Skip to content
Part 17 of 17 in the Series Kyautar Zuciya by Bilkisu H. Muhammad

*****

“Iyayen Nabila sun taka rawar gani cikin rayuwarmu, rike ‘yarsu da kyau shi ne halaccin da za ka yi musu, kuma wannan auren da ka ga na yi tsayin daka a kan fanin ka yi, za ka gane manufata a nan gaba. Allah ya yi maka albarka, Ubangiji ya yi ma rayuwarku albarka. Yau na yayeka yau ne ka zama cikakken mutum, ba ni da burin da ya wuce na ga wannan rana”.

Haka ta ci gaba da yi masa nasiha masu ratsa jiki, ta dora da fadin.

“Ka je na ga dare ya yi, amma ban ga komai a hannunka wanda za ka shiga da shi gurinta ba”.

Ya numfasa, “Ummi akwai komai a gidan”.

“Na sani, amma ai al’adarmu ce ta koyar da hakan, in ba ka shiga da komai ba hakan zai tabbatar mata da cewar ita din ba komai ba ce. Ka sani kuma bana son a sami baraka. Ga wannan shigar mata da su”.

Ledoji ne manya guda biyu.

“Na san halin yarona don haka na tanadi abina”.

Ya kinkimi ledojin jiki a sanyaye, yana jin zuciyarsa duk babu dadi. Ya sha ji ana fadin, duk wani ango yana jin kanshi cikin zumudi da farin ciki, amma shi babu abin da ke cunkushe a zuciyarsa sai bakin ciki. Allah ya gani sam ba tsara rayuwarsa da Nabila a ciki ba. Sai dai ya sani mutum ba ya tsallake ma abin da Ubangiji ya tsara masa.

Ya karbi zabinsa da hannu bibbiyu, zai tabbatar da ya zamo adali.

Kayan da aka kawo ta da shi tuni ta cire su ta sauya wasu fitinannun kaya, riga ce mai shara-shara, sai gajeran wando. Ta bi kowacce gaba tata da turaren humra, ta kunna radiyo kidan turawa mai sanyi ne ke tashi, a cikin zuciyarta tana tsara yadda za ta yi ta burge shi, a yau za ta nuna masa yadda ta damu da shi, za ta gwada masa cewar ya more da mace.

Motsin takunsa ta ji, da sauri ta mike. Yana sawo kai ta tare shi hadi da fadawa kirjinsa.

“Sannu da shigowa Yaya”.

Turus! Kunya na daga cikin abin da ke burge shi a rayuwa, komawa ta yi ta karbe ledojin hannunsa tana rike da hannunsa har zuwa kayataccen sitroom, ta dire kayan a kan carpet, ta dinga shisshige masa ita a lallai son ya yaba ma kwalliyarta. Shi kam sai faman dauke kai yake yana jin kunyar shigar da ta yi.

“Na gaji, ina son na watsa ruwa, ga leda can ki dauki abin da ki ke bukata”.

Bai jira jin abin da za ta ce ba ya wuce ciki. Ganin komai ta ke tamkar a mafarki, wai yau ita ce a matsayin matar wannan diamond man din nan. Lallai ta yi wa mata zarra, musamman in ta tuna yadda mata suka dinga kuka a kan sonsa, in ta tuna yadda yake da aji ta sani ita kadaice ta sa yi sa’a. ba shi da son mata da ra’ayinsu, ba shi da lokacin ma da zai tsaya biye musu, ita din kanta ba don ta dage ba da ba ta kai wannan matsayin ba. Sai dai ta sani tana da aiki, sai ta koyar da shi komai, babu abin da ya iya ban da hidimta wa talakawa. Da alama bai ma san me ye ake nufi da shi kansa so ba.

Lokar sitroom din ta bude, wasu jarkoki ta dauko masu dauke da magungunan mata, sai na matsi. Haka ta hau bunkarsu ta saka na matsawa, kafin wani lokaci tuni ta soma fita a hayyacinta, burinta Deedat ya zo gare ta, in ta tuno yau za su hada makwanci sai ta ji tsigar jikinta na tashi. Wani irin yarr ta ke ji a jikinta.

Wow tana son Deedat da yawa, masoya na cewa ba kasafai ka ke auren wanda ka ke tsananin so ba, sai ga shi ita din ta ciri tuta, Allah ya ba ta miji dan gaske, malti miloniya, young man, giant, gentle, handsome, ga tsananin kyawu kamar shi ya yi kansa.

Agogon da ke jikin bango ta duba, karfe goma sha daya ba dare, amma ya ci a ce ya fito a wanka.

Bedroom dinsa ta nufa, hango shi ta yi zaune a kan darduma, da alama sallah ya yi. Dadi ya kama ta, wannan sallar da ake yi ne idan za a kusanci iyali, that’s means daga yanzu zuwa koyaushe zai zo mata kenan, amma kuma an ce mata da miji ne suke yi, to ko dai kowa da irin tasa?

Bayan ya shafa, ya dan dube ta, ta koma ya yi saurin kawar da kai.

“Ba ki yi barci ba da man?”

“Barci kuma? Ta ya ya zan iya barci in ba ka? In ma zan yi barcin ai nan zan zo mu kwanta”.

“Haka ba ya cikin tsarina, ni ne zan dinga binki naki dakin a duk lokacin da nake bukata”.

Ta shagwabe murya, “Nan gidana ne, ni zan tsara komai in na ga dama in kwana a dakinka ko nawa”.

Ya dube ta a kaikaice, “Ko?”

Ya mike ya ninke dardumar, ya ce, “Ya kamata ki je ki kwanta saboda mun gaji ko?”

Wannan mutumin me yake nufi ne? ta ce a ranta.

“Wai Yaya Deedat sai ka dinga abu kamar ba ka dokina”.

“Nabila bana son magana da yawa, ki je ki kwanta”.

Za ta yi magana ya daure fuska tamau, ya wangale kofa alamar ta fice. Sum-sum ta yi waje, ya koma ya danna kofar.

Kuka ta ke yi sosai da waya manne a kunne.

“Mom, Yaya Deedat ya kore ni, ya kulle kofarsa, kuma ga shi ina jin tsoro. Ina son zan tafi gurin Ummi na kwana”.

“Kada dai zatona ya zamo gaskiya? Kada dai Ummi ce ta tursasa shi gurin aurenki? Kin ga shawararki ta yi, ki tafi ki je gurinta, ki gaya mata duk abin da ki ka gaya min kin ji ko?”

Ta katse wayar, tana sharar kwalla, mararta ce ke faman damka ga wani irin yoyo da ta ke yi, ta mike da kyar za ta tafi gurin Ummi.

A can cikin bedroom Deedat ya dinga jin bai kyauta mata ba, ya kamata a ce ya taya ta farin ciki, bai kamata ya rusa farin cikinta ba. Ya sani kowace mace daren farkonta ne daren alfaharinta, bai kamata ya yi mata haka ba, ko ma me ye ya danne, ya mike ya nufi kofar fita, ya riske ta tana kokarin bude kofar da zai sada ta da sashin Ummi.

Da sauri ya karasa gabanta.

“Ina za ki je?”

“Zan je in kwana a wajen Ummi, ina jin tsoro”.

“Ba ki da hankali ne? Wuce mu koma”.

“Yaya Deedat ina jin tsoro, don Allah ka bar ni in je”.

Duk sai ya dinga jin tausayinta.

“Shi kenan ya isa, mu je mu kwanta”.

Wani farin ciki ya lullube ta, musamman da ya rike mata hannu, gaba daya ta soma jin wani bakon yanayi, yau ita ce haka kawai Deedat ya rike mata hannu, ba su da sauran hijabi a tsakaninsu. Ita din ta zama tasa, shi kuma ya zama mallakinta.

Kamar yadda ya ce da ita bedroom dinta suka nufa, har ta kwanta sai hudubar Amina ya dawo mata.

“Ba ka mallakar da namiji sai ka maida kanka tantirin mara kunya a duk lokacin da ku ke tare da shi ka sake da shi, ka dauka daga ke sai shi ne a duniyarku ba sai kin jira ya kawo kansa ba, ke kai kanki gare shi idan kana yin haka za ka mallake shi, ka koya masa kulawa jikinsa, idan kina haka zai saba ba zai iya bacci ba a duk lokacin da ba kya tare da shi”.

Ai kuwa kamar wacca a kai wa allura, tuni ta mike ta shiga laluben kayan bacci, an sani duk irin shigar da kai wa mijinka ba ya haramta, amma a daren farko bai kamata ka nuna zakuwarka ba, duk son da ki ke wa mijinki, duk yadda ki ka kai gafitsara ya kamata a wannan gabar a danne komai, ki nuna kunyarki, yanzu ba ku saba ba ke din bakuwa ce, ke kanki idan kina nuna kunya sai kin fi aji. Shi kanshi sai ya fi nan-nan da ke, komai zai fi armashi.

Allah ya raba mu da hali irin na su Nabila.

Kallonta kawai yake yi, ba kunya haka ta kwabe a gabansa ta maida wasu fitinannun kayan da ba su da bambanci da tsirara. Abin da ba ta sani ba, haka din da ta yi tamkar ta bude kofofin rashin yarda ne a tsakaninsu, ya sani Nurat ita kadai ce matar da ta dace da rayuwarsa, yana jin ita kadaice ta gari. Yana mu’amala na kasuwanci da mata da yawa dukkaninsu halinsu daya, duk wadda wata hulda ta hada su sai ta kawo masa hari, Allah ne kawai ke kubutar da shi.

Ji ya yi kawai ta shige jikinsa, yau ita ce rana ta farko da ya taba hada shimfida da mace, yau ne rana ta farko da ya ji jikinsa a jikin mace. Babu komai, yadda zai yi ya guje ma wannan lokaci. Tunani yake yi ta ya ya zai soma? Ya fahimci abin da ta ke so ba zai iya ba, yana jin kunya, ya ma za a yi ya bari har ta ganshi alhalin bai suturce jikinsa ba? Ba zai iya ba, har abada.

Zumbur ya mike.

“Ina kuma za ka je?”

“Ki yi hakuri Nabila, kaina na ciwo, zan fi jin dadi idan na kwanta a kasa”.

“Kasa kuma?”

“Eh”. Ya ce a takaice.

Filo ya dauka ya koma kan kafet, kamar ta saka ihu, shi kam wayarsa ya zaro ya shiga danne-danne gaba daya bacci ya kaurace wa idanunsa.

Kamar a mafarki ya hangi Nurat a online ta wayarta.

Daidai wannan lokacin ita din ma ta hange shi, ta kasa matsawa ko’ina tana dai a bangarensa tana son yin rubutu sai dai tana tsoro. Ta fara da yi masa sallama, sai kuma ta yi sauri ta goge sallamar.

Daga can bangarensa ya yi murmushi, ya rubuta.

“Me ki ka goge? Gaya min”.

“Ba komai, amman ban san waye ba?”

Ya ce, “Ko? To shi kenan sai an jima, bana yin chattin da wanda bai san ni ba”.

Da sauri ta rubuta, “Aazeen ce”.

“Wow! Ki ce princess ce?”

Da sauri ta mike zaune, Yayata yake kira haka? Wani irin mahaukacin kishi ya turnike ta, amma me yake damunta haka don ya kira ta da haka bai kamata ta ji zafi ba, ita kanta ta sani shi din na Aazeen ne. zuciyarta ta fada mata hakan.

“Kin yi shiru ruhina?”

Ta cije lebe, “Zan yi bacci ne, amma na damu sosai, yaushe za ka dawo?”

“Zan dawo lokacin da Nurat ta amince da soyayyata”.

Ta kwalo ido waje, “Wayyo Allah, na shiga uku, ya san ni ce”. Da sauri ta kashe datarta.

Ya dinga murmushi.

Daga bangaren Nabila amarya kuwa, sai faman juyi ta ke a gado, ga mararta na ta damka, tana son kai kanta gare shi tare da bayyana masa bukatarta, sai dai tana tsoron kada ta bada kanta. Ta san halin Deedat ba ya taba yin abin da bai yi niyya ba, karshenta ta zubar da aji ta taya, shi kuma ya gwale ta. Duk masifarsa zuwa gobe dole ne ya sauke hakkinta, ba zai dube ta ya ce har yanzu cikin gajiya yake ba.

Shi kuwa Deedat saka da warwara yake, ya yanke shawarar komawa rayuwar su Nurat, zai biye mata gurin amincewa da Aazeen, hakan ne kadai zai kara kusanta shi da ita, ta haka ne kadai zai bi ya koya mata sonsa, dole zai yi haka, sai ya yi galaba a kanta, ba zai iya rayuwa babu Nurat ba, ba zai taba iyawa ba.

Kiraye-kirayen sallah ne ya farkar da shi daga baccin da ya yi cike da mafarkan Nurat, gaba daya ya mance ma shi din ango ne, ya yunkura cikin salati.

Nabila ya hanga kwance, bacci ta ke lakadan, ras! Gabansa ya buga, ya ja tsaki. A gaggauce ya nufi bathroom ya daura alwala, masallaci ya nufa.

Tunda ya idar da sallah ya kasa dawowa gida, lazimi yake yi, gaba daya addu’arsa a kan Nurat ne, burinsa Ubangiji ya bullo masa sassaukar hanyar da za su rayu da Nurat. Daga karshe kishingida ya yi bai san sanda bacci ya dauke shi ba, har sai da Ladan ya shigo ya tashe shi. Ya shiga tsokanarshi kasancewar akwai wasa a tsakaninsu, kuma ba su wuce sa’anni ba.

“Mutumina, ka ce kawai in tanadar maka filo, na ga kamar baccin daren na gagararka”.

Ya tuntsire da dariya.

“Ko ban tambaya ba na san an raya wannan daren”.

Ya yi waje da sauri, shi kam Deedat bakin ciki ya hana shi magana. Agogon fuskar wayarsa ya duba, karfe takwas da mintuna arba’in, ya yi saurin mikewa, kai tsaye ya nufi sashin Hajiya Khadija. Kunyar hada ido yake da ita, kansa a kasa ya gaida ta, ya koma ya zauna.

“Ummi, yunwa nake ji”.

“Yunwa kuma? Ka mance tun daren jiya na yaye ka? Ka tafi can gurin Nabila”.

“Ummita, kin san ba zan iya ba”.

Ta daure fuska, “Bana son shashancin banza, in ka shigo cin abinci ne tun wuri gwara ka kama gabanka, ka ga ni fita ma zan yi, tashi ka tafi can gurin matarka”.

Hira ya dinga takalarta da shi, wai duk don ya bagarar da ita, sai da ta dauko hijabinta sannan ya mike.

“Na san yanzu Dije ta gama shirya muku komai, tun karfe bakwai ta ke gidanku”.

A bangaren kicin ya yi arba da Dije tana ta shirya abinci a kan dinning table.

“Ina ita Nabila?”

“Na ga kamar ba ta tshi ba, don tunda na fahimci kana masallaci na nufi sashinku ina ta kwada sallama da alama bacci ta ke. Komawata uku har yanzu ba ta tashi ba”. Ta karasa maganar a kunyace.

Irin kallon da ta ke masa ne ya sanya ya tsargu, mutane sun fara yi msa wata fassarar da ba zai iya fidda kansa ba, ji ya yi ba zai iya sake hada ido da ita ba, ya yi saurin barin gurin.

Tunda ya doso falon yake jin munsharinta, ya kutsa dakin tana nan kwance ta yi wani daidai. Ya jinjina kai, filon da ta ke kwance ya fara dauka.

Ta bude ido cikin mutsika idanu, idanun nan sun yi luhu-luhu alamar ta ci kuka. Ko a jikinsa.

“Nabila, irin tarbiyyarki kenan?”

Ta daure fuska.

“To me kuma na yi daga farkawata?”

Wani irin bakin ciki ya shaka, da sauri ya kawar da kai, ta mike tana faman cika da batsewa, bathroom din da ke manne a bedroom din ta shiga, shi kuma ya wuce bedroom dinsa shi kuma wanka ya yi. Kananan kaya ya saka wadanda suka kara fito da kyawunsa.

Tana zaune a sittingroom kamshin turaren da ya fesa ta ke faman shaka, wani irin sha’awarsa ta sake kashe ta, ta ja wani irin zaman aure za su yi da Deedat? Yanzu duk irin rayuwar da ta ke mafarkin samu daga gare shi, ya zama babu.

Wayarta ta shiga ruri, sunan mom ta ta gani ta latsa kore tare da mannawa a kunne.

“Yaya amarya kin kwana lafiya?” bata san sa’ar da ta fara kwalla ba.

“Mom yaya deedat ya sauya min, kamar bashi ba sam bashi da walwalakawai ya aure nine don kada ace bashi da aure, duk wani ango, akan same shi cikin, farin ciki da ririta matarsa, amman shi kam guduna yake yi, in takaice miki allah yasa ma ya kwana, ace ina amarya mijina baya dokin hada shimfida dani”. Ran haj Aisha ya baci, amman ta danne.

“Kiyi masa uzuri babu mamaki gajiyar biki ne, zmman mu bari yau, insha allah komai zaiyi dai dai kada ki damu kinji? Yanzu yana ina ?”

“Naji muryarsa acan darning area”

“Okey to ki tashi kije kada ki kosa kiyi nta shigewa jikinsa kinji?, dole fa sai kin sauke tsiwa da wannan fitsarar a karkashinsa kike, in kika bi ahankali zai dawo tafin hannunki sai yadda kikayi da shi, yanzu kinyi wanka?”

“A’a”

“Oh god, Nabila nanfa ba gidan iyayenki bane wannan sakarci ne, rashin son wankan naki dole ki saukeshi, kin wanke baki amman?”

“Na kuskure da ruwa”

<< Kyautar Zuciya 16

Drop a Comment

Your email address will not be published. Required fields are marked *

You cannot copy content of this page.
2
Free daily stories remaining!
×