*****
“Ina son ka tambayi abokinka, shin rashin sona har ya kai ga ya kasa hada makwanci da ni? Me na yi masa haka, na ga ko ‘yan iska sukan far ma mace a yayin da sha’awa ta kama su, ana mu’amala da mace ko da ba a sonta, domin shi so daban, sha’awa daban. Dukkansu Yaya Deedat ba ya yi min kamar ma bai dauke ni a matsayin mace ba, kwana biyu kenan da tarewa ta, amma ya kasa sauke min hakkina, yana da msu rage mishi sha’awa shi ya sa bana gabansa?”
“No, kada ki sake fadar hakan Nabila, kin fi kowa sanin abokina, sanin kanki ne babu wata ‘ya mace a gabansa, ban ma taba ganin aure a irin wannan lokacin ba, ba yanzu ya tsara ma kansa aure ba, har yanzu yana cikin fushi ne”.
“Sulaiman kana son ka ce min dole a ka yi masa ke nan?”
“Eh, amma ba akan sonki ba, kin sani yana sonki amma ba yanzu ya shirya aurenki ba, amman kuma bai kamata ya yi haka ba, tunda an riga an yi sai ya rungumi al’amarin. Ki bari za mu yi maganar da shi, zan je office”.
*** *** ***
“Allah ba zai kama ni ba, ba ta da hakki kai na, domin zan sauke mata duk wani nauyinta da ya rataya a kai na, ci, sha, sutura, dukka zan yi mata bana bukatar wa’azinta”.
Sulaiman ya ja tsaki.
“Duk ba wannan ba, akwai abin da ya fi abubuwan da ka ambata, hakkinta na kwanciyar aure, hakkinta na ku hada shimfida”.
Ba su taba makamancin wannan maganar da wani ba, yana jin nauyi. Yanzu Nabila ce har ta iya budar baki ta fada wa wani sirrinta? Tana nuna wa duniya bukatarta? Ya shafa kai, shi kam bai yi dacen samun mata ba, wani irin tsanarta ya sake samun mazauni a zuciyarsa.
“Ita din ce ta sanar da kai?”
“Ba za ta yi ma karya ba, tunda ta rintse ido gurin sanar da ni, al’amarin ya ta’azzara ba za ta iya jure rike kanta ba, ba za ta iya ba! Kada ka shiga hakkinta”.
“Amman Sulaiman wannan wacce irin mata ce na aura? Na tsani matar da ke fitar da sirrin mijinta, ko ma’aiki ya hore mu da mu rike sirrinmu, ta ba ni mamaki matuka”.
“Kai ne ka ja idan ka ki ji gaba ba ka san inda maganar za ta tsaya ba, wadanda ma bai kamata su ji ba, sai sun ji wannan, ka kiyaye”.
Jinjina kai kawai ya yi.
Tunda Sulaiman ya fita maganganunsa ne ke masa yawo a kai, ya kasa tabuka komi.
Ko da ya koma gida ya tarar da ita tana ta gursheken kuka, ya tsani ya ji ana kuka abin na taba masa zuciya, duk yadda ya kai ga tsanarta haka ya danne ya zo ya zauna kusa da ita da niyyar ya danni zuciyarta.
“Wai ke me ye ne matsalarki, me ke damunki haka?”.
Ta tsagaita kukanta.
“A iya sanina duk lokacin da mutum ya yi aure yakan dauki hutun, aiki sukan bai wa juna lokaci, amman kai a washe garin kai ni ma sai da ka fita office, hakan na nufin ba ni da muhimmanci,”.
Ya sauke ajiyar zuciya,.
“Ke kam ba kya rabo da korafi, yau kin ce wannan gobe ma za ki ce wancan, ya ki ke so na yi? Ayyuka ne sun yi min yawa tun kafin aurenmu kin san wa ki ka aura, abin da na dinga jiye miki ke nan, kin sani ni kaina bani da lokacin kaina”.
“Yaya Deedat, ko cikin dare ba ka da lokacina, ko aikin naka har cikin daren ka ke yi? Ka kasa sauken nauyin komai, ka kasa yi min komai, haka za mu dinga rayuwa?”
Ya mike tsaye.
“Ban san me ki ke so na yi ba”.
Ya shige bedroom abinsa. Rufa mishi baya ta yi, ta tarar yana ta hada kaya cikin wata karamar akwatu, ta zauna kawai tana kallonsa, sai da ya gama ya zuge akwatin ta ce.
“Na ga kana hada kaya?”
“Eh tafiya ce ta kama ni, gobe zan wuce”.
Ai ko ta mike cike da bala’i.
“Tab! Wallahi ba zai yiwu ba, sai dai in mu tafi tare, ba zan amince ba”.
Darya ma ta ba shi.
“Allah ummina? To bari ki ji, babu mai hana ni wannan tafiyar”.
Sai ta nufi hanyar fita, cikin zafin nama ya janyo ta ya kulle kofar da za ta sada ta zuwa sashin umin, ya san abin da ta ke shirin yi kenan. Hakan bai sa ta fasa hankoron nufar gurin ba, ta je ta dinga bugun kofa gudun kada Ummin ta jiyo ya sanya shi nufar inda ta ke.
Ya daure fuska tamau.
“Ki fa bari”.
Ta ci gaba da bugu tamkar ba da ita yake ba. Jin ta yi biris da shi ya dauke ta cak kamar karamar yarinya, bai zame ko’ina da ita ba sai bedroom dinta, ya cilla ta a gado tana maida numfashi, gaba daya jikinta ya amsa da wani mugun sha’awarsa.
Ta lumshe ido, har yanzu kamshin jikinsa bai sake ta ba. ta mike da kyar ta sake fitowa za ta kama hanyar gurin Ummi.
A sitroom ta ganshi zaune da kwamfuta a gabansa. Yana hango ta ya sake mikawa ya kama ta da karfi ya sake nufar bedroom da ita. Kwantar da ita ya yi ba tare da ya sake ta ba, kwantar da ita ya yi ba tare da ya sake ta ba, shi ma kwanciya ya yi ta manne a jikinsa tamkar za ta shige cikinsa, ta gama sakankancewar komai zai iya faru.
Daga bangarensa bai taba jn sha’awarta ba, ya biye mata ne saboda kada ta rushe masa tafiya da zarar ta gaya wa Ummi ba za ta bari ya yi tafiyar ba, ko motsa hannunsa ya ki yi haka ne ya sa ta fidda tsammani, amma ya kamata a ce ta yi wani abu don ta motsa shi, wannan babbar dama ce a gare ta.
A hankali ta sake shige masa, yadda ya saki jiki ne ya sa ta yi zaton bacci yake yi, hakan bai sa ta fasa niyyarta ba, ta shiga yi masa tafiyar tsutsa a gadon bayansa, tana kai hanu a wasu sassa na jikinsa.
A matsayisa na da namiji mai cikakken lafiya ta so ta ci galaba a kansa, a hankali ya soma biye mata.
Ta runtse ido tana ji a can wata duniyar. Duf! Ta ji an tsaya tamkar daukewar ruwan sama, ta gama kai wa kololuwa kawai ta ji ya ja tsaki ya janye jikinsa. Filo ya dauka ya koma kasa. Wayyo! Kamar ta hadiye zuciyarta, tun tana boye kukanta har sai da muryarta ta karade dakin bakin ciki ne ya hana ta sake magana. Ta kwana da alwashi kala-kala a ranta, ga wani irin damka da mararta ke yi yi.
Ta ja tsaki da ta san ba zai yi abin da ta ke so ba, da ba ta shiga jikinsa ba, ga shi tana mugun tsoronsa ballantana ta yi masa tsiwar da ta saba, tsarinsa ba irin mutanen da za a kawo wa raini ba ne, kwarjini ne da shi na gasken-gaske, akwai shi da tsare gida, babu fuskar ma da za a kawo masa wargi.
Kasancewar akwai abin da ta kulla a ranta na rusa masa tafiya don haka ta farka da sassafe da alwashin kafin ya dawo daga masallaci ya riski Ummi a gidan, haka ne kadai zai sa ta rusa tafiyar tasa.
Da karfinta ta mike cike da murmushin keta yadda ya bata mata ita ma sai ta rama, muddin tana raye sai ta rusa tafiyar idan ba ta yi haka ba, ba ta cancanci a kira ta Nabila ba.
Ta nufi dakinsa, ta murda handle din kofar, ta ji alamar a kulle ta ke gam! Kuma key aka saka. Dam! Gabanta ya buga, takarda ta hango a soke a gefen kofar. Ta dauka ta ware.
‘Na san lokacin da za ki farka na riga na yi nisa inda na nufa, duk kudin da za ki bukata za ki samu a dirowar dakink. Ba zan dauki lokaci ba zan dawo. Na gode.
Ahmad Deedat.
Ta saki takardar hade da saka wani ihun kuka, a zafafe ta nufi sashin Ummi.
Tana zaune, jarida ce a hannunta tana dubawa. Babu sallama kawai ta ganta a falon da alamun ta ci kuka ta koshi.
Ta cire glass din fuskarta.
“To me ye kuma na tada hankali bayan babu yadda bai yi da ke ki bi shi ba ki ka ki?”
Wani takaici ya sa wani kuka mai karfi ya zo mata.
‘Ummi haka ya ce da ke? Wallahi karya yake y, ko sau daya bai yi min tayin tafiyar ba, babu yadda ban yi a kan mu tafi tare ba ya ki. Wallahi karya ne”.
Ran Ummi ya baci, yaushe Ahmad ya koy karya? Shin me ke damunsa ne? Ta shiga laluben layinsa, ga mamakinsu sai suka ji waya na kara a dakin a can kan gefen ma’ajiyar talabijin suka hangi duka wayoyinsa.
Nabila ta sake rushewa da kuka.
“Wallahi shiri ne, yana sani, rainin hankali ne”.
Ta koma ta yi zaman dirshan tana ci gaba da kuka.
“Ummi me ya sa aka yi auren nan, me ya sa ba ki fada ma su Mom gaskiya ba? Ba ki shaida musu cewar ba ya sona, me ya sa ki ka boye musu?”
“Ke me ki ke cewa hakan? Saboda kawai bai tafi da ke ba ki ke furta duk wadannan maganganun?”
“No ba saboda haka kawai ba ne, ya aure ni ne kawai saboda kada a ce ba shi da aure, amma babu abin da ya taba shiga tsakaninu, ko rabuwa muka yi bai taba dora min idda ba. ummi ki taimake ni, ki raba ni da wannan igyoyin, Allah ya gani ina matukar son Yaya Deedat amma ba zan aure shi kawai don ya dinga kallona ba, ban taba jin inda aka yi aure haka ba, ba zan iya ba, ki taimake ni”.
Ummi ta tattausa murya cike da jin nauyin maganganun Nabila.
“Ki yi hakuri Nabila, komai zai yi daidai, na fi son ki zama mai juriya kin ji? Insha Allahu za ki yi farin ciki da wannan auren, na yi miki alkawarin haka. Ki share hawayenki kada ki bari kowa ya fahimci halin da ki ke ciki, ko da Mom ce, kin ji? Ki bar komai a hannuna za mu gauraya da shi”.
Ta dinga lallashinta, karshe a gidan ta wuni.
KANO
Tunda ta ji labarin zuwansa ta shiga kokarin koyon karfafa zuciyarta yadda za ta danne sonsa, yadda za ta yi yaki da zuciyarta gurin goge zargn da yake mata, dole ne ta koyi sakewa da shi, za ta sauya taku, za ta tafiyar da shi kamar saurayin yayarta. Dole ta sake da shi su san yadda za ta yi badda bami.
Ladidi ce ta kwankwaso kofa, ta ba ta izinin shigowa.
“Wai ki zo za ku gaisa da Adam in ji Yaya Aazeen”. Ladidi ta fada.
“Okey, ki ce ga ni nan”.
Ta mike ta zari hijab ta fice daga dakin.
Daga bangaren Aazeen yadda ta ke jin Deedat za ta iya yin komai a kansa. Ta amince cewar za ta iya yin aure wannan karon, yau ta sake tabbatar da ta samu mijin aure, ba ta yi zaben tumun dare ba, hankalinta ya kwanta da shi, muddin ba zai bari su mallaki jikin juna ba, ai ko ba za ta bari ta yi asarar wannan ingarman ba, ga shi dai ya gama cika namiji sai dai ba mai son wasanni ba ne, duk shu’umancinta ta saurara ba ta iya dosarta da nufin wani abu yana yi mata kwarjinin da babu mahalukin da ya taba yi mata. Namijin gaske ne, wanda ba ya son a kawo masa wargi. Kallonta kawai idan ya yi ta kan shiga taitaiyinta, tana son haka, shi ya saka ta ke son ya zamo nata. Tana da tsananin kishi shi ya sa ta yadda cewar shi ne kadai ya dace da ita.
“Assalamu alaikum”. Nurat ta kutso kai da fuska a sake.
“Yaya Adamu yau a gari? Yaya Aazeen kuma ki ka kula shi? Inda ni ce ke zan ta fushi ko kallonsa ba zan ba, kwanansa nawa rabonsa da ke?”
Kafe ta ya yi da ido yana kokarin karantar zuciyarta, yana mamakin wai da ma ashe tana magana sosai haka?
“Kanwata haka za ki ce? Kada fa ki tunzura min ita”.
Ya fada yana murmushi cikin wani irin shaukin farin cikin ganinta yana ji kamar ya jawo ta jikinsa ya rungume.
“Kin sani yadda nake son Adam ba zan iya daukar wani hukunci a kansa ba, amma ai ya tuba, ba zai sake tafiya babu sallama ba, ko nawan?”
Ta fada tana dubansa.
“Ki kyale wannan kanwar tawa, ‘yar hadin fada ce daga zuwa babu gaisuwa kin wani hau mita, wai yaushe ma bakinki ya bude haka ne?”
Ta dan saci kallonsa, idanunsu suka gauraya, da sauri ta kawar da kai, ta ji gwiwoyinta sun yi sanyi, ta koma ta ce, “Ina yini, sannu da hanya, ina tsaraba ta?”
Aazeen ta dungure mata kai.
“Ka ji ta kamar gaske, idan ka ba ta ma ba karba za ta yi ba, muguwar matsoraciya ce, ni da Amminta kadai ta amince, ko ni da Dad sai a hankali”.
Ya yi murmushi, ya ce, “Sai kuma ni”.
“To tunda kun gaisa sai ki ba mu guri ko?”
“Ai ni ma daman ba zama na zo yi ba”. Ta fada tana kokarin barin gurin.
Karfe biyu dai dai na dare, dare sosai ya tsala ko ina yayi tsit ba ka jin motsin kowa, sai, Aazeen wadda ke zaune a gindin akwatun talabijin, tan fitinannan kallon da ya zame mata a’ada ta dole gefe tana zukar shyin nascafe, daga bangaren Nuara, yau ne karo na farko da bacci ya kaurace ma ta, a dai dai wannan lokacin, tarasa meke damunta kwatakwata bacci ya kaurace ma idanunta, kwance kawai take a gadonta sai faman juye juye take, ji take kamar kirjinta zai fashe, duk wani farin ciki ya dauke mata, in banda zugi da radadi babu abinda zuciyarta ke yi, mikewa tayi daga kwancen ta tankwashe kafafunta, kanta ne yakoma yan ani irin sarawa, da kyar idnunta ke budewa haka kawai ta ke jin tsanar Aazeen a zuciyarta komai ya kwance mata, tuhumar kanta take ko meye ita ta ja ma kanta komai, wani irin abu take ji a zucyarta game da Adamu, ta sani wannan shine son da ake magana akai, ta dade tana kallon, so kamar wani abu ne da mutum ke dorawa kansa ashe ba haka abun yake ba, ta fahimci so a’amarine wanda Allah ya halicce shi a zuciyoyin bayinsa, ita kam ta tsani wannan soyayyar, kullum tana kokarin kaucewa abinda ta ke ji, game da shi tana neman tsari babu dare ba rana, amman babu sassauci, tana jin tsoro tana jin tsoron abubuwa da yawa yaya za ta yi idan aka gane halin da zuciyarta ta ke ciki, wayyo! Allah, ina jin kunya, ina jin nauyi yaya zanyi? hand set dinta ta hango yana bada hasake, ras gabanta ya shiga dukan uku, uku.
waye zai kirata da talatainin darennan, da sauri ta mika hannu da niyyar ta kashe, lambar Deedat ta gani wanda shine lambar da ta taba ajiya a kwakwalwarta, zuciyarta t dinga azalzalarta da ta amsa, mikewa tayi kamar mara gaskiya ta dan leka windo, ba ta ji motsin kowa ba, ta koma ta zauna latsa kore ta kafa wayar a kunne.
“Me ya hana ki bacci?”. Muryarsa ta ratsa kunnenta, ba ta yi magan ba, ya sa ke cewa.
“Tunani na ko?”
A fusace ta ce “Wane dalilin zan yi tunanin ka?”
“A dlilin son da kike min,”
“Haram, wallahi haram ban taba son ka ba, mai yasa zan soka? Kai ne fa wanda yayata ta ke matukar so”.
Yayi dariya.
“Na sani, amman kuma sai ga shi ni da ke muna matukar son junanmu”.
“Kana yaudarar kan ka ne ba ka fassara dai dai ba…”