*****
“Ya aka yi haka ta faru? Ta ya ya?”
Ya dago kai, maganarshi da kyar ta ke fita.
“Wacce nake matukar kauna, wadda sonta ya zame min tamkar ciwo da wadda nake matukar kauna, na shaku da ita, wadda ita kadai nake ganin mutunci, wadda nake jin dukka dabi’unta babu na yadawa, wadda na yi hakurin zan je gare ta ko da bana sonta zan iya aurenta don kwadayin halayenta, sai ga shi ita ce ta dunkule ta zamo abu daya, ita ce! Ita ce ke kokarin kyautar da zuciyarta. Salim na rasa ya zan yi? Ta lalata komai, ban ga ta inda komai zai daidaita ba, yayarta ce Aazeen uwarsu daya ubansu daya, ba ni da dama, ta lalata komai”.
Salim shi kanshi a cikin rudu yake.
“Ina ganin nidan muka bi komai a sannu komai zai zo mana cikin sauki”.
Kallonsa ya yi da jajayen idonsa, ya ce, “Bana tunaninhaka, ba zan taba iya juya ra’ayinta ba”.
“No, kada ka karaya za ka iya, za ka jefi tsuntsu biyu da dutse daya. Kayi kokarin jan Nurat a jikinka, kai da kanka za ka koya mata sonka, idan ka tabbatar da ta shaku da kai, ka tabbatar da soyayyarka ta ratsa ta sai mu samo wani plan. Da farko ka fito da soyayyarka sosai, ina nufin ka nuna wa Aazeen soyayya. A nan ne za ka samu damar shige wa Nurat”.
“Ta ya ya zan iya haka din?”
“Dole ne ka danne zuciyarka in har ba so ka ke ka yi biyu babu ba, ba zan iya ba ka kyale ni”.
Juyawa ya yi ya fice, kawai Salim ya bi shi da kallo.
“Dole za ka bi hanyar nan duk taurin kanka ba ka da mafitar da ya wuce wannan”.
Daga daya bangaren gaba daya Deedat ya takure kansa ya kasa sukuni, kullum cikin tunanin mafita yake. Bai taba sanin yana matukar son Nurat ba sai wannan lokacin.
Kwanaki biyar yana kokarin danne sonta, yana kokarin mantar da zuciyarsa, ita yana son ta karfin tsiya ya zare ta a ransa, sai dai abun ya ci tura gaba daya ya kashe wayoyinsa.
Ummita har ta gaji da nemansa, hankalinta ya kai kololuwa kamar za ta yi hauka, duk inda ta ke tunanin za ta samu labarinsa ta rasa, ta yi kuka har ta gaji ta gama karaya, dole ta koma ga Allah, sallar dare, lazimi babu adadi, mafarkan da ta dinga yi nasa shi ya kara kidimata.
Daga bangaren Deedat, al’amura sun kara tsananta azabtar da kansa yake faman yi, ya koma kamar maraya, damanshi ba mai yawan magana ba ne, sai ga rashin maganar ta ninku. Salim ya yanke shawarar kiran Ummi, inda ya zayyane mata duk abin da ke faruwa, washegari da sassafe ta dauki hanyar Kano.
Yana kwance a doguwar kujera dafe da kai, tsananin ciwon kai ko idanunshi ba ya iya budewa, kamar daga sama ya jiyo sallamarta. Da sauri ya bude rinannun idanunsa, a sukwane ta karasa gabanta ta rufa a kansa.
“Ahmad kashe min kanka za ka yi? Me ye ya yi zafi?”
Da kyar ya mike cikin kokarin boye damuwarsa. Ya yi murmushi.
“Ummina ke ce, Ummina…”
Da sauri ta dakatar da shi.
“Yaushe ne ka soma boye mini damuwarka? Me ya sauya ka?”
“Ummi me ya sa duk ki ke fadin haka?”
“Gaya min me ke faruwa, kada ka yi min karya, ina can cikin tashin hankali, bana bacci, bana cin abinci. Bana iya komai duk saboda rashin jinka, babu abin da ban ayyana ba, ashe ba ka tausayina? Ashe za ka iya numfashi ba tare da kana jin motsina ba?”
“No Ummina, don Allah ki yi shiru, bani da lafiya ne kawai, ba kuma na son ki daga hankalinki shi ya saka. Ki yafe min, ba zan sake ba”.
Ta tamke fuska ya sauko kasa, kai ya dora a cinyarta.
“Ummi ba zan jure ba, kada ki yi fushi da ni”.
“Zan yi fushi ba kuma zan huce ba har sai ka gaya min idan ka yi min karya ba zan yafe maka ba, ba zan taba yafewa ba”.
Ya dago kai, “Ummi, kada ki yi min haka”.
Mikewa ta yi.
“Zan koma, tunda yanzu kana da wadda ta fi ni”.
Tattaki ta yi za ta fita. Da sauri ya kamo hannunta ya zaunar da ita, ya juya zai fita. Ta dakatar da shi, “Bana bukatar komai, damuwarka kawai nake son ji”.
Ya koma ya zauna.
Kamar yadda Salim ya shaida mata, shi ma bai boye mata komi ba. Ta sauke ajiyar zuciya.
“Dan Adam na iya ci gaba da rayuwa a lokacin da ya rasa uwa da uba. Kai namiji ne, dole ka koyi juriya cikin kowane hali ka tsinci kanka, kuma ma ban da abinka ai dala ka dauko babu gammo, ka dauko abin da ba zai taba yiyuwa ba, ina ka ke nufin za ka kai Nabila Ahmad, da gangan ka sanya ta a rai. Abin ba zai yiwu ba ne shi ya sa ya zo da wannan sarkakiyar, maganin wannan matsalar shi ne ga gaggauta aurenka da Nabila, komai zai dawo maka daidai, kuma ka shirya tare za mu koma”.
Duk yadda ya kai ga fahimtar da ita abin ya gagara dole ya tsuke baki, inda ya roki alfarmar ta bari zuwa gobe sai su wuce.
Da kanta ta shiga kitchen ta shirya masa abinci, tare da hada musu. Suna zaune kowannensu da kyar yake ci, tausayin junansu suke ji. Sun lura da yadda dukkaninsu suka rame.
“Ahmad kana bukatar kulawa, duk lokacin da ka bar gida sai ka canza. Ni ce nake kulawa da kai, ba ka damu da kanka ba. Na dasa maka damuwa da al’amuran mutane, amma na lura abin har ya yi yawa, kasuwanci da damuwa da rayuwar wasu zai sanya ka lahanta lafiyarka. Idan ka yi aure komai zai zo da sauki, matarka za ta kula da kai sosai. Ka kwantar da hankalinka, za ka ji dadin Nabila, ita din mutuniyar kirki ce, iyayenta na matukar kaunarka da ita, mahaifiyarta tamkar uwa ta ke gare ka, guje musu zai iya zamowa tarwatsewar zumuncinmu, iyayenta su ne wadanda suka rage mana, ba su kyamarmu ko a fuska ba su nuna mana komai face soyayya da son hada zuri’a da mu. Ina son wannan karon a yi komai a gama, please”.
Ya dinga jinjina kai.
“Ummina, zan yi yadda ki ka ce. Na amince da duk hukuncin da za ki zartar a kaina, amma ina jin Nurat kamar da jininta aka halicce ni, abin da nake ji game da ita ina tsoron kada ya haukata ni, ki yi min addu’a Allah ya sassauta min. ina ji kamar idan na rasa ta…”
“Ya isa haka, kana kona min rai. Ko da babu Nabila bana jin zan lamunce ka aure ta, wannan din za ta iya janye ka daga gare ni, za ta sa ka nisance ni. Na tsane ta!”
Yadda ta harzuka ne ya sanya shi tsuke baki, bai sake cewa komai ba, sai da zai fita ya yi mata sallama, a ciki ta amsa.
*** *** ***
“Nurat ban yi sabing din lambar daidai ba, na rasa me ke faruwa, mun rabu da shi ya ce jibi zai dawo, kwana biyar kenan, na kasa samun nutsuwa”. Ta fada tana kokarin zama kusa da Nurat.
“Duba ki gani”.
Ta karbi wayar, “Yaya Aazeen lambar ce”.
“To wai me ke faruwa ne? na shiga uku! Ko dai ya sake shawara a kaina ne?”
Ta karbi wayar ta soma kira, an nuna wayar a kashe ta ke.
“Mu kara lokaci kila wayar ce ta fadi, kin ga ba wani karfi ne da shi ba, ballantana ya samu wani”.
“Ina! Wannan ba hujja ba ce, idan sace wayar aka yi, ai ya san gidan nan. Na damu da yawa, mutumin nan zai haukata ni, bai isa ya ce zai guje min ba, bai isa ba! Nurat gaya min yadda zan yi. Ki sama min mafita, na san kina da dabaru da yawa, ke ce ki ka shigo da shi rayuwa ta, yanzu ma ina son ki dawo da shi”.
Ta matso kusa da ita sosai, tana jin tausayin kanta, son Deedat babu sassauci kullum karuwa yake yi. Tana kallon Aazeen kamar za ta zauce, amma abin da ta ke ji ita a tata zuciyr kamar ba za ta iya rayuwa ba. Ta dora hannu a kan na Aazeen.
“Na yi miki alkawari zan dawo da shi rayuwarki”.
Aazeen ta yi murmushi, cikin wani irin mayen so.
“Na san za ki iya”.
Ta shafa gashin Nurat ta fice.
Maganganun Aazeen ne ke mata yawo a kwakwalwa, ta mike tsaye ta shiga tunanin abin yi, ta koma ta zauna, ta dauki wayarta ta shiga loda lambobin Deedat a ciki, ta soma kira. Ga mamakinta ji ta yi wayar na ruri. Kamar ba za a dauka ba, daf ta ke da katsewa ta ji an daga, wata irin ajiyar zuciya ta yi, har sai da ya ji.
“Nurat!” Ta ji ya ce.
Gabanta ya buga, jikinta ya hau bari, “Na shiga uku”. Ta ce a zuciyarta.
“Kina tare da ni?”
Ta jinjina kai kamar yana gabanta.
“Ko yanzu ma za ki ce Aazeen ce?”
Ta kasa cewa komai, ya sake maimaita tambaya, “Yanzu gaya min me ye kuma?”
“Da ma mun ga ba ka dawo ba ne?”
Ta fada muryarta na rawa.
“Ba zan dawo ba, ba zan taba dawowa ba”.
Duk ta dabarbarce.
“Kada ka ce haka, kada ka yi mana haka, Yaya Aazeen tana matukar sonka”.
“Ko? Zan yi yadda ki ke so, amma kafin nan ina son haduwa da ke”.
“Ni kuma?” Ta tambaya a tsorace.
“Eh mana”.
“To amma ka sani ba a barina fita ko’ina”. Ta fada a marairaice.
“Okey, to shi ke nan, sai ki bar ni da hukuncin da na zartar, sai wataran”.
Da sauri ta dakatar da shi.
“Don Allah ka gaya min a ina za mu hadu, kuma yaushe?”
Ya dan yi shiru kamar ba zai ce komai ba.
“Kai nake sauraro”.
“Idan ki ka wuce awa daya kin watsar da damarki”.
“Wayyo Allah, ya ka ke so na yi? Ni ba a barina yawo na rantse”.
“To shi ke nan sai ki sha zamanki, amma ina son ki sani daga yanzu zan yi blocking layinku”.
“No kada ka yi haka, zan zo yanzu”.
“Wannan unguwar da na taba ganinki sanda ana ruwan saman nan, a nan za mu hadu, zan karbi motar principal dinku, kina shigowa za ki ga wata jar mota ina ciki”.
“To amma me zan ce a bar ni in fito?”
“Wannan kuma ya rage naki”.
Duf! Ta ji ya katse wayar. Komawa ta yi ta zauna, tunanin hanyar da za ta samo ta fita ta ke yi.
“Wai ke tunanin me ki ke yi ina ta nemanki ashe ke kina nan?”
“Ammina, Zahra ce ba ta da lafiya, tana asibiti”.
“Ayya, Allah ya ba ta lafiya, gobe sai mu je duba ta ko”.
“Am… Ammi da ma za ki bari sai in je, ba zan dade ba, kin ga sun kira ni takanas sun shaida min, babu dadi a ce ban je ba”.
“Haka ne, kin kawo hujja. Maza shirya ki je kada Daddy ya dawo”.
“To Ammi na gode”.
“Kash! Na mance direba ba ya nan”.
“Kawai ki ba ni kudin mota sai in tafi tunda ba dadewa zan yi ba”.
“Bana son kina fita a motar haya”.
“Ammi ni fa yanzu ba karama ba ce”.
Ta mike tsaye.
“Kalle ni fa, kin ga yadda na girma”.
“Gaskiya ne, kin zama cikakkiyar budurwa tunda ma ga shi ana kokarin ba da ke”. Aazeen da ke kokarin shigowa ta fada.
Nurat ta shagwabe fuska, “Ammi kina jinta ko?”
“Kyale ta, ai ita ba ta rabo da tsokana, je ki shirya”.
Hijabinta kawai ta dauka ta yafa.
“To maman hijab, sai ina? Dalla ji ta, ko ‘yar hoda ba ta saka ba, ballantana kwalli. Yanzu haka ma kari ta ke, Ammi ki yi mata magana”.
“Kin ga kyale ta, yi tafiyarki a hakan ma kin fi ta kyau”.
Aazeen ta dinga dariya cikin ci gaba da tsokanarta.
Tun daga nesa ya hange ta, gaba daya ya kafe ta da manyan idanunsa da addininsa ya halatta ya auri mace ko ta wacce hanya, da yau ya gudu da Nurat. Yana ji ita ce rayuwarsa, kullum sonta na ninkuwa a kan wanda yake ji.
Ya kwantar da kai a jikin allon kujera yana kallo tana ta raba idanu, can ta hangi motar. A tsorace ta karasa jikin motar, ta rasa ta inda za ta yi masa magana, da yake glass din motar mai duhu ne, babu ta yadda za ta hange shi.
Murmushi ya yi ya bude murfin motar ba tare da ya yi magana ba, ita kuma ba ta shiga ba, kusan mintina biyar suna a haka, da alama ma in ba ita ta yi magana ba za su kwana a haka.
“Ammi ta ce kada in dade”.
Ta fada kamar za ta yi kuka.
“Fitowa zan yi kan titi in tsaya kowa na kallona? Idan ba za ki shigo ba in tafi”.
“Cikin motar zan shigo?”
Ya dauke kai yana lallatsa waya.
Dole ta shiga, yadda ta kankame jiki sauran kiris dariya ta kwace masa, kawai ta ga ya tada mota ya soma tafiya, idanunta baki daya suka yo waje, g wani hawaye kwance a ciki. Ta dube shi a razane.
“Ina za ka kai ni?”
“Sayar da ke zan yi”. Ba tare da ya dube ta ba ya fada. Babu fuskar da za ta sake magana, ya hade rai, ba sassauci. Ta sunkuyar da kai, sai ga kwalla shar! Shar!! Ji ta yi ya taka birki, da sauri ta dago kai don ganin inda ya kawo ta. Sam babu gidaje a gurin sai kamfanoni, gurin shiru, jefi-jefi mutane ke dan gilmawa,
“Awa nawa aka baki?”
Ta ce, “Kada na dade”.
Ta ce da shi muryarta na rawa.
Ya kafe da ido ne yasa ta kasa dago kai
“Nurat, me yasa kika shirya wannan wasan kwaikwayon da ni?”
Ta dago kai idanunsu suka gauraya, ta yi saurin dauke idanunta.
“Menayi ?”
“Okey, duk dai ba wannan ba, yadda nake tunanin lafazinta awaya, yadda nake tunanin halaiyarta, tausayinta, kirkinta,tarbiyarta dana ganta azahiri, duk sai naga komai ya bambanta.Bazata zama ta cikin wayar ba, sam ba ita ba ce, na kara tabbatar da hakanne ta yadda zuciyata ba tayi na’am da ita ba.Yadda na damu da ita awaya sam sai naji azahiriko son ganinta bana yi, amman kin san me?Wannan abubuwan da na karanto duk na alakanta shi da ke, dabi’unku daya da ta cikin wayar, ina son sanin taya hakan ta faru?”
Ta shiga rudu sosai, ta kasa cewa komai, ya dora da fadin.
“Tun lokacin da naganki agurin maigidana jikina ya bani wani abu, da kika yi magana na dinga tunanin a ina na san muryar, saboda shakuwar da nayi da muryar a waya, saboda kamanceceniyar muryarki da muryar ta cikin wayar ya sanya na ji ina kaunarki, yanzu dai kika gayamin gaskiya me yasa kike son yin kyautar zuciyarki?”.
Ras gabanta ya buga.
“Ban gane me kake nufi ba?”
Ya kafe ta da idanu,
“Ina son ince dake, sam ban dace da ita ba”.
“Dan Allah Yaya Adamu kada kayi mata haka yaya Aazeen bata tabajin tana son wani ba sai kai, zuwanka cikin rayuwarta ya sauyata, Ammina, dani duk murna mukeyi, ba zata jure ma rashinka ba”.
Yayi murmushi “Kin damu da yayarki dayawa, na ga kina kaunarta sosai, amma kin san me?”
Ta yi saurin kada kai.
“Sai naga kamar ni da ke munfi dacewa”.
Wani irin zabura ta yi ta bude ido sosai a kan fuskarsa,
“Ba kasan abinda ya dace ba, baza mu taba dacewa ba Yaya Adamu, ba don mu yi wasa na zo ba, ja ga na dade, Allah ne kadai ya san halin da Ammi ta ke ciki, ba ta son Dad ya dawo ba na nan, don Allah mu karasa maganar na tafi”.
Ya yi murmushi.
“Ni gaskiya na gaya miki ki tambaya ki ji, Allah mun dace da juna”.
“Tunaninka ba daidai ba ne, kuma ma wannan wasan yaran ta kamata ka dakatar da shi, please ba a daura aurenku ba ballantana ka soma yi min irin wannan wasan”.
Shigowar kiran Ammi ne a wayarta ya katse musu maganar tasu.
“Ya Rasulillah! Ammi na kira ka gani ko?” Ta fada a tsorace.
“Na sani na dade”.
“Ki daga ba ki dade ba, kila wani abin ne”.
“Ina jin tsoro”.
Ya zare wayar daga hannunta, ya danne handsfree, muryar Ammi ta cika motar.
“Nurat, yaushe ki ka koma haka? Kina son in janye yardata daga kanki? Da ma na sani duk zakin suga in ya gauraya da gishiri sai ya gurbace, ga Zahra nan zaune da ranta da lafiyarta tana jiranki”.
Duf! Ta katse wayar.