Daidai lokacin Alhaji Aminu ya turo kofa, duk warin giya ya cika dakin, ga dansa kwance cikin jini yana faman amai. A sukwane ya karasa gare shi ya janyo shi kan cinya yana jijjiga shi. Sunan Nurat kawai yake faman kira, a rude ya kira likitansa a waya tare da yi mishi bayanin abin da ke faruwa.
“Zaruk ashe karya ka yi min, da man yaudara ta ka yi ka ce ka daina? Me ya sa?”
Kokarin kwacewa ya dinga yi daga jikinsa yana kiran sunan Nurat.
Kuka Alhaji Aminu ya saka, yadda ya ga jini ya tsananta zuba. Likita ne ya turo kofa. Shi kanshi hankalinsa ya tashi.
Ya dubi Alhaji Aminu, “Garin ya ya hakan ta faru?”
“Ban sani ba, kawai na dai ji yana ta ambatar wata Nurat”.
Likita ya sauke ajiyar zuciya.
“Ko wacce tana da alaka da shigarsa wannan yanayin”.
Allura ya yi masa ya yi dressing din raunikan, ya kuma dora masa da allurar bacci, kafin wani lokaci bacci mai karfi ya yi awon gaba da shi”.
Hajiya Amina da Maryam sun dawo daga gidan suna, suka riski mummunan labari.
“Da na san abin da zai aikata ma kansa da ban barshi shi kadai ba”.
A nan ta kwashe labarin komai ta shaida musu.
“Ban da abin Zaruk ya sani dole ma ya aure ta ko da ba ta so, da ita da Baban nata duk a hannun Alhajina suke shi ne fa karfin arzikin ba ko wannan uwar girman kai ya ce yana so dole ne ta amince, balle ita Nurat baiwar Allah, yarinyar da babu sa wa ba fitarwa”.
Yana zaune a tsakiyar gado ko a jikinsa halin da ya ganshi a ciki, ya sani hakan zai daga ma Dad hankali, ba zai bari ya rasa Nurat ba, sigarinsa ma ya ke faman zuka.
Hajiya Amina da Alhaji Aminu suka shigo dakin daidai lokacin wutar sigarin ta cimma hannunsa. Da gudu Alhaji Aminu ya zare tabar a hannunsa ya cillar a kasa hadi da mitsike ta a kasa. Suka zauna a gefe, gaba daya yanayinsa ya nuna yana cikin damuwa, ya yi ramar wuni daya.
Ya raunana murya, “Haba Zaruk har kana da damuwar da ka ke tunanin ba zan iya magance maka ba? Maryam ta gaya min komai kai ma da gangan ka tada hankali, ka sani ni da Alhaji Usman mun zamo daya babu abin da ba zai iya mallaka min ba”.
“Daddy, Nurat ba za ta so ni ba, ta daina kula ni, ba zan iya rayuwa babu ita ba, ina tsananin sonta, da ita kadai nake son rayuwa, ka taimaka kada ta guje mini”.
“Ya isa haka, na ji za ka auri Nurat, amma sai in na ga ka raba kanka da wadannan mugayen dabi’un, domin babu uban da zai so ka zama surikinsa in har ba ka daina ba, zan fita a harkarka…”
“Ban da ma abin Zaruk, ai ita din taka ce, ko da ba ta so dole ma ta so ka, ka kwantar da hankalinka in ba haka ba za ka kashe rayuwarka a banza, kana ji kana gani wani nan zai aure ta”.
“Mommy na yi muku alkawarin na daina har abada, ku yi hakuri”.
Suna zaune a falo dukkansu, kallon suke yi, hankalin Alhaji Usman ya karkata ga Nuratm ya fahimci kamar akwai abin da ke damunta. Kallon ta ke yi amma tunaninta na wani guri.
“Nurat wai me yake damunki?”
Ta tilasta wa kanta sakin murmushi, wato yake.
“Dad me ka gani? Lafiya ta kalau”.
“Tunda na dawo na ganta a haka, na tambaya ta ce kanta ne ke ciwo”. Hajiya rahma ta fada.
“Ai na sha magani, ya daina ciwo”.
Aazeen ta dan dube ta, ta kawar da kai, don idan tana kallon program din Ahmad ba ta son abin da zai katse ta, tana tunanin kamar za ta samu hasken inda za ta same shi.
Wayar Alhaji Usman ta shiga ruri, ya daga.
‘Subhanallahi, yaushe? Okey za mu shigo gobe, Allah ya ba shi lafiya”.
Gaba daya hankalinsu ya koma kansa. Ya ajiye wayar cikin dubansu.
“Lafiya kuwa?” Hajiya Rahma ta tambaya.
“Wai Zaruk ne ya yi hatsari”.
Aazeen ta ji wani shook, “Daddy dazun fa ya bar gidan nan?”
Ta iya yuwuwa ko a hanyar komawarsa ne ya gamu da tsautsayi”.
Duk ta gigice.
“Dad yana asibiti ne?”
“A’a yana gida”.
“Allah Sarki Zaruk”.
Ta wutsiyar ido Nurat ke duban Aazeen, ji ta ke yi kamar ta shake ta, ta ja tsaki a zuciyarta, dole ta damu tunda abokin fasikancinta ne.
‘Idan Allah ya kai mu gobe, sai ku je gaba daya”.
“Ni dai ba za ni ba, gobe wuni za mu yi a school”.
“Karya ki ke yi, ba ki isa ba, wallahi sai kin je, mara mutunci”.
Yadda ta hayayyako mata ne ya sanya ta tsuke baki.
*** *** ***
Alhaji Usman ya nuna farin cikinsa sosai, “Ban da abinka Alhaji Aminu, kai fa me iya daukar Nurat ne ka bada aurenta, ballantana yarona ne mai sonta”.
“Eh na na sani, amma duk da haka ina son ka ji ra’ayin Nurat”.
“Kada ka damu, ban da lalacewar zamani, auren fari iyaye ne ke sama wa ‘yarsu miji. In dai Nurat ce kada ya damu an gama, kawai bari zai yi ta karasa karatu, lokacin ta kara tasawa, don ita din har yanzu akwai kuruciya a tattare da ita, shekara sha shida”.
“Gaskiya ne”.
Duk wannan hirar a ofis din Alhaji Aminu ake yinta.
‘Yanzu ya jikin nasa?”
“Da sauki”.
“Yanzu na barsu sun tafi duba shi dukkansu”.
Sun zube a sitroom, ita kam Aazeen har ta isa dakin Zaruk, Hajiya Rahma suna gaisawa da Hajiya Amina da tambayar yadda mai jiki ya kara ji, hankalin Hajiya Amina na ga Nurat, tana mamakin me Zaruk zai yi da wannan tatsitsiyar yarinyar, ina ma a ce ta dan fi haka? Babu matar da ba za ta so Nurat ta zame mata suruka ba, duk dabi’unta abin so ne, kunya, biyayya, kawaici da ibada. Nan-nan ta dinga yi da ita, ta so su dan tattauna maganar da Hajiya Rahma sai dai ta ga alamar kamar ita din ba ta san komai a kan zancen ba.
“Ya aka yi na ganki ke daya?”
Cike da jimami ta ke dubansa.
“Dukkanmu muka zo, to ina ki ka baro Nurat?”
“Tana can sitroom”.
Ya dan yi shiru, zuwa wani loakci ya koma ya numfasa, “Aazeen, na karaya, kamar Nurat ba za ta so ni ba”.
Ta dan murmusa, “Ka daina shakka Zaruk, babu macen da za ta ganka ba ta yi fatan ta mallake ka ba”.
“Ki gaya min me zan yi ta so ni?”
Lakuce masa hanci ta yi.
“Dube shi don Allah, duk karamar yarinya ta gama rikita shi’.
“Don ba ki san yadda nake ji ba ne”.
“Ta ya za a yi na ji? Kai ma ka ne ka dora ma kanka,. Babbar soyayyata ita ce in gan ni da kudi. Duk lokacin da na ga account dina ya soma kasa a nan za ka ga tashin hankalina”.
“ba za ki gane ba, yanzu dai ya za a yi ki iya turo min ita?”
“Korata ka ke son yi kenan ko? Shi kenan bari na turo maka ita”.
Ta mike ta yi waje.
“Wai ke ba dubiya ki ka zo ba ne, kin wani kime a nan?”
Ta daure fuska, har kullum gani ta ke duk lokacin da suka kebance da Zaruk din abin da ta gani shi ne suke yi.
“Tare za mu shiga da Ammina”.
“Tashi ki shiga, ga ni nan”.
Ta mike cike da damuwa, ko kadan ba ta son ganin fuskarsa, kullum kara tsanarsa ta ke.
Ta dade tsaye a bakin kofar, sai da ta ji motsi kamar za a taho ta yi saurin ture kofar ta shiga hade da sallama.
Yana kwance dafe da gurin ciwonsa, a daidai wannan lokacin zogin ciwon ya addabe shi. Kasa karasawa ta yi ta tsaya a dan nesa da shi, ko son kallonsa ba ta yi.
Yunkurawa ya yi ya mike zaune cikin dubanta.
“Kanwata ga kujera ki zauna mana”.
Ta yi yadda ya ce kanta a kasa.
“Sannu, ina wuni? Ya jiki?” Duk ta fada a lokaci daya.
“Sai ki ka ji mummunan labari ko?”
Kala ba ta ce masa ba.
“Yau babu makaranta? Ammi tana sitroom?”
Haka ya yi ta soki burutsunsa ya kosa da yanayinta, ya kafe ta da ido.
“Kanwata kin canza, gaya min me ya sa ki yin shiru?”
Nan ma babu amsa, tilas ya tsuke baki cike da tunani barkatai. Ya zai yi ta fahimci yana sonta? Ya zai yi ta fahimci ita ce farin cikinsa?
Zumbur ya ga ta mike, kasa magana ya yi kawai ya bi ta da ido. Me ya sa ta daina sakin jiki da shi a daidai lokacin da ya fi bukatar haka? Me yake faruwa haka?
“Ya Allah ka nuna mini hanyar da za ta fahimci ita kadai nake so”. Ya ayyana a zuciyarsa.
“Nurat tafiya za ki yi?”
“Sallah zan yi”.
Ba ta jira jin me zai sake cewa ba ta yi saurin ficewa.
Bayan ta idar da sallah tana sani ta mike a kan doguwar kujera da fadin kanta ne ke ciwo.
Ba su bar gidan ba, sai bayan sallar magriba.
*** *** ***
Alhaji Usman ya shigo gidan cike da farin ciki.
“Daddy ta samu kenan?”
“Rangida ina cike da farin ciki, burina kullum zumuncinmu ya dore da Alhaji Aminu. Yanzu kam za mu zama daya, don ko har zuri’a za mu hada, kin ga kenan zai sake sakin jiki, babu maganar kyashi a tsakaninmu”.
Hankalin Ammi ya tattara a kansa, tana son jin inda ya dosa.
“Daddy ka batar da ni, sam ban gane ba”.
Ya numfasa, “Ina Nurat?”
“Tunda muka dawo ta ke kwance”. Aazeen ta fada.
“To lafiya kuwa?”
“Kanta ne ke ciwo, amma ta sha magani tun a gidan su Zaruk”.
“Ok, to shi ke nan Allah ya sauwake”.
“Dad ina jinka”.
“Mutuminki Zaruk ashe duk wannan abin wai Nurat yake so?”
Aazeen ta yi tsalle ta dire, har tana guda.
“Dad dole ka yi farin ciki”.
“Allah dai ya sa Nurat ta amince da shi”. Ammi ta fada tana kawar da kai.
“Duk wani abu da na tsara a gidan nan ke ce ke rusawa, an gaya miki ina son jin ra’ayinta ne? to bari ki ji, ko tana so ko ba ta so Zaruk shi ne mijinta. Ni ne na haifi Nurat ba ita ta haife ni ba, ina da ikon ba ta duk wanda na yi ra’ayi kin gane?”
Ya tashi ya shige sashensa ransa a matukar bace.
Duk jikinta ya yi sanyi, ta yi da ta sanin ba ta yi magana ba.
“Ammi, Daddy yana da gaskiya fa. Ai ita Nurat ba ta da wani ra’ayi, kawai ki sanya masa ido, don ni ban ga aibun Yaya Zaruk ba, sai dai in ke din ce ba kya son ta aure shi’.
Ita ma ficewa ta yi ta barta zaune a gurin kikam kamar an dasa ta.
Tun daga farko har karshe Nurat ta ji hirar tasu. Kifa kai ta yi a filo tana faman gursheken kuka. A haka Ammi ta riske ta, zama ta yi a gefenta, ta ma rasa ta ina za ta fara. Ita kanta ba ta so hakan ba, ba wai don ba ta kaunar aurensu ba, sai dai tana ganin nawa Nurat din ta ke da za a yi zancen aurar da ita yanzu? Ban da ma ta fara makaranta da wuri bai fi a ce tana J.S 3 ba.
Hannu ta sa tana shafa bayanta.
“Me ye na kuka Nurat? Fata za mu yi Allah ya sa haka ne ya fi alkhairi. Shi din mutumin kirki ne, Yaya yake a gare ki”.
Ta dago kai idanunta na tsiyayar da kwalla.
“Ammi ki taimake ni, wallahi bana son auren nan. Ammi, Dad har ya gaji da ni ne da zai aurar da ni? Me ya sa ba za a yi wa Yaya Aazeen ba? ta fi ni girma, ta gama karatu. Ta fi ni cancanta, don Allah ki taimake ni ki fahimtar da shi”.
Ta kai hannu tana share mata kwallan.
“Shi ke nan, zan yi hakan. Amma sai na ga kin cire damuwa a ranki kin ji. Yanzu tashi ki je ki yi wanka ki ci abinci”.
Ta mike ta yi waje, Ammi ta bi ta da kallo, gaba daya tausayinta ta ke ji.
Babu kunya ya saka wa Abbansa rigimar ba zai iya jira zuwa wani lokaci ba.
Alhaji Aminu mamakin Zaruk yake yi.
“Ka shaida mini tun tana kankanuwarta ka ke sonta, ka duba ka ga shekarun da ka diba, don ka jira shekara daya ai ba zai cutar da kai da komai ba…”
“Abbana ba zan iya ba. ina sonta kamar raina, ba zan iya ba. Ji nake kamar zan mace, Dad ina son na yi rayuwa da ita kafin in mutu. Don Allah ka saka baki na sani muddin ka ce ba ka amince ta karasa karatunta a gidansu ba zai amince. Abba kai ne fa komai nasa, da taimakonka yake samun komai’.
Daga masa hannu ya yi.
“Kada in sake jin makamancin wannan zancen a bakinka”.
“To Dad na ji, ba zan sake ba. amma ka duba, na amince ta karasa karatun a gidana”.
“Oh God, shin Zaruk ba ka san a gaban wa ka ke magana ba? ina kunyarka ta ke ne? ni ba zan yi musu dole ba, idan auren ka matsu da shi ka nemi wata cikin sati biyu zan aura maka ita. Amma ba za ka sanya ni in takura bayin Allah a kan son ranka ba”.
Ya mike a fusace ya yi waje.
Zaruk ya mike ya shiga sintiri, wani irin son Nurat na ratsa dukkan sassan jikinsa. Fuu! Ya yi waje da nufin ya koma gurin Abban nasa ya sanya masa kuka, kila ya gane abin da yake ji.
Sai dai yana sa kai ya ji tashin motarsa, ya juya a zabure zai koma ciki suka yi arba da Ummansa. Kallonsa ta ke a tsorace.
“Ciwon ne ya motsa?”
“Umma, Abba ne, ba ya son farin cikina”.
Kamo hannunshi ta yi, ba su zame ko’ina ba sai sitroom,. Ta zaunar da shi a kan kujera, ta soma magana cikin kafe shi da ido.
“Tunda ka furta kana son Nurat, ba ta da miji sai kai. Me ya sa ba za ka kwantar da hankalinka ba?”
“Oh Umma, me ya sa ba kwa ganewa? Nurat mace ce, kuma mai matukar kyau. Tana da dabi’u masu kyau, a yanzu haka tana da masu sonta da yawa, wataran za su hure mata kunne, za ta juya min baya… Umma ta ma fara yanzu haka Nurat ta daina kula ni, ba ta son ganina. Ina ganin kiyayyata kwance a fuskarta…”
“Ka ga Zaruk, kai ma ka riga ka sani aurenka da ita tilas ne, ko da tana so ko ba ta so. Na sani mahaifinka ya fi ka son wannan auren shi ya sa nake son ka nutsu”.
“Zan yi haka, amman sai dai ta dawo gidan nan, inyaso ni sai na dinga kai ta makaranta”.
“Haba Zaruk, ina ka taba ganin an yi haka? Gaskiya ba zai yiwu ba”.
Ya mike a fusace.
“Umma, ke ma ba za ki fahimce ni ba ko? Shi ke nan”. Ya juya ya koma ciki.