Aazeen tunda ake wannan abu ba ta dora ido a kan Nurat ba, kwana uku kenan ba ta zama a gida saboda binciken inda za ta samu Ahmad Deedat. Kudi ta ke ta faman kashewa har da masu bincike a yanar gizo, wasu ma karya suke yi mata da cewar sun sanshi don kawai su karbi kudi. Duk kudin kuma da ta ke kashewa ko a jikinta, kullum gani ta ke yi wataran za ta fanshe, ba ta fidda tsammanin cewar shi din zai zamo nata ba.
Yau karfe hudu ta dawo gida, kai tsaye ta fada bathroom ta yi wanka, riga da wando ta saka marasa nauyi, ta mike a kan gado, ta janyo waya. Wasu rubutukan batsa ta ke karantawa, lokaci daya ta ji kewar Zaruk, tunda ya kwallafa rikicin son Nurat ba shi da lokacinta, ita din in ba shi ba ba ta taba ganewa, ya dora ta a kan salon da ba ta iya hakurcewa da shi, dole ne ta yi wani abu a kan lamarin nan ko don ya samu nutsuwa. Za ta je ta samu Nurat, za ta yi mata wayo.
Ta shigo dakin, a bakin gado ta same ta a zaune tana ta fushi. Ta zo ta zauna a kusa da ita ta sa hannu ta kamo nata, ta kira sunanta. Ba ta amsa ba sai ma kawar da fuska da ta yi, ta soma magana.
“Kanwata kin ba ni kunya, anya kuwa Nurat dina ce kuwa? Ni dai na san tawa Nurat din mai biyayya ba ta tsallake abin da family dinta suka gindaya mata, amma yanzu duk ta sauya, me ya sa?”
Ta saki hannun nata ta kamo habarta.
“Gaya min ko akwai wani a cikin zuciyarki?”
Da sauri Nurat ta kada kai, da ido taf kwalla.
“Kullum kina yi min wa’azi ta ya ya mai dokar bacci zai buge da gyangyadi? Kin ga ke fa saukakkiya ce ga hadda a kanki, duk wasu littattafan addini suna kanki, kin kuma san hukuncin mutumin da bai bi iyayenshi ba, kin san irinku Allah ya fi kama ku da hujja”.
Wasu siraran hawaye suka biyo kuncinta, lallai wannan ‘yar rainin hankali ce. Ta fada a ranta.
“Ni bana sonsa. Ban taba sonsa ba”.
Ta kai hannu fuskarta tana share mata kwalla.
“Kin ga in dai wannan ne ta zo gidan sauki. Ke da ma ba ki san me ye so ba? Babu kowa a zuciyarki, zai koya miki yadda za ki so shi kin ji”.
Ta kama kumatunta ta ja.
“Yauwa kanwata, small”.
Maimakon murmushin sai ta rushe da wani sabon kukan, cikin shesshekar kuka, “Yaya Aazeen ai kin fi ni bukatar aure, amma ni me na yi wa Dad da yake son dauke ni a gidan nan? Ni ba zan iya ba”.
“Ni ma ina son ki yi aure ba Dad kadai ba Nurat, ina kaunarki, ina tsoro kada ki riski kanki a rayuwa irin wadda nake ciki. Yadda Ammi ta ba ki tarbiyya ina son ki dora duk inda ki ka shiga a yi alfahari da ke…”
“Yaya shi din ai ba na gari ba ne”.
Ta katse ta da fadin haka.
“Wa ya gaya miki?” Ta tambaya cikin faduwar gaba.
Shiru Nurat ta yi.
“Ni kam ban ga aibunsa ba, Zaruk dan asali, ga shi mai kyau. Za ki yi alfahari da shi”.
Zumbur ta mike tsaye.
“Da an yi magana ki ce kyau, shi kyau ba abu ne mai dorewa ba, ai ba a taba gama wa dan Adam halitta har sai ya koma ga Ubangijinsa. Halayyar Yaya Zaruk nan gaba zai iya tsintarsa a kowane yanayi, ina da yakini Allah ba zai dora kaddarar aurensa ba domin an tsarkake kaina”.
Ya dace a ce Aazeen ta gano inda Nurat ta dosa a maganganunta, sai dai ba ta gane komai ba. Mikewa ta yi.
“Shi ke nan, ni ma idan ki ka amince da Zaruk zai auri wannan Adamun zan yi duk yadda ki ke so, me ki ka ce? Ba kin ce kin yi masa alkawari ba?”
A hankali ta jinjina kai.
“Zauna, kirawo min shi, ina son ya zo in ganshi”.
Ta dube ta don gaskata abin da ta ke fadi.
“Yayata da gaske ki ke yi?”
“Mamaki zan ba ki. Zan yi komai don dorar da farin cikin kanwata”.
Take suka shiga kiran layinsa, sai dai an yi rashin sa’a wayar tasa na kashe. Dadi ne ya kama Nurat, a tunaninta wayo za ta yi wa Aazeen, ta sani in ta ganshi za ta iya sonsa, yayin da ita ma Aazeen ke murmushin mugunta, tana jin cewar dabararta ta yi.
Sun tsayar cewar duk lokacin da ya kunna wayarsa za su kira shi.
Hankalin Alhaji Usman ya kai kololuwa gurin tashi a kan abin da Alhaji Aminu ya zo masa da shi a kan Nurat, ya sani rashin amincewarsa zai iya haifar da komai, yana tausayin Nurat, ya sani kawai son rai zai nuna, bai dace a ce ya aurar da ita nan kusa ba.
Alhaji Aminu yana da kirki, ya taka rawar gani a rayuwarsa, shi ne ya koya mishi yadda zai dinga juya kudi, shi ya fito da shi a idon duniya har aka sanshi.
Alhaji Aminu ya fi karfin komai a gurinsa, akwai kunya in har ya juya wa bukatarsa baya, ya yi masa halacci da yawa. Yanzu ne lokacin da ya kamata ya rama masa, don haka ya kudiri niyar kyautatawa Nurat ko don ya shawo kanta, don haka yau bai dawo gida ba sai da ya yi mata siyayyar kayan kwalliya, kayan sawa har da sabuwar waya.
Lokacin da Hajiya Rahma ta shigo dakin, ya lura da yadda ta rame, tausayinta ya kama shi. Ya kai hannu ya janyo ta jikinsa, yana son Rahma tamkar ransa, in ban da fitina irin ta zamani mutumin da yake da kamar Rahma ya gama samun arzikin duniya, sautari in yana bakanta mata rai ya kan ji ya tsani kansa. Ta nuna mishi kololuwar so, ta rabu da komai da kowa saboda shi. Me ya sa shaidan ke hilatarsa haka?
Sakin baki ta yi tana dubansa, ya dan numfasa, idanunsa a kanta.
“Kin tsane ni ko?”
Da sauri ta kada kai.
“Me ya sa zan tsani mijina uban yarana?”
Ya sauke ajiyar zuciya.
“Na sani ban kyauta muku ba ke da Nurat, ni kaina na shiga tsaka mai wuya ne, babu abin da Alhaji Usman zai iya nema in hana shi, idan na juya mishi baya ma duniya za ta zage ni, danginsa za su yi mishi dariya. Kuma ni ban ga aibun shi Zaruk din ba”.
Idanunta fal kwalla.
“Ai ni ban ce komai ba, Nurat ‘yarka ce, ka fi kowa iko da ita. Ina fatan Allah ya sa haka ne ya fi alheri”.
Ya sake shiga jikinta yana zargin kansa da abubuwa da dama.
“Yauwa Rahmar Allah, haka nake so. Yanzu ki turo min ita”.
Ta mike jiki a sanyaye, yadda ta samu suna hira da Aazeen har da dariya ya sanya ta dan ji sanyi a ranta.
“Alhaji na kiranki”. Ta ce da ita.
Tunda ta zauna yake ta rarrashi, amma zuciyar nan tamkar rodi, musamman da ta fahimci yadda yake kokarin sai ya cusa mata son Zaruk ta karfin tsiya. Ta yadda yake ta faman yabon Zaruk, yana kururuta dacen da ta yi, da fadin jaruntarsa, son mutanensa ga addini da taimakon marasa karfi.
Ya dora da cewar, “Ki fidda ni kunya, ban taba neman abu a gurinki ba Nurat, yau na zo da kokon barata, kada ki zubar min da mutuncina, ki rufa min asiri”.
Ba ta ji dadin yadda Dad ke rokonta ba, tamkar zai yi kuka.
“Dad na amince, na yarda Dad. Ka daina rokona, kai mahaifina ne, za ka iya yin duk yadda ka so da ni. Zan aure shi ka bada aurena a duk lokacin da ka so, ba zan musa ba”.
Dadi ya kama shi, ya sani an wuce gurin, ya gama sanin ‘yarsa kaifi daya ce ba ta magana biyu, yadda ka san babbar mace.
Yake ta ke yi yadda ta ga mahaifin nata na ta rawar jiki, yadda ya nuna farin cikinsa idanunta ke kokarin zubda kwalla. Cikin dabara ta goge su ta sani zai iya tilasta mata ta aure shi, amma ba za a tilasta mata ta so shi ba. shi kenan ba ita babu wani farin ciki a duniyar nan?
Ta katse tunaninta a daidai lokacin da ya nuna mata kayayyakin da ya siya mata. Ya dauko waya ya mika mata, da cajinta full har ma an dora layi a kai. Yadda ya santa da son waya tun tana karamarta, ya yi zaton za ta nuna farin ciki, karba kawai ta yi kamar ba ta so, haka ne ya tabbatar masa cewar ba ta son Zaruk.
“Na saka miki lambata da ta Amminku, ki tashi ki je, Allah ya yi miki albarka”.
Ta kwashi kayan ta yi waje.
*** *** ***
Rashin ganin Ummita a bakin get ya sanya gabanshi bugawa. Ba ta kin tsayawa tarbarsa, duk lokacin da zai dawo daga tafiya sai in har ya yi mata laifi ko da ba ta da lafiya yana ce mata ga shi nan ya kusa karasowa ta ke cin dako a bakin get, duk ruwa duk sanyi, duk iska.
Maigadi ya yi saurin bude mishi murfin mota.
‘Sannu da dawowa yallabai”.
“Yauwa Adamu, yau kuma lafiya ban ga Ummina ba?”
“Lafiya kalau”.
Mamai ya kara kama shi.
“Adamu gaya min gaskiya”.
“Da gaske nake Yallabai, yanzu haka daga cikin gida nake”.
“Ok”. Ya ce.
Bude mishi but ya yi ya tafi ya barshi a gurin yana fara jidar kaya.
Ko da ya isa ciki bai ga alamar an shirya zuwansa ba, sabanin da da ya shigo zai dinga jin kamshin girkin tarbarsa, an cika teburi da kayan abinci kala-kala, yau ga shi wayam! Jikinsa ya yi sanyi, cikin rashin kuzari ya nufi dakinta.
Tana zaune a kujerar roba, da asuwaki a hannu, fuskar nan a kirne. Ya zauna a sanyaye.
“Ummita, yunwa nake ji, ban ga kin shirya min komai ba, bayan kin riga kin sani duk lokacin da zan dawo gida bana iya karyawa a ko’ina”.
Ta ajiye asuwakin cikin sake daure fuska.
“Daga yanzu na daina, kuma kai nake jira yau zan bar gidan nan”.
Bai san lokacin da ya dire gwiwoyinsa a gabanta ba, ya lura babu alamar wasa a maganarta.
“Ummita me na yi? Gaya min, ba zan jure fushinki ba. Kada ki yi min haka”.
“Da gaske nake yi, yau zan bar maka gida, ai ni ban san haka kudi ke sanya izza ba, ban san haka kudi ke sanyawa a daina girmama na gaba ba”.
“Wayyo Ummita, ya isa haka. Yi sauri ki gaya min abin da ki ke so na yi, in gaggauta yi”.
“Ka fi kowa sanin abin da nake so’.
“Ummita a tunanina ina yin duk abin da ki ke so, ki ka umarce ni tun ina karami. Kin tarbiyyantar da ni, kin nuna min yadda zan kyautata wa marasa karfi, rayuwata gaba daya ta tafi ne a taimakon miskinai. Na kan ajiye bukatata na yi tasu Ummita, arzikina gaba daya ya zamo ba nawa ba, na gina asibitoci saboda talaka ya ji sauki. Na gina makarantu saboda su. Na gina rayuwar mutane da dama duk domin su ma su ji cewar mutane ne, kin ce in boye kaina saboda kada yabon jama’a ya haifar min da girman kai duka na yi. Yanzu me ye ya rage? Me ye ban yi ba?”
Ya karasa maganar a raunane.
“Duka ka zubar da ladarka. Auren Nabila shi ne ya fiye min dukkan komai, wallahi idan Nabila ta mutu ta sanadiyyarka iyayenta da ni ba za mu yafe maka ba”.
A rude ya ce, “Tana ina? Me ke faruwa da ita?”
“Tana asibiti babu yadda ta ke. Wallahi kai kam Babana ba ka da imani, me ye laifin Nabila?”
Ya kamo hannunta ya rike.
“Ki yi hakuri komai zai yi daidai, bari in je asibitin idan na dawo za mu yi magana”.
“Ka ga na gaji da karairayinka babu abin da zan ji daga gare ka, na gaya maka ba za ka same ni ba”.
“No kada ki yi min haka, na yi miki alkawari za mu sasanta ki ba ni lokaci in dawo ko kuma in zauna mu gama magana sai in tafi”.
“Shi ke nan, je ka zan jirayi dawowarka”.
Receiption din cike dangin Nabila ganinsa ya sanya kowa mikewa, don nuna girmamawa a gare shi. Haka ya dinga mika hannu ga masu kokarin durkusa masa. Wani abin takaici har da tsoffi, arziki kan sanya rashin gane masoyin kwarai.
Abdul babban yayanta yana nan zaune sai faman cika da batsewa yake, yana kallon Babansu na zungurinsa a kan ya je ya kwashi gaisuwa da kansa ya karasa ya mika masa hannu. Da kyar Abdul ya mika nasa, nuna masa dakin da ta ke suka yi.
Likitoci biyu tsaye a kanta, daya na kokarin dora mata drip. Ganinsa ya sa su ma suka gaggauwa abin da suke yi, bayan sun gaisa duka suka yi waje, da alamar ba ta ji shigowarsa ba, kamshin turarensa ta shaka. Ba ta taba jin irin wannan kamshin a jikin kowa ba in ba shi ba.
Tana kokarin juyowa muryarsa ta ratsa dodon kunnenta. Ji ta yi tamkar a mafarki, kokarin mikewa ta yi.
“No Nabila, ki bi a hankali, kin ga ba ki da lafiya, kin ji?”
Wani irin dadi ya kama ta, ta dinga jin kamar ta rungume shi.
“Yaya Deedat ka dawo?”
Ya jinjina kai, tausayinta ya dinga shigarshi ganin yadda ta rame, idanunta sun fada loko.
“Kanwata me ke damunki haka?”
Idanunta fal kwalla ta ji kamar ya yi mata fami.
“Yaya Abdul ya ce na hakura da kai ba aurena za ka yi ba, ba ka sona, da gaske yake yi kai ka ce da shi ba ka sona?”
“In ji wa ya ce miki bana sonki? Kin taba jin mutum ya ki kanwarsa?”
“Yayana na gode, kuma ina sonka. Ban taba son wani abu kamarka ba. Ina matukar sonka, yanzu ka dawo ne mu yi aure ko?”
Ta tambaya cikin tsira mishi ido.
“Yaya Deedat ba haka ba ne?” Ta fada daidai lokacin da ta dora hannunta a kan nashi.
“Kin ga ki bari ki kara samun sauki sai mu yi maganar, kin ji?”
“Ba zan warke ba, ba zan taba warkewa ba in har Allah zai nuna min ranar da za ka ki aurena gwara ya dauki raina, ba zan jure ganinka alhalin ba ka zamo nawa ba”.
Cikin dabara ya zare hannunsa daga cikin nata. Ta sani kokarin ficewa yake yi.
Ta yi saurin zare drip din da ke hannunta, sai ga jini. Ya yi gaggawar gutsuro auduga ya danne gurin jinin ba tare da ya dauke hannun nasa ba. Haka ya fi komai yi mata dadi, sai ta ji ina ma su dauwama a haka? Tsananin kallon da ta ke yi masa, har ya kufula ba ya son mace mara kunya. Duk macen da ke tsura wa namiji ido haka, yana yi mata kallon mara kamun kai.
Lokaci daya ya ji yana jin haushinta, daga bangarenta ji ta ke yi tana kara sonsa. Tana jin ya fi kowa idan ta tuno da shi ko da ba ya nan nishadi ta ke ji. Ko kallonta ya yi sai tsigar jikinta ta tashi.
“Yaya Deedat bana son wannan shirun, don Allah ka ce wani abu”.
Ganin jinin hannunta ya tsagaita ya sanya shi dauke hannunsa.
“Tafiya zan yi Nabila, zan dawo kin ji”.
“Ba za ka tafi ba, ka gaya mini yaushe ne za a yi auren nan, ka ga kowa fushi yake yi da kai. Kowa haushinka ya ke ji, Ummita, Yaya Abdul, Ummata da kowa”.
Ya yi saurin katse ta.
“Ba zan tsallake lokacina ba, duk kun mance da cewar shi aure lokaci ne, da zarar Allah ya kawo lokacin komai sai ya zamo labari”.
Kalamansa sun fusatata, ta dinga jin kamar ya gama raina mata hankali. Idanunta suka juya.
“Da haka ka ke fakewa”.
Cikin daga murya ta dinga magana, ta ci gaba da fadin, “Komai sai ka ce Allah, ni na gaji! Na gaji da wannan karairayin naka”.
Yana son yin magana ta ki ba shi dama.
‘Ba zan saurare ka ba, komai ya zo karshe, ka fita ka je, na hakura, inyaso in mutu’.
Tausayinta ya sake mamaye zuciyarsa, yana cikin yanayin da ta ke ciki. Yadda yake ji ya ninka nata, inda zai iya da ya hakura da ita, sai dai halayyarta ya sanya shi yake kyamarta, ya so ya aure ta duk da cewar bai taba jin sonta ba, amma gurbataccen halinta ba su barshi ba. yana son ya yi aure, ya hayayyafa yana son yaransa su kasance a karkashin uwa ta gari. Auren Nabila zai rusa masa dukkan mafarkinsa, yana da burin auren mace daya, muddin ya auri Nabila yana da tabbacin tilas nan gaba sai ya sake aure. Zai auri Nabila ne alhalin ya auri wata, zai aure ta ne da sharadin ba zai haihu da ita ba, abin da ya san ko a mafarki ba zai yiwu ba.