“Ya Allah wai ke wace iri ce ? kinsan yadda deedat ke da tsafta, idan kinayin kwaskwarima agida kifita aksa ganewa, to yanzu nan makwanci zaku hada, idan ya kusance ki zai dinga jin bashi”.
“Oh mom, kinsan bana son sanyi, bana son wanka akwai wahala, inaga in nawanke hammata ba zai gane ba”
“Shikenan yanzu tashi kishirya sai ki tafi can gurinsa”.
Kamar yadda ta ambata haka tayi wato tsaka tsami ta wanke hammata, da kafafu, ta sheka uban kwalliya kai sai ka zaci wanka ta sheka, riga pitet ta saka da dan gajeran siket, mazaunanta a shafe tumbi ya yi dirum a gaba, ta feshe jiki da turare ta dauki takalmi mai tsini ta saka, tana tafe cikin karairaya.
Ya kasa hankali rabi na kan waya, rabi na kan abinci. Nurat ya tura wa sako.
‘Princess da fatan kin tashi cikin koshin lafiya”.
Ga mamakinsa sai ya ga tana online din, da alama kuma ta gani, amma babu amsa.
Kwas-kwas ya ji takun tafiyar Nabila ya ji, kallo daya ya yi mata ya dauke kai. A kujerar kusa da shi ta zauna.
‘Ashe kana nan?’
Da haushinsa taf! Zuciyarsa wani takaici ya kama shi.
‘Ina kwana?’ Ya ce mata.
Duk sai ta ji kunyarsa ta kama shi, ta ko kanne.
‘Da fatan kin tashi lafiya?’
Ta yi fari da ido, ‘Kalau”. Ta shiga bubbude flask din abinci. Kurum ya ji alamar shigowar sako. Da sauri ya bude.
‘Ina kwana Yaya Adamu? Yaushe za ka dawo?”
Ya ji wani sanyi.
‘Sai lokacin da ki ka so’. Ya rubuta cikin satar kallon Nabila, wadda ta soma cin abinci.
‘Ina so ka dawo’. Ta ce da shi.
Ya yi murmushi, ‘Zan dawo lokacin da ki ka amince da ni’.
‘Ina jin tsoron Yayata, tana matukar kaunarka’.
Ya rubuta amsa, ‘Ni bana ra’ayinta’.
‘Ni ma bana tunanin haka’.
Ya ce, ‘Kina nufin ba za ki so ni ba? Ba kya sona?”
“A’a kaunarka nake yi, don haka nake so ka zamo daya daga cikin danginmu’.
Ya sake satar kallon Nabila, ya maida kai. Ya sake rubuta mata.
‘Na yi amanna cewar kauna ita ce kadai mabudin farin cikinmu, so kawai wani abu ne da ake gina shi a matsayin wata cuta da ba ta da magani. Ya za ki ce kenan?”
“Ba ina nufin wannan kaunar ba, ina nufin kauna irin wadda dan uwa ke wa dan uwansa”.
“To amma ni kuma ke kadai nake so, ke kadai nake kauna. Ba zan iya zama babu ke ba, ke kadai nake ra’ayi. Ina tsantsar sonki, kuma a shirye nake na mutu a kanki. Wannan ita ce soyayyar da nake miki”.
Ta turo da hoton kuka.
‘Ka yi shiru, ka daina fadin hakadon Allah, ina jin nauyi. Ina zargin kaina, ina ji kamar ina cin amanar Yaya Aazeen, don Allah mu rufe wannan shaftar”.
“Okey, zan yi shiru, amma sai kin rantse min cewar ba kya sona”.
“Ai da ma ni ban san me ye ma abin da ka ke ambato ba, domin ban taba cin karo da shi ba”.
Ta yi saurin sauka daga online din, duk da haka bai fasa rubutu ba.
“Ba wannan na tambaye ki ba, na tambaye ki ne a kan ki rantse”.
Sai dai da alama sakon bai je ba, saboda kashe datar da ta yi.
Tuni Nabila ta gama da cin abinci ta kafe shi da ido, musamman yadda ta ga kamar yana cikin nishadi. Deedat abin so ne, kyakkyawar fuskarsa, maganarsa, dariyarsa. Ta sani yanzu ta yi zarra. Deedat ya zama nata har abada, za su rayu da shi. Wani dadi ya dinga ratsa ta,.
Jikinsa ne ya ba shi tana kallonshi, ya maida idanunshi a kanta, suka hada ido, ta sakar masa murmushi.
“Ya aka yi?” Ya ce da ita.
“Yaya Deedat sonka ne kawai ke sa ni nishadi. Ina matukar sonka mijina”.
Ya mike ya dauki handchief yana goge baki.
“Na gode da soyayyarki”. Ya kara gaba.
Ba ta taba burge shi, duk ji ta yi jikinta ya yi sanyi.
KANO
Da yamma ta dawo daga makaranta ta shiga gida, ta taras da Ammi da matar yaya Zaruk, ta gaida ta.
“Matar kanina sai yanzu kika dawowa daga makaranta?”. Ammi ta amsa da fadin,
“Jarrabawa ta gabata yanzu suna tsayawa lesson basa dawowa sai biyar”
“lalle mun kusa shan biki, sai dai bamusan daya daga cikin kawayenta ba balle mu tsara yadda bikin namu zai tafi,”. Ammi tayi murmushi,
“Kin ganta nan bata da kowa ita kadai take Rayuwarta sai wanda suka tursasa gun shige mata, ni kaina hakan yafimin dadi, kawaye suke nunama yara abinda basusani ba, suna taka rawar gani gun rugujewar rayuwar da iyaye suka dade gundora yara akai, kin sani duk zakin suger idan aka gaurayata da gishiri baci yake”. ita dai Nurat shigewa daki take ke kokarinyi, Ammi ta dube ta.
“In kin shirya Zaruk na bangaren baki”.
Ba ta ce komai ba ta shige ciki, koda ta watsa ruwa ta sanya kaya tare da zumbula hijab, komawa tayi ta zauna sai da Ammi ta kwalla mata kira, cikin bacin rai.
“Bakiji nace kina da bako ba?”
“Kiyi hakuri na mancene”. Sum sum ta mike hanyar da zai sadata da bangaren bakin.
Ta same shi jingine da allon kujera idanunsa a lumshe, kallo daya ta yi masa ta kawar da kai, hoton yadda ta ganshi da Aazeen ya kasa goguwa a kwakwalwarta, duk wata daraja da kimarsa ta gama zubewa a idanunta, ta yaya zata iya karbarsa a matsayin mijin da yake da kima, mijin da Ubangiji ya ce aljannarta a karkashin kafarsa take, ta sani in dai ta bari ya zamo mijinta ba za ta taba samun aljanna ba, wanda a rayuwar duk wani musulmi na gari ya shige ta, ba za ta yi masa biyayya ba, aljanna za ta yi mata wahalar shiga.
Danunta suka ciko da kalla, zaman dirshn ta yi kan carpet, a hankali ya ware idanunsa cikin dubanta, ya mike sosai.
Ras! Zuciyarsa ta buga, wani irin kyau ya ga ta yi masa, shi ma saukowa ya yi kasa.
“Ajiya ta babu sallama?”
Ta dago idanunta, kwalla ya gani kwance a ciki.
“Ya salam! Wa ya bata miki rai? Me ke damunki?”
Duk ya gama rudewa.
“Oh! No, no kada mu yi haka da ke, farin ciki ya kamata ki yi, na sani za ki ji wani iri, ki yi hakuri kin ji. Yanzu gaya min yadda ki ka yi kewata?”
Ta kasa magana, yadda ta ke jin tsanarsa in ta budi baki ba za ta fadi mai dadi ba, don haka gwara ta tsuke baki.
“Nurat, ina matukar bukatarki, yau Dad ya yi min albishir din da ya fi komai sa ni farin ciki, albishir din aurenmu kafin ki yi candy. Nurat ina sonki sosai, na dade da tabon sonki, da ma tunda aka haife ki na kwallafa rai a kanki, hakan ne ya sa na dinga bata lokacina gurin rainonki, gaba daya na dinga tarewa a gidanku, duk wani abin da za ki na kuruciya burge ni ya dinga yi. Fitsari, tumbudi, bahaya da ki ke yi a jikina ba ya sa wa na fasa daukarki, rayuwata ta ginu ne da sonki”.
Ya matso kusa da ita sosai, ya sake marairaicewa.
“Ba zan iya rayuwa babu ke ba Nurat, kada ki juya min baya, kada ki rusa min tanadina, ki ce kina sona ko sau daya ne tak!”
Ya karasa zancen cikin kafe ta da idanunsa, ya raunana murya.
“Nurat, ki ce kina sona. Ki fada in ji sanyi”.
“Kaina na ciwo, ina jin bacci. Ina son na kwanta don Allah ka yi hakuri”.
Zuciyarshi ta dugunzuma ya mike cike da bala’i.
“Na fahimta ba ki da tausayi, ba ki da imani, ba kya sona. To ni ina sonki, kuma muddin ina numfashi sai na aure ki, babu abin da zai sanya na janye, zan ci gaba da sonki ban damu da ki so ni ba, ko da ba kya sona na sani dole ne na aure ki, dole ne ki rayu a karkashina. Kada ma ki ce kina sona, tuni an riga an tsara cewar sai kin aure ni ni din da ni za ki rayu”.
Kuka ne ya kwace mata duk da haka bai saurara mata ba.
“Kar nake kallonki, sai na rusa farin cikinki’.
Ya koma ya durkusa a gabanta yana fuskantarta sosai.
“Na sani na san me ki ka taka, ba za ki taba cika burinki ba, ba za ki samu abin da ki ke so ba. Adamu ba shi ki ke so ba, wanda ki ka layance da cewar ki hada su ne da Aazeen kina gyara wasanki da yaudarar kanki, idan ba ki yi wasa ba sai na shaida ma Aazeen komai, yadda Aazeen ke sonsa ba za ta taba daga miki kafa ba”.
Ya ja tsaki, “Mai abin kunya kawai”.
A zuciye ya fice waje.
Saboda tsabar tashin hankali ji ta ke kamar za ta mace a gurin. Innalillahi wa’inna ilaihi raji’un ta dinga maimaitawa.
Soyayyar Adamu har ta yi shaharar da aka fahimci halin da ta ke ciki a kansa? Wayyo Allah duk sai ta dinga jin kunya, ya za ta yi idan yayarta ta fahimta?
Wannan kenan, sannan maganar da ya fada a karshen furucinsa, wai mai abin kunya, me yake nufi? Shi har yana da kunyar da zai fadi haka a gare ta? Ita da shi waye mai abin kunyar?
Yadda suka ga ya fito ne ya tabbatar musu da ba su wanye lafiya ba, babu wanda ya yi wa magana, gaba daya suka bi shi da kallo, kowa da abin da yake ayyanawa a ransa.
Maryam ta mike, “Hajiya za mu wuce”.
Gudu-gudu, sauri-sauri ta bar gidan.
Maryam na ficewa, Ammi ta yi saurin nufar gurin Nurat, tunda ta ga harabar sashin ta dinga jin shesshekar Nurat, a sukwane ta karasa. Tana zaune ta hada kai da gwiwa, ta kai hannu ta dago kanta, idanun nan sun yi luhu-luhu alamar ta gaji da kuka.
“Subhanallahi Nurat, lafiya? Wani abin ya yi miki?”
Ta jinjina kai.
“Kada ki boye min”.
Ta budi baki da muryarta da ta karasa dashewa.
“Ammi, kina ganin na yi dacen mijin aure? Ammi ba ku sani ba, Yaya Zaruk mugu ne, azzalumi ne, damuwarsa ce kawai damuwa, kuma ma Ammi nawa nake da ku ke neman raba ni da gidanmu? Don Allah ki yi wa Dad magana, kuma…”
“Ya isa, ke ce ki ka san abin da yake daidai ko? To muddin kina son farin cikina kada ki juya wa bukatar Dad dinki baya, kin sani ba zai taba lamunta ba, zai iya yi komai a kan haka. Ai tunda na ga ya fita na san wani abun ki ka guma masa”.
Ta koma ta sassauta murya.
“Ki yi biyayya, muddin ki ka zabi iyayenki ba za ki tabe ba, ko ma ya yake Allah zai ba ki sa’a a kansa, ba koyaushe ka ke samun abin da ka ke so ba, ballantana ke nawa ki ke da za ki iya tantance so da rashinsa? Me ki ka sani? Zaruk si ne mutum na farko da ki ka tsaya da shi a matsayin saurayi. Shi ne kuma zai zamo na karshe, don haka kada ki kuskura Dad ya ji wani abu, ba ke ba, har ni sai ya saba min. don haka ki rufa mana asiri don Allah. Tashi mu je ki wanke fuska kada ki sake ki bari kowa ya fahimci halin da ki ke ciki kin ji ko?”
Ta kada kai.
*** *** ***
“Ka kasa fahimtar abin da nake nusar da kai. Ina son ka gane ita din ba ta taba yin wani saurayi ba, tana da karancin wayewa shi ya saka tun farko na ce ka nemi Aazeen, ita ce daidai da kai”.
A fusace ya dakatar da ita.
“Kada ki kara budar baki ki gaya min na nemi auren Aazeen, na rasa tantance ni din kina kauata kuwa? Idan da a ce kina kaunata ba za ki so na zabi Aazeen a matsayin abokiyar rayuwa ba, yarinyar da ba ta da tarbiyya, fasika ita ce ki ke so ta zame mini uwar ‘ya’yana? Okey! Saboda ke ki dinga haihuwar salihan ‘ya’ya a matsayina na kanin mijinki, ni kuma na dinga haihuwar yaka-halak-yaka-haram ko?”
Ta sanyaya murya.
“ba haka ba ne”.
Ya kafe ta da rinannun idanunsa.
“To ba haka ba ne, mene ne?”
“Shi kenan ta wuce, a bar zancen, amma dai ka bi ta a hankali, kai ne da kanka za ka koya mata sonka gurin danne duk wani bacin ranka yayin da ta ke gaya maka babu dadi, don har yanzu ita din ba ta gama hada hankalinta ba, kuma ina son ka sani a matsayinta na mace mai kunya, ba za ka taba samun bayannanniyar soyayya a gurinta ba, maleji za ka yi har zuwa lokacin da aka yi bikin sai ka maida ta duk yadda ka ke so”.
Ya sauke ajiyar zuciya.
“Na fahimce ki, zan kwatanta matar Yaya, zan bi a hankali, ban san dalili ba kullum ina jin zuciyata kamar za ta fashe. Ina sonta, ina kishinta idan na tuno da wani abu kamar na yi hauka”.
“Me ke nan ka ke nufi?”
Ya furzar da huci.
“Ni na bai wa kaina sani, idan lokaci ya yi zan bayyana miki”.
“Okey to shi kenan, Allah ya jisshe mu alkhairi”.
Ta koma ta zauna tana tunani. An yi ganganci, wannan hadin bai yi daidai ba, za a cutar da Nurat, da a ce ita din ‘yar uwarta ce sai ta yi sanadiyyar lalata komai, ta yi wa Zaruk sanin da ko iyayensa ba su yi masa ba, tana da masaniyyar irin karuwan da yake mu’amala da su, tana da sanin yadda ya maida kwayoyi da barasa ruwansa. Yana yaudarar iyayensa da nuna musu shi na gari ne. iya takunsa ne ya sa ba kowa ne ya san asalin halayyarsa ba, amma Zaruk shu’umi ne na gaske, tana tausayin Nurat, za ta taya ta da addu’a, shi ne kawai zai kubutar da ita.
Al’amura sun tsananta a gare ta, komai ya cakude mata, yayin da ta ke kara jin wani irin son Deedat da son ganinsa a zuciyarta, wani irin razanannen tsoro ke ziyartar zuciyarta, ta daya gefen ma ta kan tsani kanta ga yadda zuciyarta ta kasa sakat da son wanda Yayarta ke matukar so, shin wannan wane irin abu ne? Wannan al’amari ko a tatsuniya ba ta taba cin karo da kwatankwacinsa ba.
“Nurat, Adamu na kirana”. Aazeen ta katse mata tunani da fadin haka.
Ta dora da fadin, “Ni ce zan amsa, zan koyi amsawa”.
Ta latsa kore, “Ran ruhin raina ya dade, amma fa na yi fushi, kana can abinka ka mance da ni ko kirana ba ka son yi, anya kana yina kuwa?”
“Sosai kuwa, ina sonki”.
Ta runtse ido ta bude, wani irin farin ciki ya lullube ta, ta kawar da wayar daga bakinta, ta dubi Nurat wadda ta kafe ta da ido.
“Tsaya ki ji abin da yake cewa”.
Ta mayar da wayar handsfree, muryarsa ta karade dakin.
“Ina matukar kaunarki, jibi zan dawo. Na dokanta da in sake ganin kyakkyawar fuskarki”.
Nurat ta koma ta kwanta lamo, ji ta ke yi kamar ta toshe kunnuwanta, hawaye ne ya dinga gangarowa ta gefen fuskarta.
“Ka gaya min me ka ke so, in tanadar maka?”
“Duk abin da ki ka tanadar min zan ji dadinsa, amma ina kanwarmu?”
“Ga ta nan a kusa da ni”.
“To ba ta mu gaisa”.
Tana jin haka ta yi saurin rufe ido, a hankali ta shiga dukanta, fir ta ki tashi, ta tuntsire da dariya.
“Yanzun nan fa muke hia, amma wai har ta yi bacci”.
‘Okey, ba matsala a ce ina miko gaisuwa’.
“Ba matsala za ta ji”.
Idan ta ci gaba da jin wannan yanayin za ta mutu, dukkan farin cikinta ya koma labari, komai ba dadi, shin yaushe walwalarta za ta dawo? Yaushe ne za ta koma kamar kowa?
Tana jin fitar Aazeen tana faman wake-wakenta, da alama tana cikin nishadi.