Skip to content
Part 16 of 17 in the Series Kyautar Zuciya by Bilkisu H. Muhammad

“Wayyo Allah na mutu”. Ta fada cikin maimaita innalillahi da allahumma ajirni, duk ta gama gigicewa.

Gaba daya ya ji tausayinta, cikin dasasshiyar murya da wani irin haushinsa da ke kwance a ranta.

“Ka gani ko? Ammi ba ta taba fushi da ni haka ba, yau ga shi a saboda kai na yi mata karya, na yi mata karyar za ni asibiti duba kawata, yanzu ga shi Zahra tana gidanmu, ya ya zan yi?”

Zai yi magana ta balle murfin motar za ta fita.

“Ki bari in kai ki”.

Ba ta da alamar tsayawa. Hannu zai kai ya dakatar da ita.

“Ammi ta ce idan na bari namiji ya taba min hannu zan haifi shege”.

Da sauri ya janye hannu yana kallo ta fita.

Kuka ya ga tana yi sosai, hankalinsa ya yi bala’in tashi, ji ya yi gaba daya ya tsani kansa.

Tafe ta ke a kasa duk motar da ta tsayar ba ta tsayawa, daga can nesa ya hango dan sahu ya tsaya, ta shiga tukunna ya samu nutsuwa.

Tabbas ta amince ko wane tsanani yana tare da sauki, Ammi, Daddy, Aazeen da alama duk suna cikin farin ciki, tsananin firgicin da ta ke ciki ya soma sauka.

“Kanwata, ke din mai tsada ce, Zaruk ya cancanci yabo. A dalilinki Dad ya samu kwangila wadda bai taba samun irinta ba. Ga Zaruk ya siya miki tsadaddiyar mota abin farin ciki sun kawo kudin na gani ina so, shi kuma Dad ya mallaka musu ke, candy kawai muke jira mu sha biki. Sai abu na gaba wanda zai ba ki mamaki…”

Ta janyo hannunta tana figarta, ita dai kawai binta ta ke a baya, ga wani irin juyawa da kanta ke yi. Bangaren saukar baki suka nufa, inda ta yi arba da Deedat.

“Kin ganshi gaba daya sai da ya gama daga min hankali, ashe wai ba ya gari ne. ki ba shi labarin halin da na shiga don shi har yanzu bai yarda ba, ina zuwa”.

Ta yi saurin fita.

Deedat ya mike ya dawo gabanta, “Ina fatan tafiyarki ba ta jawo matsala ba?”

Ta dan jinjina kai.

“Masha Allah, na ji tsoro sosai… am dama na zo ne in ba ki hakuri, ni ne silar komai ko? Na sani yanzu kina jin haushina”.

“A’a ta ya ya zan ji haushinka?”

“Yanzu ki gaya min yaushe za mu karasa maganarmu”.

Ta dan dube shi a kaikaice.

“Jinake yi komai ya wuce tunda ga shi har ka zo?”

“No, na ce na zo ne in ba ki hakuri”.

Motsin takun Aazeen suka ji, da sauri ta ja da baya.

“Ina za ki kuma? Ai ki tsaya yau da ke za mu yi hirar”.

“Daidai kenan, ga Zaruk can suna gaisawa da Ammi, yanzu zai karaso”. Aazeen ta fada.

“Waye haka?” Deedat ya tambaya.

“Shi ne wanda za ta aura, yau din nan aka tabbatar masa da an ba shi ita”.

Nurat ta bi Deedat da kallo, irin kallon kurillar nan. Kwakkwaran motsi kasawa ya yi, wani irin gumi ke karyo masa tun daga tsakiyar sumar kansa har zuwa kafafunsa. Wani zazzabi ya ji ya soma rufe shi, da kyar ya lalubo yawu a bakinsa.

“Allah ya sanya alkhairi”.

Aazeen ta ci gaba da fadin.

“Tun tana karama yake sonta, daga ni sai shi muka sani, ita kanta ba ta san da hakan ba sai a kwanakin nan”.

“Ina son zan wuce, ina sauri ne”.

Ya katse ta daga furta maganganun nata wanda yake jinsu tamkar saukar garwashi. Bai tsaya jin me za ta ce ba ya nufi kofar fita. Kicibis suka yi da Zaruk har sai da suka bangaji juna.

Deedat bai tsaya bi ta kanshi ba saboda ko gabansa ba ya gani, Zaruk ya bi shi da kallo cike da tunani barkatai.

Aazeen ce da sauri ta yo waje inda ita ma suka ci karo da shi.

“Waye wannan na ganshi ya fita?”

“Waje ya yi, na ga ban hango shi ba?”

“Ina tambayarki ke ma kina tambaya ta?”

“Oh God, shin me ke damun Adam ne?” Aazeen ta fada.

“Okey na gane, shi ne mijin da Nurat ta yi miki ko?”

Wata uwar harara ta galla masa.

“An gaya maka na yi kama da wadda za a yi ma miji?”

“Yo wa ya sani abu a duhu? Yanzu gaya mini ina Gimbiya?”

“Tana ciki”.

Nan ta barshi ta fita.

Tana hango shi ta yi saurin durkushewa kasa, wata irin tsanarsa na kara ratsa ta, ba ta taba ji a ranta zai zama mijinta ba, ta sani babu yadda za a yi Ubangiji ya kaddara mata auren mutum kamar Zaruk, don haka hankalinta yake a kwance, damuwarta kawai shi ne yawan kusantota da zai dinga samun damar yi a yanzu.

“No, kada mu yi haka da ke my one, ina son ki sake da ni fiye da da, kin manta ni din abokinki ne, abokin shawararki, ko da mun rayu tare za mu dorar da abotarmu”.

Ya sassauta murya.

“Nurat, ban taba sanin haka soyayya ta ke ba sai a kanki. Ban taba sanin yadda na damu da ke ba sai da Dad ya wana ni a kan cewar ba za a ba ni ke ba, ina fatan za ki samo min wadataccen matsuguni a zuciyarki. Ni a gurina kaunarki abu ne da ba zai taba gushewa ba”.

Dago kai ta yi ta watsa masa wani kallo.

“Yaya Zaruk zan je na kwanta, ba ni da lafiya”.

Ta mike ta raba ta gefensa ta wuce. Ya bi ta da kallo baki a bude, ya koma ya cije lebe tare da dunkule hannu ya kai ma bango duka. Zubewa ya yi a kan kujera, tuni kwakwalwarsa ta shiga saka masa abubuwa kala-kala.

“Ya dai?” Aazeen, wacce bai san shigowarta ba ta tambaya.

Kamo hannunta ya yi ya zaunar da ita cikin kunar rai ya soma magana.

“Yadda muka shaku da Nurat ban taba tsammanin za mu samu matsala da ita ba, ki bincika min akwai wani a ran Nurat, kuma wallahi sai na gano shi, kuma ba zan taba janyewa ba ko da za ta mutu saboda kina ba zan janye ba. Ko yau ta mutu ba zan bari a kai ta makwanci ba sai na tabbatar da aurena a kanta. Ina matukar son Nurat”.

Ta tuntsire da dariya hadi da lakuce mata hanci.

“Ka yi, amma na shawarce ka da ka sassauta”.

“Da gaske nake ita ce rayuwa ta, ba zan bari ta guje min ba, ba zan kuma bada damar wani ya shiga rayuwarta ba”.

Ta koma ta daure fuska.

“Ka dinga sanin a gaban wa ka ke, na ga ka zake da yawa, da alama ba ni da wani tasiri, a kaina ya kamata ka yi kishi ba ita ba, me ta ke ba ka? Tsawon shekaru biyu muna mu’amala ban ga kana nuna damuwa a kaina ba, ba ka taba kishina ba”.

“Aazeen ki daina wannan zancen, tsakaninmu da ke wani abu ne can daban, ita fa wannan a hannunta gaba daya nake son damka rayuwa ta da ita nake son…”

“Ya isa haka, na gaji da jin wannan shirmen naka”.

Ta ja tsaki ta yi waje. Ya bi ta kawai da kallo.

“Kada dai a ce wannan dakikiyar kishi ta ke?”

Ya tabe baki tare da daga kafada.

Deedat ya dawo gida cikin rudu da tashin hankali, tare da neman mafita a zuciyarsa.

Yana kwance a kan doguwar kujera inda yake ci gaba da yakar zuciyarsa da tursasa masa da cire Nurat daga cikinsa, maimakon haka sai jin da yake yi ba zai iya rayuwa babu ita ba, duk irin abubuwan da yake somace ta kasance da shi, Nurat na da shi, abin da ya saka yake kara girmamata shi ne, kunyarta. Ya sani tunda Nurat ta shiga rayuwarsa ba za ta tashi a banza ba, dole ne ma ta zama mallakinsa, a duniyar nan duk yadda ka ke muddin kana da kudi aibunka yakan buya. Zai karya alkawarin Ummi, zai fito ya bayyana wa duniya kansa, idan ya yi haka zai mallaki iyayenta, zai je zai siye shi wannan saurayin nata, sai ya same ta ko da bayyanar waye shi zai zamo sanadiyyar barinsa duniya.

“Ahmad akwai ranar da za ka iya yin fushi da mamanka, ashe dama akwai wacca za ta iya yanke kaunar da ke tsakanin uwa da danta? Deedat wane irin so ne ke neman canza min kai, wace ce wannan? Wace ce ita din?”

Da sauri ya mike zaune, “Ummi, na dawo kina sallah, ki yi hakuri”.

“Ahmad ni ce zan bar sallah a kaina har zuwa wannan lokacin? Duba fa ka gani, karfe nawa?”

Sai ya rasa bakin magana.

“Da na ji shiru na yi zaton ko…”

“Ya isa haka, ya kamata ka wakilta Salim a kan komai, na yanke daurin aure rana ita-yau, kuma wannan karon babu dagawa, na tura wa Nabila duk abin da za ta bukata”.

Bai iya ce mata komai ba, zuciyarsa ce ke yi masa zafi, yana tsoron idan ya ce zai yi magana zai iya fada ba daidai ba.

“Ahmad ba ka ce komai ba”.

Nan ma bai yi magana ba, gaba daya ya ki kallonta. Hannu ta kai ta dago kansa.

“Ahmad, in har kana son ka faranta min ka karbi Nabila a matsayin mata, ba ta da wani aibu, tana da iliminta, mata ce ta nuna wa sa’a. Tsananin son da ta ke maka ba zai bari ta cutar da kai ba, kuma ma ka sani kowa ya sani kuna son junanku, kowa ya san kai ta ke zaman jira, shi ke nan cikin kankanin lokaci wata za ta sauya ka? Don Allah ina son ka rufa min asiri ka fitar da ni kunya, ka san yadda muke da iyayenta”.

Ta dira a kan gwiwoyinta alamar tana rokonsa. Da sauri ya rufa mata baya ya rike hannayenta.

“Ummi kada ki yi min haka, don Allah ki yi hakuri na amince zan yi biyayya, ba ma Nabila ba idan ma da wata ki karo, na yi miki alkawari ba zan bijire wa umarninki ba”.

Ya koma ya mike yana hada kayansa cikin akwatu. Kawai ta bi shi da kallo tana mamakin wannan wane irin so yake wa yarinyar nan? Ita din wace ce?

Deedat ya bi umarninta ne cikin fushi, ba za ta nuna masa cewar ta gane hakan ba, za ta barshi a hakan muddin zai amince da Nabila.

“Ummi na gama shirya kayana, za mu iya tafiya an yi mana booking din jirgi”.

Ya ce da ita, gobe za su tafi ga yanzu ya dawo ya ce su tafi yau, ta kada kai, tausayinsa ta ke ji, sai dai idan ta nuna mishi karayarta zai iya cin galaba a kanta, yadda yake yin komai a zuciye za ta ci gaba da biye masa, in an gama komai ta lallaba shi, da ma ita ba ta zo da komai ba sai kayanta kala daya, jakarta kawai ta rataya.

Tunda suka dawo aka shiga shirye-shiryen biki ka’in da na’in, Salim ne ya zamo tamkar ango, duk wani abu da ake bukatar ango ya yi, Salim ne ke yi. Shi kam Deedat gaba daya ba shi da wani kuzari tamkar wani mara lafiya, damuwarsa ce ta tsananta, sai dai kasancewar ba mutum ne shi mai yawan magana da hayaniya ba ne ya saka babu wanda ya fahimci halin da yake ciki.

Ana igobe za a daura aure wayarsa ce rike a hannunsa, hotunan Nurat yake kallo, ya numfasa.

“Na yi alkawarin cewar babu wanda zai dakatar da ni daga sonki har abada, muddin ina raye sai kin zamo mallakina”.

Motsin Ummi ya ji suna magana da ‘yan biki, ya dauke hoton Nurat daga fuskar wayar, daidai lokacin ta shigo. A kusa da shi ta zauna ta kuma kasa magana, kallonshi kawai ta ke yi tana kara nazarinsa. Tsawon mintuna biyu ta bude baki.

“Ahmad, har yanzu kana kallon cewar na yi maka dole ko?”

Ya dube ta a raunane.

“Ummi, me kuma na yi?”

“A’a ban ce ka yi komai ba, kawai dai ina zargin kaina ne da cewar na tursasa ka a kan abin da ba ka ra’ayi”.

Ta yi shiru ta sake fadin.

“Gobe ne za a daura aure, amma har yanzu ka ki sakin jiki, don haka na zo maka da zabi, ba zan shiga rayuwarka ba, na tuba ba zan yi maka dole ba. Yanzu zan dakatar da auren duk kuwa da makudan kudaden da na kashe, da ma ba kowa ne ya san za a yi auren nan ba, saboda tsaron lafiyarka”.

Da sauri ya jinjina kai.

“No, Ummi kada ki yi haka, ni fa danki ne, kuma ma ai tun farko ita din zabina ce”.

Ya fadi haka ne saboda damuwar da ya ganta a ciki.

Ta sake kura masa ido don gaskata abin da bakinsa ke furtawa.

“Na gode Ahmad, Allah ya yi maka albarka”.

Ala dole ya saki fuska yana murmushi, hakan ne ya ba ta kwarin gwiwar barinsa.

BAYAN DAURIN AURE.

Nabila na ta fushi wai saboda an kaskanta aurenta. Ta dubi Mamanta cikin muryar kuka.

“Haba Mom ki ga fa daurin aure kamar na kananan mutane, wannan ai tamkar ba ya farin ciki da aurena ne, yana inganta farin cikin wasu can fiye da nasa, abokinsa har ya fi shi hobbasa, ya fi shi doki, kun biye masa anayin komai a rufe kamar ba shine didat din da sunansa ya kewaye gida da waje, ni wallahi kawaye na nayi mini dariya, kuma kun kasa yin komi akai.

“Nabila kin kasa ganewa, da yaya yaronnan yasan munada arzikin da aurenki zaiyi tambari akasarnan, to amman kin bin umarninsa zai iya kawomana baraka”. Ta goge kwallar fuskarta,

“Ni dai kawai an cutar dni, an rusa min wani burina”.

Haj. Amina kanwar mamanta ta dafa kafdarta

“Kina da wani buri daya wuce Deedat ya zamo mallakin ki ne? atinani na wannan shine babban burinki, shagalin da kike korafin   ayiaba ai duk shirme ne, in kika yi hakuri nan gaba zaki haihu a lokacin kin gama sauke shi dag layin da yake akai”

“Aunty, Amina ban gane ba, kina nufin tsattsauran ra’yinsa, kin bayyana shi waye kinga ke zaki fito ki nunawa duniya waye sh, idan shi bai zo duniya dan ya hole ba, ke sai ki huta da kudinsa, dole ki fantama, matan ministoci dana gwamnoni sune zasu zama abokan mamanki, ko dan kawai ki sake makake zuciyarsa, ki jajirce gurin dora shi  akan, wannan layin… kuma ki yi kokarin nuna masa tattali yarage wannan almubazzarancin da yakeyi”.

Mom dinta ta amsa da fadin haka, ta ci gaba da fadin

“Ni ban ma taba ganin irin wannan batan basira ba, kadinga kyauta cikin boye kanka, atakeka awuce ba a san kai bane, kiyi masa kwanciyar mage mai daukar rai”. Nabila ta dinga jinjina kai kamar mai daukar darasi.

Daga ranar Juma a zuwa lahadi an shirya walima takai bakwai, anyi watsi da naira kamar ba a so duk da hakan ba a burge Nabila ba, tana ganin rashin halartar Deedat gurin wani kaskanci ne, haka ta je fakar idon mutane ta yi ta sharar kwallar takaici.

“Haba Nabila, kina son a fahimci halin da ki ke ciki? Ina ruwanki da rashin zuwanshi, tunda ya sakar mana kudi irin yadda muke so, ina ruwanmu? Kada ya zo mana”. Munira kanwarta ta ce da ita.

“Ba haka ba ne Munira, na fara tantama Deedat ya daina sona, ina tsoron Deedat ya canza da yawa, sai ka ce ba shi ba”.

Munira ta ja tsaki.

“Kin ga in dai za ki dora ma zuciyarki cewar lallai sai namiji ya so ki kina tare da wahala, kuma ma shi din ina ya ga wani lokacin nuna wa mace soyayya? Ya kamata ki san abin da ki ka aura, ki share hawayenki don Allah”.

Haka ta dinga lallaba ta har ta saki jiki.

Karfe takwas na dare aka kai amarya gidansu, inda aka ware musu sashinsu daban, Ummi ba ta bari sun bar gidan ba tana son ta ga yadda zaman nasu zai kaya kafin ya koma tanfatsatsen gidan da ya gina. Nan ma Nabila ta shaka, in banda tana sonsa ba za ta amince da wannan kaskancin ba, da kuma duba cewar Ummi ce ta tsaya tsayin daka gurin tabbatuwar aurensu. Duk wani kayan alatu an zuba a sashin nasu, ba za ka ce a Nageria ka ke ba idan kana cikin gidan.

<< Kyautar Zuciya 15Kyautar Zuciya 17 >>

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×