta ganshi ba, ya zauna daya daga cikin kujerun.
“Sun tafi hankalinki ya kwanta, ban ce zan auri daya daga cikinsu ba. Da sun ci gaba da zama ina jin sai kin kone su. Ni ban taba jin uwar da ke kishi da yaranta ba, ita kanta Aazeen kishi ki ke da ita, ko wata kyautar na yi mata sai kin nuna damuwarki. Wallahi sam ba ki da tunani”.
Ba ta so tanka mishi ba, sai dai a wannan gabar ba ta jin za ta iya yin shiru.
“Ko a tarihi ban taba jin inda aka ce ga wata uwa can na bakin ciki da abin da uba ya yi ma diyarta ba, ballantana Aazeen wadda nake jinta tamkar numfashina. Aazeen na fara samu a duniya, ina sonta fiye da komai, duk son da za ka yi mata ba za ka fi ni ba. Don haka nake kiyaye duk abin da zai rusa mata tarbiyya, idan za ka siyi duk abin da ke duniyar nan ka ba ta zan fi kowa farin ciki, amma ka dinga yin abin da addininmu ya halatta”.
“Tunda dai su din sun tafi komai ya wuce ko?” Ya fada yana kokarin matsawa jikinta.
“Ki yi hakuri, taso mu je ciki zan nuna miki wani abu”.
Shi kanshi ya yi mamakin yadda yake faman kimtsa kansa kamar wani mace, wankan shadda ya yi gizna, ash colour, hularsa ma ash, hatta takalminsa ash ne, ya feshe jiki da turare ya fito sitroom cikin kokarin gyara link din hannun rigarsa.
Maryam zaune tana kallon talabijin.
“Wow, karamin maigidan ka fa yi kyau, sai ina?”
Ya yi murmushi, “Matar Yaya yau zan tunkari mutuniyar. Yau zan yi mata zuwa na musamman”.
“Okey, kana son ka ce iyanzu ta san komai kenan?”
“Ke dai kawai ki yi min addu’a, ki bari sai na dawo mun yi maganar”.
Ya dauki key din mota ya yi waje. Ta bi shi da kallo cikin tabe baki.
Da alamar Hajiya rahma ba ta nan, hakan ya yi masa dadi, kai tsaye ya doshi bangaren Nurat.
Tana kwance a gado, bacci ta ke lakadan, iskan fanka na faman watsi da gashin kanta. Gabansa ne ya fadi, ya wani irin bugawa wani abu ya tsarga masa tun daga tsakiyar kai har zuwa yatsunsa. Duk yadda yake zana halittarta ta wuce nan, ashe dai bai ga komai ba?
Wani irin sha’awarta ya dinga shigarsa, zuciyarsa ta dinga ingiza shi da ya afka mata. Ya yi tattaki zuwa gabanta, ya dan rankwafa a kanta, wani kamshi ya shaka nan ya kara fitinuwa. Hannu ya kai zai dauke gashin da ya zubo fuskarta, ya ga ta dan motsa.
Tsam! Ya kame a tsaye, can ta kara nutsuwa cikin baccinta haka ya ba shi damar tattare gashinta yamaida shi baya. Ya dan matso da kansa daf da fuskarta zai sumbaci dan mininin bakinta. A karo na biyu ta sake motsawa, ya tuna idan ta farka ta ganshi akwai matsala. Da sauri ya fice daga dakin cike da tsananin so da sha’awarta, sai kuma ya jira ta a gurin Aazeen.
A daidai wannan okacin ta fito daga bathroom, bai san sa’ar da ya afka mata ba. sun gama shagalta da juna, gaba daya sun mance a inda suke, hankainsu ya fita a jikinsu, shi kam Zaruk ji yake yi kamar tare yake da Nurat, surarta ce ta dinga yi masa gizo.
Daga bangaren Nurat firgigit ta farka, ta dinga ji a jikinta tamkar wani abu ya faru da ita. Ta mike zaune, kamshin turaren Zaruk ta shaka. Dam! Gabanta ya buga, da sauri ta dubi jikinta, riga ce a jikinta iya gwiwa mai dan siririn hannu. Ta mike cikin sauri, hijabi ta dauko ta dora a kai ta shiga bathroom ta wanke baki. Al’adarta ce ko da baccin minti goma ta yi ba ta iya fuskantar kowa sai ta goge baki, ta dauraye fuska.
Ficewa ta yi daga dakin, kai tsaye sashen Aazeen ta nufa, duk takun da ta yi yana daidai da bugun zuciyarta. Haka kawai ta dinga jin wani tsoro na ziyartar zuciyar tata. Daf da za ta kutsa kai ciki ta dinga jin wasu irin surutai marasa kan gado, ta dan yi turus! Abu ya ki karewa kawai sai ta tura kai ciki da karfi. Gabanta ya buga, kanta ya yi wani irin sarawa yana kuma juyawa, jikinta ya hau bari. Ta yi saurin runtse idanunta ta kasa aminta da abin da ke gabanta, me ya sanya ta yi irin wannan mafarkin? Me ke faruwa da ita? Idan bacci ta ke Ubangiji Ya gaggauta farkar da ita.
Ta bude idanunta, har yanzu suna nan, wayyo Allah ba mafarki ta ke yi ba, “Allahumma ajirni fi masibati…” Ta shiga maimaitawa cikin zuciyarta.
Kunyar kanta ce ta kamata, ta juya cikin matsanancin kukan da ke son kwace mata, gudu-gudu, sauri-sauri ta nufi dakinta inda ta zube a kasa. Wani irin azababben kuka ya kace mata, wani irin tsanar Zaruk ta dinga darsuwa a zuciyarta. Tana ji a ranta ba ta taba tsanar wata halitta kamarsa ba.
Yaya Zaruk mutumin da ta ke matukar ganin mutuncinsa wanda magana ba ta cika damunsa ba, idan yana magana wani lokacin tamkar wani limami.
Ta runtse idanu, kuka ya sake kwace mata, ‘Babu kama Yaya Zaruk babu kama, waye ya san tsawon lokacin da suke aikata hakan?”
Hirarsu da Fa’iza kawarta ta fado mata, “In dai rike hannu ne ashe da kowa ya samu ciki, da shegu sun cika duniya. Ke da Allah can tsokanarki Amminki ta ke yi, kawai tana tsoratar da ke ne kawai, ba kya ganin ‘yan Indiya har rungume juna suke yi da namiji, to su me ya sa ba su taba samun cikin ba? ‘Yan matan zamanin nan iyayen shan minti duk me ya sa ba su samun ciki?”
Nurat ta ce, “ko ma me ye ni dole ne in kiyaye, mahaifiyata ce yadda uwa ta ke da girma zai iya yiwuwa idan aka rike hannun nawa in iya samun ciki”.
Ta dawo daga duniyar tunani, lokaci guda abin da ta gani ya dinga dawo mata.
“Yayata kin ci amanar Ammina, Zaruk na tsane ka, ba zan yafe maka ba”.
Takarkarewa ta yi ta turar da shi, ya zube gefe yana faman ajiye numfashi.
“Kai wai ka mance a inda muke ne, ba ka tsoron wani ya ganmu?”
Da sauri ta janyo rigar ta saka.
Ya dube ta da lumsassun idanunsa,
“Aazeen, ina son Nurat, ki taimake ni kada in rasa ta”.
Ta daure fuska tamau.
“Ba ka taba ganewa furta mata wani kalaman so zai iya nesanta mu da juna. Ka bari da zarar ta zana jarabawa sai ka yi duka daya dauka”.
‘Ba zan iya ba, ba zan taba amincewa ba. wannan karon dole ne kowa ya sani. Na gaji, ina zuwa”. Ya ce da ita ya mike.
Ta bi shi kawai da kallo.
Nurat ta gaji da kuka, idanun nan sun yi jawur har wani tasawa suka yi.
Takun tahowa ta ji, ta yi saurin kifa kai cikin filo, ga mamakinta muryar Zaruk ta ji a kanta.
‘Nurat, tashi za ki yi, ina son za mu yi wata magana da ke. Na zo ne kawai don ke, na san kina jina’.
Ji ta ke yi kamar ya watsa mata garwashi. Ya kada ya raya ko motsawa ta ki yi. Ya koma yi mata magiya tamkar dutse haka ta koma mishi, kamar zai yi kuka, tilas ya bar mata dakin, takaici bai sa ya bi ta kan Aazeen ba.
*** *** ***
“Sam-sam sonka ne ba ta yi, ta gane inda ka dosa shi ya sa ta dauki wannan matakin”.
“Ba zai taba yiwuwa ba akwai alaka mai karfi tsakanina mahaifina da nata, in na ga dama sai dai kawai ta ga an daura aure. To amma don in fita hakkinta ne ya sanya na shaida mata. Amma ita din ma…”
“Zaruk kenan, kada ka mance kamar yadda Dad ke kaunarka ita ma haka nata ke kaunarta. Ina ba ka shawara in ka ga ba ta ra’ayinka ka hakura ga mata nan da yawa?”
“Matar Yaya idan na kyale ta mutuwa zan yi, ni kaina ban san yadda nake sonta ba, wallahi dole sai na aure ta duk bala’i sai na mallake ta”.
“Uhum Zaruk kenan, shi kenan Allah ya ba ka sa’a, Ubangiji ya zaba mana abin da ya fi alkhairi”.
“Daga baya kenan, ni kam ko babu alkhairin zan aure ta, sai fa na auri Nurat. Shekara kusan goma ina gadinta, lokaci daya na fado? Ina! Allah ba zai dora mini wannan ba, ba zai taba dora min ba’.
“Shi ke nan”.
A can bedroom dinsa sambatu ya yi ta yi tamkar mahaukaci. Ya sha sigari babu adadi duk ba ta gamshe shi ba, ya bude firij ya dauki kwalbar giyar da rabonshi da ya sha ya fi wata uku, tun lokacin da ya yi ma Dad dinshi alkawari, bai ma san akwai ragowa a firij din ba sai da ya hange ta.
Kafa kai ya yi bai sauke kwalbar ba sai da ya ga babu komai a ciki, ya kwanta rigingine, Nurat ce ke masa gizo. Ya mike tsaye yana sanda wai zai kamo ta. Haka ya yi ta yi, daga karshe ya yi wani irin wawar faduwa, har sai da ya fada kan kwalbar ta fashe ta yi masa wata muguwar yanka a gefen fuska da kirji, jini ya balle.